DUHUN DARE

PAGE 50

by @oumameer2671

D U H U N D A R E

A 2026 N O V E L

BOOK ONE

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHEEM

OUM-AMEER

Arewapen: @Oumameer2671

Wattpad: @Ummu-Amir

BOOK ONE

PAGE 50

Numfashinsa na wani fita a rikice ya ƙarasa maganar cikin tsananin fushi, ba tare da ya bari Alhaji Mas’ood ɗin ya ce uffan ba kawai ya katse kiran.

Shiru ne ya mamaye wurin na ɗan lokaci yayin da Hannunsa ke ɗauke da wayar har yanzu yana mai kallon screen ɗin tsabar mamaki.

Hajiya Nasmah da ke zaune gefensa ta ɗan matso kusa da shi cikin damuwa ta ce.

"Alhaji lafiya kuwa? Waye yake maka magana haka kamar zai cinye ka?"

Ɗago kai ya yi a hankali ya kalleta, idanunsa cike da wani irin ƙuna ya ce.

"Gimba ne..."

Ji ta yi zuciyarta ta yi wani irin bugawa da ƙarfi, sai kuma ta zaro ido a ɗan razane ta ce.

"Subhanallah... me yake faɗamaka haka Alhaji? Ni fa wallahy ina tsoron sharrin mutumin nan, tun abinda ya aikatawa Mukarram har yau wannan shock ɗin bai bar ni ba Alhaji..Mutim ba kyau Alhaji..."

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yana mai ture plate ɗinda ke gabansa ya ce.

"Abinda nake ta gudu shi ne ya faru Hajiya Nasmah..maganar nan ta Faris da Rabi'a ta kai kunnen sa. Wata ƙila Faris ɗin ne ya faɗa masa."

"Faris ɗin ma ai nasan zai iya tunkararsa tunda shima ba baya bane indai gidan zuciya ne."

Wayar da ya ajiye a gefe ita ya sake ɗauka ya kira numbern Alhaji Ridwan, bayan sun gaisa ya ce.

"Ka yi wata magana da Gimba ne?"

Jinjina kai Alhaji Ridwan ɗin ya yi daga can nasa ɓangaren tamkar suna ganin juna ya ce.

"Eh, Faris ne ya kira ni akan zancen yana son auren Rabi'a kuma Mahaifinsa ya hana, yasan cewa mu kaɗai ne ke iya taka masa burki domin ko 'yan uwansa baya saurara, shi ne na kashe wayan na kira shi domin mu samu mu fahimci juna amma kasan halinsa kawai ya hau zage-zage kawai ya katse kiran."

Girgiza kai Alhaji Mas'ood ya yi ya ce.

" Uh uhm! Yara ne dai ka haifesu baka haifi halin su ba...."

" Alhaji Mas'ood... "

Alhaji Ridwan ya kira sunan Alhaji Mas'ood ɗin sannan ya ce.

" Kun shirya aurawa Faris ɗin Rabi'a?"

Cike da shakku Alhaji Mas'ood ya ce.

"Anya? Kafa san inda muka fito...."

"Alhaji Mas'ood kada ka biye ta kansa kafi kowa sanin cewa Gimba mahaukaci ne. In banda rashin hankali taya za ka kama ɗanka daga zancen aure kawai ka hau sukan sa kaman wani ka samu jaki."

"Duka??"

Alhaji Mas'ood ɗin ya ambata cike da zallar mamaki.

"Wallahy wai dukansa ya yi saboda kawai Alhaji Gimba yana da motsin ƙwaƙwalwa. Saboda haka kada ka biye shi ai shi namiji ne ba mace ba, kuma tunda har suke son juna matuƙar dai kun amince ni ne nan wanda zai tsaya masa a matsayin wakili har ayi komai a gama. In yaso ya kai mu kotun lahira ma idan zai iya.. "

" Subhanallah! Alhaji Ridwan ka yi istigfari domin wannan kalma bata kama ce ka ba a matsayinka na musulmi... "

" To Astagfirullah! Ya kai mu duk kotun da ya ji zai iya amma wannan aure an yi shi an gama. Wallahy ni yaron ma ya bani tausayi musamman yanda yake magana, yace ya nemi Anaam an hana shi yanzu kuma ace za'a hana shi wannan ɗin..."

"To ni ma ai shi nake dubawa, tabbas ni ne da kaina na hana shi Maryam domin itama ta ce ba ta yi, to amma ita wannan ɗin ta kafe ita da Uwar ta cewa shi suke so..."

"Duk wanda ya ce zai haɗiye gatari sakar masa ɓota Alhaji Mas'ood. In sha Allah zan yi ƙoƙari in dawo next week, idan na dawo zan je mu samu 'yan uwansa a can Bunguɗu sai mu tattauna, daga nan sai mu zo idan Allah ya yarda sai a saka rana da komai da komai..."

