IMSAL

Motive

by @fatoumspassion

***
It's fatoumspassion IMSAL 
Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM, INTENSE LOVE, EHSAAS and SCARRED.

Chapter 14

Seda aka zuge gate ta dena hango shi baki ɗaya sannan ta juya ta shige ciki da ledojin niƙi-niƙi a hannunta tana mamakin jinsu da nauyi da tayi.

A main parlour ta samu Natasha harta cire uniform ɗinta ta sauya zuwa kayan gida, tana danna waya, sallama tayi ta ɗago tana amsawa tana binta da kallo basarwa tayi ta ƙarasa zata wuce saman dining ta ajje kayan, karaf idon Natasha ya sauka akan ledojin hannunta ɗan miƙewa tai tana gyaran murya
“Ehem ehnnn…”
ta faɗa tana shan gaban Imsal, tana kallon ledojin tace
“Wannan kuma fa?”
Imsal ƙoƙarin zagayeta tayi don ta ajje,
taje tai sallah tasan ta biye mata zata sata ɓata lokaci,
Ganin haka yasa taɗan riƙota cikin rainin wasa take faɗin 
" Wai ma ina kuka je?
 daga ina kike yah Imsal tun ɗazun fa kin rigani ta howa"
Ganin ta ajje kayan bata kulata ba yasa tace 
"Kodai date kukai"
tana zaro ido irin she can't believe it,
Imsal girgiza kai tai tana mata kallon takaicinnan tace 
"ni matsamin in wuce kinaji anata sallah,"
tace 
"ya Imsal aiba inda zan bari kije sekin faɗa min inda kukaje in details dame dame kukayi,"
Imsal ta wani galla mata hararar wasa tana faɗin
“Sannu Mummy, amman dai kinsan naje islamiyya ko…”
Da sauri ta gyaɗa kai tana faɗin
“Eh na sani… amma wannan fa?”
ta nuna ledojin.
“Ya Mu’allim shopping yayi miki ne shine don yaudara babu gayyata?”
Ta ƙarasa tana fara budewa, Imsal riƙe hannunta tai tana
“Nats ki bari, se an nunama Hajiya”
Natasha jan ledojin  tayi ɗayan gefen da sauri tana dariya tace
“abeg, aikinsan ba abinda zatace tunda shine.”
“Let me see what my so called in-law is doing…”
ta faɗa tana buɗe ledar farko,
Wani Ice Cream Box ne me bala'in kyau aciki
"Wow"
Natasha tafada ganin Italian gelato ne aciki da Pistachio mai laushi, se tarkacen su Belgian chocolate mai kauri da Strawberry cream da wani vanilla mai ɗauke da gold flakes,
Natasha ɗaga kai tai tana kallon Imsal tana washe baki tace
“Yah Imsal… wannan dai nawane koh shi likita ne ai yafi kowa sanin cewa bakyashan kayan sanyi?”
Imsal hararar ta tai tana faɗin 
“Ki rufe shi…”
“in rufe kuma? Lallai wasa ma kike”
Spoon data gani a gefe ta ɗauka ta ɗan ɗiba kaɗan, ta saka abaki, lumshe ido tayi tana faɗin 
“Ya Allah…”
ta buɗe ido da sauri,
tana faɗin 
"Yah Imsal amman da kinsan irin wannan za'a siyo aida kin ɗan kyaramin na biki"
Dariya Imsal tayi tana faɗin 
"kanki akeji ni dai nayi gaba,"
wucewa sama tai don tai Sallah tana haurawa kuwa Natasha ta shiga buɗe ɗayar bag ɗin.
kamshin abincin mai daɗi ne ya daki hancinta, ganin food pack yasa taciro tashiga bubbuɗe wa, Grilled chicken ce mai creamy sauce, se Pasta mai cheese mai mugun laushi da fresh salad, Natasha murmushi ta shigayi tai saurin rufewa.

