KOMAI TSANANI

40

by @oumfatima33

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
    *KOMAI TSANANI* 

             *By*

         *KANSA'U* *BELLO* 
    
   *(OUM FATIMA)* 
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

   *PAGE 040* 

 *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*



******** 

Ƙarfe 8 dai-dai aka, fara ɗibar mutane zuwa ƙayataccen hotel ɗin da za'a gudanar da dinner ɗin wacce Mus'ab ne ya ɗauki nauyin ta, duk irin burin da Ya Ammar yaci don ɗaukar masoyiyarsa hakan bai samu ba don kai tsaye Mamah ta bashi umarnin ɗaukar Suhaima wacce tazo wurin bikin. Ba yan da ya iya dole ya kira Nanah ya sanar mata cewa ta jira zai je ya dawo ya ɗauke ta don ba zai iya saɓa umarnin Mamah ba.

   Lokacin da ya fito general perking lot in da ake ta ɗaukar waɗan da suka rage zuwa wurin dinner ɗin, jikin motarsa yaje ya tsaya yana danna waya kafin su ƙara so. Mabaruka wacce ta fito tun ɗazu taƙi bin ko wacce mota sabo da zaman jiran fitowar Ya Ammar ɗin da take yi don yau tayi alƙawarin ba zata bari ya ɗauki Nanah ba, kai yau ɗin nan tayi alƙawarin sai ta kawo ƙarshen alaƙar sa da Nanah baki ɗaya. Ƙara gyara wa tayi sannan ta shiga taka wa in da yake cike da yanga da fatan ta burge sa, sai dai cikin rashin sa'a kamin ta ƙara sa in da yake su Meenah suka shiga ya tayar da motar yayi gaba.

    Tsaya wa tayi ta cije yatsa cike da takaicin rasa damar bin sa da tayi.

    "Amma ba komai ai zamu haɗe a can ɗin." Ta faɗa tana juya wa ta koma don samun motar da zata bi.


 *Mooh....*

     Gaba ɗaya baya son zuwa wurin dinner ɗin nan kawai don dai Ammy ta buƙa ci daya je ne amma da ba zai je ba, duk da haka sai da Mus'ab ya takura masa kafin ya tashi yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya masu matuƙar kyau da tsari waɗan da da suka dace da Muhammad (Mooh) ɗin 

   Masha Allah kawai zamu ce domin Hammah Mooh ɗin naku ba ƙaramin kyau yayi ba ku hango shi kawai, yayi matuƙar kyau a shigar kwarjinsa ya ƙara fitowa sosai musanman da fuskarsa take kame kamar ko yaushe. 

  "Ka cinye du ango, masha Allah kayi matuƙar kyau." Cewar Mus'ab yana miƙe wa gami da ɗaukar Car key ya nufi hanyar fita. Ɗan ƙaramin murmushi yayi masa iya fatar baki yace.

   "Thanks Bro." Daga haka suka fice a ɗakin. Kai tsaye ɓangaren Ammy suka nufa yayin da duk wan da suka ci karo dashi sai ya furta kalmar.

   "Masha Allah." Sabo da irin kyawun da Mooh ɗin yayi. Ammy tayi matuƙar farin ciki da ganinsa a cikin shigar nan a matsayin ango, babu abin da zata ce sai godiya ga Allah. Addu'a tayi masa sosai kafin tace suje kar su makara tuni an kammala shirya amarya.

  A dai-dai in da aka ajiye motocin da zai fita dasu kamar an ce ya ɗaga idonsa ya hango ta a tsaye tayi matuƙar kyau tamkar wata tarwaɗa tana magana a waya cike da shagwaɓa wan da kai tsaye zuciyarsa ta raya masa cewar da Ammar ne take yin wayar. Take yaji annan abin mai nauyi da yake danne masa zuciya idan irin hakan ta faru.

