blackmail
by @surayyahms
17..🦋🦋🦋
Hannunsa ya dora akan cinyarta yanamai sakar mata wani irin shu'umin murmushi ayayinda suke kallon juna yace "are u sure? tana dan lullumshe ido tace"yes. anything for u gyara xamansa yay yace" my birthday is coming up next week..cikin gwalo ido tace really? ya shafa gefen fuskarta yana murmushi ahnkli yace yes babe.
kafin tace wani abu cikin datsar numfashinta yace
"so here is the plan, dama akwai wata student ne datake so ta bata min suna acikinku, infact, yau tagaya min ido da ido cewa she is going to report me sbd aganinta ban dace da matsayina ba kuma nasan kawai attention dina take so desprately shiyasa take so tay min sharri nd it wll seriously affect my career.
cikin katsesa da mamaki tace ban fahimce ka ba sir, kana nufin har akwai wacce take so tamaka sharri a camp din nan,.i tot all the girls here are crushin on you..
cikin lumshe ido da budewa yace"yes but not all babe, akwai wanda bayana kawai suke son gani dan ban kulasu ba nd today she even threathen me..
deeja tace wow amma waye ne yarinyr haka?
yadan yi shiru suna kallon juna sai can yace"hmmm i cant tell you..adan dame tace why not?i tot ure my bf now,..ya riko hannunta yace yess, yess my love. kawai dai banason kiji babu dadi aranki ne, u knw i love u, kuma yarinyar najikinki ne sosai gaskiya banason na hadaki rikici da wata. inaga ma zan fasa kawai gara a koreni anan din kinga sai akawo muku wani mei ilimi da basira yazo ya karasa muku.
cikin gwalo ido tace "noo, haba kadena cewa haka mana mr abdul ka tabbata yarinyar najiki na ne?
ahnkli ya gyada mata kai
cikin sauke ajiyar zcya tace toh dan Allah nide kagaya min wacece nd i will help you da koma minene ai alkwari namaka.
da murmushi me sanyi a fuskarsa yace "dats my girl. ni ko da baki taimakamin ba wnn kalaman naki kadai yana sakani cikin nishadi
tay murmushi tace thanks amma har yanxu dai baka fadi sunan wacace makirar yarinyar datake ta raba ni dakai so soon haka ba.
ya riko hannunta kmr maijin nauyi ahnkli yace "i think her name is Ush..sumting kee ni ban dai rike sunanta dakyau ba amma ai naga kmr kawarki ce ko?
da yanayin mamaki tace kana nufin ushna???
ya gyada kai, da karfi tace wow...oh my god amma meye ya hadaku...
da fuskar tausayi yace wallh haka kawai ta tsaneni, so i ask her meyasa bata zuwa field nd she said alot of bad things abt my skills. na lura kmr yarinyar tana mugun ji dakanta ne maybe is bcos she thinks she is so smart.
Cikin kyabe baki tace yeah, she is smart. the only economics topper for yrs. kuma kasan tunda tasamu gulf royal invite a dubai dinnan take wani daukar kanta wani abu. nikaina da kake gani ynxu haka ba shiri muke da ita sosai ba she is soo annoying, she thinks she is bettr than anyone
yace 'Well i mean no harm for her, amma ynxu fa dole sai da taimakonki kafin nan zan samu daman cigaba da zama dake anan, saiya danyi shiru, can kuma ya daga ido ya kalleta yace "tsakanin ni da ita one of us had to go. dan idan tana nan wallh zata cigaba da saka mana ido idan kuma bata nan kinga zamu iya yin abunda mukeso witout fear you can even visit my lodge anytime u want kinga ahaka zamu kara shakuwa ko
tana murmushi tace "to me kake so ayi?
fararen idonshi ya daga sama kamr mei tunani can sai ya hau gaggaya mata plan din muryasa kasa kasa har saida ta gamsu sosai ta kuma masa alkwarin hakan zaiyu.
bayan sun gama kulla sharrinsu hakanan ma ya lallatsata tare da mata alkwarin soyayya da aure dan har sunan iyayenta yanemi ya sani da karyan cewa bada jimawa ba zai tura gidansu anema masa izinin nema.
kdeeja tana cikin tsananin farinciki har tafice a motar ta dawo field abunta.
