MATAR SADAM

PAGE 81 - 85

by @swrites22




Ya sake kallon umma " ke kuma ki sani nasan duk wani takun ki da makircin da kike shiryawa na sani , mai nabila da yayan ta suka tare maki a gidan nan, adalci dai iya gwargwado ina kwatantawa a tsakanin Ku to mai kuma kike so bayan haka, umma da gaban ta ya fara faduwa tace alhaji wani abun kuma akace nayi ? 

" Au sai an fadamin kinyi ne umaimah ko bani da Ido ne , ke yanzu ashe har bokaye kikebi dan kawai ki cusawa baiwar allah bakin ciki mai ta miki ta rikeki tsakani da allah ta dauki yayanki matsayin ya yanta bata taba nuna babanci amma ke ki rasa mai zaki saka Mata dashi sai sharri wallahi kinji kunya amma kanki kikawa ance idan Kana haqa ramin mugunta haqa daidai misali domin in yayi zurfi da yawa Kai zaka fada, bari in gaya miki shi sharri dan aikene Kana aikashi zaiyo kwana ya dawo gurin Wanda ya aikashi , idan Ka yiwa dan wani fatan alheri danka ka yiwa haka kuma idan ka yiwa dan wani fatan sharri shima naka Ka yiwa, gashi nan tun a duniya Allah ya fara saka Mata ya nuna nafisa wanna ma kadai ta isheki , ban taba tunanin zaki iyayin haka ba na dauka abun naki iya baki ne kawai ashe ke da zuciya biyu kike zaune da ita, to duk wani kulle kullenki a tafin hannu na suke dan haka ki tattara ki koma gidan alhaji nuran zanzo muyi magana dashi ban amince ki tafi min da Yara ba dan bada su kika zo ba.

  Hannu umma ta daura aka tare da sakin kuka ta shiga fadin 
"wayyo na shiga uku dan Allah alhaji Kayi hakuri sharrin shaidan ne na tuba bazan Kara .

"kash wai maisa kowa sai yayi san ransa ya dawo yace shaidan ne to in ma shaidan ne ai kece babbar shaidaniyar kuma na gama magana ki tashi kije kuma ki fara masa bayanin abinda kikayi kafin na karaso Yana gama fadin haka ya tashi ya wuce side din sa .

Tashi tayi ta nufi part din ta tana share kwalla, nafisa da dama bacci ta fara umma ta tasota ta Mike tabi bayan ta Afnan ma ta rufa masu bayan .

Adnan ne ya juyo suka hada Ido da nina ta galla masa harara, cikin farin cikin abinda daddy yayi ya kama kunnuwan sa da fadin 
" afwan ninan mu tuba nake ,mikewa tayi tabar parlourn ba tare da tace komai ba .

cikin zumudi da jin dadi adnan ya daga waya ya kira sadam, yana kwance Yana tunanin seena wayar sa tayi Kara ganin sunan adnan Kan screen din ya sashi dauka tare da fadin Adnan how far, labarin duk abinda ya faru ya bashi har hukuncin da daddy ya yanke sosai sadam ya cika da mamaki bai taba tsammanin umma zata iya abinda tayi ba shi dai yasan tana tsananin kishi da nina Wanda hakan yasa take matukar jin haushin ta, ashe ita tsanar data musu ta wuce zato haba ashe saisa dazu daddy ya kirashi yana masa nasiha akan rayuwa tare da bashi addu oi harya jefa shi tunani ashe abin da ke faruwa Kenan , sun dade suna tattaunawa kafin sukayi sallama.

