Chapter 2
________________________✍️
Kallonta iya tayi tana mai faɗin
"Kiyi haƙuri Maryam Papan ku yana iya ƙoƙarin sa, amma haryau shiru kakeji Allah yasani ina tausaya miki sosai, domin wannan matar batada tausayi ko kaɗan, kanta kawai tasani sai kuma yaranta."
Share kwallar idanunta tayi.
"Iya ban san menene yake damuna ba. haryau nakasa sanin ni wacece?.
Wai dama mutum yakan manta ko shi waye?. A'ina ya fito?, suwaye danginsa? Hatta mahaifiyata nakasa tunawa fa."
Ta ƙarasa maganar tana mai sake fashewa dawani sabon kuka
mai cike da ƙunar zuciya.
*Abuja, Nigeria*
Zaune yake a gaban Dressing Mirror
yazu bawa wani katafaren zane da akayi na Art kyawawan idanun sa.
Kallon zanen yake yi yana zubar da zafafan kwalla,
magana yake tamkar wani zautacce.
"A'ina kike ne?, me yasa kika min hakan,
Shinko kin san wani kalar raɗaɗi nake fama dashi a silar rashin ki?,
Me yasa biki yi tunanin irin halin da zan shiga ba, a dalilin rashin ki?..."
Kai duba na nayi kan fuskarsa kyakkyawan Namiji mai cikar kamala da kwar jini ma abucin
kyawun fata dana fuska, fuskar tasa zagaye
da siririn gemu irin na gayun wannan zamanin.
Duk da cewar a zaune yake hakan bai hanani gano tsayin da Allah ya hore masa yana da tsayi
dai dai misali, ƙara duban sa nayi sai yanzu nagano wai ashe yanada tabon sallah ago shin sa.
Yanda yake magana zaka ɗauka tare yake da wani ko wata a Bedroom ɗin, duba da yanda yake kallon gefe ɗaya.
Turo ƙofar akayi tare da sallama,
ko motsawa bai yi ba yadai amsa sallamar sanin muhimmancin ta.
Macece matashiyar tsohuwa mai ki manin shekaru Arba'in a duniya.
Kallonsa ta tsaya yi nawasu Ƴan mintuna sanna ta ƙaraso kusa dashi, dafa kafaɗar sa tayi.
hakan yasa ya juyo ya kalle ta bata ce masa komai ba ta fara share masa hawayen fuskarsa.
Har ta kammala bai yi magana ba. cikin muryar rarrashi ta fara magana.
"Marwan kayi haƙuri mana kaza ma Namiji mai juriya mana. Tabbas na sa ni abin da ciyo, amma ya zamuyi da hukuncin Allah?.
Insha Allah za'a ganta kaji, nan bada jimawa ba.
Kasan Doctor yace 'Ka ra ge tunane tunane sosai,
Please karka ja mana ciwon ka yatashi zamu wahaltu sosai."
Kallon mahaifiyar tasa ya yi cikin karayar zuciya Yake faɗin
"Momy juriya fa kika ce?,
Zan iya juriyar komai a duniya tabbas, banda rashin ta. Bazan iya jurewa ba. Haƙuri Momy taya zan yi haƙuri?,
Zuciyata ba za ta ɗauka ba ji nake kamar zan yi hauka Momy.
Please Momy ki gaya min inda ake cire soyayya, naje a cire min soyayyar ta daga zuciyata, wata ƙila zan samu sassaucin abin da na ke ji.."
jin yadda yake magana yasa Momyn fashewa da kuka ita ma cikin tausayawa ta ce
"Haba Marwan dan Allah kayi shiru mana kasan baka da wata isasshiyar lafiya, so kake ciyon ka ya tashi ne?."
Cikin zubta kwalla mai zafi ya girgiza kai
"A'a Momy nakasa jure wane kawai."
"Kayi hakuri Marwan taka kalar ƙaddarar ke nan."
Rarrashin sa ta ci gaba dayi har tasa mu ta shawo kansa ya daina kukan
da suru tanda yake yi, ta fita ranta na mata suya.
Kasan cewar Ranar Friday ne yasa shi miƙewa yanufi toilet.
A kalla yashafe one hour kafin ya fito
ɗaure da towel.
A wurin da ya tashi a nan ya koma zauna, nan ya fara shafe jikin sa da Body Lotion na maza masu matuƙar tsada da ƙamshi dama shiɗin ma'abocin ƙamshi ne, yakai kusan twenty minute's yana abu ɗaya kafin ya miƙe ya nufi zuwa Closet ɗin sa yaciro wata arniyar Shadda Golding color.
Kama daga Takalman ƙafafunsa A gogonsa, Hularsa duk Golding color's ne..
Sai da ya kammala feshe jikinsa da daɗa-ɗan Turare masu ƙamshi, sannan ya kalli kansa a Mirror idanun sa suka ciko da kwallar baƙin ciki, duk lokacin da ya yi shirin fita wani wajen sai ya tunata ita wato Tauraruwarsa.
Saurin kawarda tunanin ya yi ganin zai makara.
Farfajiyar gidan ya fito gidane ƙaton gaske mai ɗauke da manyan part guda huɗu, gidan zagaye yake da flowers masu ƙamshi da sanyaya rai.
Securities suna hangosa suka ta so da han zari dama all ready a shirye suke.
Buɗe masa motar ɗaya daga cikin securities ɗin ya yi yana mai ƙamewa alamar girmamawa.
M̆̈ŏ̈r̆̈ĕ̈ C̆̈ŏ̈m̆̈m̆̈ĕ̈n̆̈t̆̈😇☆☆M̆̈ŏ̈r̆̈ĕ̈ T̆̈y̆̈p̆̈ĭ̈n̆̈ğ̈📲
αʅƙαʅαɱι ყαϝι ƚαƙσbi
Following up to my channel 👇
***
***