"Okay,Allah ubangiji ya yi mana jagora yasa mu wanye wannan abu lafiya."

"Amin Ya Allah."

Yana katse kiran ya kalli Hajiya Nasmah ya ce.

"Ɗauko min waccan wayan Hajiya in kira Alhaji Salisu da Madu Muji yanda za'a yi. Na san mukarram ko mai zan yi ba zai shiga maganar nan ba."

"Hmm! Mukarram! Mukarram ba zai taɓa daina halin shi na zafin rai ba."

*******

A ɓangaren Faris kuwa.... Tunda ya fice daga gidan bai koma ba har yau, ji yake gabaɗaya ina ma ace wani mahaifi ne ya haife shi! Mutum kullum faɗa kullum tashin hankali? Babu abinda ake shiryashi da shi a kwashe lafiya sai an yi rigima.

Ba zai iya ci gaba da zama a wannan gidan ba, tunda har baya girmama muradinsa to shi kuma bai ga amfanin ci gaba da zama a gidan ba.

Hakan yasa yau ya yanke shawarar wucewa wani gidansu dake Kaduna domin ya huta ko zai huce wannan baƙin cikin da mahaifin nasa ya ƙunsa masa. Mamaki yake har yanzu wai ta yanda har Daddy ya iya saka ƙarfinsa yana dukansa tamkar wani bawa da uban gidan sa.

Tafiya yake akan titi yana ta sharara uban gudu tamkar zai tashi sama amma kuma daga ƙarshe ya samu gefen hanya ya yi parking, idanun sa sun cika da wani irin ɓacin rai sun yi masa jajir yayin da zuciyar sa ke wani irin tafarfasa ya wani daki steering motar da ƙarfi ya ce.

"Why Daddy? Why?"

Girgiza kansa ya yi da ƙarfi tare da saka hannayensa duka biyu ya dafe kansa ya ci gaba da faɗin.

"I’m not a kid anymore… I deserve to choose my life…I have every right to be with who ever I want"

Wata iska ya furzar mai ƙarfi sannan ya janyo wayarsa ya kira Rabi'a.

Ita kuma Rabi'ar tana nan kwance a kan gado wanda duk ilahirin gidan idan ka cire Ammie da Abbah babu wanda take shiga shirginshi, musamman da ya kasance ta samu yanda take so Abbahn ya goya mata baya akan auren Faris ɗin.

Cikin Farin ciki ta yi picking call ɗin, but daga yanayin muryansa sai yasa murmushinta ya dawo damuwa a sanyaye ta ce.

"My Farrab Lafiyanka kuwa?"

"Beeyh Daddy yaƙi ya amince...daga yanda actions ɗinsa ya nuna he will never accept you..."

Wasu irin hawaye ne suka zubo mata jin wani irin labarin da ke nema ya zama shamaki ga samuwar farin cikinta. Murya a karye ta ce.

"To me zai faru kenan? Haƙura za ka yi dani ko me? Farrab ni fa na jure kuma na jajirce sai da na shawo kan iyayena..."

"Shhhhh!"

Ya ambata yana mai lumshe idanunsa a hankali. Jin ta yi shiru ɗin da gaske ya sake cewa.

"Do you trust me?"

Jinjina kanta ta yi murya a ƙasa sosai ta ce.

"Eh.."

"In sha Allahu aurenmu ba jimawa zai faru. Kin san sometimes you have to fight for your happiness, Saboda haka ki fara shiri kin ji ko?"

Cike da ƙwarin gwiwa ta ce.

"Thank you my Farrab..."

"Gani zan je Kaduna, ki kula."

*******

Anaam kuwa, bayan sun sauka gida har ya gama wanka ya shirya ya yi nafila tana nan zaune a bakin window ko kayan da ta zo da su bata canja ba ballantana ya yi tunanin ya ga wani annuri a fuskanta.

Jikin windown ya zo ya tsaya a kusa da ita tare da ɗaga kansa ya kalli sararin samaniya wanda itama abinda take kallo kenan. Duk da cewa ko'ina kewaye yake da haske but da ka kalli sararin samaniyar za ka tabbatar da cewa DUHUN DARE ne wanda dukkan wani mahaluƙi ya zamto mahuta a gare shi.

Lumshe idanunsa ya yi a hankali yana mai jin wani iri a ransa tuna wasu shekaru da suka shuɗe masu makamancin dare irin wannan da suka bar tarihi marar daɗi wanda tunawa da shi ma babu abinda yake ƙarawa sai danasani wacce ta kasance marar amfani.

