3&4
by @autaralheri
🐝🐝 🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝 *ZUMAH*🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
ZUMAH
GAZAƘI GA HARBI
MAGANINKI🙄
(SEDA WUTA🔥)💃
Erotic love funny with sexy story 🥳🥳🥳
Writer by
Autar alheri✍️
🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝
Up'up'upp Dr Yasmeen 🥳💃
Oh'oh'ohhhh 💋🔥
This story bance komai ba 🤭 amma fa idan kinsan bakida miji akusa koda ke matar aurece please ki haƙura kawai zefi🤷
Bismillahirahamanirrahim
Book 1
Page 3&4
"Banza tayi mata taci gaba da dariyarta tamkar wadda ta zare. Sanin halinta yada jadda tayi banza da ita, taci gaba da laziminta. Kuluwa kam seda tayi me isarta tukunna ta tsagaita kana tace "wai jadda wannan yaa Khalifa ɗin kwana nawa zeyi ne yabar mana gidanmu? "Jeki kitambeshi ai shiyanifini sanin ko kwana nawa zeyi. Jin amsar da jadda tabatane yasa ta turo baki gaba kafin ta juya tayi kwanciyarta, ran fal farin ciki tayi maganin indo.
Indo kuwa har gari ya waye tana duƙe akan fantekar, tana famar cin ƙullun ƙuliƙuli😢 koda ɗanta Ilu, yashigo gidan yasameta acikin wannan halin, yayi matuƙar tsorata, cikin tashin hankali yake tambayar ta mike faruwa. Amma ina sam taƙi kulashi domin gani take dazaran ta miƙe wannan aljanar zata gani, gaya sefamar kuka takeyi tanacin kullun. Ganin abin nata kamar bana lafiya bane yasashi ɗauke fantekar daga gabanta yana cewa "dan Allah iya kidenajin wannan abin karya illataki. Ɗagowa tayi da sauri ta kalli ilu, aiko taƙara sakin kuka tana faɗar "aljana ilu, aljana ce wlh gatanan zata kasheni ne wayyoo ni indo wlh dana sani dabanje gidan jadda ba shi kenan najanyowa kaina fitinar aljanu. "Me gidan jadda dai? Mikikajeyi acan ɗin? "Kulawa ce ta ɗauki kulikuli na tabawa wancan isiya batare da tabiyaniba, shine naje nagayawa kakarta tunda duk abinda tayi bata ganin laifinta, aka biyani kuɗin ashe akwai aljanu agidansu bansaniba, tana gama faɗar hakan cikinta na mirɗawa hakan yasa tayi yunƙurin miƙewa batare da tajira abinda ilu zeceba. Shimadai fasa maganar yayi ganin tana neman miƙewa tsaye, cikin sauri yatemaka mata tamiƙe ɗin, sedai tana miƙewa tsaye, gudawa na bacce mata ko birki babu, hakan duk tawanke jikinta da zawon ƙullun gyaɗa masƙi zalla kamar tayi zawon mai. "Innalillahi wa'inna'ilaihi rajiun, ilu yafaɗa yana riƙeta sosai yakaita bayi, ya kai mata ruwa, aiko ko tsugunawa batayiba ta shiga fesa wani abin babu kama hannun yaro. Acan ilu yabarta ya dawo ya gyara wurin, tass kana yakoma bayi ya fito da indo. Ajiyeta yayi yakira wata maƙociyarsu takuma kishi da ita, yaje yasiyo mata magani, bayan tafice daga idan yake saƙa yadda zeci Uban kulawa domin baya raba ɗayan biyu wannan aikinta ne tun da kowa yasan wacece kuluwar jadda acikin shuwarim.
