PAGE 49
D U H U N D A R E
A 2026 N O V E L
BOOK ONE
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
OUM-AMEER
Arewapen: @Oumameer2671
Wattpad: @Ummu-Amir
BOOK ONE
PAGE 49
Tana shiga ɗakin ta wani rungume Ammie dake tsaye gefen Na'ima tana taimaka mata wurin breastfeeding Babyn.
Da sauri Ammien ta tare ta gefe ɗaya tana faɗin.
"Ah ah! Ki yi a hankali Anaam kada ki faɗowa yaron na ki..."
Marairaicewa ta yi tare da langaɓar da kanta gefe tace.
"Eyyah Ammie haka aka yi wa Autar Abbah ko?"
Dariya sukayi sannan Na'ima ta ce.
"Kuma wallahy koda Abbah ya kira kin nan jiya misalin 8pm duk muna asibitin nan. Yaa Mukkaram ne yace kar a sanar miki a bari sai an haihu domin kina iya ki ɗaga hankalin ki, ni kuma sai na ce kada a sanar miki a bari kawai sai idan kin zo ki gani."
Juya ido ta yi tana wani hararenta ta ce.
" To ai ya miki kyau Yaa Na'ima kin kyauta. Ni daman nasan yanzu kin daina so na.."
Ita dai Na'ima cikin yanayinta na masu haihuwa tana jin sai a hankali ta yi murmushi ta ce.
" Sowie sweetheart, kema kin san har abada ba zan daina son ki ba. Sannu da zuwa. "
Gaisawa suka yi sannan ta karɓi babyn ta zauna tana ta santi suna ta farin ciki tana faɗin tasan irin zallar farin cikin da Haisam yake ciki a yanzu.
Suna nan suna ta fira sai ga Yayar Haisam ta shigo wato Barrister Hajara ita da yaranta su uku. Ɗakin ta bar musu har da Yaa Amina bayan sun gama yiwa juna barka ta wuce Office ɗin Yaa Mukarram ta shiga a hankali tana dariya.
Ajiye Wayar hannunsa ya yi bayan sun haɗa ido cike da farin cikin ganinta ya miƙe tare da ware hannayensa ta shige tana dariya.
"Amarya yaushe a gari?"
Ɗago kanta ta yi tana dariya ta ce.
"Kai Yaa Mukarram wane irin amarya..."
"Amarya mana. Ai ke amarya ce, ga ki kuma naga kin yi kyau abin ki masha Allah,.."
"Uhm! Yaa Mukkaram ni dai bana son tsokana. Ina wuni ya aiki?"
"Lafiya ƙalau ya kike? Ina mai gidan?"
Shiru ta ɗan yi tana tunani domin ita kam sam ta ma manta da cewa wai ta baro wani Maheer a waje amma daga ƙarshe sai ta yi murmushi ta ce.
"Yana waje..."
Dariya ya yi ya ce.
"Auta manyan duniya, shi ne za ki zo da mutum ki bar shi a waje? Ko ya shigo yaga babyn ne?"
Girgixa kai ta yi ta ce.
"A'a..."
"Please ki je ki shigar da shi ya ga babyn sannan ki shigo da shi nan, kina ta abu kaman wata marar wayau."
Da to kawai ta amsa ta juya ta fice ta sake komawa ɗakin da Na'ima take tana faɗi a ranta cewa indai sai ta shigo da shi saidai har abada kada ya shigo, sanda yake zuwa yawon sa ita ce take kai shi ko shi ne yake kai kansa. Aikin banza kawai. Hakan yasa ta yi banza da shi tare da ci gaba da sha'anin gabanta.
********
Maimuna kuwa, gabaɗaya duniyar ta juye da ita a lokaci ɗaya. Wannan gatan, wannan soyayyan gabaɗaya ta manta daɗinsu domin dai Alhaji Gimba ya sauya mata gabaɗaya.
Haka ta dawo gidan yanzu ba ta da wata power kaman ba ita ce a baya take ta wulakanci ba.
