SARTSE COMPLETE

02

by @legendspen

*SARTSE*

-Amanar-Janafty-

*Sayyid Legendspen*

MAH/2026/001


Sadaukarwa.


RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA

(Mai Dambu) 



Shafi na biyu

    (02)



Goge hawayen na shiga yi, na rasa me yake mini daɗi, Allah Ya gani ina mugun so da ƙaunar mijina, kamae yadda shima na tabbatar yana sona, to me zai sa na tsaya akan gas ina ɓata masa rai. Tashi na yi na je na kashe Gas ɗin sannan na ce. 


“Ka yi hakuri dan Allah, idan ban tausaya maka ba wazan tausayawa a duniya? Wa nake dashi da zan zo bayan kai?” 


“Nana ai naga alamun kamar ana son shiga tsakanin mu a hure miki kunne.” 


Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushin da nake kallo a matsayin soyayya mai girma, sannan ya ƙara cewa. 


“Nana ina son na nemi alfarma a wajenki guda ɗaya.” 


Na gyaɗa masa kai sannan na ce. 


“Ina sauraronka.” 


“Nana duk runtsi duk wuya ka da ki bari wani ya shiga tsakanin ki da mijinki, ina faɗa miki hakane a matsayina na mijinki, mai ƙaunarki.” 


Cike da farin ciki da gamsuwa da soyayyarsa na ce. 


“Tom in sha Allah, yanzu kaje ka yi wanka zan kunna wutar gawayin na soya na kawo ma.” 


“Tom ki yi sauri kinsan dai fita nake son yi.” 


Ya faɗa yana juyawa ya fice, ni kuma na kulle ko ina na kicin din na fara ƙoƙarin kunna wutar. 


Gaba ɗaya kicin ɗin ya turniƙe da hayaƙi wanda ya tsaya mini a maƙwogarona na fara tari babu ƙaƙƙautawa, ba shiri na tsugguna a ƙasa na fara kakari, ina jin kamar hanjin cikina zai fito waje, da ƙyar na iya tashi na fara buɗe kokafin bayan na ga wutar ta kama. Idona fal da ƙwallar da ta taru sabida hayaƙi na tashi na ɗakko farantin silba na shiga firfita wutar har takama. 


Na sakko da kaskon daga kan gas din na ɗora akan kurfotin, ina yi ina firfitawa har man ya yi zafi na fara sanya fanken ina soyawa. Kusan minti talatin sannan komai ya kammala na juye a filas na fito falo, yana zaune kan kujera ɗaure da tawul ɗin wanka. 


Kan Dining na nufa na ajiye plast ɗin, sannan na koma Kicin na ɗakko kufuna da faranti na dawo na jera akan dining sannan na dawo cikin falon. 


“Komai ya kammala.” 


Na faɗa ina ƙoƙarin zama sabida sandarewa da na ji bayana ya yi, sakamakon durƙushen da na yi na soyawa fanken, kallona ya yi sanan ya ce.


“Ni ai ban kammala ba! Ko ni zan shirya kaina ne?.” 


Murmushin yaƙe na yi sannan na ce. 


“Aha ba dai! Ya zaayi ka shirya kanka ni ina nan, mene amfanina?.”


“Babu kam, idan har ba zaki yi mini biyayya ki faranta rai ba, babu.” 



“Mene haka?.” 


Na faɗa arazane sakamakon abinda nagani, sosa ƙeya ya fara yi sannan ya ce. 


“To na buɗe zan shirya tun da naga kina kicin, kuma ni banga kayan da suka yi mini ba shine sai na fito dasu duka.” 


Yanayin yadda ya yi magana ya yi matuƙar burgeni, ya kuma goge mini dukkanin ɓacin ran da sheɗan yake son san ya mini. 


Na yi murmushi ina matsowa sannan na ce. 


“Ai da ka jirani, amma bari na duba maka nina san wa’yanda zasu yi maka kyau.” 


Na tsugunna a ƙasa na fara kwashe kayan da ya zuzubar a ƙasa ina zuba su kan gadon, sai da nagama kwashe su tsaf sannan na ce.


 “Bari naga wanda zaifi maka kyau.” 


“Hon!.” 

Na ji sassanyar muryarsa ta kira sunan ds na tabbatar sai soyayya ta yi daɗi yake kiranshi. 


“Naam Hon!.”

Na amsa masa nima cikin tawa sassanyar muryar da nasan ba ta yi ko rabin tasa a daɗi da sanyi ba, abu guda ɗaya da nake ƙara yararwa kaina shine. Sardauna Mijina ba tsarar aure na ba ne, Sardauna ba aji na ba ne, Sardauna yafi ni komai, ko naƙi ko na so Sardauna alfarma ya yi mini ya aureni, sabida yana sona. 