   Maimakon ya ƙara sa ya shiga motar da tuni aka buɗe masa kawai sai ya samu kansa da tun karar in da take.

   "Ya Khalid manah!." Nanah ta faɗa dai-dai lokacin da Mooh ya ƙara so kuma a kan kunnensa ta furta hakan wan da ya bashi natsuwar jin wan da take ma wannan shagwaɓar.

   A ɓangaren Nanah kuwa bata san da zuwan sa ba don waya take da Ya Khalid ɗinta tana masa ƙorafi a kan ya ɗauke Sis ɗinta sun tafi sun bar ta, shi kuma Ya Khalid ɗin ne ke zaulayarta da cewar ba Ya Ammar ta tsaya jiran ya dawo ya ɗauke ta ba ita ga mai maso yi. Shine ta ambaci sunansa cike da shagwaɓa da kunya. Jin yawaitar ƙamshin Hammah Mooh a hancinta yasa ta ɗan juyo kaɗan sai kawai ta gan sa tsaye a bayanta ya zuba mata waɗan nan kyawawan idanun nasa masu azabar kwarjini.

   Ɗan daburcewa tayi ta juyo gaba ɗaya tana zame wayar daga kunnenta tare da furta.

   "Barka da fito wa Hammah." Ta faɗa tana jin kamar ta ƙara da sanar dashi irin kyan da yayi wan da yasa take ɗan satar kallonsa. 

   "Me kike yi a nan ɗin." Ya mata tambayar cikin yanayin tausasawar daya saba yi mata magana wan da shi kansa baya sanin lokacin da yake aikata hakan yayin yin magana da ita.

   "Dam... Dama...." Shiru tayi ta kasa sanar masa cewa Ya Ammar take jira.

   "Dama me?." Ta tsinci Muryarsa yana tambayar ta gami da tsare ta da idanunsa. Kasa jure kallonsa tayi don haka ta duƙar da kanta a hankali tace.

   "Dama zan je wurin dinner ɗin ne." Ta ƙara sa maganar tana jin tamkar ta fashe da kuka don har ga Allah idan ya tsare ta da idanunsa rasa in da zata saka kanta take yi. Da wani irin salo ya janye idanunsa waɗanda suka kasa gajiya da kallonta a yau ɗin. 

   "Let's go." Ya faɗa a hankali yana nuna mata hanya, cikin rashin fahimta ta ɗago ta kalle sa da neman ƙarin bayani don a saninta ita dai shida amaryar zai tafi ai. Ganin ya zuba mata ido ba tare daya furta komai ba yasa ta yin gaba a ɗan daburce tana tafiya tana ɗan waigen sa, kansa kawai ya gir-giza yana mamakin abinda ya ruɗa tan.

   Ɗaya daga cikin securities ɗin ya matso da nufin sake buɗe masa motar ya dakatar dashi yasa hannu da kansa ya buɗe, da idanunsa ya nuna mata ta shiga. 

    "Hammah?...." Nanah ta kira sunansa a dan ruɗe sabo da hango amarya da babbar ƙawarta Suhaima a tsaye suna kallon ikon Allah.

   "Get in." Ya faɗa a hankali sosai yana kallonta babu alamar wasa a muryarsa. Babu yan da ta iya a hankali ta ɗaga ƙafarta ta shiga cikin motar ta zauna. Hannun yasa ya gyara mata mayafinta daya dan sauka ƙasa sannan ya saka hannunsa ya rufe marfin ya zagaya ɗayan side ɗin in da cikin sauri security ya zagaya ya buɗe masa kafin ya ƙarasa. Mus'ab dake tsaye ya buɗe baki da hanci yana kallon ikon Allah a kan abin da Mooh ɗin ya aikata kuma ya fuske abin sa ko a jikinsa, duk da cewa bai yi wani mamaki sosai ba kasancewar ya san wace Nanah a wurinsa. Sai dai abin da yayin tamkar cin fuska ne ga amaryarsa don ita ya kamata ya bawa wannan kulawar.