Yanzu ma zaune suke ita da Aunty Halira wacce ita ce ta kira ta da kanta ta zo har gidan na ta akan ta koka mata irin halin baƙin cikin da take ciki musamman rikicin da suka yi jiya har ya kai ga yi mata saki ɗaya wanda daƙyar Allah ya taimake ma yau yace ya mayar da ita da safe bayan kwana roƙon shi da suka yi ita da Hajiya Salamatu.
Wani kallon Aunty Halirar ta yi mata ta ce.
"Wai wannan wane irin iskanci ne Maimuna? Ta ya za ki kirani in zo kuma ki zauna ki tasani a gaba kina mini Kuka banza kuma ke ba ƙaramar yarinya ba. Mts! Haba!"
Girgiza kai Maimunan ta yi cike da baƙin ciki ta ce.
"Aunty Dole na yi domin ina cikin tsananin baƙin ciki. Yanzu gabaɗaya na dawo banza wofi a wurin Alhaji sai ka ce ba amarya ba."
Taɓe baki ta yi ta ce.
"Uhm! na san daman za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Ai tun farko na faɗa miki cewa zama a irin wannan gidan haka nan babu wani shiri wallahy ba zai yiyu a gare ki ba. Gabaɗaya kwanakin baya auren ko wata nawa ya yi, amma haka ya saka ƙafa ita matar shi da ɗan shi suka yi tafiyar su suka barki kina gadin gida, ƙarshe kuma da kika tafi wulaƙanci ne ya biyo ba... "
" To ai aunty wallahy yanzu abun ya fi yawa ma fiye da baya, ga shegen faɗa idan ya fara tamkar wani uba da ɗansa, zagi ta uwa ta uba, ga bala'in rowa Aunty Halira ga ƙazanta..."
" To ai shi ne nace miki matuƙar waccan matar tana gidan nan biyar bokaye da 'yan tsibbu ba zai taɓa bari ki gane kai nai ba..."
Saurin girgiza kanta ta yi ta ce.
" A'a Aunty Halira...wallahy tallahy Aunty Salamatu ba ta da wani laifi domin haƙurin da take da shi da iya ɗaukar rigimarsa ni ban iyawa. Wallahy tana ƙoƙari kuma tana matuƙar haƙuri da shi. Na aure shi don na huta amma ban ƙarar da komai ba sai baƙin ciki, jiya ma daga maganar arziki na ce ya bani jari in fara saro kaya daga China tunda wurin zuwansa ne shikenan ya hau zagina ta uwa ta uba yana ta cimin mutunci. Ƙarshe da nuna ɓacin rai na fa Aunty Halira sakina ya yi... "
Wani irin dafe ƙirji Aunty Halira ta yi tare da zaro ido waje ta ce.
" Saki Maimuna? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... Amma dai wannan Salamatu anyi tsohuwar munafuka..."
"Aunty na faɗa miki fa ba tada laifi wani, wallahy har da ita ta tayani bashi haƙuri wanda sai ɗazu da safe ne na samu ya mayar dani.."
Cike da tsantsar ɓacin rai Aunty Halira ta wani kalle ta ta ce.
"Shashashar banza marar hankali. Ita kishiyar ce kika yarda ta ji sirrinki har ki bari wai ta ji cewa an sake ki? Lallai Maimuna sai yau na tabbatar cewa baki da hankali. Wayyo Allah na tuba ta ina za'a haɗa hankalinta da wayonta da naki? Macen da a haife ma ta haife ki amma shi ne kika zauna kina biye wa makircinta? To wallahy tallahy kin ji na rantse miki da Allah sai kin tashi mun tafi gidan Malam don ubanki. Daga tambayar jari zaa ce saki ya shiga ai kowa ya ji wannan yasan cewa makirci ne. Wannan mutumin mai uban kuɗi za'a ce wai yana rowa?... "
" Uhm! Aunty Halira kenan! Wallahy tallahy mutumin nan ya wuce inda kike tunani, kuɗin sa ba sa ciyuwa... "
" Ƙarya ne! Ni na ce miki Ƙarya ne makirci ne kawai, saboda haka ta shi ki ɗauko mayafinki ki shirya mu tafi yau in sha Allahu sai mun samo maganin wannan matsala. Kuma yau wannan matar sai ta gane cewa ba ta da wayau. Kuma nasan halin ki Maimuna...wallahy ko da wasa kada ki taɓa yarda ki ce za ki faɗawa su Inna wata magana dangane da wannan lamari. Kibar komai a hannuna zan miki maganin su."