tundaga ranar kuma tafara sakawa ushna ido sosai dan haka kawai suna zaune xata kafa chapter mr abdl dantaji abunda ushna zata fada, nd frm her dismissive comentz tafara gane tabbas kmr ushna tana da wani matsala da mr abdul ta lura kmr ma ita kadaice a grp din kawai gayen baimata ba. tuni ta dau zafi dan dama kuma tunda ushna ta samu dubai invite din nan take jin haushi da kishinta bana kadan ba
haka suka hade kai da mr abdul, kwana biyu ushna ta dawo field amma sai taga komi yana kkrin canzawa
mr abdl yafara kama ajinsa yana baya baya da mata snn yana son taimako, da tsananin nuna tausayawa wa dalibai a fili, at first ushna ta dauka duk na ganin ido yakeyi kodan sabda kin aminta da abotansa datay amma saitaga kusan ko wani rana practical dinsu nayin dadi sosai,is full of fun moments yana tsayawa yanuna musu practically dalla dalla
bayan kamr kwana hudu da tafara sake jiki tana fita sai kuma taga abubuwa kala kala na bn mamaki yana faruwa da ita, girls are alwys coming at her rudely haka kawai sai taga an tureta akasa, ko an tsoma ta ruwan pool, ko awatsa mata abu marar tsafta ajiki in the most embrassing way acikin mutane nd then mr abdull is always the one helping her just to appear as a good guy.
Ita kanta deeja bata gane cewa ba ita kadai ce macen da mr abdul ya latsa a bayan gida ko motarsa snn yayiwa karyan zai auresu ba duk dan su tayashi aiki akan ushna.
wanda kusan dabia ne na mayaudarar maza zasu iyayin komi dan suga sun durkushar da yarinyar datafi karfinsu ko sukaga da alaman bazata taɓa fadawa a tarkonsu ba.
bayan kwana biyar ana zuwa field ushna bata gane meke faruwa da ita ba, mr abdl is now the one defending her while her frend deeja kullum sai tace mata laifinta ne da komi yake faruwa da ita sbd tana nuna ma jamaa ita mai ilimi da kyau ce dole kuwa ta rika samun matsala da mutane.
maganganun deeja yakan mata zafi amma bata daukesa wani abu ba kwasam aka fara hirar birthday na mr abdul duka members na grp B suka taru sukay meeting nan aka shirya cewa kowa zaiy kawo gift na white shirt, ko hanky, da hand writen note da za'a bawa mr abdl as birthday camping debut kuma surprise duba da yadda yake musu kirki yake jansu ajikinshi snn yake taimaka masu sosai
kai tsaye ushna tace musu tunda ba part of abunda yakawosu nan ba kenan ita gaskiya bazata iya ba..
mutane dayawa sunji haushinta aransu wasu basu damu ba saidai suna komawa dakinsu Deeja ta jefa mata wani irin mugun kallo maicike da takaici kafin nan tace cikin murya mai rawa rawa da ɓacin rai
“Kin san me ushna?
ushna ta juyo tana kallonta batace komi ba..
deeja ta matso tana kallon cikin kwayar idonta da bacin rai tace "tun ranar dana fara saninki kika kasance haka, sooo selfish kinada mugun son kanki, ure egoistic nd self obessesd Kullum kina kallon mutane kmar wayaye ankasa kaiwa inda kike
Ushna ta dago jajayen idanunta tana kallonta cikin rashin fahimtarta amma deeja bata tsaya ba.
Wallahi baki tsani mr Abdul saboda yayi miki wani abu ba,kin tsane sa ne saboda baya bin salonki. we all know that Kina son ki zama centre of attention a koyaushe. yes kowa yasan Kina da kyau, kina da ilimi, everybody knows that! tun da aka fara wannan bootcamp ɗin nan baki taba tunanin feelings din wani ba sai naki Kullum sai kin nuna mana kamar ke kinfi kowa hankali tunani da wayo.
zuciyar Ushna yana bugawa da karfi sosai tace deeja what the hell are u talkig abt...ban fahimce ki ba fa
da harara da kima tsawa deeja ta kara matsowa kusa da ita cikin fushi tace "ohh now hou want to claim mrs oblivious? kina nufin baki gane cewa kowa ya tsaneki a camp dinnan ba ne sbd ure always againts everything
da bacin rai ushna tace "i am not againts everything deeja, ni ban taɓa hanaku yin duk wani abun da zakuyi ba, ban hana kowa yin kalar muamalr dayake so yayi a camp dinn ba, dan nace ni bazan yi abu irin naku ba i dont think it shud be a problem for anyone. my life, my rules, my choices.