    Ganin security na ƙoƙarin rufe ƙofar yasa Mus'ab yayi saurin dakatar dashi, murmushin yaƙe yayi ya kalli Noorah data shaƙa don tun da take da Mooh bai taɓa mata abin da taji ranta ya ɓaci ba irin yau ɗin.

   "Bismillah." Mus'ab ya faɗa yana nuna mata ɗayan gefen Mooh ɗin kasancewar motar wadatacciya ce. Kamar tace ba zata shiga ba tsabar baƙin ciki sai kuma taji ba zata iya yin hakan ba don haka ta shiga zuciyarta babu daɗi. Rufe ƙofar Mus'ab yayi sannan ya juyo ya kalli Subai'ah wacce tafi Noorah shaƙa da abin da Mooh ɗin ya aikata yace.

   "Bismillah." Yana nuna mata ɗayar motar alamar ta shiga nan. Da ƙyar ta iya danne kanta ta shiga motar daya nuna mata ta zauna sannan driver ya tayar suka bayan motocin ango. Motocin na kammala ficewa ƙus-ƙus ya fara tashi daga bakuna ma'aikatan da abin ya faru a gabansu da kuma mutanen dake kai-kawo a wurin a kan abin da Boss ɗin ya aikata ya kuma maze ko a jikinsa.



***** Shiru ne ya ratsa motar baka jin motsin kowa sai sautin kiɗa dake tashi ƙasa-ƙasa wan da Mus'ab ne dake zaune a kujerar mai zaman banza ya saka duk don Mooh ɗin ya kula sa su raba hali amma ya masa banza, sai ma kwantar da kan sa da yayi jikin kujera ya lumshe ido.

    A ɓangaren Noorah ba ƙaramin ɓata mata rai hakan ya kara yi ba bayan abin da ya mata tayi tunanin zai kulata ne idan ta shigo motar, amma sabanin haka tun da ya amsa gaisuwar da tayi masa lokacin data shigo ya ɗauke kai bai ko kalli inda take ba. Takai ci da baƙin ciki yasa ta kasa amsa gaisuwar da Nanah tayi mata sai ma wani kallo mai kama dana tsana data jefa mata wan da bata taɓa mata irin sa a baya ba. Ji take tsanar yarinyar na ƙoƙarin mamaye mata zuciya wan da akwai mutunci a tsakaninsu tana son Nanah sosai ita da Anisa a matsayinsu na ƙannen Mijinta.

   Amma yanzu ganin abin da Mooh yayi mata a kan Nanah yasa taji gaba ɗaya yarinyar ta fice mata a rai sai ma tsanarta dake ƙoƙarin mamaye zuciyarta, sabo da duk Macen da Mooh zai bawa Muhimmanci fiye da ita a wannan duniyar dole ta zama maƙiyiyarta. A tsarin da Subai'ah ta ɗora ta a kai cewa tayi ko Mahaifiyar data haife sa kar ta sake ta bari ta fita matsayi a wurin Mijinta, kuma ta ɗau wannan huɗubar ta ajiye a cikin ƙwaƙwalwarta don bata da burin daya wuce ta mallaki Mooh ita kaɗai har abada.


******* A ɓangaren Nanah kuwa tun da ta shiga motar ta takura jikinta ta kasa sake wa hakan yasa take ta ƴan motse-motse ta kasa natsuwa wuri ɗaya, ta matuƙar matsu su ƙarasa wurin ta fice sabo da ta lura da irin mugun kallon da Aunty Noorah ke bin ta dashi duk in suka haɗa ido. Musamman ma data gaishe ta taƙi amsa mata wan da ba haka suka saba ba. Mooh kuwa yana ankare da duk abin da Nanah keyi share ta yayi kamar bai san halin da take ciki ba.