Jinjina kai ta yi a wannan karon alamar ta yarda sannan daga ƙarshe ta miƙe yi jiki sanyaye ta shiga ciki ta shirya ta fito suka fito, a main parlour suka tarar da Alhajin yana karin safe wanda tun bayan da suka yi rikici daren jiya ya koma ɓangaren Hajiya Salamatu ya yi kwanciyar sa.
Aunty Halira tamkar za ta kifa haka ta shiga gaishe da Alhaji Gimba wanda ko kallon arziki ba ta samu a wurinsa ba a matsayinta na babbar yayar Maimuna amma haka ya wani amsa a daƙile a ransa yana jira ta yi mai wata magana dangane da rigimarsu ta jiya ya ci mata mutunci. Sai ga shi bayan sun gama gaisawa ta sa kai ta yi gaba.
Kallon shi Maimuna ta yi a ɗan darare ta ce.
"Alhaji Zamu je wurin duba wani ƙanin Babanmu ba shi da lafiya..."
Taɓe baki ya yi ba tare da ya kalle ta ba ta ce.
"Koma dai wurin nemomin asiri za ku tafi wallahy ni nafi ƙarfin ku domin baku iya komai dani. An zo an aure ni domin a ci banza ko? To wallahy ƙwandala ta ba zan iya bayar ba domin a yi sharholiya, idan kuma Macce ta gaji hanya a miƙe take kuma ƙofa a buɗe take. "
Wucewa ta yi gaba tana mai jin wasu irin hawayen baƙin ciki suna wanke mata fuska. Irin cin mutunci da tozarcin da ya yi mata a daren jiya ba ta fata ta sake jin irin sa, hakan yasa ta yi gaba kurum ta ƙyale shi.
Bayan ya kambala cin abincin ne ya dawo parlour ya zauna tare da ɗaukan Remote control ya kamo News Yana kallo.
Yana na nan a zaune sai ga Faris ya fito cikin shirinsa na fita Office ya zauna a hankali ya gaishe da shi sannan Alhajin Gimban yana kallonsa ya ce.
"Ba za ka yi breakfast ba ne?"
Girgixa kai ya yi ya ce.
"No, am good for now, Idan 12pm Idan na isa office zan ci wani abun.."
Ya ƙarashe maganar yana mai ƙara gyara zamansa sannan kai tsaye ya ci gaba da cewa.
"Ahm..Daddy daman I have something important to discuss with you. Matar aure ce na samu wacce last few months ago nace maka Idan mun kai ƙarshe mun yanke zancen aure zan sanar maka domin a tura a nemomin auren..."
Cikin wani irin farin ciki ya tare numfashinsa da faɗin.
"Alhamdulillah masha Allah. Gaskiya wannan labarin ya yi matuƙar faranta min ba kaɗan ba. Daman rashin auren nan naka ya dame ni Faris, don kawai bani da yanda zan yi ne. Amma yanzu tunda Allah ya kawo ƙarshen abun magana ta ƙare. Wace yarinya ce wannan? Su waye iyayenta. "
"Daddy ba wata ba ce, Rabi'a ce ta gidan Alhaji Salisu na Alhaji Mas'ood Galadima..."
A hankaɗe ya bi shi da wani irin kallon wanda duk irin tsaurin idonsa sai da ya ji hantar cikin sa ta kaɗa.
"Wane Mas'ood ɗin?"
"Daddy wane Mas'ood ɗin wanda ya wuce abokin ka wanda kuka taso tun yaranta..."