Ganin ya zo ya tsaya yasa ta miƙe da nufin shigewa caraf ta ji ya damƙo hannunta ya ce.

"Are you still angry?"

Girgiza kai ta yi ba tare da ta kalle shi ta ce.

"No..."

Juyata ya yi suna facing juna ya ce.

"Maryam....give me a chance..."

"Why did you marry me?"

Lokaci ɗaya tambayar ya ji ta bugi zuciyarsa kai tsaye wanda yasa ba shiri ya ɗago kansa ya kalle ta. Sosai yanayinta ya sake sanya shi cikin damuwa da wata irin fargaba domin sam bai yi expecting irin wannan question ɗin ba.

"Daman abun da na tsamma kenan daga gareka..."

Saurin girgiza kansa ya yi ya ce.

"Na yi miki kuskure na yarda...but I promise to fix it, let me prove the love I have for you Maryam..."

"Ina jin bacci please.."

Daga haka ta zame hannunta a hankali ta shige ɗakinta ta canja zuwa towel ta yi wanka sannan ta fito ta haye gado ta kwanta ba tare da ko shafa lotion a jikinta ba.

Yana shigo ɗakin bayan kusan 1 hour da shigowanta sai ya hango ta can ta ƙudundune ta yi tana ta baccin ta.

Girgiza kai ya yi tare da samun wuri akan Sofa ya kwanta har bacci ya yi nasarar sace sa.

Washegari ta riga shi farkawa ta ganshi a kwance wanda kallo ɗaya za ka yi masa ka gane cewa kwanciyar ba ta yi masa daɗi ba amma duk da haka kuma ga mamakinta har ya yi iya yin bacci haka mai nauyi.

Tsayawa ta yi tana ƙare masa kallo na tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta wuce ta shige toilet ta yi alwala sannan ta fito amma koda ta fito ta tarar baya nan har ya fice.

Tana kambala sallah ta fito ta nufi kitchen domin sama masa abincin da zai taɓa kafin ya fita wanda bata sani ba ko sammako zai yi kaman yanda ya yi a ranar da za su tafi Abuja.

Tana shiga ta ga komai an zube shi na amfani wato ya ma shirya kenan akan za ta dawo.

Aikin ta ta shiga yi a hankali wanda tana yi tana ta tunani iri-iri wani mai amfani wani kuma marar amfani. Tana nan ta ji Phone Vibration wanda ta ɗauki tsawon lokaci ta na ji ba tare da an daina ba.

Fitowa ta yi sai ta hango wata waya keypad ajiye a ƙarƙashin throw pillow dake kan one seater.

Matsawa ta yi ta ɗauki wayar ta shiga kallon sunan da ke kan screen ɗin wanda har yanzu ake ci gaba da kira ba tare da an daina ba.

"My Maami..."

Sunan da ta gani kenan ya yi appearing wanda take ranta ya bata cewa wannan ɗin wata ƙila mahaifiyarsa ce.

Ta ɗauki lokaci mai tsayi tana kallon kiran sannan daga ta ajiye.

Sai da ta kai bakin ƙofan kitchen ɗin sai kuma ta juyo ta dawo ta sake ɗaukan wayan tare da receiving a darare ta kara ta a kunnunenta cike da mamakin dalilin irin wannan kiran hakan.

"Maheer!...Hlo Maheer are you hearing me?.....Abiyh was on admission tun around 2am and his condition is getting worst this time around..."

Wannan shi ne sautin da ya shiga kunnuwanta wanda ta ji muryar wata Mace wacce bata san kowace ce ba.

A hankali ta kai hannu ta yanke kiran tare da shiga ta goge amsa kiran da ta yi sannan ta ajiye ta a yanda take ta koma kitchen da sauri ta ci gaba da aikin da take.

Shi kuwa yana can masallaci bai dawo ba sai da haske ya ɗan fara sannan ya shigo shaf-shaf ya wuce ɗakinsa ya shiga neman wayar wanda sai daga baya ya tuna cewa tana parlour tun daren jiya sannan ya dawo ya ɗauka. Miss calls ɗin Maami su ne abin da ya gani rututu wanda ba shiri ya kira ta hankalinsa a tashe.

"Maheer wai miye abinda yake damunka ne a 'yan kwanakin nan? Yanzu ba daman mutum ya kira ka sau ɗaya ka yi picking dole sai ya yi ta kira sannan za ka ɗaga? Your attention was derived away by something else wanda ban san mine ne ba..."

"I'm sorry Maami! Koda kike kirana ina masallaci sai yanzu na dawo..."

Cike da ɓacin rai ta dakatar da shi da faɗin.

"Ko daren jiya na yi maka almost 5miss calls but no response..."

