DUHUN DARE

PAGE 55

by @oumameer2671

D U H U N D A R E

A 2026 N O V E L

BOOK ONE

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHEEM

OUM-AMEER

Arewapen: @Oumameer2671

Wattpad: @Ummu-Amir

BOOK ONE

PAGE 55

Katse kiran ta yi jin da gaske Yaa Na'ima neman ƙara mata zafi take akan wanda take ci sannan ta kai hannu kan lips ɗinta tana shafawa a hankali abinda ya faru a tsakaninsu na ƙara dawo wa a ƙwaƙwalwarta. Haƙiƙa wannan abin ya shige ta ba ka ɗan ba. Ji ta yi gabaɗaya duniyar na juyawa da ita.

Daga jiya zuwa yau abubuwa da yawa sun faru waɗanda suka bata mamaki kuma suka sanyata jin cewa Maheer wani mutum ne na daban. He's very gentle and nice also.

Kamar yanda yace yana sonta tabbas itama a yau soyayya ta ke ji, soyayya take jin tana yi masa ta musamman. Yanayin da take ciki daga jiya zuwa yau ta tabbatar mata da cewa yafiye mata lokutan baya farin ciki wanda take ji a ranta cewa ina ma ace lokaci ya tabbatar da su haka? But hakan tasan cewa ba zai faru ba because yanayin aikin nan nasa yana ɓata mata rai a halin yanzu.

Wani tunanin na daban kuma zuciyarta ta ɗarsa mata na cewa ko yana ina a yanxu? Miye yake yi? Oho!

Tana nan tana ta tunani iri-iri ƙarshe taje ta kunna TV ta zauna tana kallo ko za ta samu ya rage mata kewar da ke damun zuciyar ta.

Tana nan har sai da lokacin sallah ya yi sannan ta tashi ta shige ta yi sallah. Tana kambalawa kiran Friendy ɗinta ya shigo wayanta. Tana ɗagawa ta ce mata tana bakin gata. Da kanta taje ta shigo da ita Na'ima Hassan sai santin ta take tana cewa ta canja sosai ta yi kyau.

Suna shiga Friendy ɗin ta kalle ta ta ce.

"Result Alhamdulillah! Have you checked yours?"

Dariya ta yi ta girgiza kanta ta ce.

"Ina fa,ba abin da na duba, har Yaa Mubarak nace ya karɓi details ɗina ya dubamin yace ba zai yi ba kinsan halin sa..."

"Bari mu dub..."

Saurin dakatar da ita ta yi ta ce.

"No! Kada ina zaune zaman jindadina ki ɗaga min hankali..."

"Wane irin ɗaga miki hankali nima fa na duba."

"To ke kika ce, ai ke kinsan abinda kikayi to ni fa?"

Jinjina kai friendy ta yi ta ce.

"In sha Allahu ma you made it, I trust you."

Wata dariyar Anaam ta yi sai kuma ta ja hannun ta ta ce.

"You trust who? Abeg zo muje mu ci abinci muyi firarmu, bana son zancen school ki bari sai jibi idan mun koma. Ya Mum da Pa?"

"Lafiya lau suke Alhamdulillah, sun ce in gaishe da ki."

"Allah sarki na gode. Ina samarin ki?"

Taɓe baki ta yi ta ce.

"Babu, kema kin san ba bu.."

"Uhm! Wai ke haka za ki yi ta zama?"

"Noo! Ba haka bane, ban isa dai yanzu a 100level ba in kai wani gidanmu, Pa zai kashe ni ina faɗa miki, but zuwa 300level to 400level wannan duk zan iya ya yi."

"OK, Allah Ubangiji ya baki nagari amin. Ni ma fa ƙa'idan Abbah a can baya ba zai aurar damu ba sai mun gama degree, to sai gashi kana naka Allah yana shi, sai ga ƙaddararmu ta sauya daga ni har Yaa Na'ima..."

Firar su suka sha har zuwa ƙarfe biyar sannan drivernta ya dawo ya ɗauke ta suka tafi.

Tana nan ta cika ta batse akan rashin zuwan su Yaa Na'ima kawai ta ji sallamansu. Koda ta fito kamar daga sama ta ga Abbah, Ammie, Yaa Mukarram da matar shi da yaran su, Yaa Amina, Yaa Na'ima, Sannan kuma da Rabi'a.

Cikin ihun murna taje ta maƙalƙale Abbah tana dariya tace.

"Welcome all...welcome...Abbah.."

Muryarsa ta ji yana faɗin.

"Anaam kada fa ki ƙalla min wuyana.."

Dariya suka fashe da ita sannan ta sauka ta shiga gaishe su ɗaya bayan ɗaya, da ta kai ga Rabia ta ce.

"Welcome...ashe kin dawo?"

"eh, sannu da zuwa, an ce kema jiya kika dawo?"

"yeah..."

Parlour ta kai su sannan ta kira Kudirat ta ce ta kawo musu ruwa da komai sannan ta shirya musu abinci. Kallon ta Abbah ya yi ya ce.