Wata irin zabura ya yi ya miƙe tsaye yana mai jin maganar ɗansa tamkar a mafarki ya shiga jinjina kansa da mamaki ya ce.
"Mas'ood Faris? 'ƴar gidan Salisu yayan Mas'ood jinin Mas'ood ka zauna a gabana kake faɗamin cewa za ka aure ta? Jinin manyan maƙiyana, abokan gaba na, waɗanda ba sa son ci gabana za ka ce kana so Faris?..."
Wata irin super ya yi tamkar wani mahaukaci ya faɗa kan Faris ɗin dake zaune kan kujera ya shiga kai mishi naushi. Hakan ya yi daidai da fitowan Hajiya Salamatu wanda yasa a gigice ta yi kansa cikin tsananin tashin hankali ta shiga kicaniyar janye shi tana faɗin.
"Na shiga uku na lalace ni Salamatu ni yau mi zan gani haka!!"
Dukansa yake ta ko'ina yana kai mishi naushi cikin tsananin zafin rai yana ta tsine-tsine tamkar wani mahaukaci sabon kamu.
"Alhaji Dan Allah Dan girman Allah ka yi haƙuri ka sake shi, kada fa ka je ka ji mishi ciwo fa...Alhaji ka daina dukansa na roƙe ka san Allah ka daina...miye ya aikata maka da zafi haka da har ya cancanci wannan hukuncin haka?"
Tana rufe bakinta ya taso ya juyo kanta ya kifa mata wani irin mari wanda sai da ya saka ta yin baya-baya tamkar za ta kifa sannan ya ci gaba da zage-zage yana faɗin.
" So kuke kuga bayana da ke da ɗan ki kuma wallahy Allah ba zai bari ba domin na riga na yi muku nisa. Ni za ku kawowa iskanci? Ni za ku rainawa wayau? Ku rasa waye za ku haɗa baki da sunan wacce zai aura sai 'ƴar maƙiyana?..."
Miƙewa Faris ɗin ya yi a tsananin zuciye wanda daga kallon sa za ka fahimci cewa baya ma cikin hayyacinsa tsabar ɓacin rai.
Allah sarki uwa! Duk da irin marin da ta ji ya shige ta, ganin yanda ya miƙe yasa ta sha gaban sa a ruɗe tana faɗin.
" Faris ina za ka je? Wai miye ka aikata masa haka?"
Ta gefen ta ya zagaya ya fice tamkar zai tashi sama kai tsaye yaja mota ya bar gidan.
Sake dawo da kallonta ta yi gun Alhajin ta ce.
"Wai miye abunda yake faruwa ne? Ni kun bar ni a duhu, miye kuke magana a kai?"
Wata hararar ya maka mata sannan ya ce.
"Munafuka kawai! Duk abunda yake ai da sanin ki yake yinsa. Rabi'ar gidan Salisu Galadima ai da sanin ki da izininki yaje neman auren ta kuma wallahy tallahy na rantse da Allah ba zai aure ta ba...ke ko wata ɗiyar da ta taɓa alaƙa da gidan wallahy tallahy ba zai aure ta ba ballantana ɗiyar Salisu. Ɗiyar Ridwan ma ba zai aura ba ballantana jinin Galadima....."
Sake girgiza kai ya yi cike da wani irin raɗadin baƙin ciki yace.
"Wato kun raina ni Salamatu ko! Kun yi matuƙar raina matsayi na, ni da gidana amma kun mayar dani banza. Kun nuna ni ban isa da gidana ba, da ace kun san zafi na kun ɗauke ni da daraja ba za ku taɓa fara tunanin mafarkin haɗa jinina da jinin maƙiyana ba..."
Tijara ce mai zaman kanta ya shiga surfa mata wanda sai da ya saka Hajiya Salamatu zubo da ruwan hawayen baƙin ciki. zagi da cin mutunci sai abinda ya manta sannan daga ƙarshe cike da rashin arziki ya ce.
