FARASHIN IZZAH

Chapter 3

by @hauwajaywrites

Book 1 
Chapter 3

....Sun fi minti biyar a haka, kowa da abin da ke saka wa a ransa. Kawai wayansa yayi ringing. Kallon bed side drawer yayi inda wayan nasa yake. Ga mamakinta, zareta yayi a jikinsa ta tsaya tana kallonsa har ya karasa wajen wayan. Satan kallonta yayi ta gefen ido kafin yayi receiving call ɗin.

Shi dai banda amsa da yake bayarwa ma wanda suke waya da “Eh, uhm, okay,” kawai yake cewa, sannan ya kashe kiran ya ajiye wayar.

A hankali ta ce, “muje mu ci abinci ko? Ko fita zamuyi?” Tayi hakan ne ba wai don yunwa take ji ba, kawai dan ta samu lokacin sa, ta jasa da magana har ta fahimci meke faruwa.

Kallon agogon taga yayi, sannan ya kalle ta yace, “I’m full.” Zata sake magana taga yayi hanyar toilet.

Ta karasa jikin gadon ta zauna, ta kurawa wayan nasa ido. Can sai gashi ya fito. Suna haɗa ido ya sakar mata da murmushi. Bata san sanda ta langabar da kai ba tana kallonsa itama da murmushi.

Bayan ya gama shiryawa, taga kayan da zai sa. All what she thoughts pajamas zai saka, sai kawai taga ya sanya jamfa da hula. Wani irin bugawa zuciyarta yake yi.

Ta bata rai sai daya gama shiryawa saf sannan ya nufa wajen wayansa zai ɗauka. Ta sha gabansa da sauri tana masa wani kallo tace, “ina zaka je kuma a daren nan?”

Ya ɗaga mata gira ɗaya yace, “baki ji ana kiran Isha’i bane?”

Ta sauke ajiyar zuciya, amma ba wai hankalin ta ya kwanta bane. Taja baya tana kallonsa. Yace, “bari na tafi masallaci.”

Ta kasa ce masa komai har ya fita. Ta dade zaune tana sake-sake a rai. Jin har an idar da sallah yasa ta miƙe taje tayi alwala. Tana cikin sallah taji karan fitar motarsa. Har mancewa tayi tana sallah, bata san sanda ta fashe da kuka ba.

A haka ta samu ta idar da sallahn. Yanzu kam ta gama jin ta tsane Ibrahim. Tunanin abin daya fado mata rai wanda kullum take kokarin nesanta sa da zuciyarta ne ya faɗo mata. Hakan yasa ta sake fashe wa sosai da kuka, har da shesheka.

Ta jingina da gadon tana tunani. Wannan wani irin masifa ce? Mutum babu soyayya, babu kalamai masu dadi, babu zama da miji ayi hira da wasa. Bashi da lokacin ta, baya dawowa gida da wuri sai passed 12 na dare. Idan ya dawo kuma da wuri sai yayi wannan fitan. Babu sannu balle madallah.

Toh ita bata ga amfanin wannan auren nata ba. At this point tana jin zata iya hakura da shi dan taga ta fara ɗaurawa kanta damuwa.

Tuna wacece ita a social media yasa jikinta yayi mugun sanyi. A hankali tace, “Allah ka taimake Ni, ka sassauta min abin da nake ji a raina. Allah kana gani bana son na kawo wani 3rd party a maganar nan.”

Karan ringing ɗin wayarta ne ya katse mata tunanin data ke yi. A hankali ta kai hannu ta ɗauka. Mami taga take kiranta. Sai data daidaita kanta sannan ta daga kiran.

A hankali ta ce, “Mami.”

Mami tace, “Na’am, kun koma gida lafiya?”

Tace, “lafiya lau Mami.”

Sai tayi shiru.

Mami tace, “Baby meke damunki? Tabbas nasan akwai abun dake damunki dan ba haka kike ba da.”

Tayi shiru dan da gaske kuka ne ke son taho mata. Ta daure tace, “Mummy babu komai fah, ki yarda dani. Kawai bana jin dadi ne kwana biyu.”

