SARTSE COMPLETE

05

by @legendspen

*SARTSE*
-Amanar-Janafty-
*Sayyid Legendspen*
MAH/2026/001

Sadaukarwa.

RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA
(Mai Dambu) 

Shafi na biyar
    (05)


Tunda Alhaji ya fara magana gabana yake faduwa, aure kuma? Ni ba auren ba ma wallahi kwata kwata bana son mutum ya girmeni sosai, gaba daya shekara ta sha bakwai, Isah Nadabo a yanzu ya kai wajen talatin, ni nafi son yaro dan shawalwali, wanda baifi 26 ba haka, maganar Hajiya ce ta katse min tunanin da na shiga da na tana cewa. 

“To Alhaji kamar Isah Nadabo ai yafi ƙarfin haka a wajenmu ko, da an bashi.” 

“Kai Hajiya!” 

Na faɗa a raina, Alhaji ne ya ce da ita.

“A’a dai, ai bama za ayi haka ba ita yarinyar ba ta da zaɓi ne?” 

“Ai shikenan dai, Allah Ya bata na gari.” 

Alhaji ya ce.

“Amin.”

Ni dai nan zaune bance ko ƙala ba, amma naji dadi gaskiyya, na auri Isah Nadabo na ce na auri wa, ƙanin babane ko me? Babba dashi da ace ya yi aure a shekara goma sha wani abun da yanzu yana da yarinya kamar ni, kowacce ta girmi ni ma. Gashi wani baki ma, ni Allah Ya gani ina son dan gayu dan zamani, shi kam kallo daya zaki yi ma Isah Nadabo kinsan mutum ne mara walwala, kansa a kulle yake. 

Daga wannan rana ba a sake wata magana da ta shafi Isah Nadabo ba, kuma nima na ji daɗin haka, haka na ci gaba da rayuwa ina ‘yan matancina a gida har zuwa ranar da ƙaddarar Yallaɓaina ta faɗa mini. 

Ranar wata lahadi bayan sallar magariba na fito daga gida ina shirin tafiya makarantar dare da nake zuwa, wacca gaba daya banfi a sati biyu da fara zuwanta ba. Tafiya nake kamar ko yaushe cikin nutsuwa,kamar ance ɗaga idonki. 
Kyakyawan matashin saurayi, mai kyakyawan yanayi da kyakyawar shiga, fuskarsa fara ce sosai yana da tarin kwantacciyar suma. Gaba ɗaya kammaninsa ba sa yanayi da na ‘yan nigeria sabida yanayin idonsa har wani walƙiya suke mai daukan ido, hancinshi mai matsakaicin tsini haka bakinsa, wani kyakyawan gashin baki ya yi masa ƙawayan ya gangaro gefe da gefe ya haɗe da ɗan ƙaramin gemunsa. 

“Ya Hayyu Ya Qayyum!” 

Abinda na faɗa a raina, sannan na ce.
“Wasu kamar sune suka hallicci kansu, sabida tsabar tsagwaran kyau, ina ganin Yaya Ridwan yafi kowa kyau ashe mummunane a gaban wannan.” 

A hankali ya fara ta kawo yana tun karo ni, wani irin “Dif! Dif!” Na ji ƙirjina yana bugawa, ƙafafuna suka fara karkarwa, ƙwalla ta taro a idona sakamakon matsanancin bugun da zuciyata take mai ƙarfi. A lokacin da ya matso gab da ni, sai da na ji numfashina ya ɗauke na daƙiƙa.

“Salamu alaikum.” 

Wata sassanyar murya mai yanayi da busar sarewa ta shiga kunnena, bayan sassanya ƙamshin turarensa ya cika min rayuwa gaba ɗaya.  

“Ina wuni?.” 

Na tsinci kaina da faɗa har da durƙusawa, ya yi murmushi sannan ya ce.  

“Gidan can zan aiki ki.” 

Ya faɗa yana nuna min gida dake kallon namu, na juya na kalli gidan sannaan na ce. 

“Toh!” 

“Nan ne gidan Alhaji Hadi ko?”