Ice cream ɗin ta ɗauka ta saka a fridge ta nufi kitchen ta ɗakko plate ta shiga dishing ɗin wanda zataci ta barma Imsal iya wanda take tinanin zataci taja gefe ta soma ci tana waƙa abinta seda ta kusa cinyewa Imsal ta sakko tana sanye cikin riga da skirt English wears da hularta ta rufe kanta sinkif.
ta ƙaraso saman dining ɗin tashiga buɗe food warmers ɗin abincin dare d Mama Zuhra ta jera awurin, rufewa tai takalli Natasha tana faɗin 
"Sannu da aiki,"
Murmushi tai mata tana faɗin 
"dan Allah a ina ya siya muku kayayyakin nan ke kinji daɗi, taste ɗin gaba ɗaya ba  irin ordinary taste bane yah Imsal, na duba sunan wurin jikin ledar amman bansan shiba duk yawo na"
Murmushi Imsal tayi 
Kafin tace mata 
"Nima bansani ba, kiduba babu address ne"
Natasha tace 
"kamarya ba dake kukaje kuka siyo ba, ni fa kinsan bin Google map ɗinnan cakar dani yake"
Zama tayi tana janyo ɗaya ledar ta ukun wacca Natasha bata buɗe ba tana faɗin "dani mukaje amman bansan gurinba da nisa dai, kuma ni ban bishi ciki ba,"
Ta ƙarasa tana buɗe ledar Glass jar ne mai ribbon, mai ɗauke da layered strawberry mousse da cream se gold flakes.

Natasha miƙewa tsaye tai tana leƙawa ganin abinda ke ciki yasa ta zauna tana murmushi tace
"Hmmm wasa wasa fa dai ba lefi ya iya love, kuma baida rowa"
Girgiza kai kawai Imsal tayi kawai,
Da sauri Natasha tace 
"bafa dan ina sonshi nake son kayansa ba kawai dai kinsan bana ganin abin taɓawa na kyale"
 ta ƙarasa tana jawo jar ɗin gaban imsal ta shiga warware ribbon ɗin,
Imsal tace 
"toh ina ice cream ɗin nishi zansha ki ƙarasa abincin ba ci zanyi ba,"
Natasha girgiza kai ta farayi tana faɗin "ba zaki sha ice cream ki lafkemin ba,
kinsan sarai yadda jikin ki yake reacting ma sanyi"
 banza Imsal tai mata ta nufi fridge tana buɗe wa aiko ta ciro ta fito ta zauna gefenta tashiga buɗewa.
Natasha ta ɗan ɗago tana faɗin
"Yah Imsal...."
murmushi tai mata tana faɗin 
"nothing will happen wai yaushe rabon da kiga ya tashi,
 ai tunda Yah Mu'allim ya ɗaura ni akan daily medication shikenan,
i can do alot of things da banayi abaya kuma shima aida yasan ze cutar dani baze siya ba"
tafaɗa tana kai wanda ta ɗibo bakin ta,
Natasha tace 
"His turning you into something else ba kunya kike cemin wai da yasan ze cutar dake baze siyaba, Yah Imsal abi me saurayi"
Murmushi Imsal tai tana rufe fuska don se yanzun abinda tafaɗa yabata kunya,
Natasha itama ɗaukar nata spoon din tayi ta jefa suna sha tare tace 
"nidai idan kika lafke baruwana saurayin ki ne sanadi karma kice banfaɗa miki ba,"
Dariya Imsal tai tana faɗin 
"kanki akeji,"
Hajiya ce ta fito tana tambayar su me suke ci, nanfa Natasha take bata labarin ai Abdullah ne ya siyama Imsal kayan kwaɗayi.
Hajiya ta ɗanyi jim tace
"Imsal ba dai ce mai kikai zakici ba koh,"
 da sauri ta girgiza kai Natasha tace 
"haba hajiya se kace bakisan Imsal ba tayaya zata ce ya bata abu,"
ƙarasowa tai ta zauna tana faɗin 
"na sani amman ki kula sannan banason ki ringa yawan binsa amotar nan kinji koh,
yanzun mutane babu Allah aransu nasan Abdullahi mutumin kirkine amman kada yan unguwa afara muku muguwar fassara" jinjina kai Imsal tayi cikin fahimta, Natasha ta taɓe baki tana tambayarta da zataci girgiza kai tayi tace 
"rabani da kayan zaƙinnan naku ni zubamin abinci"
miƙewa tai tai serving ɗinta suka shiga cin abinci anayi ana taɓa hira.

