87
by @zahrabmrs02
A dakin otal dinsa dake Washington, AK ya kasa zaune ya kasa tsaye. Yana ta zagaye dakin, kansa yana sarawa.
"Dama tana da kudin karatu? Ta ina ta samu?" ya fada a ranta, zuciyarsa tana tafasa da kishi da kuma wani irin nadama. "Na zata idan ta bar gidan nan, rayuwarta ta kare. Amma gata yau, hatta Alhaji Dan-Azumi yana girmamata. Maryam... wato har kin wuce ni?"
Ya dauki wayarsa, ya kalli saƙon da ya tura mata wanda ba ta bude ba. Ya fara rubuta wani sabon saƙon: 'Maryam, don Allah mu hadu mu yi magana. Don Allah...' Amma sai ya goge. Girman kansa har yanzu yana hanawa zuciyarsa gaskiya.
bazan taba bari na rasa ki ba farhana dik yanda zanyi sai nayi kin dawo min ,am not a loser
Har yanzu da tashiga jirgi donyin IR ,text din abbi ke mata yawo ,inshaAllah zata tattara ta tafi abuja nanda 1 month Kamar yadda abbi ya bukata
"Maryam, Maintain 3,000 feet, turn left heading 240," muryar Captain Miller ta fito ta kunne.
Farhana tana kokarin hada lissafin inda take, da yadda iska take tura jirgin, da kuma bin muryar Miller. Gaba daya kwakwalwarta ta kulle. Ta ji kamar jirgin yana karkata, amma na'urorin suka ce jirgin a mike yake. Wannan shi ne babban kalubalen—Spatial Disorientation (inda jikinka zai dinga gaya maka karya, na'ura kuma tana fada maka gaskiya).
"I can't do this, Captain! Na ji kamar jirgin zai kifar da ni!" Farhana ta fada, muryarta tana rawa.
"Karka cire Foggles din nan, Maryam! Trust your instruments, not your body!" Miller ya daka mata tsawa.
Tashin hankali ya sanya Farhana ta rasa yadda za ta sarrafa jirgin. Ta ji wani irin jiri yana kwasarta, tsoro ya ziyarci zuciyarta cewa yau za ta iya faduwa da jirgin nan. Suna sauka a kasa, Farhana ba ta ma iya fita daga jirgin ba. Ta kifa kanta a kan sateyarin jirgin ta fashe da kuka.
Kuka take yi na gaske, kukan da ya tuna mata da dukkan wahalar da take sha. Kukan gajiya.
Gajiyar Jiki da Ta Zuciya
Ta dawo gida a mace, ko abinci ba ta iya ci. Isabella ta ganta ta tausaya mata. "Maryam, ki huta mana."
"Isabella, wannan karatun ya fi karfina," Farhana ta fada tana kuka, idanunta sun kumbura. "Ganin da nake yi da idona shi ne nake amfani da shi, yanzu kuma an ce in daina gani, in dogara da agogo da na'ura. Na kasa fahimtar lissafin."
Kwanaki uku tana zuwa makarantar tana dawowa tana kuka. Akwai ranar da aka shiga cikin matsanancin gajimare don gwada ta, Farhana ta rude sosae har sai da ta kusan taba wani dutse da fikafikan jirgi idan ba don Miller ya karbi ragamar jirgin ba.
"
Farooq ya iske ta a kofar makarantar tana zaune a kan dakali, kanta a tsakanin gwiwowinta, tana kuka a hankali. Ya zo ya zauna a kusa da ita, ya mika mata ruwa.
"Baby girl, me ya faru?"
"Farooq, zan daina. Wannan Instrument Rating din ba nawa ba ne. I'm failing," ta fada cikin shashshekar kuka.
Farooq ya kamo hannunta, ya goge mata hawaye. "Maryam, kinsan me yasa aka sanya wannan matakin? Domin lokacin da zaki tuka jirgi daga Amurka zuwa Najeriya, ba kowane lokaci zaki ga hanya ba. Akwai daren da babu wata, akwai gajimaren da babu gani. Idan baki koya yanzu ba, yaya zaki zama International Pilot dinda kike mafarki?"
Farhana ta dago kai tana kallonsa.