Ya tambaya, ni kuwa jikina har ɓari yake amsa tare da gyaɗa kai. 

“Eyh! Nan ne.” 

“Ki shiga ki ji yana nan? Idan yana nan ki ce masa Fahad Ta’ambo ne, wanda su ka zauna tare a jirgi daga Dubai zuwa Nigeriya, ya yi mantuwar ne a cikin jakata shine na zo kawo masa.” 

Tun da ya fara magana gabana yake faɗuwa har ya ƙarashe. Yana gamawa kamar wacca aka umarta na fara tafiya, ban tsaya ba sai da na shiga gidan, bayan na isar da saƙon Alhaji Hadi ya ce dani yana zuwa, na dawo na faɗa masa ya yi min godiya, amma maimakon na kama hanyar makarantar sai na dawo gida, gaba daya ji na nake wani sukuku, unguwar ta yi min faɗi, ƙamshi turarensa ne ka dai yake yawo a kwanyar kaina, sai kuma maganarsa tun daga farko hat karshe, ban manta ko kalma daya ba. 


“Ki shiga ki ji yana nan? Idan yana nan ki ce masa Fahad Ta’ambo ne, wanda su ka zauna tare a jirgi daga Dubai zuwa Nigeriya, ya yi mantuwar ne a cikin jakata shine na zo kawo masa.” 


Abinda na fada kenan da safe bayan na buɗe idona, da sauri na daki kaina tare da faɗin. 

“Rawasiya wake-up, me yake damunki ne haka?” 

Miƙewa na yi tare da nufar banɗaki na wanke baki na na fito zuwa tsakar gida, sai da ƙamshin turarensa har yanzu yana yawo a hancin na, 
yanayin da na ji jiya yana nan kamar yanzu yazo unguwar. 

Haka kwana daya ya wuce ina jin wannan yanayin a tare da ni, kwana na biyu ya wuce, sai da na yi sati sannan na ji yanayin ya fara raguwa, sai da na ɗau tsawon wata guda ina fama, kafin manta amma kuma har lokacin kammaninsa da sunan sa suna nan a kwakwalwata, domin a kallo daya kwakwalwata ta dauƙi hoton sa, wanda ya tsaya a a zuciya.

Ranar da Allah Ya nufa zan sake ganinsa ranar wata laraba da yamma, lokacin Hajiya ta aiki ni gidan wata ƙawarta a fagoji, banson zuwa fagoji kwata kwata, ni ba ma fagoji ba gaba daya ban fiya son zuwa wani waje nesa ko kusa ba. Daidai bakin titin Rasheed shekoni special hospital mashin din da nake kai  ya tsaya, me mashin ɗin ya tsaya yana duba mashin ɗin ni kuma na sauka ina jiranshi.  

A jiki na naji ido na yawo a kaina baya ga matsananciyar faduwar gaba da naji. Ina kai idona bakin asibitin na ganshi tsaye ya harɗe hannusa a ka faɗa yana kallona. Da sauri na sunkuyar da kaina ƙasa ina faɗin. 

“Wayyo Allah.” 

Dan wani irin ƙarfaffan bugu zuciyata ta yi lokacin da muka haɗa ido dashi. 

“Sannunki.” 

Na ji muryarsa dab da ni sai dai na kasa ɗagowa, idanuna suka kai kan ƙafarsa, takalminsa ma kaɗai abun tsayawa a kalla ne. 

“Kamar ke ce ta unguwarsu Alhaji Hadi ko?” 
Da sauri na gyaɗa kai, tare da faɗin. 

“Eyh! Ni ce.” 

“Lol, me kike yi anan?” 

“Mashin ne ya sami matsala, amma gashinan ya gama dubawa.” 

Ya kalli mashin din sannan ya kalli ni. 

“Kuma a wancan unguwar kike?” 

Ya faɗa yana baya da hannu alamun can. Na gyaɗa kai tare da cewa. 

“Eyh! Yalwawa.” 

“Uhm! I see.” 

Ya faɗa yana shafa gashin bakinsa daga tsakiya zuwa gefe sannan ya ja shi zuwa ƙasa. 