*Boston Logan international airport*

 Ahankali Mummy ke tafiya tana taku ɗaiɗai da high heels ɗinta da ƙaramar handbag a hannunta na dama se hannunta na hagu data ke jan wata yar mitsitsiyar trolley.
Harta ƙarasa fitowa daga airport ɗin,
a jikin wata taxi taga ya jingina idonsa akan ta ya harɗe hannayensa a kirji yana kallonta cikin shigar sanyi yana murmushin sa mai laushi daya narkar da zuciyarta, 
itama murmushin ta sakar masa tunkan ta ƙaraso ya ƙarasa gareta yana cire jacket ɗinsa ya ɗaura mata asaman doguwar rigar abayar da take jikin ta don yasan tabbas zataji sanyi batai expecting samun garin ciki sanyi haka ba shiyasa tayo wannan shigar.
murmushi tayi tace mishi 
"thank you"
ya ɗan rungumota yana faɗin 
"Your Welcome Barrister"
Jan dogon hancinsa da taga yayi jajir alamar sanyin ya shige shi sosai tai, tace
"Doctor yasha sanyi kenan,"
jinjina mata kai yayi bayan ya buɗe mata ƙofar taxi ɗin ya ɗan leƙa yace
"Inama kan sanshi,
 sedai nace bazan sake wata shekarar anan ba,"
 dariyar tsokana ta shiga yi masa ya zagayo yana zama gefen ta gidan baya,
taxi driver ɗin yaja ta shiga kallon garin, tana jin daɗin weather ɗin don ita tafi sonta akan ta inda ta fito.

Ahankali taji yace 
"ya yarana,"
juyowa tai
tana watsa mishi hararar wasa tace 
"au yaranka ma kaɗai kasani baka ce ni ya nake ba,"
murmushi yayi ya kama hannunta yasa cikin nasa yace 
"your a strong woman I know your fine, your always fine, tawan"
jinjina kai tayi taja numfashi don so take yi cikin tafiyar nan ta samu ta shawo kansa ya amince da auren Imsal da Farouq shine ma dalilin zuwan nata dan tasan idan tace seya koma Nigeria zata mai maganar mahaifiyarsa zata iya zama katanga a tsakanin su.

Kwantowa tai zata ɗaura kanta saman ƙirjinsa ahankali yace mata 
"the driver is watching us fa, Barrister get up"
bata saurare shiba ta wani maƙalƙale mishi don so take ta faranta mai ta yadda itama inta shigo da tata buƙatar ze mata cikin gaggawa tasan yadda Dr Umar ya keson ta ringa clinging to him irin haka tana nuna mai soyayya, 
"nidai nagaji
barci zanyi keep quiet"
tafaɗa tana ɗaura mishi yatsa saman lips tanajin tashin sautin murmushinsa.
Itama murmushin take aranta tanajin tarkonta ya fara ɗanuwa.

Ahaka tai luf ajikinsa har suka ƙarasa apartment ɗin da yake zaune, yawanci bata cika sauka gurin sa ba,
koda tazo Boston amman yau saboda tanada target batace akaita gidan wantaba nan ɗin kawai ta biyo shi directly zuwa apartment ɗinsa dake Cambridge.

koda aka saukesu shi ya ɗakko mata jakarta da trolley ɗinta zuwa one parlour, one bedroom apartment ɗin nasa,
Bedroom din ta shiga bayan ta rage kayan jikinta da ruwan ɗumi tai wanka ta fito.