    Tunanin Abubuwan daya ringa faruwa ya shiga yi especially tsakanin sa da seena yace ko su daddy ya suka Kare da ita oho , wata irin kunyar ta tare da tausayin ta yaji sun saukar masa lokaci guda taya zai iya hada Ido da ita after all this maisa umma zatayi including dinta, ita Mai ta Mata baiwar Allah, take zuciyar sa tace saboda ta shafe Ka ta dalilin ka ta shiga ciki.

  wanna dare dai yayi shine cike da tunanin seena da yadda haduwar su Zata kasance da wace fuska zata kalleshi ? Gsky yayi Mata laifi dayawa Wanda shi kansa wani lokacin Yana yi ne kawai ba tare da san ransa ba yakan tsinci kansa da jin haushin ta ne idan har ya tuna tana matsayin matar sa ne bayan kuma deep down ba hakan bane har cikin ranshi shin zata iya mantawa da abinda ya wuce ko kuma zata qi shi ne ? da wanna tunanin har saida yayi sallar asuba sannan ya samu bacci ya dauke shi.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya seena ta dawo walwalar ta tada har wata yar kiba tayi ga girma da wani kyau data Kara, hankalin ta ya kwanta bata da wata damuwa sai ta sadam wani lokacin ta kanyi zurfi a tunanin irin wanna auran nasu amma sai ta barwa Allah komai ta ci gaba da neman zabin sa.

A wajen umma kuwa sosai tayi nadama ta gane kuskurenta ta kuma nemi yafiyar su nina, ba tare da jin wani abuba suka yafe Mata a cewar nina Allah ma Muna masa laifi ya yafe mana bare kuma mu Yan Adam, sai dai dukda haka daddy yaki dawo da ita har saida ninan ta nuna bacin ranta sannan ya amince umman ta dawo .

wani irin zaman lafiya suke Wanda ko lokacin da umma ke amarya ba suyi irin hakan ba hajiya haleema kuwa jin cewa umma ta zubar da makaman yaki ya sata zuwa har gida ta zazzaga mata goma ta tsiya, sukayi rabuwar batta uwar bare.

A batun nafisa kuwa abu ya gagara domin sace jiki take ta fice , ganin abin Yana neman fin karfin su umma ta shaidawa daddy gaskiyar al amarin abinda yake faruwa da nafisan baiyi kasa a guiwa ba ya samu malam na tsangaya ya fada masa , aka fara Mata rubutu tana sha da Yan addu'o'i allah da ikon sa kuwa ta fara nutsuwa  .

Ta bangaren sadam kuwa wani irin son seena ne ya masa mugun kamu ba abinda yake son ji da gani sai ita badan aikin daya rike shi ba tuni ya tsufa a Nigeria saisa kullum Yana kan kiran najwa dan yaji maganar seenan ko motsin ta , sau da yawa ma Idan suna fadan nasu na gado itada najwa kamar yadda suka saba zai cewa najwan karta kashe wayar domin yakan tsintar kansa cikin nishadi aduk lokacin da yaji muryar ta, sai dai ya kasa cewa ta bashi su gaisa amma duk lokacin da ya kira bai ji motsin taba sai ya tambaya tana ina.

  Yayin da ita kuma seena duk lokacin  da najwa zata fara yi mata zancen sadam din sai ta canja akalar maganar ta hanyar shigo da wani zance .

Saura sati biyu su fara exam din third term sai SS 3 suka shirya birthday party su uku duk da ita najwan nata ya wuce  Afnan ne da seena daidai sai dai itama Afnan month din nata ya wuce na seenan nai dai nata on time.
    birthday party suka shirya sosai tare da gayyatar friends din su.

  Tun 4 suka fara sai wajen 8 aka watse , fada suke tayi akan wani gift seena tace na tane najwa tace na tane nina tana gefe tana masu dariya adnan da nafisa da Afnan kuma sun raba team wanna tace na wanna ne wanna tace a a na wancan ne .

wayar nina ce ta fara neman agaji tana dubawa taga sadam ne ke Kira dauka tayi suka gaisa yace nina hayaniyar mai nakeji haka ko har yanzu masu birthday dinne basu gamaba (dayake najwa ta fada masa harya basu gift din kudi suka hada a shopping dinda sukayi amma seena bata sani ba) , dariya nina tayi ta shiga fada masa abinda sukeyi shima dariyar yayi sai kuma yayi shuru nina tace hello emir .

"naam! , " au Kana ji na ma shine kayi shuru na dauka Ka kashene ai .