"Kuma tun da har cin amana ta da son ganin bayana shi ne abinda kuke so to har abada ba za ku taɓa yin nasara ba..."
Girgiza kanta ta ci gaba da yi tare da kama hanya ta shige shashenta ta bar shi nan yana ci gaba da cin mutuncin.
Wayar ta ta ɗauko ta shiga kiran Faris ɗin amma kuma tana ta ringing ya ƙi ya ɗaga wanda daga ƙarshe dole ta haƙura tare da zaunawa a bakin Gado ta sake fashewa da kuka. A ranta faɗin take yaro ne dai ka haifeshi ba ka haifi halin sa ba. Idan ba shi ba taya Faris zai ɗauko zancen auren Rabi'a wai kace bai san abinda ake ciki ba? Sai ka ce bai san takun saƙar da ke tsakaninsu da familyn Galadima ba? Shi yanzu ko a makarfi akace masa ya nemi Rabi'a ai bai kamata ya aikata ba. Kai da suka rufe a cell har ka wuni ka kwana akan laifin da ba su da hujja amma shi ne don rashin zuciya za ka koma daga baya ka ce kana son 'ƴar su? Ga shi kuma da yake shiryayye mutumin wofi ko ita ɗin bai taɓa sanar mata ba, yanzu duk abinda za ta ce Alhaji ba zai taɓa yarda da cewa ba ta san da wannan zancen ba. Kuma ko ita ta goya baya akan cewa ba zai aure ta ba, idan kuma mutuwa zai yi to ya mutu tana jira ta gani.
*******
Suna nan a asibitin ba jimawa aka basu takandan sallama hakan yasa suka ɗunguma suka koma gida.
Kafin ƙarfe shida na yamma su Aunty Aysha da yaransu duk sun cika gidan ana ta farin ciki wanda Anaam ita ce zaune a ƙugun mai jego tamkar ita ce mai haihuwar.
Shigowa Nene ta yi ɗakin da suke ta fira ta kalli Na'ima ta ce.
"Na'ima ki taso an kwashe ruwan zafin ki yi wankan..."
Dariya Anaam ta fara yi mata tana faɗin.
"Miƙo min Babyna ki wuce wurin wankan ki Hajiya..."
Wani kallon ta yi mata tana mai mere baki ta ce.
"Ai kema dai ba jimawa turn ɗin ki zai zo saboda haka ki daina yi min dariya..."
Cikin jin wani iri a ranta tana wani murmushi ta ce.
"To ai ni bana haihuwar ballantana ki zauna jiran wannan lokac..."
A hankali ta haɗiye sauran magananta ganin kiran Maheer da ya shigo yanzu a wayanta wanda ta zuba ido tana kallo har sai da ta gama ringing Sannan ta mayar ta ajiye tare da ɗago babyn da yake hannun ta tana kallo tana ta murmushi.
Zamanta a wurin ya yi mata miss calls ɗinda suka kai talatin wanda ko sau ɗaya bata ji nadamar rashin ɗaga kiran nasa ba domin bata so ma ta yi magana da shi.
Tana nan a zaune har Na'ima ta fito wanka suka ci gaba da firarrakinsu sannan daga baya sai ga Yaa Mubarak ya shigo ɗakin.
Wani irin tsalle ne ta yi ta ɗane dokin wuyansa wanda saura kiris su zube ƙasa sannan ya yi nasarar kauce mata yana dariya ya kalle ta sai kuma ya kalli Na'ima yana mai riƙe baki ya ce.
"Toh! Ashe Na'ima idan mutum ya yi aure ya tafi Lagos zarewa yake shi ne ba ki faɗamin ba?"
Dariya suka fashe da ita sannan Na'ima ta ce.
"Ai kam dai sai dai muyi tayata da addu'a Yaa Mubarak...sannu da zuwa."
Jinjina kai ya yi yana dariya ya ce.
"Yauwa Na'ima. Barka, congratulations, Allah ya raya ya baki lafiya.."
"Amin Yaa Mubarak, na gode."