sanda ta fito gani tai harya shiryo mata abincin daya mata order a tray ya ƙaraso yana riƙota ya zaunar da ita cikeda soyayya yake ce mata 
"nasan kinji yunwa dayawa, I ordered your favourite tawan"
murmushi tai tana ƙarajin ƙaunarsa aranta don mutane da dama sun gaza gane dalilinta na aurensa ita kaɗai tasan kalar sa ta ainahi,
ta nuna kulawa da soyayya da sauƙin hali wanda yarsa Imsal ta gada daga gurinsa banbanci sa ɗayane da imsal shi idan yayi fushi baya saurin sakkowa ita kuma kana bata haƙuri ta hakura kenan har abada.

 Zama yayi gefen ta tana cin abincin yana kallon ta yana gyara mata gashinta ɗan dogo madaidaici daya fara zubowa afuskarta,
dark brown skin ɗinta na kyalli hutu da sheƙi yadda kasan bata haifi Rayyan, Imsal da Natasha ba don yadda take kula da kanta.
Ɗan kallonsa tai kafin tace 
"yaran ka suna nan lpy fa amman rabona da ganinsu tun last month da ɗanka ya dawo ya sakamin yarinya agaba naje na raba faɗan,"
ɗan murmushi yayi kafin yace 
"hutunsa ma ya ƙare bansan dalilin ƙin dawowarsa ba,"
Mummy ɗan kallonsa tai tana faɗin
"Really"
saboda ita da taimai maganar komawa cemata yayi hutunsa be ƙareba.
Jinjina kai Daddy yayi yace 
"inaga fa baze yadda ya cigaba da zama anan ba kamar ya fison Nigeria da sauri Mummy ta juyo zata fara faɗa se kuma ta tina motive ɗinta taɗan ja numfashi,
shi kansa Daddy yayi mamaki ya zata zatai faɗa kan duk kuɗin data kashe ze tashi abanza amman batace komai ba, yace "Barrister kinyi shiru,"
Tace
"me zance doctor,
ai Idan hakan yafi so mu ƙyaleshi kawai, kasan taurin kansa,"
murmushi Daddy yayi don yaji daɗin maganarta yace 
"hakane A'isha naji daɗi dakika fahimta,"
Murmushi tai tace 
"naga wani lokacin dole se ina ɗan ɗaga musu ƙafa yaran sun fara girma kar mu ringa fito na fito dasu, kaga ba daraja" da sauri ya jinjina mata kai alamar ya fahimta,
Wayarta ta ciro tana cemai 
"bari kaga hoton da naima yarinyar ka bata ma san na mata ba, ban turama ba saboda i want it to be surprise, nasan kaf cikinsu itace batason maka hoto ta turo maka, look"
 tashiga nuna masa video ɗin Imsal datai mata aɗakinta ne tana kwance suna magana da Natasha tana murmushi, 
karɓa yayi yana kallonta yana murmushi yace 
"naga kamar ta ƙara girma"
jinjina kai tayi ahankali tace 
"she's growing fast,
 Manema nata zuwa,"
ɗan murmushi Daddy yayi kafin yace 
"har nawa Imsal ɗin take?"
Murmushi Mummy tai tana wayancewa tace 
"nima haka nace fa kawai yarinya anbi atakura mata,
Amman kasan ba laifinsu bane ba fa they can't resist gene ɗinka dake jikinta"
ta faɗa tana jan hancinsa irin na Imsal saksak se alokacin yayi murmushi tace Daddy
"yanmata nawane suke sonka sanda kana ɗan saurayi,
K still remember yanzun hakama akwai wata cardiologist da take sonka a MGH ai Aunty Nadra ta bani labari faɗa makane kawai banyi ba,"
Murmushi yayi yana mikewa yace 
"don't mind her"
ya buɗe trolley din Mummy yana ciro mata kaya masu ɗan nauyi da zatasa ba tareda taji sanyi ba tace 
"I have to mind ooo,
 kar aimin kwacen miji ina zaune,"
Ciro kayanta yayi be dai cemata komai ba ya ƙaraso ta cigaba da cin abincinta seda ta kammala ta ɗan kalleshi tana faɗin "kamin banza ma ko Doctor, kodai kana sonta ba,"
Murmushi yayi yana riƙo hannunta cikin nasa yace 
"kinsan ba gurbin wata arayuwata bayan ke, kece uwar yarana kuma duniyata baki ɗaya, so don't stress yourself over things like that,"
murmushi tai tana faɗin 
"doctor na barrister,"
shima murmushin yayi yana cewa 
"Barrister ta doctor,"

