*🪻SAWUN KEKE...🪻*
by @auntyindo
a hankali Macijin ya fara sauya kamanninsa daga maciji zuwa mutum.
Dattijuwar mace ce fara sol kyakkyawa, fuskarta ɗauke da murmushi ta ke kallonsa cike da kulawa, ɗan shafa kansa ta yi gami da gyaɗa masa kai alamar ta na sane ta tashe shi.
"What Happened my Mother?" ya faɗa yana zuba mata rikitattun idanunsa, cikin nutsuwa ta buɗe kyakkyawan bakinta ta magantu cikin zazzaƙar muryarta me cike da kamala da dattako, "It's time for prayer!"
Da sauri ya tashi zaune yana lumshe idanu, cikin sassanyar muryarsa ya ce "Okay Mommah!"
dafa hannunsa ta yi cikin nutsuwa ta ce "Ya na da kyau ka je makaranta yau"
"For what?"
"Calm down, akwai me jiranka ne idan ka je za ka san dalilin.
Gyaɗa kai ya yi sannan ya yunƙura ya miƙe ya nufi toilet wanda aka gina shi da zallar farin dutse, kuma aka yi masa ado da tsirrai da fulawoyi masu furrai kala-kala gwanin sha'awa.
Sai da ya watsa ruwa sannan ya ɗaura Alwala, ya na fitowa ya shirya cikin riga da wando na saƙi farare tass, a samansu ya ɗora doguwar Alkyabba me kyawun ado, itama fara ce an yi mata ado da launin baƙi da ja, ya yi kyau matuƙar kyau wanda zaman misaltashi ma aiki ne.
bayan ya idar da Sallah ya yi addu'a ya miƙe cikin taku irin na wahainiya ya fito daga makeken ɗakin, a bakin ƙofa ya tsaya ya na rarraba ido.
Gine-gine ne na dutse wanda aka yi ɗakuna da kuma madafa sai banɗakuna, ko ina a ƙawace yake da koren ganye fululu da fulawoyi masu furanni ja yalo pink milk da dai sauransu, idan ka kai dubenka nesa kuwa tsaunuka ne manya da ƙananu da ƙoramu masu gudana da ruwa fari ƙar me kyawun kalla, daddaɗan sanyi ne ke tashi ta ko'ina gami da ƙamshin furanni da tsirrai, abin ba a magana.
cikin cool voice nashi ya ce "Mother!" bata kusa amma ta ji kiran da ya yi mata kuma ta amsa, ba ɓata lokaci ta iso gabansa fuskarta ɗauke da yalwataccen murmushi "Amma za ka ci abinci kafin ka tafi.
Girgiza kai yayi alamar aa.
Ba ta yi masa musu ba don kuwa ta san ba zai cin ba, bai kuma cewa kanzil ba ya fara taka korayen tsirrai da ke shimfiɗe a ƙasa tamkar carpet, da ido ta bi shi har ya ɓacewa ganinta sannan ta ci gaba da aiyukanta.
Ana tsaka da karatu ya shigo ajin, cikin yanayinsa na jin kai ya isa gaban Sheikh Auwal ya durƙusa ya gaishe shi kamar yadda kowane ɗalibi ke yi wa malaman makarantar.
Sheikh Auwal ya zuba masa idanu shi kansa ya na yi masa bala'in kyau a irin shigar nan kamar mutumin kirki, sai dai kashh! albasa ba ta yo halin ruwa ba, Ya kasa amsa gaisuwar ya tafi tunani, ganin haka ya sa Risslaan miƙewa zai nemi gurin zama, "Dakata Akhiee! zauna" Sheikh Auwal ya faɗa cikin sauri.
da yake yau ba ƴan gardamar akansa zaman ya yi dafa'an murar kwaɗi ya na sauraren ƙalu-balen da Sheikh Auwal ya zo da shi don a cewarsa ba sa faɗen Alkairi kuma ba sa neman mutum sai ya yi laifi.
Sai da ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ce "Me yasa kwana biyu kenan yau ba ka zo makaranta ba??"
"Ba na cikin yanayin zuwan ne" ya bashi amsa kai tsaye ba tare da shakka ba.