" umm ah ah nina plz bata wayar

" wa kenan ninan ta tambaya? Kamar Wanda ke tsoron sunan yace seenah , murmushi tayi tare da fadin " babyyy come over 

Zuwa tayi still tana magana dasu najwan Mika Mata wayar nina tayi jin kiran daddy tace yayan ku ne ke magana in kin gama ki samin wayar a chargy barin je naji daddynku na Kira saura kuma ki jefar min da waya na fada maki.

  Nina na barin wurin ta ajje wayar Kan kujera ta koma wajen su suka ci gaba da magana tama manta da maganar waya saida suka gama ta tuna da sauri ta karasa ta dauki wayar tana fadin innalillahi ni whl sharp na manta da wata waya whl.

Afnan tace ana tabka wanna uban muhawarar ina zaki tuna da waya kallon screen din wayar tayi "laaa ashe ma har yanzu bata katse ba sunan da ke Kan screen din tabi da kallo kafin ta Kara wayar a kunnen tana fadin  "helloh" baby voice dinta ta doki kunnen sa, lumshe Ido yayi Yana gyara kwanciya yace birthday girl.

" umm ta amsa,  "happy birthday Allah yaraya ki yayiwa rayuwa Albarka wishing you all the best lyf could offer 

"ameen tnx , sai kuma yayi shuru can yace ya school? "alhamdulillah shuru ne ya sake ratsawa jin kamar bashi da abin cewa yasa ta dage wayar daga kunnen ta ta shiga hira dasu najwa.

shuru yayi yanajin hirar tasu can kuma yace hello yaji shuru hello ya sake fada dan shuru tayi tana sauraran labarin dramar yusra da Adnan taji Yana ta hello hello maida wayar kunnen ta tayi tana mai kyalkyalcewa da dariya shima samun kansa yayi dayin murmushi yace bawa najwa wayar toh, mikawa najwa wayar tayi da fadin better half ungo.

waye ne najwan ta tambaya 

"yayan ki ne taso ki karba nagaji dayawa bazan iya tashi ba .

sake maimaita abinda tace yayi "yayanki ne" hmmmm ya sauke ajiyar zuciya lalle akwai aiki a gabana Allah yasa komai yazo min da sauki muryar najwa ce ta katse masa tunanin daya tafi bayan ta gaishe shi yace kituromin birthday pics din naku yanzu

" ohk but emir wayar na chargy ne yanzun ka bari zuwa anjima 

" ke ni tashi ki dauko ki turo min now now I'm waiting ganin ya kashe wayar yasa ta tashi tana gunguni ta dauko wayar a chargy selecting all kawai tayi tai masa sending sannan ta rufe datar ta maida charging ta koma ta zauna aka cigaba da hira.

Yana jin karar shigowar message yayi saurin daukar wayar ya bude saida yajira suka gama budewa sannan ya fara kallo armless din doguwar riga light pink sukasa sai white long sleeve daga ciki sunyi rolling da dan karamin white veil Wanda ko gashin Kansu bai gama rufewa ba, family pics ne gaba daya Wanda ya kasance harda daddy da umma sai kuma Wanda sukayi da friends dinsu da Wanda suke su kadai sai videos na wanda suka yanka cake, sai kuma wani pic mai ita kadai ta daga balloons Mai dauke da 16 ba karamin kyau ta masa ba ganin yadda takara girma a yan watannin da yayi tafiya zooming din hoton yayi Yana murmushi kafin ya sake swipe kan wani hoton Wanda suke itada Adnan ta shafa masa cream din cake a goshi shi kuma ya daga hannu haka zai rike nata da take kokarin sake shafa masa a hanci, wani kululun abu yaji ya tokare shi a wuya Wanda ya rasa dalili, tsaki yaja tare da danna delete bottom ya goge pic din ya ci gaba da swiping haka ya dinga bin hotunan da videos din Yana kallo sai a karshe yaga wani video nata sanye da farin wando da top peach Wadda ko kugunta bata kai ba sosai kayan suka bayyana body structure nata playing videon yayi ya fara kallo , ta hau Kan centre table tana rawa sai dariya take, murmushi yake tayi sai videon ya Kare sai ya sake playing saida ya kalla wajen sau goma sannan ya rufe wayar ya sake fadawa tunanin ta, saida yaji shigowar sako sannan ya janyo wayar ya duba Yana tashi ya dauko system dinsa ya fara aiki.