   Mus'ab dake gaba yana kallon su ta madubi dariya ce fal a cikinsa ganin yanda ya wani hakimce a tsakiyar mata biyu tamkar duka nasa ne. 'ina fatan hakan ta kasance a kusa tun kafin abokina ya ƙarasa zare wa.' Mus'ab ya faɗa a cikin ransa. Ganin yan da Noorah ta cika tayi fam yayin da Nanah kuma take a tsorace amma mutumin ku yayi kamar bai san da kowa ba a wurin bare halin da suke ciki, wan da kuma yana da tabbacin cewa yana ankare dasu baki ɗaya.

    A haka motocin suka ƙara sa ƙofar babban hotel ɗin wan da a ciki za'a gudanar da dinner ɗin, motar na tsaya wa securities ɗinsa suka fito cikin sauri suka tsai-tsaya a jikin motarsa suna jiran fitowar su. Ɗaya daga ciki ne ya saka hannu ya buɗe ta gefen da Noorah take zaune, ƙin fita tayi duk da cewar an buɗe mata sabo da ba zata fita ta bar su tare ba. Ita kuwa Nanah ana buɗe wa ta fice da sauri har ƙafarta na lanƙwashe wa ta tafi zata faɗi. Cikin matuƙar zafin nama Mooh ya saka hannu ya riƙo ta ta faɗo jikinsa wan da tsoro yasa ta ƙan-ƙame sa tana runtse ido don ta matuƙar tsorata da kalar faɗuwar da zata yi. Kyawawan idanunta waɗanda aka ƙawata eye lashes ɗinta da maskara suka miƙe zara-zara ya zuba ma ido yana kallon yan da take ɗan motsa su tana son buɗe su.

   A hankali ta buɗe idon ganinta a jikinsa gaba ɗaya yasa kunya kama ta tayi ƙoƙarin sauka da sauri, riƙe ta yayi ya saukar da ita a hankali gudun kar ta kuma faduwa yana furta.

   "Be careful mana." Tana jin ƙafafunta sun tsaya a ƙasa bata ko juyo ba tayi gaba da sauri don barin wurin don Allah ya sani a matuƙar takure take da zama wuri ɗaya dasu ɗin. Ɗaya daga cikin securities ɗin mai suna Jide yayi wa umarnin yabi bayanta sabo da tsaro kafin ya mayar da kallonsa in da Noorah ke zaune har yanzu bata fita ba, da sauri tasa hannu ta ɗauke ƙananan hawayen da suka tarun mata tana duƙar da kai ƙasa. Kallo ya ɗan tsare ta dashi don ganin kamar tana kuka, ko me aka mata na kuka ita kuma oho? Ya raya a zuciyarsa yana ɗauke kai a nutse ya zira ƙafarsa ya fita a motar ya tsaya. Sai a lokacin ita ma Noorah ta sauke ajiyar zuciya ta fita a motar, tarin mutanen dake tsai-tsaye a wurin suna jiran fitowar su don yi musu rakiya ciki yasa Subai'ah da taga duk abin da ya faru tsakanin Mooh da Nanah matso wa kusa da Noorah tayi mata raɗa a kan ta saki fuskarta sabo videos da ake ta ɗaukar su.

   "Kiyi ƙoƙari ki danne fushinki kar ki bari mutane su fuskanci wani abu a kan fuskarki, kin ga dai yan da ake ta ɗaukar duk wani motsinki. Ki bar komai a hannuna zamu warware shi daga baya." Abin da Subai'ah ta faɗa wa Noorah kenan wan da ya bata ƙwarin gwuiwar matsa wa sosai kusa da Mooh a dabarance ta riƙe hannayen sa wan da ya ɗago ya kalle ta tayi saurin narke masa idanu alamar roƙo kar ya bata kunya a idon duniya har a fahimci cewa babu wata shaƙu wa a tsakaninsu.