Sheikh Auwal ya jinjina kai sannan ya ce "Akhiee Don Allah ka zamo mutumin kirki ka watsar da harkar banzar nan, ba a son raina komai yake faruwa ba, ka duba ka ga tinda Allah ya sa ka zo duniya mahaifinmu ya ɗauki so da ƙauna ya ɗora maka, kuma har yake kiranka Malam, ya na da burin ka zamo malami babban mutum tamkar shi, dalilin da yasa ya raɗa maka sunansa kenan, sai gashi an wayi gari ka kasa zama ka sauke Alƙur'ani ko da sau ɗaya, zuwa makaranta ma ba ka yi, ka ga mahaifiyarmu ta rasu ta na me begenka tare da sa ran za ka zamo bango ga al'uma, don Allah ka canja rayuwa Akhiee!!!"
Maza Gumbar dutse!! ba shakka nasihar Sheikh Auwal ta taɓa masa zuciya musamman da ya taɓo sashin iyayensa wanda ya fi ƙauna fiye da komai a rayuwarsa.
Shiru ne ya ratsa tsakani kafin Rislaan ya ce "Mu ga tafin hannunka Ya Sheikh!" ba musu Sheikh Auwal ya buɗe tafin hannunsa, shima Akhiee buɗe nasa ya yi ya dangana shi da na Sheikh Auwal, cikin tattausar murya ya ce "Iyayenmu ɗaya, jininmu ɗaya, amma ka ga tsagar tafin hannunmu ma kaɗai ta bambanta, to akwai abubuwa da yawa ma waɗanda su ka bambanta, ba mu muka tsara hakan ba Allah ne ya tsara, tabbas sunanmu ɗaya da Abhi amma ruhinmu daban-daban ne, ka ga dole ƙaddararmu ta bambanta, kowa da kalar ta sa ƙaddarar; ni wannan ita ce tawa, ba zan yi muku Alƙawarin zan canja ba domin ba ni da tabbas akan haka, kuma ance jumu'ar da za ta yi kyau tin daga laraba ake ganeta, ni kuma babu alamar rayuwata za ta canja daga haka, ina me bada haƙuri Akhiee!!!"
Tabbas zuciyar maza ta karye, Sheikh Auwal ya kasa cewa komai don kuwa idan ya furta zai iya rushewa da kuka, kalaman Akhiee sun yi mugun tasiri akansa, tsananin tausayin ɗan uwan nasa ya kama shi.
Akhiee kuwa tashi ya yi ya nemi guri ya yiwa kansa masauki, ya na zama duk na kusa da shi su ka dare su ka bashi wuri su ka koma can nesa da shi, sai ya kasance shi kaɗai a wurin, bai damu ba don kuwa in da sabo ya saba kuma shi ma hakan ya fi masa daɗi don a arashi ma mutum zai iya ɓata masa rai ya illata shi a banza don haka ya fi so su dinga nesanta kansu da shi.
Tinda ya zauna bai ce uffan ba shi bai yi karatun ba bai yi surutu ba.
Hakan ba baƙon abu bane don komai yawan dukan da za'ayi masa ba zai taɓa yin karatun ba don haka Sheikh Auwal bai damu ba bare ma ransa ya ɓaci.
Sai da aka tashi domin yin sallar la'asar sannan ya tashi ya nufi sama wurinsa na gado wato inda ya saba tsayawa.
Husnee jikinta har rawa yake don son ta je ta iske shi, ta na shirin fita daga ajin Sheikh Auwal ya kirata, ba don ta so ba ta amsa kiran gami da zuwa ta durƙusa a gabansa, cikin yanayinsa na dattako ya ce "Me ke faruwa ne naga kamar a kwanaki biyun nan kullum cikin kuka kike?"
maganar ta shi ma dariya ta bata amma sai ta maze ta ɗan murmusa gami da cewa "Ba kuka na ke yi ba Ya Sheikh Idona ne su ke ciwo"
"Kin je asibiti?" gyaɗa kai ta yi alamar eh kafin ta ɗora da cewa "Na je sun ce ba komai a idon"
Abin ya bawa Sheikh Auwal mamaki, jinjina kai ya yi gami da cewa "To fa! ikon Allah, to Allah i sauwaƙe tashi ki je." zumbur ta miƙe kamar wadda aka sokawa kibiya a mazaunai, cikin sauri ya dakatar da ita da cewa "Wani hanzari ba gudu ba."