Seda Mummy tayi sati ɗaya cif cif a Boston tare da Daddy tana lalatashi da soyayya iri iri don ita macece yar duniya wacca idan ta saka target ɗinta akan mutum da wiya kaga be kamashi ba shiyasa ta kasance ɗaya daga cikin lawyers ɗinsa da ake jidasu a Nigeria.
kwata kwata bata sakewa Daddy maganar anason Imsal ba,
rayuwa kawai sukeyi kamar wasu turawa don har office rakashi takeyi,
kashe wayar ta tayi ma don batason wani abu yayi distracting ɗinta daga mission dinta ya zamana koda yaran zatai waya seta wayarsa,
daga karshe dai da kyar ta lallaɓashi ya ɗau leave na sati biyu bayan da Natasha tafaɗa mata date ɗin da zasu gama jarrabawar SSCE baki ɗaya, don si kasance tare dasu lokacin graduation ɗin.

A washegarin da zasu koma Nigeria tana zaune tana shirya musu kaya, suna hira ta jefo mishi maganar Farouq, tace 
"Doctor"
yace 
"na'am tawan tace 
"waiko katina Hajiya Farida,"
ɗan jim yayi kafin yace 
"kamar naso na santa abakinki koh,"
 jinjina kai tayi tana faɗin
" matar Ja'afar Babagana fa,"
Murmushi Daddy yayi yana faɗin 
"Mutumin kirki, i still remember sanda yana senator ta hanyar scholarship ɗin dayake samowa yan Arewa fa nasamu damar yin karatu aƙasarnan ashe matarsa ce"
 jinjina mishi kai tayi tana faɗin 
"waifa itace take taimin nacin step son ɗin ta ya taɓa ganin Imsal a gurina yanaso kuma fa da aure,
shine nace mata ni sam Imsal yarinyace bama ta isa aure ba, babanta nada burin tai karatu mai zurfi bazan aurar da itaba se tayi degree ɗinta nima kamar yadda akaimin koh ya kace Doctor?"
ɗan jinjina kai yayi kafin yace 
"it depends Aisha,"
Tace 
"shine fa yaron yake ta binbini duk inda naje muka haɗu seya gaisheni sometimes ya kan aikomin da su ɗan gifts na bata, "
Tashi zaune taga yayi murmushi tai ganin tension a body dinsa tai saurin sauya magana tana faɗin 
"his into fintech, shine fa duk wani gadget da yasan ze temaka wa yara yan makaranta gurin karatu yake kawowa abata wai shidai ze jira so samu ma ya samu consent ɗinka don asan da zamansa yaron nada tarbiyya, bayason ya fara samun yarinyar directly,"
 jinjina kai Daddy yayi ya koma ya kwanta, tace 
"kuma ni bama bata nakeyi ba nasan zaka iyayin faɗa doctor shiyasa, gashi ma har karatun yazo ƙarshe"
Yace 
"aida kinbata tunda abin karatu ne and beside duk namijin da yakeson mace har ya biyo ta hanyar ɗaya daga cikin iyayenta is worth a girmamashi don shima ya girmama yarinyar da gaske yake,"
Wani irin daɗi Mummy ta keji jin haƙarta ta cimma ruwa ta juyo tana kallonsa tace
"Doctor ni nafiso Imsal tai karatu mai zurfi," girgiza kai yayi yana cewa 
"nima haka amman kinsan zamanin ya canza A'isha musamman Imsal she get too much attention from people saboda yadda take,
muma idan tayi auren kamar hankalinmu zefi kwanciya and karatun data ɗakko inaga is not that hard zata iya haɗawa biyu fatana dai Allah ya zaɓa mata miji nagari mutumin kirki wanda zeji ƙanta,
 ya tausaya mata kina gani duk cikin yaranmu ba wanda yakaita haƙuri da juriya kodan lalurarta zanso ta auri yaron kirki,"
Mummy tace 
"Allah ko Doctor"
 Gyaɗa mata kai yayi, kafin yace 
"indai kin yaba da hankalinsa ki haɗasu kawai Barrister, I trust you,"
yafaɗa yana miƙewa tsaye da sauri tamiƙe cikin disbelief ɗinnan tace 
"Doctor na haɗasu fa kace"
 yace
"yes she's eighteen, university zata shiga, let's give it a try idan bata sonshi shikenan,"
Bata nuna jindaɗi sosai ba tace 
"toh zan faɗama Farida seta sanar dashi, nasan kam yau Farouq akwai kwana murna,"
 daddy murmushi yayi yana fadin 
"Ashe sunana ne ma dashi"
tace 
"yes sunanka ne Umar Farouq shima yake, kuma har sanyin halin ku ma irin ɗaya,"
Da wasa yace 
"anya kuwa akwai Farouq me sanyin hali A'isha"
Karasowa tai tana tayashi zira agogonsa tana kallonshi cikin ido tace
"Gwarzona mana yana da sanyin hali kuma baya fushi se ankaishi maƙura"
Murmushi yayi yana haɗa goshinsa da nata yace
"A'isha tawa, muyi faɗa mu shirya"
Murmushi tai tana farfara mishi ido,
Jitai yace mata
"amman dai kinyi bincike koh,
 Barrister nasan ki aharkar bincike ba kida wasa,"

