HADIN KADDARA

Chapter 17

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                     By

         AyshaNalado 


Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍


BOOK 1


Page  17


Ajiyar zuciya Aunty Rukayya ta sauke lokacin da aka ɗaga kiran, “Na'eemarh.” Ta ambata a sanyeye cikin taushi, “Na'am Mummy, ya aka yi ne?“ wata siririyar murya ta amsa daga ɗaya hannun a yangance. Jim ta yi tana tauna abin da za ta fadan tare da tunanin makomar fadar, nata, saihar sai da ta ji Neema ta saki ƴar karamar tsaki, kafin ta yi ta maza ta ce “ Ki yi hakuri Baby, abinda zan fada miki ba mai daɗi ba ne, an yanka ta tashi.” “ Ban gane ba Mummy, wa aka yanka? Mene ne ya tashi?” zuciyarta cike da shakkarta, ta daure ta sake cewa, “Maganarki da Ahmad tana tangal-tangal, yau General ke sanar min ya yi masa mata...”  “Kutumar babbar kaza kazan can!”  Neema  ta ja wata doguwar ashar cike da rashin tarbiya tana  miƙewa zaune daga kwancen da take, ƙanƙance ido ta yi cike da fitsara ta ce   “Mummy! Mummy! Mummy! So nawa na kira ki.” Aunty Rukayya da ke amsa duk kiran da take yi mata, a sanyaye ta ce, “So uku Baby.”  “Wallahi ba ku isa ba daga ke har mijinki kun yi ƙadan ku wulaƙanta ni, Ina son AA,  ina son na auresa kin fi kowa sanin hakan,  kuma wallahi tallahi ba zan taba hakura ba, ko sama da ƙasa za su hade sai Ahmad ya aureni, babu ruwana da yadda za ki yi, ni dai kawai ki aura min shi, idan kina buƙatar kwanciyar hankalina.” cikin rarrashi da kwantar da kai Anty Rukayya ta ce “ Na sani Na'eemarh, na san kina son Ahmad, wannan dalilin ne ma yasa na kira ki domin mu hada hannu mu yi wa tufkar hanci tun wuri, kin san ina son ki, kuma ina son duk abin da kike so, wallahi tallahi na fi ki son na ga kin mallaki  Ahmad, ba zan yi saken da za ki rasa shi ba,  ki kwantar min da hankalinki, in dai ina da rai da lafiya Ahmad zai aure ki, na yi miki alkawari.“ shiru kamar ba za ta sake magana ba, sai kuma ta fesar da numfashi  kafin ta ce “ Yanzu me ki ke so na yi?“  “ Ki dawo 9ja, ki matso kusa da Ahmad ki nemi kusanci da shi, ki bayyana masa soyayyaki, ta haka ne kawai zan iya cika miki burinki.“ “ Ai ko ba ki ce ba dama dole zan dawo, don wallahi tallahi duk wacce ta auri Ahmad ta auran ma kanta masifa, don haka maganin kar a yi kar ma a soma, ki saka idon ganina ko da yaushe cikin sati mai kamawa.” Murmushi Aunty Rukayya ta yi nan da nan farin ciki ya bayyana a fuskarta,  tana jin kamar ta janyo tilon yar Tata ta cikin waya ta rungume tsabar so da ƙauna, “ Mummy ina buƙatar kudi, account ɗina ya yi ƙasa. ” Muryar Neema ya dawo da ita hayyacinta,  gabanta ya faɗi domin cikin satin nan ta tura mata kuɗi masu kaurin gaske, amma saboda gudun ɓacin ranta, sai ta hadiyi miyau ta yi yar dariyar yaƙe cikin yanayin wasa ta ce,  “Kai Baby,  kina nufin har kudin ran nan sun ƙare?" “ E sun ƙare, ina buƙatar wasu, ko babu?” Yadda ta yi maganar cike da raini, amma sam Aunty Rukayya bata ga hakan ba, da sauri ta ce, “ No a kwai kuɗi baby, ba Ni minti biyu.“ tana gama wayar ta datse kiran a take a tsaye a inda take ta yi mata transfer na 2M, sannan ta sake kiranta, “ Oh thank you My lovely Mummy, Nagode Sosai i luv you so much.  Muahhh!  Ta sakar mata kiss a kunne daga haka ƙit ta kashe wayarta, ba tare da ta bata damar sake yin magana ba. Murmushi Aunty Rukayya ta yi tana bin wayar da kallo zuciyarta wasai domin kalaman Baby na karshe sun wanke duk wani damuwar da ta cusa mata na tatsar ta da take yi kamar shanuwar tatsa......