“Mu tafi ko?” 

Mai mashin ɗin ya faɗa, na juya zan hau mashin ɗin sai na ji ya ce. 

“Na ce ki tafi?” 

Ba shiri na tsaya kaina a ƙasa. 

“You’re eager to go, kin gaji ko?”

Ya faɗa cikin wani irin yanayi na fushi, da sauri na girgiza kai sannan na ce. 

“A’a, bangaji ba…. Me mashin ɗin.” 

Kallon me masahin ɗin ya yi sannan ya ce. 

“Malam ka jira.” 

“Alhaji sana’a fa nake, idan na ajiyeta wasu zan ɗauka.” 

Hannu Ya sa a aljihu ya zari kuɗi ‘yan dubu dubu da a ƙalla sun kai guda goma ko sha, ya miƙa masa. Ba shiri me mashin ɗin ya amsa tare da matsawa gefe ya zauna, a raina na ce. 

‘Yanzu mu dai babu yaren da muke ganewa sai na kuɗi.” 

“So ba zaki tambayi sunana ba?.” 

Ya faɗa yana kafe ni da idanun da nake jin su tamkar na zaki sabida kaifi. 

“Ka yi hakuri ai naga ranan ka faɗa min.” 

“Ni… when?” 

“Da ka ce na cewa Alhaji Hadi Fahad Ta’ambo ne.” 

Shiru ya yi yana kallona na kusan minti biyar sannan ya ce. 

“So kin ma riƙe sunana, shine da kika ganni kika yi kamar baki sanni ba ko? Na gode.” 

“Ba haka ba ne, ban kula da kai ba.” 

Na faɗa murya ƙasa ƙasa. 

“Amma ni na kula da ke?” 

“Ka yi haƙuri.” 

“It’s fine, you can go. Na gode.” 

Shiru kamar an shuka ni a wajen na kasa matsawa. 

“You can go fa.” 

“Ka yi haƙuri.” 

“Kije kawai.” 

Ya faɗa yana barin wajen, sai da ya shiga cikin motarsa sannan na iya matsawa zuwa ga mai mashin ɗin, ya ɗauke ni muka ci gaba da tafiya. 

Gaba ɗaya hankali na ba yaga hanya, na tafi tunanin wannan mutumin, komai na shi burgeni yake, ya iya magana. Amma abinda ya bani mamaki shine kwata kwata banji ya tambaye ni sunana ba, ko da yake mene alaƙarshi da sunana da zai tambaya, kamar daga sama na ji ana cewa. 

“Mun kusa wuce jakshon ɗin fa.” 

Na kalli me mashin ɗin na kalli hanya, sannan na ce. 

“Wannan layin zaka shiga.” 

********

08:30pm

Kamar wancan lokacin na farko da na haɗu da Fahad Ta’ambo na kasa mantawa da komai na shi, to yau ma haka. Tun dawowa ta na ƙure a ɗaki ina zaune ni kaɗai ina maimaita duk wata kalma guda ɗaya da ya faɗa a cikin zuciyata. 
Hajiya ce ta leƙo tare da faɗin. 

“Rawasiya me kike yi a ɗaki ne, bazaki ci abinci ba ne?” 

“A’a Hajiya na ci acan, duk gjiya ce wallahi ke ci na.” 

“Mene abin gajiya a zuwa Fagoji? Sai ka ce yau kika fara?” 

“Bazaki gane ba Hajiya.” 

Na faɗa ina juya baya. 

“Eyh, bazan gane wannan karatun sangartarba.” 

Ta faɗa tare da ficewa, ni dai daren nan haka na ƙarar dashi a ɗaki ina ta hango kammanin kyakyawan matashi Fahad Ta’ambo. 

Washe gari ma dai da mafarkin kyakyawar fuskarsa na tashi, ni dai ban taɓa soyayya ba, amma nasan yanayin da nake ji game da Fahad na san yanayi ne na soyayya. A gurguje na yi shirin makaranta na fito tsakar gida na ɗauki abin kari na na yi, bayan na karya na amshi kuɗin makaranta wajen Alhaji na nufi makaranta. 