Kallon Inda Anaam ɗin take ya yi sannan ya ce.
"Mijin ki yana waje tun ɗazu yana jiranki. Da alama kin baro wayan wani ɗaki hakan yasa yake ta kira baki ɗaga ba."
Tana jin haka ta miƙe a hankali ta fito ta zo har inda yake zaune a motar sa ta tsaya a bakin ƙofan motan ba tare da ta yi magana ba.
Hakan yasa ya fito a hankali ya ɗan matsa kusa da ita yana kallon fuskar ta murya a ƙasa sosai ya ce.
" Barka..."
Jinjina kai ta yi alamar ta masa ba tare da ta buɗe bakinta tayi magana ba.
Lumshe idanunsa ya yi ya buɗesu a hankali still idanun shi a kanta ya ce.
"Ahmmm! Daman Excuse ɗinda na ɗauka is only for today...so, I think Idan kinga Baby za mu iya komawa zuwa 7 to 8pm haka..."
Girgiza kanta ta yi ba tare da ta kalle shi ba ta ce.
"Ni dai zan zauna a nan yanzu,and if you are interested too...akwai ɗaki a ta can ɓangaren sai a baka.."
"Maryam na yi alƙawari zan dawo dake kafin Naming ceremony day ɗin..."
"Ai ni ba yarinya ba ce ƙarama da za ka ce sai ka tsare ni gudun kada na ɓata, daman kaga ka saba tafiyanka ka barni sai sanda ka ga dama kake dawowa saboda haka kada ka ce za ka min doka."
Jinjina kai ya yi yana mai jin ciwon kalaman ta murya a can ƙasan maƙoshin sa ya ce.
" Okay....ni zan koma yanzu. Please take care!"
Jinjina kai ta yi ta ce.
"In sha Allah, thank you. Allah ya tsare."
Kallonta yake yanda take tafiyan cike da nutsuwa har sai da ta shige sannan ya juyo da nufin bude mota sai kawai suka yi ido biyu da Rabi'a wacce itama shigowanta gidan kenan.
Saurin kawar da kansa ya yi tare da buɗe mota ya shige a hankali ya ja ya tafi.
Ita kuwa sai wani kallon shi take har sai da ya shige motar sannan ta nufi cikin gidan kai tsaye ta shige.
Duk wanda ya haɗu da ita sai ya yi mamaki musamman Yaa Mubarak wanda yasan cewa ya baro ta a gida ta ya kuma za'a ce ta zo nan gidan?
"Yaa Mubarak Ina wuni."
"Lafiya lau..."
Daga haka ya sa kai ya wuce yana mamakin abinda ya sake dawowa Da ita gidan nan kuma.
Tunda ta shigo gidan babu wanda ya koma sabganta domin ko Na'ima tana shiga ɗaki ta duba ta ita da baby ta fito ta dawo ɗakin Ammie ta yi kwance a parlour kan kujera har sai da Abbah ya dawo bayan sallan Isha ya ce a kira ta yana nemanta.
Koda ta shigo parlourn cikin rashin sa'a suka yi ido biyu da Mukarram wanda ya wani maka mata harara a kaikaice itama kuma sai ta hutar da Kanta ta janye idanunta daga kallonai domin bai da mutunci ko kaɗan.
Wuri ta samu kusa da ƙafar Abban ta zauna tare da gaishe da shi tana mai ƙara soke kanta.
"Rabi'a..."
Abbah ya ambata yana mai kallon inda take zaune.
Ɗagowa ta yi a hankali ta amsa ma sa sannan ya ce.
"Waɗannan da kike gani duk en uwanki ne kamar ko yaushe..so nike in ji gaskiyar zance daga bakin ki dangane da bayanin da Alhaji Salisu ya yi mini a kanki..ke yanzu Kina ganin dacewarki da Auren Faris Rabi'a?"