  Cikin tsari mai kyau suka shiga wurin tare da abokansa manyan ƴan kasuwa da yaran manya har ma da ƴan'mata masu ji da Class da gata waɗan da suka mace a soyayyar Mooh ɗin amma yaƙi basu dama. Securities ne tako ina suke bada tsaro kasancewar manyan mutanen dake wurin da kuma shi kansa uban gayyar. Ɗaukar kai tsaye ake yi na duk abin da ke faruwa a wurin dinner duniya na kallo ta hanyar gidajen television da kafafen sada zumunta. Cikin ƙan-ƙanen lokaci labarin bikin matashin ɗan Kasuwa Muhammad Ridwan (Mooh) mamallakin M. M Master Mind Design and Build shahararren companyn dake fitar da zane da manyan gine-gine dake tashe a faɗin duniya baki ɗaya ya zagaye ko ina a duniya ya zama shine labari mafi shahara dake trending a kafafen sada zumunta.

   Biki yaci gaba da gudana cike da tsari domin kuwa abin na manya ne don duk wan da ka gani a wurin to ya kai yazo ɗin, sai dai amarya ita kaɗai ke rawar kai a wurin don ango a kamen sa yake kamar ko yaushe wan da hakan ya jawo cece-kuce daga bakin al'umma ƴan bani na iya waɗan da ke zauna a gefe suna ƙona datar su suna biyar abin da ke faruwa suna furta abin da ke bakin su. Wasu su faɗi alkairi wasu saɓanin haka, don kai tsaye wasu ke ƴada cewar auren dole ne aka masa baya so. Yayin da wasu ke ƙaryata hakan ta hanyar cewa babu wan da zai yiwa Mutum kamar Muhammad (Mooh) auren dole, kawai dai jiji da kai ne irin na masu kuɗi. 

   Wasu kuma a gefe kariya suke bashi ta hanyar cewar ba jiji da kai bane kawai tsananin kame wa ce da kwarjinin da Allah ya bashi, to kowa dai da abin da yake faɗa wan da shi wan da ake yi a kan nasa bai san suna yi ba hasali ma hankalinsa gaba ɗaya yana kan Nanah da tunanin in da ta shiga don tun da suka shigo bai ganta ba sai daga baya ne idanunsa suka kai kanta tana zaune ita kaɗai a sit yayin da hankalin wasu samari biyu dake zaune a gefen ta yake kana. Ji yayi ran sa na masifar ɓaci don ya lura cewar duk wani Namijin da hankalinsa ya kai kan Nanah baya taɓa iya dai na kallonta, gaba ɗaya zama a wurin ya gundere sa don haka yana gab da tashin dinner ɗin baki ɗaya.

***** A ɓangaren Nanah kuwa lokacin data samu ta fita daga motar da take jinta tamkar kurkuku ajiyar zuciya ta sauke ta shaƙi iska sosai, sai da ta tsaya ta natsu kafin ta shiga takawa zuwa cikin hole ɗin. Bata san cewa security na bin ta ba sai da ta isa bakin ƙofa zata shiga aka dakatar da ita don masu tsaron ƙofar basu santa ba tun da ba na Mai ƙusa Mansion bane na musamman ne aka ɗauko su. Tsaye tayi ta rasa abin cewa don ita dai ba wani kati ne da ita ba da zata nuna kasancewar su ƴan gida yasa basa buƙatar nuna kati, tana ƙoƙarin juya wa ne gurd ɗin mai suna Jide ya mata magana.