Hararar soyayya tamai dukda yadda kirjinta ke dukan tara tara tace
"Ko kai nasaka agaba ai bazaka shaba wannan field ɗina ne, na duba sama da ƙasa baida wani issue shiyasa ma naji hankalina ya kwanta dashi,"
Murmushi yayi yace
"nima zan ɗanyi looking into it meye ma kikace sunansa?"
Wani ras taji ƙirjinta ya bayar kafin tace "uhmmm...mekace?
 ɗan juyowa yayi yana faɗin 
"his full name"
 tace 
"Umar Farouq Ja'afar Babagana,"
Jinjina kai Daddy yayi kafin yace 
"I'll see you later zanje na ƙarasa wani aiki a office,"
"Allah ya kiyaye hanya"
tace masa tana rakashi har bakin ƙofa seda uber ɗinsa yazo sannan ta koma ciki ta zabga tagumi aranta tana tunanin yanzun idan Daddy yayi bincike yagane Farouq sam bashida tarbiyyar datake faɗa fa, idan yagane cewar kwaɗayin muƙamine yasata takeson haɗa auren fa, tasan Daddy dama baze taɓa aurarda ɗaya daga cikin ƴaƴansa batare da bincike ba, amman bata ɗauka ɗan babban gida kamar Babagana's duk kyakkyawan reputation ɗinsu aƙasar suma se an bincike su ba, da sauri ta jawo handbag ɗinta ta kunna wayarta don yakamata tasan abinyi duk wata hanya da Daddy zebi yasan asalin halinsa da tarbiyyar sa seta toshe shi kansa Farouq ɗin seta gyara masa abubuwa da dama ayanayin appearance ɗinsa kafin tai presenting ɗinsa gaban mijin nata.