Cikin tsabar mamaki da al'ajabi kowa ya zubo ido yana kallonta, daman Mukarram, mubarak, Anaam da kuma Ammie su ne a ɗakin sai Yaa Naseer da ya zo da ita wanda Abbah shi ne da kansa wanda ya bada umarni tare da rarrashin zuciyar Alhaji Salisu ya ce ya turo mishi ita.
Cike da rashin haƙuri Mukarram ya miƙe tsaye yana wani kallonta sai kuma ya Kalli Abbah ya ce.
"Alaji wane Faris ɗin ne take cewa za ta aura?"
"Faris na gidan Alhaji Gimba."
Kamar wani abun arziki ya matsa yana ƙare mata kallon mamaki sai kuma kwatsam suka ji ya fasga mata wani marin da sai da ta dafe kuncen ba shiri. Yana batun ƙara mata wani marin Mubarak ya yi saurin riƙo hannunsa ya ce.
"Ya Mukarram ka barta please..."
Duk da cewa an janye shi hakan bai hana shi saka ƙafa ya sake yi mata wani irin harbi ba wanda sai da ta matsa baya ba shiri tare da fashewa da wani irin kuka.
Wata irin tsawa ce Abbah ya daka masa wacce ta yi sanadiyyar sanya shi ja baya yana mai ci gaba da ɓata fuska ya ce.
"Alhaji wannan yarinyar ba 'ƴar mutunci ba ce ka barni da ita na yi mata shegen suka ko za ta dawo hayyacinta..."
Da sauri Abbahn ya ɗaga masa hannu tare da girgiza kansa ya ce.
"Ka barta kawai Mukarram..."
Daga haka ya sake kallonta yana mai matsowa gaba kaɗan kan kujerar ya ce.
"Rabi'a Faris kike so ki aura?"
Jinjina kanta ta yi tana mai share hawayen ta da gefen veil ɗinta ta ce.
"Eh Abbah, ni shi nake so kuma ya amince zai turo iyayen sa..."
"Kin tabbata kina son sa Rabi'a?"
"Eh, Abbah..."
Ajiyar zuciya ya sauke yana mai ƙara jinjina al'amarin Rabi'a da uwarta a zuciyarsa sannan ya ce.
"Shi kenan...ta shi ki tafi. Allah ya tabbatar da alheri yasa mu dace..."
Shima Naseer ɗin cike da mamaki ya ce.
"Alhaj..."
Saurin ɗaga masa hannu ya yi tare da faɗin.
"please ina so kowa ya tafi ya bani wuri magana ta ƙare.."
Miƙewa Mukarram ya yi cike da jin wani irin ƙullutun baƙin ciki ya ce.
"Gaskiya Alhaji magana ta gaskiya idan har kace za ka biye zancen wannan yarinyar har ka mara mata baya to baka yi mana adalci ba. Alhaji kasan waye Alhaji Gimba, don Allah kada ka sake janyo mana rigima da shi."
Daga haka ya fice wanda suka fita ne gabaɗaya sannan Ammie ta kalle shi ta ce.
" Alhaji nima na yi mamaki da har ka Iya tsayawa ka saurare ta. Alhaji ina amfanin haɗa Zuriya da Alhaji Gimba? Ni na san ba zai taɓa amincewa ba kuma ba zai taɓa goyon bayan wannan abun ba...bana so aje a ƙara maimaita abun da faru baya wanda bamu san ma wannan ɗin dame zai zo ba..."
Duk maganganun da take shiru ya yi kawai bai ce mata ba tamkar ma baya ɗakin haka ya yi mata, hakan yasa ta miƙe tayi tafiyanta zuwa wasu sabgogin.
******
Sati Ɗaya har da kwana biyu Anaam ta share a gidan inda suka ci bukin su suka yi hidima mai daɗi inda yaro yaci suna Mas'ood (Khalipah). Haisam shi ne wanda ya saka sunan da kan shi wanda hakan ba ƙaramin girma ya ƙara masa a idon su Anaam da sauran dangi ba.
Tana nan da Yamma around 6pm ita da Na'ima da kuma Na'ima Hassan suna zaune suna cin Chicken Pepper soup ɗinda aka kawo wa Na'ima suna ta nishaɗin duniya sai ga Yaa Amina ta shigo tana faɗin.