   "Madam yo can enter." Ɗago ido tayi ta kalle sa sai kuma ta ɗaga kai ta wuce ganin masu tsaron ƙofar sun buɗe mata da girmamawa wan da bata san mai Jide ɗin ya faɗa musu ba. Koda ta shiga cikin wuri kawai ta samu tayi zaman ta don ta duba bata ga Sis ɗinta ba ko Ya Khalid sai su Nihal da sauran yaran Mai ƙusa Mansion dake ta shagalin su

    Tana zaune ita kaɗai abin ta wanda ya mata magana su gaisa har Ya Ammar ya samu ya zame daga wurin Suhaima data maƙale masa ya fice ya kira Nanah a waya ya sanar mata cewa ta fito yana waje yana jiran ta. Babu musu ta miƙe ta fice sabo da zaman cikin ya ishe ta koda ta kira Anisa kuwa sanar mata tayi suna tare da Ya Khalid ga su nan zasu ƙara so.

   A kan idanun Mooh Nanah ta miƙe ta nufi hanyar fita yana kuma kallon waɗan nan samarin suka miƙe suka bi bayan ta. Kai tsaye in da Ya Ammar ya faɗa mata yana can ta nufa in da ake ajiye motoci kusa da motarsa ta same sa a tsaye yana danna waya. Da sallama ta ƙara sa ya ɗago yana amsa mata fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    "Shine baki jira nazo na ɗauke ki ba." Ya faɗa yana kallonta don ta matuƙar yi masa kyau ba kaɗan ba. Murmushi Nanah tayi masa tace.

   "Hammah Mooh ne yace na biyo su." Kallonta Ammar yayi yana ƙoƙarin magana su Mabaruka suka ƙara so wurin ita da Yusrah, Nihal, da Nawal sai Siyama yarinyar Hajiya Badariyya da suke tare da Yusrah. Mabaruka ce ta gayyato su duka don a kan idonta Nanah ta fito hakan yasa tabi bayanta.

   "Allah yasa dai ta faɗa maka cewar ita ɗin sauran ƙartin ƙauye."

   "Maganar Mabaruka kenan data shiga kunnuwan duka waɗan da ke wurin ta gir-giza zuciyar Nanah da Ammar baki ɗaya har ma da Samarin da suka biyo ta da niyyar yi mata magana. Ɗagowa Nanah tayi ta zuba wa Mabaruka ido tana kallon fuskarta don tan-tance abin da magan-ganun ta ke nufi.

   "Wace irin maganar banza ce wannan ɗin?!." Ya Ammar ya faɗa a matuƙar fusace tamkar zai kai mata duka. Da sauri Mabaruka taja da baya tana cewa.

   "Daka ta Ya Ammar, nifa taimakonka kawai zan yi gudun kar ka ɗauki kura da fatar akuya ne...." Shiru tayi kafin ta juyo ta kalli Nanah ta nuna ta da yatsa tace.

    "Baka san wace ce asalin yarinyar da kake ɓata lokacin ka a kan taba.... Wannan da kake gani ba wata kamila bace kamar yan da take nuna wa. Ita ɗin munafuka ce makira wacce ta gama yawon iskancinta a ƙauye tazo nan take yaudarar mutane da nuna kanta a matsayin wata saliha, dalilin da yasa ta baro ƙauyen ma shine kamata aka yi tana zina da wani ɗan bautar ƙasa da yaje ƙauyen da take... Tun tana shekara sha uku ta gama wulaƙanta kanta sabo da haka tun wuri gara ka nemi matar aure don wannan bata dace da kai ba." Mabaruka ta ƙare maganar hankali kwance ba tare da jin komai ba a kan tozarta ƴar uwarta da tayi ba a gaban mutane.

   Ai kuwa gaba ɗaya salati mutanen wurin suka ɗauka yayin da su Yusrah suka shiga tofa albarkacin bakinsu suna aibata Nanah tamkar basu haɗa jini da ita ba. Hayaniyar da suke yi ce ta fara janyo hankalin mutane zuwa gare su don haka cikin ƙan-ƙanen lokaci maganar ta fara yaɗuwa a wurin. Ya Ammar dake tsaye tamkar gunki kallon Nanah kawai yake yana jiran jin wani abu daga bakinta. 