Shiru taji mamin ta mata. Tasan kuma Mami ba zata sake cewa komai ba, dan Mami haka rayuwarta yake da uban miskilanci musamman idan tasan karya kake mata, bata kuma cewa komai.

Kittt… kawai taji alamun ta kashe wayan.

A hankali ta zare wayan a kunnenta ta ajiye wayan a gefenta. Tace, “Khalil wani irin rayuwa kuma kake son jefa Ni? Ka taimaka min ka dawo Ibrahim Khalil dana sanka.”

Wani ringing ɗin tayi. Ta dauka sai taga Firdausi ce. Ta dauka.

Bayan sun gaisa, Firdausi tace, “Nagode sosai Zahra, Allah ya saka da Alkhairi ya...”

“Its okay Firdausi,” Zahra ta katse ta. “Ai yiwa kai ne. Ni da ke ai mun daɗe da zama daya, so bana son wani godiya.”

Tace, “Tohm, ga Mama zaku gaisa.”

Zahra tace, “toh bata.”

Bayan sun gaisa, ta mata ya jiki. Tace da sauki. Tace, “ya me gidan naki?”

Zahra tace, “lafiyansa kalau Mama.”

Tace, “Tohm Allah kara hada kanku ya baku zuriya nagari.”

A hankali tace, “Amin Mama na gode.”

Daga haka suka yi sallama. Bayan Mama ta mikawa Firdausi, Zahra tace, “In Shaa Allah gobe zan shigo na duba Mama.”

Daga haka suka yi sallama.

Ta miƙe ta naɗe sallayan ta sauka kasa ta haɗa tea tasha. Ta daɗe zaune a parlorn ga wuta amma ta kasa ko kunna TV ne.

Ta mike ta wuce daki ta canza kayanta zuwa sleepwear. Ɗaukan wayanta tayi ta wuce gado da shi. Ta shiga media account dinta duk da lots of comments da messages bata jin zata bi takan ko ɗaya.

A haka bacci ya ɗauke ta.

"Can a cikin baccinta taji ana buɗe gate. Ta buɗe idonta a hankali ta dauki wayan gefenta ta kalli lokaci. Murmushi takaici tayi ganin har 12:20am.

Ta miƙe taje ta buɗe curtains taga yayi parking amma still yana cikin motar yana danna danne a waya. Ta kura masa idanu duk da ba wai sosai take ganinsa ba. Ya sauko yana tafiya irin ta kasaita.

Ta koma ta kwanta. Can taji yaje ya buɗe kofar dakinsa ya shiga. Taji hawaye mai mugun zafi ya sauko zuwa kuncinta.

A haka har taji ya buɗe nata ɗakin ya shigo. Alama dai acan yayi wanka ya canza kaya. Tana ji ya kashe wuta ya kwanta. Ji tayi kamar ta tashi ta bar masa dakin.

A ranta tace tasan me zata masa gobe. A haka har bacci ya ɗauke ta.

Washegari da safe, bayan ta gama breakfast ko takansa bata bi ba, ta zauna tana nata breakfast ɗin. Sai gashi ya sauko daga sama alamar ya gama shiri.

Ya ce, “Baby kin gama breakfast din shine ba zaki min magana ba?”

Ta share sa.

Yace, “yau kuma da wulakanci kika taso ne? Ko gaisuwa kina jin kinfi karfin ki gaishe Ni?”

Har sannan bata ce masa ci kan ka ba.

Ya karaso dinning ɗin ya zauna yayi serving kansa a plate ya fara breakfast. Duk idanunsa yana kanta amma ita ko da wata taki yarda ta kalle sa.

A hankali ya kamo hannunta cikin nasa yace, “Baby…”

Sai sannan ta masa wani banzan kallo.

Yace, “haba mana sweetie wai menene?”

Ta kwace hannunta tace, “idan baka daina kira na da sweet names ba zaka sha mamaki.”

Da mamaki yake kallonta.

Ta miƙe tsaye zata bar wajen.