"An ji daɗin gida an manta da miji ko? To sai ki tashi ki tattara naki da naki ki wuce ga shi can yana jira a waye.."
Wani irin faɗuwar gaba ta ji wanda har ba ta san lokacin da ta wani ɓata rai ba ta ce.
"Yaa Amina yanzu za'a ce na tashi na haɗa kaya zuwa Lagos?"
Wani kallon Yaa Aminar ta yi mata sannan ta ce.
"iyyeh! Mu za ki faɗawa haka? Ai na san kin san da zancen tafiya ki daina ma wani wayance mana ki daina jin kunya, saboda haka ki tashi ki tafi kawai Allah ya tsare..."
"Yaa Amina.."
"Abbah fa tun ɗazu na ji yana faɗan cewa miyasa ma ya barki har tsawon sati ɗaya. Ki rufawa kan ki asiri ki tashi ki tafi."
Ta shi ta yi ba tare da ta sake furta komai ba ta shige ɗakin Ammie ta ce Nene ta haɗa mata kayanta wanda sai da ta gama son ran ta sannan ta yi musu sallama cike da kewa ta zo ta shige motar ba tare da ta yi magana ba.
Lumshe idanunsa ya yi a hankali wanda tunda ta fito yake kallonta ita da su Aunty Aysha har suka yi mata sallama suka koma.
Hannun ta ya riƙo a hankali muryar nan tasa a natse yana ɗan murmushi ya ce.
"Fushin ne har yanxu Maryam? Har yanxu baki huce ba?..."
Ƙara ɗago hannunta ya yi sama ya sumbata a hankali wanda hakan yasa ta janye ba shiri tana mai jin wani iri a ranta ta ƙara haɗe fuska ta ce.
"Bana so..."
"Please I'm sorry...ya kamata ace kin tausayeni hakanan...ba zan iya jurar wannan yanayin da muke ciki ba dani dake...i know that I have wrong you in so many ways, but na yi miki alƙawarin gyara kuskure na. Tunda na koma na kasa yin wani cikakken aiki, kullum duniya ta da tunanina a kanki suke ƙarewa, idan na kira bakya picking, Idan na miki message bakya replying, please forgive me.. "
Ƙara turo cute lips ɗin nan nata ta yi zuwa gaba waɗanda suke matuƙar burgeshi cikin shagwaɓewa ta ce.
"Ni fa ba jimawa zan yi resuming lectures..."
"We will add only one week in sha Allah sai na dawo dake."
Shiru ta yi tana mai ƙara nazarin maganan na tsawon lokaci. Abubuwa ne da yawa a ranta, tana da tambayo yi da maganganu zuwa gare shi waɗanda take tunanin idan ta samu amsar su to wataƙila ta iya samun nutsuwa da shi.
Ganin ta yi shiru tsawon lokaci yasa ya tayar da motar a hankali yaja suka wuce zuwa Airport.
******
Alhaji Mas'ood na zaune bayan ya dawo daga masallacin Isha yana cin abincin dare sai ga kiran Alhaji Gimba kaman a mafarki.
Ɗagawa ya yi tare da yi masa sallama domin a tunaninsa wataƙila wannan karon abun arziki ne.
Sai dai cike da hargagi ya fara faɗin.
"Mas'ood Galadima wato kun kasa yin nasara a kai na shi ne ku ka koma wurin ɗana ko? To wallahy tallahy ba zan yarda ba, kuma ko mata sun ƙare babu abinda Faris zai yi da jinin ku, ni daga kai har Alhaji Ridwan wallahy na ƙare da labarinku har abada. Sannan kada ku manta cewa an yi mana iyaka a kotu., sai da ku ka sa hannu sannan na sa, saboda haka idan ba ku fita har iyalina ba wallahy ko yanzu ita ce za ta rabamu a karo na biyu..... "
✍️ OUM-AMEER ✍️