  Nanah kuwa tun da ta ɗauke idonta daga kan mabaruka ta shiga bin fuskokin mutanen wurin da kallo har zuwa kan Ya Ammar daya zuba mata ido tana son yi magana amma abin da ya danne mata ƙirji ya hana ta furta komai, tun da take a rayuwarta bata taɓa jin ta muzanta irin yau ba. Kai ko waccen ranar da wan cen tsautsayin yaso faruwa da ita bata jin kunya irin yau ba, hasali ma a wancen lokacin tsoro ne da firgici suka tarar mata. Amma a yau data girma tayi hankali, a yau da wacce ke amsa sunan ƴar'uwarta tayi mata irin wannan tozarcin a gaban wanda take burin aure, wan da take so ya ganta da mutunci da ƙima fiye da kowa sai taji ta tsani kanta.

   "Say something Maryam." Muryar Ya Ammar ta dira a cikin kunnuwanta, ƙoƙarin buɗe baki tayi zata yi magana kawai ta yanke jiki ta tafi zata faɗi inda cikin ikon Allah ta faɗa a hannun Mooh da isowarsa kenan ya maza ya tare ta zuciyarsa na bugawa da ƙarfi ya ƙwala kiran sunanta, a dai-dai lokacin ne kuma Ya Khalid da Anisa suma suka shigo wurin. Kallo ɗaya ya yiwa Jide ya fahimci abin da take nufi don haka cikin sauri yaje ya matso da mota wurin.

   Hannu Hammah Mooh ya saka ya ɗauke hannun Ammar dake ƙoƙarin riƙe Nana shima duk a ruɗe, miƙe wa yayi ɗauke da ita ya shiga cikin motar da Jide ya buɗe masa ba tare daya furta komai ba don ransa a matuƙar ɓace yake. Ya Khalid da Anisa suma da gudu suka ƙara so wurin suna kiran sunanta da tambayar abinda ya faru, sai dai kafin suyi wani yunƙuri driver ya tayar da motar ya fice da mugun gudu, cikin sauri suma suka faɗa motar suka bi bayansu gaban Ya Khalid na wani irin tsits-tsin kewa.......

   Alhamdulillah!! A nan ne na kawo ƙarshen labarin Komai tsanani par 1 wan da yazo maku a free. Mu haɗu daki a part 2 don war-ware-war duk wani abin da ya shige maku a duhu....

  Yaya rayuwar Nanah take kasancewa bayan wannan bankaɗar sirrin da Mabaruka tayi mata?.

   Shin wai ma a ina Mabaruka ta san wannan sirrin na Nanah bayan bata taɓa sanar da ita ba?.

  Shin Nanah zata cika burinta na zama Nanar da tayi ma Mamanta alƙawari?.

   Yaya rayuwar Mama da Sulaimanu ta kasance a ƙauyen Cigama bayan baro war Nanah?.

  Ina labarin Salmanu da Ilu da Mooh yasa aka ɗaure?.

  Wane hukunci Ya Ammar yake yanke wa a kan alakar sa da Nanah bayan jin wannan maganar?.

   Meye asalin abinda Hammah Mooh yake ji a game da Nanah?.

   Rayuwar Noorah a gidan Hammah Mooh?, burin Subai'ah a kan Mooh da duk abin da ban lissafo ba zaku same su ne a cikin *Komai* *tsanani* par 2 wan da zai fara zuwa gare ku ranar Monday 11/5/2022. Labarin zai zo muku ne akan farashi Naira dubu ɗaya (1k). Ƴar'uwa ki hanzantar biyan naki don ci gaba da wannan zuzzufar tafiyar wacce ta ƙunshi abubuwa da dama a cikin ta , abin da zaki yi kawai shine ki tun-tube Ni a wannan number *** don biyan naki kuɗin domin samun damar shiga Paid group wan da a can ne zaki samu duka amsoshin tambayoyin ki.

   Taku Oum Fatima wacce ta saba kawo maku labaran da