Durƙusawa ta yi cike da takaici ta ce "Ina ji Ya Sheikh"
"An kawo min ke makaranta ne don ki yi karatu ki ƙara samun nutsuwa da tarbiya ba wai ki lalace ba, to don haka ki gujewa shiga hurumin Akhiee, shi wani irin mutum ne da ba wanda ke son mu'amala da shi, kinga ƴan uwansa maza ma ƙaurace masa su ke yi bare ke mace, ba zan so wani abu mara daɗi ya faru da ke ba don hakan zai zamo alhakinmu tinda amana aka bamu ke, lallai ki kula."
Kai kawai ta gyaɗa masa ba don ta gamsu da kalaman nasa ba.
Ya na bata izinin tafiya ta tashi ba ta zame ko ina ba sai kusa da Akhiee, lokacin da ta ƙarasa kusa da shi waya yake, abinda ta tsinkaya ya na cewa "Da wane irin makari kuka kashe shi??" ba ta ji abinda aka ce masa ba sai kawai ta ga ya kashe kiran, ta saki baki ta na kallonsa kafin ta ce "Dama ka saba kashe mutane? ashe har sawa ka ke yi a kashe??" gyaɗa kai ya yi alamar eh sannan ya ce "What are you doing hare?"
Mantawa ta yi da zancen da takeyi cike da rawar kai ta ce "Me yasa jiya ba ka zo makaranta ba?"
Kallonta ya yi kafin ya buɗe baki a nutse ya ce "Ke sabuwar zuwa ce?" gyaɗa kai ta yi gami da cewa "Yo eh mana, ranar asabar waccan na fara zuwa, kuma ba taɓa ganinka ba sai wannan lahadin, sai kuma naga ana ta dukanka abin tausayi" ta ƙarasa maganar ta na marairaicewa.
"Ya sunanki?"
Murguɗe baki ta yi cike da iyayi da feleƙe ta ce "Husna ko Husnee"
"Asma'u! to shekararki nawa?"
Da sauri ta zagayo gabansa suna fuskantar juna tsabar rawar kai da jin daɗin kulatan da ya yi har ji take kamar ta yi tsalle ta ɗafe shi.
"Shekarata Goma sha bakwai, saura shekara ɗaya na yi candy!" daga yadda take magana ma kaɗai ya isa nuna irin tsantsar farin cikin da take ciki.
Idanunsa masu matuƙar kaifi gami da kashe jikin wanda ya kallesu ya zuba mata, ƙara sassauata murya ya yi kana ya ce "Shekarunki sha-bakwai amma shine kamar akanki aka fara ƙuruciya aka ƙare?"
"Ahh?! to me na yi na ƙuruciya?"
"Wai kuka kike don an dokeni, ni da jin zafi ke da yin kuka, duk wannan ba ƙuruciya bace?"
Rausayar da kai ta yi gami da jingina a jikin ƙarfen makari, a sanyaye ta ce "Ni wallahi tausayinka na ke ji."
Dafa hannayensa ya yi akan ƙarfen gefe da gefenta ya sanyata a tsakiya ya na kallon kyakkyawar farar fuskarta, "Asma'u!!!" ya kira sunanta cikin wata irin murya me rikita lissafin ɗan adam, hakan ya tilasta mata ɗago idanunta da ke fama da hawaye ta jefa su cikin ƙwayar idanunsa.
Ganin ta maida hankalinta kansa ya bashi damar ci gaba da cewa "Ni ba abin tausayi bane, kar ki ƙara tausaya min, ko ni bana tausayin kaina idan kika ce za ki tausaya min kuma ke za ki zamo abar tausayi, sannan ki dena yawan kallona, zuciya gareni kamar glass da ta buga shikenan zan iya illata miki rayuwa, wata rana za ki iya rasa ganinki indai ba ki dena ba."
Kamar macijin da aka zarewa dafi haka ta ke jinta sululu, gashi dai ta na sauraren gargaɗin nasa amma ta kasa dena kallonsa kamar wadda ake ce ta na ɗauke idanunta zai ɓace ta dena ganinsa.
Iskar bakinsa ya hura mata akan idanun nata ta yi saurin rintse su da ƙarfi ta na jan wani dogon numfashi....
by Aunty INDO