"Please Maami I'm sorry, in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba, kin san lokaci kaɗan ne ya rage na kambala assignment ɗina so I'm working so very hard ta Yanda zan kambala komai na cikin tsari da ma'ana. Shi ne kawai, but bayan wannan babu wani abu kuma... "

Yana jiyo sautin yanda ta sauke ajiyan zuciya a hankali sannan ta ce.

"Shikenan! Allah ya taimaka ya bada sa'a, Allah ya taimake ka ya sanya albarka a cikin wannan aikin."

"Amin Maami. Good morning..."

"Good morning! Daman Abiyh ne aka yi admitting na shi around 2am Kuma condition ɗin masa har yanzu sai a hankali.."

Ido ya zaro a hankali ya ce.

"Subhanallah! Baya shan maganinsa ne ko me?"

"Yana sha daidai kuma akan Lokaci,Allah ne ya kawo masa wannan ɗin."

"Allah sarki! I wish him speedy recovery..."

"Amin yah Allah, thank you."

"Ahm...I'm sorry Maami, kwanakin nan ina da ayyuka sosai wanda bani da wata daman da zan ɗaga na bar su, but In sha Allah zan zo idan na samu chance.."

"Ba damuwa, ai daman idan aski ya zo gaban goshi yafi zafi. Allah ya taimaka ya nuna min kambala ka dawo gida wallahy hankali sai yafi kwanciya."

Cikin faɗuwar gaba ya amsa da Amin Maami amma kuma can ƙasan ransa Anaam ce kawai yake tunani. Har yanzu bai hasaso yanayin ba sai yanzu da Maamin ta furta masa waɗan nan kalamai.

Lokaci kaɗan ne ya rage masa ya kambala, ta yaya ta ina zai fara?

Jin yanda hankalinsa ya tashi yasa ya yi saurin kawar da wannan tunanin a cikin ransa ya wuce direct ya yi wanka ya shirya ya fito ya shiga ɗakinta. All his thoughts tana nan tana bacci,amma kuma sai ya tarar bata nan hakan yasa ya fito ya tarar da ita a dining area tana gyara tana arranging table ɗin.

Fuska ba yabo ba fallasa ta ɗan kalle shi cikin shirinsa na uniform wanda yake ƙara fito da shi a kullum ta ce.

"Good morning..."

Murmushi ya yi tare da jinjina kansa ya ce.

"Good morning,...Ahm..na ɗauka kina bacci ne?"

Girgiza kai ta yi ta ce.

"A'a. Nasan za ka fita da wuri shi ne nace bari na sama maka wani abun.."

Zaunawa ya yi cikin nuna farin ciki ya ce.

"Thank you so much."

Ciki ta koma ta yi wanka ta shirya cikin wani material doguwar riga da hula ta fito wanda hakan ya yi daidai da tashin sa domin wucewa.

Kallonta ya yi daga sama har ƙasa yana murmushi ya ce.

"Komai kika saka yana miki kyau."

Shiru ta yi tare da kawar da kanta daga barin kallon shi sannan ta ji ya ce.

"Zan tafi Base Maryam. Ina da meeting idan muka gama training, but in sha Allahu zuwa 3pm zan dawo."

"Allah ya tsare ka ya bada sa'a ya kuma dawo da kai lafiya."

"Amin Ya Allah, na gode."

A nan suka yi sallama ba tare da ta rakashi zuwa waje ba kaman yanda ta fara a can baya. Yana fita ta zauna taci abinci sannan ta ɗauko wayarta inda itama ta tarar da miss calls din su Ammie da Su Na'ima da yawa wanda sai daga baya sannan ta bi su ta kikkirasu.

Bayan ta gama ta koma ɗaki ta kwanta a hankali maganganun wannan matar wacce ya rubutawa Maami suna dawo mata. Wace ce Maami? Mahaifiyarsa ce ko waye? Waye kuma Abiyh?

Tambayoyinda ta shiga yiwa kanta kenan na tsawon lokaci wanda tasan cewa ko kwana za ta yi tana tunani ba za ta taɓa samun wannan amsar ba sai dai idan ta tambayeshi domin shi ne kaɗai wanda zai iya warware mata wannan.

Da wannan ƙudurin a ranta ta zauna tana ta saƙa irin tambayar da take so ta yi mai, sai yanxu ne ma take na damar miyasa tun farko ba ta tsaya ta yi copying number matan ba? Shirme da yaranta. Ta faɗawa kanta tare da miƙewa taje ta yi masa girkin rana mai rai da motsi sannan taje ta yi wanka ta shirya cikin wata Atamfa riga da skirt masu bala'in kyau ta zauna zaman jiran shi.

             ✍️ OUM-AMEER ✍️