Abuja
Wani katafaren gida na hango wanda faɗin girmansa ma ɓata lokaci ne, gidane babban gida kuma gidan masu hannu da suni, get uku ne a gidan, tsakanin kowanne get da ɗan uwanshi akwai tafiya me taraza koda da motane kuwa. Daga jikin kowanne get kuwa sojojine kegarinshi, musamman get ɗin farko da yake kamar barikin sojoji, dakuma get ɗin ƙarshe wanda ze sadaka da cikin gidan, giga gigan sojoji ne wanda basumasan minene dariya ba,
Daga cikin gidan kuwa, kusan pert 5 kowanne da sojoji acikinshi, harabar gidan kuwa motocin dake parking space bazasu ƙirguba, part tsakiya na shiga domin naga sojojin sunfiye sintiri ajikinshi. Koda na shiga parlor nagani babba tsantsararrre da wasu mutane aciki, dattijawa su huɗu, mace biyu maza biyu, sekuma matasan manyan samari masuji da kansu kusan su ta kwas, kuma kowanne da kayan sojoji ajikinshi, gasu kyawawa dasu tamkar ƴaƴan Larabawa. Tsayawa nayi inabin kowanne da kallo ɗaya bayan ɗaya ibabin farin ƙarfen dake manne ajikin rigunansu da kallo, *CANAL YUSUF KHAMIS DAMSAK,- MAJOR KHAMAL KHAMIS DAMSAK,- GENERAL ABDUL KHAMIS DAMSAK,- MAJOR FARUK KHAMIS DAMSAK,- IG MUKHTAR KHAMIS DAMSAC, - COMMANDER JUNAID KHAMIS DAMSAK,- GENERAL UMAR KHAMIS DAMSAK,- CAPTAIN YASEER KHAMIS DAMSAK,* hakan nariƙa bibiyar sunayensu ina karantawa ɗaya bayan ɗaya ina nazartar kowanne su sedai makasa fahimtar komai game dasu, kowannesu yana tsaye ga dukkan alamu wani abin ne me mahimmanci ya tsayar dasu, kafin canal Yusuf yaƙara kusan ɗaya dattijon yace "kayi haƙuri pappi in sha Allah komai dassanu komai zekoma nomal indai muna raye bazamu taɓa bari iyayenmu su zubda hawaye ba. Murmushi pappi yayi kafin yace "Allah yayi muku albarka Yusuf yatemakeku akan aikinku da duk sha'anin rayuwarku baki daya. Ameen ameen y Allah. "Datti nidai zan wuce lokaci yatafi zanyi let. "To Junaid Allah yatsareku yabaku sa'a ɗaya dattijon yafaɗa wanda Junaid yakira da datti, hakan suka rinƙa rungunar iyayen nasu ɗaya bayan ɗaya suna musu kiss har matan, suna ficewa daga gidan, wanda yayi na ƙarshe da fitane kuma tun ɗazu bece komaiba seyanzu ya mannawa ibba kiss wato mahaifiyarshi, kana yace "sena dawo ibba, yafaɗa muryar shi adake. Murmushi ibba tayi itama cikeda son yaron nata tace "to Umaruna adawo lpy, daga hakan yajuya Shima yafice daga gida.
Dukkansu motocinsu suka shiga, kowanne ya shiga tashi tare da yaransu suka bar gidan. Humm wato dai idan na fahimta dede wannan gidan SOLDIERS FAMILY ne kamar yadda yake rubuce a get ɗin gidan na farko da aka rubuta *SOLDIERS HOUSE* suna gama ficewa daga gidan aka ƙara rufeshi kamar yadda yake farko kana kowanne soja yaƙara kamewa babu wasa balle annuri a fuskarsu...!
Humm salon wannan book dabanne domin ba abinda be haɗaba aciki, kudai kubiyoni kawai domin kar ayi babuku💃 *ZUMAH MAGANINKI SEDA WUTA*💃💃
Book ɗin ZUMAH paid book ne 1k kacal 👌zaki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 9112799371 moneypoint sha'awanatu kasim. Idan kuma a Niger kike zaki turawa anan 👉 *** My Nita sha'awanatu kasim, kana kituramin shedar biyanki a wannan nomber 👉 *** on WhatsApp 🙏
Autar alheri✍️