Yace, “shikena Tohm, but kar ki manta anjima zamu fita.”

Wani irin murmushi tayi mai wuyar fassarawa sannan ta wuce sama.

Yana gama breakfast ya dauki briefcase ɗinsa ya fita.

Bayan ta fito a wanka tace, “zaka sha mamaki na Khalil.”

Shiryawa tayi saf cikin lace. Ta fito a ainihin Zahran ta, the beauty personified.

Ta dauki handbag ɗinta ta sauka kasa. Direct wajen motar ta ta wuce ta shiga. Ta kunna sannan ta bar gidan.

Bata tsaya ko ina ba sai gidansu Firdausi.

A kofar gidan tayi parking sannan ta sauka ta shiga da sallama a bakinta.

Brothern Firdausi Abdul ne a compound din yana wanke kayan Mama. Ya daga kai yana kallon Zahra da murmushi yace, “Anty Zahra sannu da zuwa.”

Tace, “Sannu Abdul, ya gajjiya?”

Yace, “Alhamdulillah.”

Tace, “ya jikin Mama kuma?”

Yace, “da sauki, ki shiga suna ciki.”

Daga haka ta karasa bakin kofar dakin.

Mama tace, “Zahra’u shigo mana.”

Ta shiga tana murmushi ta zauna ta gaishe ta tare da mata ya jiki.

Sai ga Firdausi ta fito tana murmushi tace, “Tauraruwa karaso mana.”

Zahra ta miƙe tana dariya tabi bayanta zuwa dakin Firdausi.

Bayan sun zauna Zahra tace, “nikam hope jikin Mama da sauki.”

Tace, “chap da sauki sosai fah, sai dai yanzu kam muce Alhamdulillah.”

Zahra tace, “ai yayi kyau toh.”

Zahra ko harda bacci sai can bayan Azahar Firdausi ta tashe ta tayi sallah. Bayan ta idar suka ci abinci.

Wasa wasa dai Zahra ta kusa wuni a gidan tun safe.

Suna hira can Firdausi tace, “Zahra kiyi hakuri zan miki kasalanda a rayuwar ki nasan ba lallai ki so ba.”

Zahra tace, “bana son iskanci yau Ni ɗin har wata bakuwa ba zama a wajenki.”

Firdausi tayi murmushi tace, “kin san zuciya fah bata da kashi.”

Zahra tace, “Ni dai ina jinki.”

Firdausi tace, “kina cikin damuwa ne Zahra? Kinga yadda kika koma?”

Zahra tayi shiru.

Firdausi tace, “don Allah kar ki boyemin komai Zahra, kin san ba zan taɓa fitar da sirrinki ba. Ki tausaya kar kisa Ni cikin damuwa da tunani.”

Zahra ta sauke ajiyar zuciya tace, “Firdausi banda ke ban taɓa fada wa wani ba. Babu wanda yasan halin da nake ciki. Amma tabbas ina cikin damuwa mai tsanani.”

Firdausi tace, “SubhanAllah, don’t tell me tsakanin ke da mijinki ne?”

Tace, “tabbas Firdausi, nayi dana sanin auren nan. Idan kinga naga Khalil a gida toh cikin dare ne ko kuma da asuba. Amma kwata kwata ya canza. Babu magana mai daɗi, babu lallashi, babu bani lokacina. In takaice miki yadda kika san Ni ba matar sa bace haka ya ɗauke Ni.”

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un,” Firdausi ta dinga maimaita.

Tace, “tabbas Zahra wannan abun damuwa ce. Ba zan iya kuma ce miki kala ba yanzu, har sai nayi tunani mafita.”

Zahra ta sauke ajiyar zuciya.

Khalil banda trying number Zahra da yake yi babu abinda yake yi. Ya kira yafi sau hamsin. Tun karfe biyu ya dawo gida amma yanzu karfe 4 babu Zahra a gida.

Damuwarsa ya sanar mata zasu fita amma ta kama tayi tafiyarta dan ta bakanta masa rai. Babu abinda bai saka a ransa ba, sai uban zufa yake haɗa wa.