da ihu deeja tace "But this is a group work fr god sake meye aciki dan anhada kai anyi abu dake ehh, what did u think you are, a queen??? see, naga alama kmr wnan friendship din namu ba zaije ko’ina ba msmn idan kika cigaba da wannan giant ego dinkin dan a ƙarshe kece zaki rasa mutane saboda kina ganin kamr kowa bai kai matakin tunani da iliminki ba.
afusace ta juya zata fita ushna ta tsaya cak, sai kuma ta juyo tana kallon ziyada idonta ya ciko da ruwan hawaye ahnkli tace 'ziyada...u havent said anything
..ko kema abunda kikeji kenan akaina
ziyada tace “Khadija was mean nd not entirely right abt ur personality…but comn ush, meye ne aciki idan kin bada gudumawa wa gayen nan, beside is a camp debut yakamata ace kowa yayi .kuma gayen nan has helped u many times dis week, haba kodan haka zaki bashi just to rmber.
hawayen da suka taru a idonta suka zuba ta share ahnkli tace "its okay,.naji.
daga haka bata kara cewa kowa komi ba ta cigaba da abunda ke gabanta duk dama ranar magangnun deeja ne kawai yayita yawo acikin brain inta
dagata dayan bangaren kuwa tuni deeja taje ta sanar da mr abdul cewa ga nan abinda tayiwa ushna a daki and she is sure she wll take part in d debut after that melt down sbd tasan ushna tana da taurin kai amma kuma tana da sanyin zuciya da hakuri.
bayan kwana biyu yau yakasance birthday din mr abdul kuma haryau deeja da ushna basu kara cewa junansu uffan ba.
daga fanin mr abdl kuwa duka yan matansa na camp din dayawa tuni suka tura masa birthdy texts da safe amma ko guda daya bai iya bari awayrsa ba kusan yana karantawa atake yake marza marza wajen gogewa dan hatta na matarsa rihanna bai bari ba sbd tsaro...
haka ushna ta danne zucyarta ta saya pure white calvin klein shirt din da sukace asaka, kusan ta internet duka akay siyayya kowa ya kure adakarsa wajen zabo abu mekyau da armashi, ita kuma rigar kawai ta saka acikin gift wrap kuma bata tsaya yin wani hand wrting note ba sbd harga Allah bata san me zata rubuta masa ba dan bataga dalili da zata shiga rayuwarsa ba.
badon matsalar da suka samu da deeja ba ma da dik bura ubar da zaayi da bazata jonasu ba, bt deeja was her childhood frnd,, tare sukay primary har scndry a boarding house, inde har deeja zata iya gaggaya mata maganganu irin haka masu tsananin zafi toh hala laifinta ne,nd dats why kawai ta hakura ta siya rigar amma badan komi ba.
sosai ziyada taji dadi dataga ushna ta saya da sassafe suka shirya sunje cin abinci kenan deeja ta sabule acikinsu daga baya tadawo ta shigo dakin cikin sauri sauri ta bude gift din ushna ta saka mata wani irin white designer handky dayaji turare ta tula pack na condoms aciki tay wraping, snn ta rubuta note agefe dayake cewa 'Happy birthday mr abdul,Consider this condoms as my way of asking for a private moment with you after the lights go out. Just you, me, and whatever tension we’ve both been pretending not to feel.
from..ushna..
bayan ta shirya komi she make sure tamaida duka wrappings din kamar ba ataba ba, tay sauri ta koma wajen cin abinci kamr bata aikata komi ba. text kawai ta tura masa cewa tagama aikin dayasata in sha Allah yau he wont only get to suspend ushna from the camp har disgracing inta agaban dalibai sai yayi.
atunaninta yau ta kawo karshen ushna kenan a wann camp din, she was so relaxed har suka gama cin abinci lafiya suka dawo daki domin daukar jakan su.
da gefen ido take lura dasu har saida kowa ya saka gift dinsa ajakrsa suka wuce pavilion wajen da kowa zai taru, dan sunyi akan tare za'a bashi gift din tunda basu da yawa a grp din, he will open every gift agaban su duka ana masa video da wakan birthday snn xai karanta each nd every hand writen notes din su agabn kowa.
suna isa pavilion suka samu an cika waje ga malamai da matrons da oda student daga grp A,C,D har E duk sunzo dama 10 students each aka rabasu.
anan ne ma ushna take sanin cewa ashe mr abdul shine general senior supervisor na duka LSE bootcamp program din kowa da kowa yazo nan ne dan ayi celebrating dinsa a matsaynsa na shugaba.
SHARE UR COMENTS
AND SHARE.
TALES OF THE WAZEERIS
BY
SURAYYAHMS
***