“Kayan nan kamar ba’a taɓa gogesu ba ko?.” 


Ya faɗa yana taɓa kayan a yamutse kamar ba na sa ba. Da mamaki na kalleshi, sannan na kalli kayan, inda sardauna yake kai wanki da guga ba ƙaramin waje ba ne a Duste, idan suka yi maka wanki zaka rantse kayan ba a taɓa sa su ba, gasu nan suna sheƙi amma yake cewa kamar ba’a taɓa gogewe ba, ‘ko ya fara ciwon ido ne?’


“Ko?” 

Ya sake faɗa, sai da na yi murmushi sannan na ce .


“Wai Hon me ka gani ne?”


“Duk sunyi wani sikwizin, kamar an ƙwato su daga bakin kura.” 


Na yi dariya ganin yadda yake taɓe hanci, kamar yana riƙe da kashi. 


“To ai duk kaine ka yi musu haka.” 


Na faɗa ina ci gaba da duba kayan. 


“To ai bansan zasu yi haka ba, yanzu haka zan dinga fita kamar almajiri?.” 


Ya faɗa kamar zaiyi kuka, gaba ɗaya naji nustuwata tana shirin barin gangar jikina, a ruɗe na ce. 


“A’a Hon! Ya zaayi ka fita a haka? Zan bawa Madu ya kai wajen guga a sake gogewa, tun da kaga mu nan bama amfani da abu mai jan huta, mussaman dutsen guga, Tv, hita, da kukin gas, wani lokacin ma cewa kake a kashe fanka sabida Mita kuɗin wuta da wahala.” 


“To ya zaayi idan abu yakama dole ayi, ki yi amfani da dutsen kawai ki gogesu, amma kafin na dawo fa dan Allah Hon.” 


Haka kawai sai naji jikina ya yi wani iri, Miji na da nake so, nake ƙauna sama da komai shine zai dinga haɗani da Allah akan na yi masa guga, guga dai abar banza. 


“Haba Hon! Haba Haba! Kafin ka dawo angama in sha Allah.” 


Na faɗa ina miƙa masa wani light bulun yadin. 


“Kaga wannan bai yi sikwizin sosai ba.” 


Karɓa ya yi yasa, ni kuma na ɗau mataji na hau taje masa gashi, sai da gashim ya yi kyau sannan na sa masa hularsa, na fesa masa turare muka fito. 


“Nifa na makara gaskiyya, na yi birek fas a ofis kawai.” 


Ya faɗa yana niyar ficewa.


 “Haba Hon, ka tsaya dan Allah.”


“Hon it is almus 10:30, na makara sosai fa, ki ajiye min idan na dawo na ci.”


Bai jira amsa ta ba ya fice, yunwar da nake ji tun ta daren jiya da kuma ƙarin ta yau da safe ya sa na nufin kan dinning ɗin na fara cin abincina, bayam na kammala na kwashe koma na kai kicin, sannan na shiga ayyukana. 


Ban ni na kammala komai ba sai wajen ƙarfe tara da rabi, Sardauna ya kawo mun masu aiki har guda huɗu amma ina sallamarsu, Allah Ya gani ina tausayin mijina bana so na ga yana ta kashe kuɗi a aikin banza, shi ya sa da ya kawo nake sallamarta, amma sai ya sake kawo wa, wai ance yawan aiki yana sa mace ta tsufa shi kuma bai son ma tsufa, sai da na yi da gaske kafin na fahimtar dashi cewar na haka ba ne. 

 

Ina zama kan kujera bacci ɓarawo ya yi gaba dani ba tare da sani na ba. ‘Gur! Gur! Gur!’ Cikin bacci nake jiyo kukan wayata, ba shiri na buɗe ido na kai hannu na ɗauka, sunan Fauziyya ya bayyana akan Skirin ɗin wayar, bude ido na na yi gaba daya na ƙarewa wayar kallo, ina son ɗauka ina jin tsoron Sardauna ya rabani da kula ƙawaye, haka wayar ta ƙaraci kukanta ta gama kiran ya katse, sai a lokacin na duba naga wannan shine kira na bakwai da ta yi mini. 


“Ko mutuwa aka yi?.” 


Na tambayi kaina, ba shiri na fara kokarin buɗe wayar na kira ta, sai dai ban kai ga kiran ba na ta kiran ta sake shigowa, ɗagawa na yi da faɗin. 


“Salamu alaikum, Fauziyya.” 


Na faɗa murya ta ƙasa ƙasa. 