   Ahaka su seenah suka gama exams , ganin aunty fatima na shirin tafiya kano ganin gida yasa su cewa daddy zasu bita suyi hutu acan, ba musu daddyn ya amince masu sannan ya dora da
" dama mahmahn taku tace min za suje gaishe da hajjo ku wuce ta can in munzo sai mu taho gaba daya da murna suka tashi suka wuce daki suka fara hada Kaya harda su afnan a tafiyar Wanda daddy ne ya bukaci hakan.

  washe gari sukayi sallama dasu nina suka wuce gidan aunty fatima Inda daga can kuma zasu wuce kano.

Tafiyar su da sati uku sadam ya diro Nigeria kwata² bashi da labarin cewa su seenah sunyi tafiya dan ba Wanda ya sanar masa, duk da yaji gidan shuru amma bai tambaya ba har dare akayi dinner nan ma yaga bai gansu ba .

  Bin nina yayi daki tana cikin duba wani abu a wardrobe ya shigo da sallama ta amsa tana chi gaba da abinda take yi , zama yayi kan sofa yana fadin ni kuwa nina ina yaran naki ne naji duk gidan yayi shuru.

" Chab su najwa ai sun tsufa a Kano inajin cikin satin nan ma Ko na gaba zasu wuce gembu , da sauri ya tashi daga zaunen da yake "whattttt!!! nina harda seenah Kenan .

juyowa tayi tana kallon sa " bangane harda seenah ba da ina zaa barta harda ita mana .

" haba Nina dan Allah yanzu abinda akayi anyi daidai kenan da auran nawa take gantali har ta tsallake tabar garin kuma bada izinina ba ban sani ba ko a waya ba Wanda ya fada min saidai kawai ace sun tafi toh ni mai aka maidani kenan .

sosai Nina tasa dariya ganin yadda ya hakikan ce yanata fada harda cewa wai da auran sa zata tsallake Kenan yanzu ya saduda ya yarda da auran tun ma kafin ya ganta Ido da Ido lalle za'a sha kallo, cikin tsokana tace kaida kace Mai zakayi da yar ficiciyar yarinya sa'ar karamar kanwar ka amma yanzu ko kunya baka ji ba katsaya gabana Kana fadin wai da auran naka take gantali, kai baka ji kunyar Kiran karamar yarinya a matsayin matar Ka ba ta karashe da sautin dariya .

     Tashi yayi cikin kunya da kuma haushin tafiyar su seenan ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, nina kuwa dariyar ta ta chi gaba dayi tace Zama kayi bayani ne.

Su seena kuwa tunda sukaje Kano yawo suke sha sosai yau suna gidan Muhammad gobe suna gidan Asif jibi gidan Nabil sosai sukejin dadin zaman Kano , sai abinda suke so zasu yi dan ma wani abun mahmah na dan hanawa saboda seena haka sukayi three weeks sannan suka fara shirye shiryen tafiya gembu Inda gaba dayan su zasu tafi harda su Asif da matayen su.

A bangaren sadam kuwa fushi yake dasu Nina saisa ko waya ya daina Kiran najwa Ko ta kira ma kashewa yake, ganin yadda sadam din ke behaving yasa daddy tambayar nina akan Mai yake ta wani ciccin magani, ita kuwa ta fada masa dalili ,dariya kawai yayi yace share shi zai ma daina ne .

A gidan da suka saba sauka duk lokacin da sukazo anan suka sauka , daddy ne ya sayi gidan a ciki gari, da su hajjo yaso su dawo nan ita kuma taki hakan ya sashi saye sauran gidajen dake kusa dashi ya gina big mansion suke sauka anan idan sunzo , ya raba keys din gidan ya bawa abida(mahmah)makulli daya shima ya rike daya, sai kusan 9pm suka isa hakan yasa wanka kawai sukayi suka ci abincin sannan suka bi lpyr gado.