"Ki kuka idan kike so, amma gobe ki koma ki sake gwadawa. Ba zan barki ki karaya ba lokacin da kika rage saura kadan ki zama tauraruwa. Trust the process, and more importantly, trust yourself."
Farhana ta dauki dadduma ta yi sallah, ta roki Allah ya bude mata kwakwalwa. Ta kwashe kwanaki tana duba littattafai har karfe hudu na asuba. Ta fara amfani da kwanon girki a daki tana nuna kamar shi ne na'urar jirgi, tana juya hannunta har sai da lissafin ya fara zama a ranta.
Garin Boston ya gudanar da wani matsanancin sanyi da iska mai karfi, wanda hakan ya sa karatun Instrument Rating din ya kara zama tamkar azaba. Farhana tana cikin dakin Simulator (na’urar gwaji ta kasa), inda aka saita mata yanayin da babu komai sai duhu da ruwan sama a na’urar.
Rikicewar Lissafi
"Maryam, you're off-course! Duba Localizer dinki, kina shirin barin hanyar sauka!" Muryar Captain Miller ta fito ta speaker din simulator din, tana duka kamar tsawa.
Farhana ta rude, hannunta yana rawa a kan sateyarin. Tana kallon na'urorin, amma lissafin ya ki zauna mata. Ta ga kamar hancin jirgin yana sama, ashe yana kasa. Ta tura hancin sama, sai karar faduwa ta tashi a simulator din. Crash.
Ta yi kuskure na hudu a rana daya.
"Enough for today, Maryam," Miller ya fada cikin muryar takaici. "Idan a jirgi ne na gaskiya kike yanzu, da tuni kin kashe kanki da fasinjojinki. Kije gida ki sake tunani ko lallai tashi jirgi kike son yi ko kuwa wasa kike yi."
Wadannan kalaman na Miller sun soki zuciyar Farhana fiye da mashi. Ta fito daga makarantar ko kallon inda take takawa ba ta yi. Tana iske gida, ta iske su Isabella ba sa nan, hakan ya ba ta damar sakin kukan da take boyewa.
Ta zube a tsakar dakin, ta fashe da wani irin kukan dake fitowa daga can karkashin zuciyarta. Kuka take yi tana kiran sunan mahaifiyarta, "Diddi! Diddi na gaji! Me ya sa rayuwata take da wahala haka?"
Ta tuna lokacin da take gidan AK, ko lissafin kudin cefane ba ta iya yi balle na'urar jirgi. Ta ji wani irin kaskanci, ta ji kamar gaskiyar AK ce cewa ita "ba kowa ba ce".
"Ba zan iya ba!" Ta rinka fada tana buga hannunta a kasa. "Zan bari! Zan koma Najeriya in zauna a matsayin wadda ta fadi a rayuwa. Wannan karatun na masu kwakwalwa ne, ni kuma kwakwalwata ta gaji."
Farooq ya shigo gidan da sallama, ashe Isabella ce ta bashi makulli ta ce ya duba Farhana don ba ta ji dadi ba. Ya iske ta a dunkule a kasa, kyakkyawar fuskarta ta yi jawur, idanunta sun kumbura sun kusan rufewa saboda kuka.
"Maryam?" ya kira sunanta cikin wata lallausar murya mai cike da kauna .
Ta dago kai, tana ganinsa ta sake fashewa da kuka ta nufi kirjinsa. "Farooq don Allah ka mayar da ni gida. Na kasa. Captain Miller yace zan kashe mutane idan na taba jirgi. Ni ba Pilot bace Farooq, mafarki nake yi wanda ya fi karfina."
Farooq bai ce komai ba, ya bar ta ta yi kukan a kirjinsa har sai da ta fara shashsheka. Ya dauketa tamkar jaririya ya dorata a kan kujera, ya debi ruwa ya fara goge mata fuskarta da kyalle mai sanyi.
"Kinsan wani abu Maryam?" ya fada yana kallon kwayar idonta. "Shi kansa Captain Miller, ya sha faduwa a simulator kafin ya zama Captain. Babu wani Pilot da ya zama gwanin tashi a cikin duhu ba tare da ya taba jin tsoron mutuwa ba."
"Amma ni tawa wahalar ta yi yawa Farooq..."