Firdausi tace, “dan Allah Zahra ki tashi ki koma gida. Kinga kar yazo bai ganki ba ku sake samun wani issues ɗin.”

Zahra tayi shiru tana kallon wani waje.

Can tace, “Firdausi ba zaki gane bane naji na tsane rayuwar gidan ma gaba ɗaya.”

Firdausi ta ce, “please ki daure ki tafi. Na miki alkawarin gobe zan shigo.”

Sai sannan Zahra ta miƙe ta fara shirin komawa gida.

Bayan ta gama ta fito Firdausi ta raka ta taje ta ma Mama sallama sannan suka fita waje har jikin motar Zahra.

Zahra tace, “toh Nagode Firdausi, ina jiranki gobe ɗin ko?”

Tace, “In Shaa Allah zan shigo. Ni dai damuwa ta bana son kina saka damuwa a rai har kina ramewa kowa ya fara magana.”

Ta ce, “Tohm shikenan zan rage.”

A haka suka yi sallama. Zahra ta ja motar ta tayi gida.

Tana parking ta sauka. Wani farin ciki taji ganin motarsa a parke. Ta tabbata ya neme ta bai sameta ba.

Tana shiga parlorn ta gansa tsaye ya haɗe fuska kamar ba shi ba.

A ɗan fusace yace, “ke daga ina kike?”

Tace, “calm down Malam, ka rage murya kamin magana cikin sanyin murya dan kasan na taso cikin gata ba’a min ihu akai.”

Ya sake baki yana kallonta yace, “wai wa kika ɗauki kan ki ne?”

Ta ce, “Fatima Zahra tauraruwa wacca ake tururuwa akanta har ta faɗa tarkon maciji.”

Wani kallo yake mata yace, “look Zahra baki isa ina faɗa kina faɗa ba. Ya kamata kisan da wa kike magana. Sannan ki faɗa min da wa kika tambaya kafin kika fita.”

Ta sake baki tana kallonsa tace, “kamar yadda kake da right na fita at anything kuma ka dawo duk lokacin da kaga dama toh hakan Nima take.”

Wani ihu yayi wanda har sai data tsotsa yace, “kar ki gaya min maganar banza mana! Dama naga take takenki ke da wannan banzan Yayan naki mara tarbiyya har yake wani rike miki hannun kuna sauka a stairs yana jin daɗi, nasan akwai wani abu!”

Zahra tace, “auzubillahi, lallai yau na tabbatar Khalil kana da ƙarancin ilimi. Yayana ubanmu ɗaya dan ya riƙe Ni har zaka iya kawo wani abu ranka? Lallai abin naka yayi nisa.”

Suka dinga exchange words.

Can ya buga wani cup yayi zuciya ya fita daga parlorn.

Parking space ya tafi ya buɗe motansa ya shiga yayi dialing numbern wata. Tana ɗagawa yace, “ina son mu haɗu nan da 30mins. Babe kiyi wanka na kece raini, zan zo zan ɗauke ki zaki raka Ni wani waje ne.”

Tace, “Babe…” Yace, “uhum.”

Tace, “meya faru naga ranka a bace?” Yace, “kinji abinda na fada miki?”

Tace, “eh naji, waya bata maka rai?” Yace, “ki bari sai mun haɗu.”

Daga haka ya kashe kiran.

Ya lumshe idonsa, kawai sai ga fuskarta ta bayyana masa. Da sauri ya buɗe ido. Ya manta cewa ba zata iya masa abin da Zahra zata yi ba. Bata da komai...ba kyau ba, ba iya turanci ba, a haka zata fitar da shi a kunya?

Kai, gaskiya da sake… wannan sai Zahra don duk Zahra ta haɗa wadannan qualities ɗin.

Haka ya sauka a motar. Ya gwammaci yaje ya bawa Zahra hakuri, koma me zai faru su shirya. Ta taimaka su tafi tare.

A haka ya nufi hanyar cikin gidan."


#Jiddatulkhayr writes 
#***