Washe gari suna tashi suka shirya suka wuce gidan hajjo ,  tana zaune kan tabarmar ta tana cin goron ta hade da sauraren radio.

da gudu seenah ta shigo gidan tana Kiran hajjo hajjo kina ina , ganin hajjon zaune ya sata karasawa ta rungume ta tana dariya, ture ta hajjon ta danyi tana fadin Kinga ni dagani karki karasa karyani , dariya tayi tace kai hajjo har yanzu halin dai Yana nan sallamar su mahmah ce takatse su.

washe baki hajjo tayi tana fadin "Ashe yau manyan baki ne dani muhammadu har daku , ummi ce ta fito daga daki tana fadin
" Mahmah kune tafe lale maraba sannun ku da zuwa da gudu seena ta tafi ta rungume ta tana dariya , ture ta tayi da fadin "ke miye hakan wato kedai baza ki nutsu ba ko , shagwabe fuska tayi " kaiiii ummi kinfa dade baki ganni ba shekara biyu amma ko kewata bakya yi ganin hararar da mahmah ke aika Mata yasa ummin yin murmushi ta koma daki ta dauko wata tabarmar, Asif ne ya karba ya shimfida masu suka zazzauna .

   fura ummi ta dama ta kawo masu  , nan aka shiga hirar yaushe gamo , a nan su Nabil suka barsu .
   Sai dare su mahmah suka tafi aka bar seenah da najwa Afnan da nafisa sosai seena ta makalewa ummi dan dole ta sake Mata, kwana sukayi suna hira suka dauko tsarabar da suka yi musu suka raba ma hajjon da ummi .

  washe gari kuwa sai 11 suka tashi dan basu kwanta da wuri ba, bayan sun gama abinda za suyi suka shirya zasu fita ummi ta kalli seenah da fadin "ba dai fita zakiyi ba? "ummi zamu je gidan su yiha da saudat kuma zamu dan zagaya gari dasu ya nafisa kinga su basu san garin ba .

"kin tambayi mijinki? Hada Ido sukayi da najwa da sauri ta dauke kanta tana murmushi kasa² duban ta ta maida ga ummi tace eh ummi shi yace ma muje " shikenan to adawo lpy cikin kitchen ta koma ta tsokano hajjo sannan ta fito da gudu tana dariya tayi waje , ummi ma murmushin da batayi niyya bane ya subuce Mata a zuciyarta tace Allah yakara shiryamin ke seenah.

Suna fita gidansu riha suka nufa duk Inda suka wuce sai an tsaya ana kallon su wasu sun kasa yadda seena ce duk Wanda aka fadawa sai ya taho da gudu idon sa ya nuna masa sukuwa basu masan sunayi ba haka suka karasa gidan suna hira 

a tsakar gida suka samu maman riha tana daka tana ganin seena ta kama baki " haseeena kece dariya tayi nice goggo ashe baki manta kamanni na ba "habawa haseenah ai bazan taba manta kamannin ki ba, sannun ku da zuwa Ku karaso daga ciki mana ta fada tana shimfida masu tabarma suka zauna suna gaishe ta .

seena tace goggo ina yiha kafin ta rufe baki riha ta shigo rike da leda a hannun ta ai tanayin arba da seena ta wurgar da ledar cikin sauri seena ta nufe ta suka rungume juna suna dariya sai su dago sukalli fuskar juna saisu sa dariya su afnan ma dariyar suke musu kafin suka karaso suka zauna gaisawa sukayi dasu ya nafisa sannan aka bude babin hira, saida sukayi sallah azahar sannan sukaci abincin rana danwake ne da yaji yajin garlic ko su Afnan saida sukayi santin sa suna gamawa seena tace yiha tashi muje ki rakamu gidan su saudat.

"gidan su ko gidan ta kinga ni murnar ganin ki tasa na manta ban fada maki ba saudat tayi aure ai .