****************************


Tun a hanya AA ya kira Mother ya sanar mata da zuwansa. Daga muryarsa da yadda yake magana ɗaɗdaya Mother ta fahimci yana da damuwa, sai dai bata ce komai ba tunda gashi nan zuwa gidan nata koma mene ne za ta ji. Mikewa ta yi ta sauka ƙasa zuwa kitchen domin ta samar masa abinci, tunda bata san da zuwa nasa ba girkinta kadan ta yi ita da Suraj kuma ba wani na musamman ba ne, ta san ba zai so shi ba, sauƙinta ma tana da sauran fura, ta san shi zai fara nema kafin wani abin. Kai tsaye frizan da take ajiye masa damammiyar furan ta nufa, ta bude da nufin ta dauka ta gyara masa kafin ya iso, sai dai wajen  wayam, ko bowl ɗin babu a  balle ta saka ran samun ko ƙadan ne a ciki. Goshi ta dade cike da takaici tana mai jerowa Suraj addu'ar shiriya a zuciya, ta san dai shine ya dauka domin su biyu ne a gidan, baya da haka sai da ya tambaye ta, ta ce masa kar ya sha na Bunayya ne amma da yake shi mai kunnen ƙashi ne, ya shammaceta ya ɗauke, tun da ya mayar da ita kakarsa.  Ɗakinsa ta nufa a fusace  tana mita, domin ta kirasa ya zo ya je wajen Inna idan Allah ya taimaka a samu rogowar ajiya a wajenta, sai ta dama masa wani tunda tana da sauran kindirmo mai kyau a fridge,  yana kwance ya yi ɗaɗɗaya akan makekiyar gadonsa yana sharar bacci, daga shi sai yar boxes. ga bowl ɗin furan nan kife a tsakiyar ɗakin. Ɗakin ta shiga bi da kallo tana girgiza kai, ko ina a hargitse, kamar ba jiya ta ɓata lokaci mai yawa wajen gyara masa ɗakin ba, kayan cikin wardrobe kusan rabi a ƙasa, ga takardu ya barbaza wasu a kan gado wasu a ƙasa kar dardumar da ya yi sallah,  banda ledojin dangin su chocolate da ya sha ya zuzzuba su duk inda ya samu kofar toilet a bude, ga kofuna  da plate da ya ci abinci girgiza kai ta yi cike da taikaci,  “Oh ni  Asma'u wai ɗakin saurayi ɗan jami'a kenan kamar na ɗan goye saboda sakarci, zan ga ranar da za ka girma suraj.” ta kai karshen zancen tare da kai masa duka a baya, firgigit ya mike tare da banƙarewa yana sosa bayan idanunsa na sake lumshewa saboda barci. “Surajuddeen!“ Ta kira sunansa da karfi, da sauri ya ɗago shanyayyun idanunsa cike da barci ya zuba mata, sai lokacin ya kula da wanzuwarta a ɗakin, “ Mother!” ya faɗa yana wartsakewa da kyau, hararar ta ɓalla masa, kafin ta ce, “Wato da na hana ka daukar furan Bunayya jiya, sai da ka dauƙa din in yi abinda zan yi ko?” Da sauri ya girgiza kai, “ To ba zan yi komai ba, Allah ya shirye ka. Sai ka tashi ka shiga gidansu Maamah, ka tambaya min  Inna idan da ragowar ajiyar fura a wajenta ta bani, ga Bunayya nan a hanyan zuwa yanzu.”  kalamanta na karshe suka shi sauyin miƙewa ya fito daga gadon ya faɗa toilet, ya yi brush ya wanke fuska ya fito, a gurguje ya dauki jallabiya ya zura ya yi waje. Mother dake tsaye tana kallonsa ta girgiza kai, kawai ta fito to rufo masa kofar ta koma kitchen ta ji gaba da aikin gabanta kafin ya dawo.