Number ɗinsa ta ƙasar ta shiga kira bugu biyu secretary ɗinsa ta ɗaga tace mata ya shiga meeting,
Sanar mata ita wacece tai tana cemata inya fito ta saka ya kira ta, da toh kawai ta amsa mata ta katse wayar ta shiga calculation.
Ta kai rabin awa agurin tana tinani kafin ta saki murmushi don ta samu solution,
Imsal itace weapon ɗinta itace solution ɗinta ma duk wani obstacle,
zata fara haɗa Farouq da Imsal tasan yadda tayi ta koya ma Imsal son Farouq kafin ya samu haɗuwa da Daddy,
koda Daddy yaji be maiba tasan idan har Imsal na sonshi babu yadda Daddy zeyi seya aura mata shi.

Murmushi Mummy ta sakeyi a hankali tana kallon wayarta.
Ba zata taɓa bari komai ya lalace ba, after working hard irin haka, da sauri ta ɗauki wayar ta sake danna number sa,
Ba a jima ba aka ɗaga still secretary ɗin nasa ce tace
“Ma’am, he just stepped out of the meeting yashiga office”
Mummy tace
“Give him the phone.”
In few seconds taji muryarsa thats very deep and masculine don bata katse ba yana faɗin
“Barrister Aisha…”
tace
“Mr Farouq.”
Shiru yayi yana sauraronta batai mamakin rashin gaisheta da beba daman be iyaba kuma bayi yake ba tace masa 
“We need to talk.”
Daga ɗaya ɓangaren karkatar da kansa yayi,
 yayi ma secretary ɗinsa alamar ta bashi guri tana fita yace
“I’m listening.”
ɗan jan numfashi Mummy tai kafin tace masa
“Doctor ya amince.”
Shiru yayi because he didn't expect it,yace
“…are you serious Mummy?”
Murmushi tayi kaɗan wato they are back to Mummy again,
tace
“Ya amince ku haɗu da ita.”
Kamar be yarda ba saboda ciki dabai ya bincika kowa cikin family ɗin Imsal beyi expecting babanta ya yarda haka ba, amman yasan koda ya yarda kobe yarda ba Imsal ta sace koda aure koba aure tunda yaji yana sonta babu namijin daya isa ya mallaketa idan ba shi ba,
Yace
“For real…”
Jinjina kai tayi kamar yana ganinta tace
“Amman fa kamar akwai matsala..”
Jim yayi kafin yace
“I’m listening.”
Gyara zama tayi tana faɗin 
“Doctor zai yi bincike akanka.”
Murmushi yayi kafin yace
“I expected that.”
Da sauri tace mai
“No… you don’t understand.”
taɗan yi ƙasa da murya tana faɗin 
“Ba irin binciken nan bane wanda zaka iya fitowa clean,
kasan na sanka nasan waye kai everything da kakeyi a Abuja da outside nasani ni idan na fahimce ka shi kam ba lallai, don Doctor Umar baya wasa da abin da ya shafi ‘ya’yansa, musamman Imsal yana sonta sosai"
Farouq cikeda iskanci yace
"Nima haka, I love her more than him"
Kallon wayar tai tana hararar ta kamar yana gabanta shidai baze taɓa zama serious ba,
Tace 
"Farouq idan ya gane baze baka aurenta ba ina mai shawartar ka, remove everything da zesa yagane, be clean, stop it or go low-key I know you can do that, stop doing it publicly, Understand?”
Murmushi taji yayi kafin yace 
"I'm not doing anything illegal Mummy, is just fun, but don't worry I get you, I'll try to control it for Lulu"
Jinjina kai Mummy tayi kafin tace
“Ba zan sake mishi karya ba kanka,Na riga na yi enough.”
Tana jin voice ɗinsa sounding very childish this time around yace
“So you’re protecting me now Mummy?”
Cikeda attitude 
Taɓe baki tayi tace
“I'm protecting my daughter.”
A gadarance yace mata
“Nafiki sonta, so calm down, there’s nothing to protect her from I'll take care of her.”
Kallon wayar tai tai kwafa kawai kafin tace mai 
“Good.”
Yace 
"Mummy I'll be her husband no matter what,
stop stressing yourself, she's mine already"
Jin abinda yace yasa tace
"Farouq"
Yace 
"Yes Mummy"
Tace 
"Yadda kakemin magana has to change, Imsal will not be happy taji kana min magana haka"
ɗan jim yayi yana dawowa very serious yace 
Mata 
"Okay Mummy 
I'll try to change that,
When I'm I going to meet Lulu,
My PJ is ready, we can go back together if you want"
Da ɗan mamaki tace masa
"Ya akai kasan ina nan?*
Murmushi taji yayi kafin yace 
"I have my ways Mummyyyyyyy"
Tace 
"Stop calling me Mummy,"
Kamar yana gabanta yayi pouting red lips ɗinsa yana faɗin 
"Why Mummy,
Lulu will not be happy taji ina cemiki Barrister Aisha?"
Ya mayar mata maganar da tai akanta.