FUD STAFF SCHOOL
11:30am. 

Tun da aka fita break ban matsa ko ina ba daga kan bencina, duk ƙawayena su Fauziya Tasi’u su Malaika sun fita sun dawo amma sun tarar dani anan zaune. Malika safwan ce ta zauna kusa dani tana faɗin. 

“Nana meke dumunki ne haka? Tun ɗazu kina zaune sai faman murmushi kike?” 

“Murmushi?”

Na faɗa da alamun tambaya. 

“Au baki ma san kina murnushin ba, sai dake malamar soyayya.” 

Ta faɗa tana dariya, na kalleta na ga yanayin ta ko a jikinta, daman Malika irin wayayyun ‘ya’yan nan ne, dan a yanzu haka ma tana da saurayi abunta, idan anyi magana sai ta ce ‘idan basu yi min aure ba, jiƙani zasu yi su sha?.’ A yanzu haka har cikin Malamai tana da saurayi, sabida wayewarta ma Malaika Arora ake ce ma ta. 

“Ni Malaika ban faɗa wata soyayya ba.” 

Na faɗa bakina yana rawa, kallona ta yi sannan ta ce. 

“Mai da karuwa ‘yar iska.” 

Tana faɗin haka ta juya ta shiga sabgoginta ta barni da faman tunani. 

“Ya zaayi ace na faɗa soyayya, faɗawar da har wani zai iya ganewa, ko da yake a wayewa da gogewa irinta Malika ba abun mamaki ba ne dan tasan haka, amma ta ya zaayi na fara soyayya da mutumin da ko sunana bai ta ɓa tambaya.” 

Haka na yini sukuku, har washe gari ma hakan, sai da aka sake ɗaukan sati ina cikin wannan yanayin kafin na ji na dawo daidai, sai dai a cikin wannan satin fa duk ƙawaye na sun yarda da maganar Malaika kan na faɗa soyayya. Ni kam tsakanina dasu sai da ido, daga baya ne ma na fara biye musu har wata rana suka ce wai sai na zayyane musu kammanin mutumin, da na rufe idona kawai sai na ganshi ya harɗe hannu yana kallona. 

Duk yadda na kai ga gaya musu cewar yadda na fasalta musu shi, haka yake a gaske sun ƙi yarda, dan daga masu cewa jaruman indiya nake fasaltawa, sai mai cewa larabawan Dubai ne, ni kam daga ranar ban sake biye musu ba. 

A lissafina ranar da na cika kwana goma da haɗuwa da Fahad Ta’ambo na sake ganinsa, sai dai abun da ya yi matuƙar bani mamaki shine inda na gansa, daga can gaban gate ɗin makarantarmu, da sauri na juya baya sai dai naga idanun ƙawaye na akansa. Fauziya ta yi saurin matsowa kusa dani sannan ta ce. 

“Ke Rawasiya! Wannan ai shine sak mutumin da kika fasalta mana, ko shine?” 

Na gyaɗa mata kai, gaba ɗaya na rasa nutsuwa ta, kamar ko da yaushe. Da zarar ya ɗor ƙawayar idonsa a kaina, shikenan na rasa nutsuwata. 

“Gaskiyya ƙarya kike Rawasiya.” 

Mailaka ta faɗa a saitin kunnena. 

“Kina ganin yadda yake kollonta, zaki ce ƙarya ne.” 

Amina Aminu ta faɗa.. 

“Wannan ai yafi ƙarfinki Rawasiya, bama haɗi wallahi.”

Na ji muryar Malika ta faɗa, a take Amina Aminu ta cafe da cewa. 

“Ni ban ma yarda ba, gashi dai gani nake da idona, amma na kasa gasgatawa.” 

“Kinsan kuwa wane ne Fahad Ta’ambo?” 