“Nana ina kika saka wayarki, ina ta kira?.” 


“Wallahi bacci nake Fauziyya, Ya kike?.”


“Ina lafiya, matar nan gaskiyya kina hutawa abunki. Sardauna ya tsaya miki.”


Na yi murmushi mai nuna jindaɗi, sannan na ce. 


“Wallahi tun da ya fita kawai na kwanta.” 


“Ai haka ake so, kin ga nazo bayan ku ne gidan yayar mijina shine na ce ko kina gida na biyo, kuma gashi na samu tabbaci.” 


Dum! Dum! Na ji gabana ya shiga faɗuwa, Sardauna baya sona da kowacce ƙawa, bai taɓa ce mini kar da ƙawayena su zo, amma ya fito ya nuna baya son ina kula su, ba ma iya su ba kowa ba ya so, ni kuma duk wani abu dai zai ɓata ran Sardauna bana maraba dashi. 


“Kinyi shiru?” 

Muryar Fauziyya ta dawo dani daga tunanin da na fara. 


“Dan zaki zo gidana sai kin tambayeni? Kawai ki tawo, amma da wuri dan Allah kafin huɗu zai zo mu fita.” 


“Ah to ko ba sai na zo ba.” 


“Kai! Ya zaayi kive haka, kizo mana dan Allah.” 


“Toh shikennan yanzu zaki ganni.” 


Daga haka ta katse kiran, na miƙe na shiga ɗakina na ɗaura alwala na gabatar da sallah azahar ganin karfe ɗaya  ta yi, ina idarwa na shiga kicin na ɗora taliya jollop, sanin cewa zata iya zuwa a kowanne lokaci yasa na yi amfani da gas na ɗora girkin.


Ina fitowa daga Kicin ɗin, na koma ɗakin Sardauna na fara haɗe kayan ina ninke su, daniyar idan ta tafi sai na goge su tunda mu nan bama rasa wuta kwata kwata.


Ina cikin ninke kayan na ji sallama a falo, Allah Ya gani bana maraba da dukkan abinda zai ɓata ran mijina, na yarda da Allah, na yarda da cewar ina son Sardauna sama da komai.  Hakan ya sa bana farin ciki da zuwan Fauziyya, ƙaramin tsaki naja sannan na miƙe na fito, sai na zo dab da falon sannan na janyo murmushin yaƙi na sanya shi a fuskata. Itama fuskarta ɗauke da murmushin ta tare ni da cewa. 


Ƙawatah, ƙawar yarinta, ƙawar girma.” 


Na yi dariya na zauna akan kujera ina faɗin. 


“Tawo mana.” 


Zama ta yi tana ƙare mini kallo. “kin canja gaba ɗaya abinki, kinsami aljannar duniya.”  


Na yi dariya da faɗin.


“Alhamdulillah wallahi, bara na kawo miki ruwa kafin mu ci abinci.” 


“A’a yana ji ba sanyi a wannan zafin?.” 


Ta faɗa bayan na kawo mata ruwan, na yi murmushi sannan na ce.


 “Kinga ni mura nake, shi kuma kwata kwata ba ya shan sanyi.”


Sai bayan na faɗa na yi mamakin yadda na iya shirya ƙarya a lokaci guda, na tuna lokacin da muka yi magana da Sardauna akan firjin. 


“Nana! A gidanku babu firinji, baki sa ba shan sanyi ba, sabida yanayin unguwar ku ma zafi ake yi, dan haka anan ma ba zai zama wani abu ba dan na ce ba zaki dinga kunna firinji ba, sabida yanayin jan wutarsa.” 


Allah Ya gani ina tausayin mijina, ko bai ce ba nasam yadda kuɗin wuta yake anguwar masu kuɗi, shi ya sa ma yana faɗin haka, na ce Babu matsala. 


Kicin na shiga na zuba mana abinci, na kawo mana falo jallop ɗin taliya da ta ji naman kaji zaƙwa zaƙwa, haka mu ka zauna muka ci, muna ci muna hira ko ba komai na ji matuƙar daɗin zuwanta.


Bansan cewar ina zama kaɗaici ba sai da tazo, bansan cewa zaman da nake ni kaɗai ba, a ƙuntace nake ba sai da ta zo. 


Muna tsaka da cin abincin aka yi sallar la’asar, hakam yasa muka gaggauta muka ci mu ka yi sallah, bayan mun idar ne Fauziyya ta ce. 


“Gidanki ya yi kyau sosai, arziƙi da wadata faca-faca, sai dai ke din duk kina zaune babu wani kuzari kamar ba matar da take auren wanda take so ba?.” 


Murmushi na yi mata sanan na ce.