"Maryam na ji kina cewa a shirya abinci, yanzu fa za mu koma..."

Wani irin marairaice fuska ta yi ta ce.

"Kai Abbah dan Allah..! Gaskiya kuna nan sai kunci abinci sannan, ai baku taɓa cin abincin gidana na... Ammie dan Allah ki ce ya tsaya kada ya tafi."

Dariya suka fashe da ita sannan Ammien ta ce.

"Muna nan Auta sai mun ci abinci kin ji ko? Ina mijin ki?"

Kallon Yaa Na'ima ta yi sai kuma ta sake kallon Ammie ta ce.

"Ya koma ɗazu da safe."

"okay. Allah ya taimaka ya bada sa'a."

"Amin amin."

Fira suka sha wanda saida suka ci abinci sannan suka tashi zuwa salloli, a ɗakin da ta kai su Yaa Amina ta tsaya ta yi sallah inda a nan Rabi'a ganin babu wanda ya yi zancen aurenta har suna batun tafiya sai ta ciro IV daga bag ɗinta ta miƙawa Anaam ɗin tana faɗin.

"Kamar baki san da zancen aurena ba ko? Ga kati, saura 2weeks yanzu.."

Hannu Anaam ta saka ta karɓa ba tare da tace komai ba.

"Kina da labarin cewa Faris zan aura? Ɗazu ma ya tura min 5M domin na fara business idan mun yi aure kin san Baba ya hanani karatu..."

Idon ta ta ɗauke daga katin ta zuba su tana kallonta kamar yanda su Yaa Amina su ma suka shiga kallonta cike da tsantsar mamaki da al'ajabi.

Ganin kaman zancen ya ɗan girgiza su yasa ta saki wani murmushi cike da gadara ta yi wani war-war da ido tace.

"Yaa Amina shin duk kuma baku da labari ko? Wallahy ɗazun nan ya turo min su. Lefena ma yana hanya."

"Allah ya sanya alkairi..."

Abinda Anaam ɗin tace kenan tare da miƙa mata Invitation Card ɗinta.

"Sai naga kaman baki yi farin ciki da wannan labarin ba Anaam..."

Wata irin tsawa ce Na'ima ta daka mata tare da yi mata wani kallo cike da takaici ta ce.

"Wai Rabi'a miye haka? Wane irin iskanci ne wannan?"

Itama Yaa Amina girgiza kanta ta yi  ta ce.

"Rabi'a bakya son zaman lafiya a rayuwa. Ta ya za ki iske mata har cikin gidanta kice za ki ci mata fuska."

Aunty Aysha ta karɓe da cewa.

"To miye ma zai sa Anaam ta nuna rashin jindadi tun da ba saurayinta ba ne, abu ɗaya zai sa in yarda da zancen ki shi ne za ki auri ɗan mutumin da baya son iyayenki yake neman ganin bayan su...mutumin da ya sace yayanki, ya cutar da 'ƴar uwarki da ahlinki ai dole ta yi baƙin cikin za ki aure shi..."

Turo ba ki ta yi tana mai jin haushin kalaman Aunty Aysha ta ce.

"Aunty Aysha baku da wata hujja akan hak..."

Ji ka yi Tas! Na'ima ta ɗauke ta da kari wanda sai da ta bawa kowa mamaki a ɗakin sannan ta ce.

"Waye za ki yi wa rashin kunya a nan wanda yake tsaran ki?"

Girgiza kai Anaam ta yi ta ce.

"Ai da ba ki mare ta ba Yaa Na'ima. Ki bar ta indai surukuta da Alhaji Gimba ne za ta gani ga ƙwaryar shanta.."

Tana dafe da kunce ta cika ta batse tamkar za ta fashe ta ce.

"In ga Alheri wallahy. Kuma wallahy Yaa Na'ima wannan ya zama shi ne na ƙarshe domin wallahy idan kika sake marina daga yau zan baki mamaki."

Daga haka ta wuce ta fice gabaɗaya taje jikin mota ta tsaya, daman Abbah yace daga sun gama sallah za su wuce.

Ajiyan zuciya mai ƙarfi Na'ima ta sauke sannan ta ce.

"Rabi'a har abada ba za ta yi hankali ba..."

Yaa Amina ta ce.

"Namiji ne kuwa zai gyara mata zama."

Khalipah Anaam ta saɓa a Kafaɗanta suka fito suka tarar da su Ammie daga nan ta rakosu har bakin mota cike da kewa ta yi musu sallama. Babu wanda ya koma kan Rabi'a har suka bar gidan.

******

Cikin azama Hajiya Salamatu ta fito parlour inda Ramatu mai aikin ta tace Faris ya shigo yana can zaune a parlour ya ce ta zo.

Wani kallon ta bishi da shi na tsawon lokaci wanda shi ko a jikinsa. Bayan ta gama kallon shi da kyau ta gane shi ɗin ne dai ba wani ba kawai ta hau shi da masifa abinda bata saba yi ba. Faɗa sosai ta yi mai sannan daga ƙarshe ta ce.