Gida huɗu ne tsakanin gidansu da gidansu Maamah a cikin Estate, don haka bai yi wata doguwar tafiya ba ya isa,  akwai tazara mai yawa tsakanin gidansu Maamah da gidansu Suraj, ta wajen kyau da ababen more rayuwa, duk da tsari da zubin ganinsu ɗaya, sai dai gidan su Maamah ba gidan sama bane saɓanin na su Suraj wanda yana daya daga cikin manyan gidajen dake cikin Estate ɗin.

Tun daga bakin kofa ya fara rangaɗa sallama yana kiran Inna, Maamah dake kwance a doguwar kujerar falo ta mike zaune tana hararar kofa da jiran ya ƙasaro,  Inna kuma dake kitchen ta fito da sauri tana amsa sallamarsa. 

Dattijuwar Bafulatana kyakkyawa da ita, ta tarɓesa cikin tsananin fara'a. Shima da  fara’a ya ƙarasa kusa da ita ya ɗan risuna ya ce
“Jam na Inna?”  Murmushi fal fuskarta 
“Jam tan, Surajuddeen,” ta amsa da gangariyar fullancinta na  kwararrur ba irin tasa ta masu ci da karfi ba,. Ya sosa kai ya ɗaga kai alamar yana tunani , sannan ya ƙara  cewa,
“On jaaraama?” Wannan karon dariya sosai Inna ta yi kafin ta ce“Jam tan, alhamdulillah. A jaaraama, on?”
Shima dariyar ya yi cike da jin daɗin bai ɓace a gaisuwar ba yau kamar yadda suke yi kullum sai ta ci gyaransa, ya sake c wa 
“Jam tan, Alhmdlh Inna.” 
Inna ta girgiza kai cike da nishaɗi ta ce
“Ehee, lallai Surajudeen ya zama fulfulde . Ka yi kokari sosai, yaron kirki.”   “Laamiiɗo haala, a arii ɗum!” Maamah ta faɗa tana hararansa, juyowa  ya yi ya kalleta ba tare da ya game me tace ba, ya ce, “E ɗin.” Dariya su ka yi a tare ita da Inna don suna da tabbacin ya dai amsa ne kawai ba tare da yasan me ta faɗa ba. Sun ɗan taba wasa da Maamah kamar yadda suka saba matsayinta na kawarsa kafin ya isar da saƙon Mother.  “ Ayya, ai kuwa babu furan nan Surajo, yanzu dai na ke yi, ka gansi  can a turmi,ka bashi hakuri ka she ya jira ƙadan, yanzu zan gama sai Maamah ta kawo mata, bai yi magana da wuri ba, da tunda safe zan yi  mata ai.”  sai da Suraj ya gama shan dariyar Hausar Inna kafin ya fice daga gidan don ya kai saƙo.


Yana daf da shiga gudansu motar Ya B na sawo kai, dakatawa ya yi har ya kasaro, a tare suka karewa ciki bayan mai gadi ya budewa AA get, duk da halin da zuciyarsa ke ciki sai da ya sakarwa Suraj murmushin ya mika masa hannu suka gaisa, kafin  su shiga cikin gidan hannayensu sarƙe dana juna.


******************


Kasancewar shagon salon din babba, kuma babu layi don sun je  da wuri yasa nan da nan aka kammala yi musu abinda ya kaisu, Salman ya zauna a mota ya jira su har suka fito, suka shiga ya kamo hanya domin ya kaisu wajen shopping kamar yadda suka so,  Suraj ya kira, don ya sanar da shi su hadu a can, Suraj ya sanar da shi ba zai samu fitowa ba saboda Ya B ya zo gidansu yanzu, zaro ido Salman ya yi ya ce, “ Ka rantse.” “ Wallahi  ko na kira ka bidiyo call ne don ka tabbatar,  “ No bar shi, ga  mu nan zuwa gidan  yanzu muma.“ yana katse wayar ya karya kan mota zuwa gidan Mother ba tare da ya nemi  shawarar abokan tafiyar nasa ba a kokarinsa na yi musu surprise.......



Yau za ku ga ba yawa, hakan ya faru ne saboda kuma comment da reaction ɗin ku na jiya ba yawa, ehe daidai ruwa daidai gari😜