"Saboda ladanki zai yi yawa ne Maryam," Farooq ya rada mata. "Ina so ki dauki wannan kukan a matsayin wanke zuciyarki daga tsoro. Gobe, ba zaki koma simulator ba. Gobe ni da ke zamu fita mu yi yawo, mu sha iska. Ina so ki manta da jirgi na sa'o'i ashirin da hudu. jibi, zaki koma makarantar nan, kuma ni zan kaiki da kaina."
Farhana ta kalli Farooq, ta ji wani irin kauna daban ta sake ziyartarta. Mutumin nan ba wai kawai masoyi ba ne; shi ne bishiyar da take jingina da ita idan iska ta taso mata.
"Ka tabbata zan iya?" ta tambaya a hankali.
"Ba wai kawai zaki iya ba, Maryam. Ke ce zaki tuka ni a matsayin mata zuwa duk inda muke so a duniyar nan. Don haka, babu maganar dainawa."
Daren ya yi tsit, sai sautin taguwar ruwan teku dake bugawa a hankali a gefen birnin Boston. Farooq ya fito da Farhana wani wuri mai zaman kansa, inda fitilun birnin suke haskowa daga nesa kamar lu'u-lu'u. Suna zaune a kan wani benci na katako, iska mai sanyi tana kadawa, Farhana ta kwanta a kafadar Farooq, tana wasa da zoben da ya ba ta.
Farooq ya juyo ya kalli kwayar idon Farhana, ya kamo hannayenta duka biyu ya matse a cikin nasa.
"Maryam," ya kira sunanta cikin wata lallausar murya mai dauke da shauki. "Kinsan cewa kowace rana da nake tashi, godiya nake yi wa Allah da ya sake hada hanyata da taki? Na taba tunanin na rasa ki har abada, amma yanzu da kike kusa da ni, bana son ko kifta ido in yi saboda tsoron kada ki bace mini."
Farhana ta yi murmushi, idanunta suka cika da kwalla. "Farooq, wani lokacin ina jin tsoro. Ina jin tsoron cewa wata rana zaka gaji da ni. Ka ga ni fa... na taba aure. Kuma ina da yara biyu. Ni ba kamar sauran 'yan matan da kake gani a ofis dinka kowace rana ba ne."
Farooq ya murtuke fuska kadan, alamar bayyana rashin jin dadin maganar da ta yi, sannan ya sa hannunsa ya dago fuskarta.
"Listen to me, baby girl," ya fada cikin natsuwa. "Wannan maganar ita ce ta karshe da nake son ji daga bakinki. Aurenki na baya kaddara ce, kuma kaddarar nan ita ce ta gina ki kika zama wannan jarumar macen da nake gani a yau. Yaranki kuma? Lamido da Sultana ba yaranki bane kadai, yara na ne ma. Ina son su kamar yadda nake son maman su."
Ya gyara mata gashin kanta dake neman rufe mata fuska. "Aure da kika yi ko yaran da kika Haifa, ba za su taba rage ko da digo daya na son da nake miki ba. Hasali ma, suna kara mini kwarin gwiwar nuna miki cewa akwai namijin da zai iya baki soyayyar da kika rasa. Ke ce sarauniyata, kuma yaranki sune sarakunan gidana na gaba."
Farhana ta ji wani irin dadi ya ziyarci zuciyarta, dadi mai sanyi kamar ruwan kankara. Ta kara shigewa jikin Farooq, tana jin dumin jikinsa.
"Farooq, baka san yadda wadannan kalaman naka suke warkar da raunukan dake zuciyata ba. Na dade ina jin kaina a kasa, amma kazo ka daga ni sama. I love you more than words can express."
Farooq ya sumbaci tafin hannunta. "I love you more, my Captain. Kuma ina so ki sani, ranar da zamu shiga gidanmu na aure, zan kaddamar da ke a matsayin matar da ta fi kowace mace daukaka a wurina. Ba zan taba barin kowa ya kalle ki da wani kallo na daban ba."
Suka dade a wurin, suna kallon taurari, suna rera wa juna kalaman soyayya wadanda suke sanyawa kowane radadi gushewa. A wannan daren, Farhana ta gane cewa dukkan kuncin da ta sha a hannun AK, Farooq ya zo ne domin ya maye gurbinsa da farin ciki marar iyaka.