Jin takaicinsa ze iya ɓata mata day ɗinta yasa kawai ta kashe wayar tasan tunda ta faɗa mishi seya toshe duk wata hanya da Umar zeyi bincike akansa indai Farouq ne sheɗantar kansa tafi ƙarfin shekarun sa.

Gani tai yana sake kiranta,
Babu yadda ta iya haka ta ɗaga 
Yace 
"Mummy ya kika kashe ko credit ɗinki ne ya ƙare,"
Banza ta mishi jin haka yace 
"come on Mummy I'm just pulling your legs nasan your together with my father in law your handsome husband, bazaki so ki tafi tare dani ba, I won't intrude your honeymoon "
 tace 
"Farouq"
da sigar gargaɗi yace 
"my dear Mummy just tell me sanda zanga matata I'll let you be,"
Tace 
"she'll be graduating next week Thursday, zan shirya mata surprise graduation dinner party, so I'll be expecting you early on Thursday inaso kaje tare damu can school ɗinsu be there for her and you'll be her date for the dinner,"
Yace 
"kinsan me Mummy?"
Da ɗan mamaki tace 
"what?"
Yace 
"ina sonki Mummy,
 your very,
very experienced and romantic 
I like how your brain is always braining,"
Ba tareda ta shirya ba taji tana murmushi kawai don iya shegen da yake mata ya isheta baze samata hawan jini tana zaune kalau ba,
Tace
"Farouq kaji dashi and please wear something decent,"
Yace
"done Mummy,
see you there "
yana katse wayar,
Secretary ɗinsa ya kira da sauri ta shigo ya miƙa mata wayar yana faɗin 
"Prepare our trip,
we are going back to Nigeria next week, 
get an event planner, fashion designer.....uhmm just everything that a girl will need for graduation party I want the best Julia,"
Jinjina kai Julia tayi tana faɗin 
"yes Sir,"
Girgiza kai yayi 
Yace
"I want perfection, is for my girl"
Waro ido Julia tai tana murmushi cike da mamaki don duk kalar fitinar Farouq bata taba ganinsa da mace ba ko yace mata ga waccan budurwarsa ce, matan da yake mu'amala dasu abokan kasuwancinsa ne kawai his not much into women.

It's fatoumspassion IMSAL 
Don't forget to 
Vote 
Share
Comment 
Like

SPECIAL ANNOUNCEMENT 
Ina farin cikin sanar muku cewa zan fara posting sabon novel dina IMSAAL a ArewaPen da Wattpad 🤍

But don’t worry… WhatsApp readers are still my priority 🫶🏽
Nothing is changing here, this is still home ❤️
To celebrate this, I have something special for my real supporters 
🎁 The FIRST 20 PEOPLE to:
✔ Follow me on ArewaPen
✔ Follow me on Wattpad
Will get FREE entry into my paid WhatsApp group 💫
🎁 HOW TO QUALIFY 🎁
After following me,
📌 Take a screenshot showing you’re following me on BOTH platforms
Then send it to me on WhatsApp 👇
📩 ***
⚠️ Include your username
⚠️ Only the first 20 valid people will be accepted
⚠️ No screenshot = no entry 👀
ArewaPen @fatoumspassion
Wattpad @fatoumspassion
Hurry… once the 20 slots are gone, that’s all 🔥