"Ni ma na goyi bayan mahaifinka ba za ka auri Rabi'a ba..."

Hankalinsa a kwance ya kalle ta yana girgiza kai ya ce.

"Mum ki daina biye mijinki. Yanzu dan Allah time ɗinda ya auro wannan yarinyar mu a son ranmu ya auro ta? Yarinya fitsararra haka ya auro ta ta yi ta wulaƙanci tana haɗamu da shi kuma muka yi haƙuri shi ne ni zan yi aure saboda kawai wani son rai na shi na banza yace ba zan aure wacce nake so ba... "

" Faris... "

"Mum sai na auri Rabi'a...ga Invitation card nan ki raba Mum idan za ki raba, amma dole zan auri Rabi'a..."

Maimuna dake laɓe tun shigowan Hajiya Salamatu tana sauraren su ta koma ciki ta iske Alhaji Gimba dake kwance yana baccin safe ta tashe shi ta ce.

"To sai ka tashi Alhaji. Ga Faris can ya shigo yana ta faɗin maganganu marasa daɗi yana zaginka yana faɗin wai kai baka isa ka hana ya auri wacce yake so ba, ko kamawa ta yi ya yanke alaƙa da kai zai yi hakan matuƙar barunsa zai cika. Sai wasu irin maganganu yake babu daɗin ji.."

A ƙufule ya ce.

"Waɗan ne irin maganganu ne yake faɗi Maimuna? Don Allah ki faɗamin.."

"A'a Alhaji. Wace ni ace na haɗa ka da iyalinka. Yana nan a main parlour kaje ka jiyewa kunnenka."

Zuruf haka ya diro tare da janyo jalabiyarsa ya zura ko takalmi bai saka ba ya fito.

Ta bayansa Faris ya jiyo taratsin Daddyn nasa tamkar zai tayar da gidan yana masifa yana ƙarawa yana faɗin.

" Faris ni za ka kunyata? Ni za ka nunawa duniya cewa ban isa ba? Shi ne kaje ka saka wasu waɗanda ban haɗa komai da su ba akan su shige gaba wurin nema maka aure?"

Lumshe idanun sa ya yi ya buɗe a hankali sannan ya girgiza kai ya ce.

"Daddy..."

Hannu ya ɗaga masa da sauri yace.

"Ka yi min shiru! Bana son jin komai daga gareka. Ka janye maganar Auren Rabi'a ka je gidan Alhaji Hamza Salmu 'ƴar sa na nan Ruƙayya yace ya baka ita..."

"I'm sorry to say Daddy....Ni ba ita nake so ba Rabi'a nake so."

"Haka ka ce Farisu?"

"I'm sorry Daddy.."

"Shi ke nan! Shi ke nan Farisu kaje tunda ɗiyar maƙiyana ka zaɓa kaje babu ni babu kai har abada, ka manta cewa ka taɓa sanina a matsayin mahaifi a rayuwar ka..."

Hannu Hajiya Salamatu ta ɗora aka ta fashe da wani irin kuka tace.

"Wayyo Allah ni Salamatu na shiga uku na lallace! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Alhaji miyasa za ka biye shi dan Allah?"

Cikin fushi ya wani kalle ta yace.

"Hajiya Salamatu idan kika sake kiran ko sunan Faris a cikin gidan nan wallahy tallahy a bakin aurenki kin ji na rantse...ya tashi bar min gidana."

Hannun Faris ɗin ta riƙo a gigice ta ce.

"Wai kai Faris wace irin zuciya ce take cikin ƙirjinka? Yarinyar nan tunda ba 'ƴar gwal bace ka haƙura mana kaje ka nemi Ruƙayya. Faris kana iya canja mata amma ba za ka iya canja mahaifi ba. Don Allah na roƙeka ka daina duk wannan..."

Fisge hannunsa ya yi ya miƙe kawai ya fice daga gidan.

Komawa tayi daɓas akan kujera ta zauna ta ci gaba da rusa kuka yayin da Maimuna ta shiga ba ta wani haƙurin gulma amma can ƙasan ranta farin ciki ne kamar ya kashe ta.

Tana ganin Alhaji Gimban ya koma ciki ta zauna a gefenta tare da ɗora hannun ta a Kafaɗanta murya a ƙasa ta ce.

"Hajiya kiyi haƙuri, in sha Allahu wannan duk zai wuce. Kin san mu yaran zamanin nan idan muka kafe, amma don Allah ki kwantar da hankalinki tunda Rabi'ar ita yake so ki bar shi ya aure ta, Alhaji in sha Allahu zai sauko, kema kin san ba zai iya rayuwa idan babu Faris ba..."

Haka dai ta yi ta ba ta magana kaman da gaske har ta samu taji zuciyarta ta yi sanyi.

      ✍️  OUM-AMEER ✍️