" ke dan Allah wai dagaske kike ? 

"wallahi kuwa tashi ma muje gidan ki gani mikewa sukayi seena ta mikawa goggo tsarabar ta sannan tabawa riha ma ta ta, mikawa goggo riha tayi ta ajje Mata sai sun dawo sañnan suka fice.
abun hawa suka tara zuwa gidan saudat din dan akwai dan tazara tsakani, su dai su nafisa binsu kawai suke.

Suna shiga suka rungume juna suna ihu saudat ta kalli seenah tana dariya tace seenah kinga yadda birni takarbeki kuwa , kuzo mu shiga daga ciki sannun Ku da zuwa.

parlourn ta suka shiga suka zauna takawo masu zobo mai sanyi tana fadin yaushe kuka zo ne wai ?  Seenah tace shekaran jiya.

"ina mijin naki yar dariya tayi tace Yana can , can Ina saudat ta sake tambaya ?
"to wai ke goya shi zanyi in dinga yawo dashi ko mai kefa shikenan mun shiga uku tunda aka Miki aure.

dariya saudat din tayi "ai kafin nayi auran ke kika fara kin fini sanin dadin sa, hararar ta wurga mata duk suka sa dariya, nan fa suka barke da hira najwa tace bata tare bane tukunna sai nan gaba saisa kukaji ba lbr , nan suka fara Mata shegantaka ba tare data Kula su ba ta dauko wayar ta ta fara danne dannen ta saudat ce ta tabota tana fadin  "ke hajiya ashe dai ba'a shige daga ciki ba saisa har yanzu bakin bai bude ba.

harara ta sake watsa Mata da fadin "ke fa iskancin naki gaba yake Kara yi .

" la la la ke miye na iskancin auran ne iskanci sunna ce fa kinga kawai ki kwantar dakai in fada maki sirrin ah tou, kwashewa sukayi da dariya gaba daya suka rufe seena da tsokana tun tana maida masu martani har ta rasa mai zata che musu tayi shuru.

Tashi tayi zata fita saudat tayi saurin shan gaban ta " ya hakuri kawalli wasa fa ake dan Allah koma ki zauna mun daina riha kisa baki mana, dakyar suka samu ta dawo ta zauna .

najwa ta shiga basu labarin yadda zasu  tsara bikin tariyar nanda 7 months , bata ce musu Kala ba har suka gama suka shiga hirar tarihi, nanne ma tasa baki aka fara maida zance sosai suke dariya riha tace nikuwa najwa ya kukayi da rigimar seena a birni ? 
" ai in gaya maki riha can ma saida aka taba , da yawa kuwa saida suka samu rabon su kafin daga baya kuma aka nutsu bakya ganin yanzu yadda ake komai da class , saudat tace aaa nifa nagani gashi nan an waye wayaga matar oga .

   haka suka ci gaba da hira seena tayi ta musu hotuna a wayar ta, anan sukayi sallar laasar har mijin saudat din ya dawo suka gaisa sannan sukayi exchanging number da saudat din, seenah ta karbi wani medium bag Mai kyau daga hannun najwa ta mikawa saudat din "ga tsarabar ki nan data Inna in kinje ki bata.

godia ta mata sosai sannan ta rakosu har waje saida taga sun sami abun hawa sannan ta juya ta koma.

Suna sauka a abun hawa riha ta musu sallama da cewa zata zo da daddare su kuma suka wuce gida suna shiga suka samu mahmah da aunty fatima sai Asif da matar sa da yarsa karasawa sukayi suka zube a gajiye.

seena ta daura kanta Kan cinyar mahmah tana fadin 
"wash mahmah nagaji sosai nafisa tace wallahi Nima nagaji gashi yau rana ta bude gaskiya ba zamu Kafita da wuri ba sai la'asar

" toh nima ai ban san ranar za tayi karfi haka ba kin san garin nan rana bata cika budewa sosai irin haka ba , Asif ne yace ke seenah tun dazu fa muke jiran ki ni da umm manan zaki rakamu muga gari.