Malaika ta faɗa, daidai kuma lokacin ya fara takawo kusa da mu, ni kam gaba ɗaya sai na ji maganganunsu sun tsayan a raina, ni kaina nasan tabbas wannan saurayin yafi ƙarfina, bazan taɓa samun wannan saurayin ba domin kuwa duk wani abu da ake nema ya haɗa. Kyau, kuɗi, Nasaba, gayu, ilimi da duk wani abu da ‘ya mace ke nema wajen datattacen Namiji. 
Gaba ɗaya daskarewa na yi na kasa motsi, kar na yaudari kaina Fahad ba tsarar aure na ba ne. 

“Yau ba magana ne, kin wane tsari ni da ido kamar yau kika fara kallona?” 

Ya faɗa daidai lokacin da ya iso, gaba ɗaya yau sai na rasa wannan yanayin da nake ji idan yana gabana, jikina sanyi ƙalau na ce da shi. 

“Ina wuni?” 

Kallona ya yi sannan ya kalli ƙawayena ya ce. 

“Baki da lafiya ne?” 

“A’a, ina da lafiya.” 

Na faɗa ina kallonsa.

“Uhm.” 

Ya faɗa yana taɓe baki irin bai damu ba. Ganin na yi shiru kusan minti biyar, kuma ban tafi ba ya sa shi cewa. 

“Ina so mu yi magana ranki ya daɗe, naga yau a saurauniyar ki kike.” 

Bin shi kawai na yi a baya, ƙawaye na dai suna bina da na mujiya. Har mu ka ƙarasaa bakin motarsa ina jin idanunsu akaina. 

“Me yake damunki?”

Ya faɗa yana kallona, girgiza kai na na yi sannan na ce. 

“Bakomai” 

“ƙawayenki ne?”

Na ɗaga sannan na ce. 

“Wai sun ce idan kai saurayi na ne yaudarata zaka yi ba zaka taɓa aurena ba. Sabida kafi ƙarfina.” 

“To ke me kika gani?” 

Ba tare da wani lissafi ba na ce. 

“Da gaske suke.” 

Ya yi murmushi sannan ya ce. 

“Rawasiya daman ni na ce saurayinki ne?” 

Na gwalalo ido waje sannan na ce. 

“Kasan suna na? Aina?” 

“Taambayar da na yi miki kenan?”

Na girgiza kai sannan na ce. 

“A’a da a’a.” 

“Mene a’a da a’a?” 

Ya tambayeni yana kallona. 

“Da ka ce tambayar da ka yi min kenan shine a’a ta farko, a’a ta biyu da ka ce daman ka ce kai saurayi na ne?” 

Murmushi ya yi sannan ya ce. 

“You’re very funny, I love it girl.” 

Na yi murmushi sannan ya ce. 

“Baki tambayeni me nake yi anan ba?”

A raina na ce. 

“Duk inda nake ganinka da na taɓa tambayarka me kake yi a wajen?” 

“Sabida yau wajenki na zo shi ya sa na tambayeki.” 

Na ji muryarshi ta katse min tunani na. 
“Shekararka nawa?”

Na tsince kaina da tambayarsa, sai da ya ƙare min kallo sannan ya ce. 

“Ashirin da shida.” 

Wani daɗi na ji ya ratsani, irin mijin da nake so. 

“Ke fa?” 

Na ji ya tambaya. 

“Goma sha bakwai da rabi.” 

“Ko ba rabi ba?.” 

Ya tambaya yana dariya.

“Yau na ganka da sauƙin kai, daman haka kake?” 

Na tambayeshi, sai dai ya yi dariya sannan ya ce. 

“Au da da zafin kai nake zuwa kenan?” 

“ƙawayena bari na tafi.” 

Na faɗa ina nuna masa su, nan take ya haɗe rai ya dawo asalin Ta’ambo da nasani. 

“Je ki.” 

Ya faɗa cikin wani irin amon murya, ba shiri na tsaya na kasa tafiya. 

“Je ki mana.” 

Ya faɗa yanzu muryarsa da alamun fusata. 

“Ka yi haƙuri.”

“What do you do? Kin nuna sun fini amfani da muhimmanci to sai me?” 

Gaba ɗaya jikina ya fara rawa, duk na rikice lokaci ɗaya, bakina har rawa yake na ƙara cewa. 

“Ba haka ba ne fa.”

Legendspen
***