IMSAL

Daddy's Girl

by @fatoumspassion

***


SPECIAL ANNOUNCEMENT 
Ina farin cikin sanar muku cewa zan fara posting sabon novel dina IMSAAL a ArewaPen da Wattpad 🤍

But don’t worry… WhatsApp readers are still my priority 🫶🏽
Nothing is changing here, this is still home ❤️
To celebrate this, I have something special for my real supporters 
🎁 The FIRST 20 PEOPLE to:
✔ Follow me on ArewaPen
✔ Follow me on Wattpad
Will get FREE entry into my paid WhatsApp group 💫
🎁 HOW TO QUALIFY 🎁
After following me,
📌 Take a screenshot showing you’re following me on BOTH platforms
Then send it to me on WhatsApp 👇
📩 ***
⚠️ Include your username
⚠️ Only the first 20 valid people will be accepted
⚠️ No screenshot = no entry 👀
ArewaPen @fatoumspassion
Wattpad @fatoumspassion
Hurry… once the 20 slots are gone, that’s all 🔥

It's fatoumspassion IMSAL 
Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM, INTENSE LOVE, EHSAAS and SCARRED.

Three more chapters to go........💃💃💃💃💃
Free pages is coming to an end soon,
Pay 300 naira only get into
Opay
 9121869191
Fatima Rufa'i Nasidi 
To join Imsal premium lounge inda zamu cigaba da posting daily kamar yadda muka saba.


Chapter 15

Daddy's Girl

IMSAL na kwance saman gadonta tayi ruf da ciki tana answering past Q na final paper ɗin da zasuyi taji wayarta na ringing, miƙewa tayi zaune ahankali tana dafa kanta don takai awa ɗaya da rabi agurin tana abu,
ɗaya jawo wayar tai tana picking lazily ta kara jikin kunnen,
"Assalamu alaikum ya umri"
yayi mata sallama cikin nutsuwa me tattare da tarin kulawarsa a gareta.

Ahankali tace 
"Ameen Wa Alaikummussalam Yah Mu'allim,"
Hankali yace 
"baki barci ba,"
Gyaɗa kai tai kamar tana gaban shi kafin tace 
"Eh yah Mu'allim"
Yace 
"ya preparations?"
Tace 
"alhmdlh, I'm almost done,"
Tana ɗan wasa da biro ahannunta
Yace 
"hope I'm not distracting you?"
 jinjina kai tayi kamar tana gabansa 
Yace 
"what of UTME result kin dubashi?"
gyaɗa kai tayi kamar tana gabansa,
Ahankali yace 
"words my lady"
 don koda baya gabanta jin tayi shiru yasan sana'ar tata tai masa wato body language ahankali tace mishi 
"naduba yaya?"
Yace 
"me muka samu?"
Ahankali ta ɗan turo baki tace mishi 
"280"
Yace 
"wow congratulations babe,
 I'm very proud of you kice da gudu za'a bamu admission"
rufe fuskar ta tai kamar tana gabansa 
Yace 
"dama na faɗa miki your worried about nothing tunda kuka rubuta nasan you'll ace it,"
Murmushi kawai tai batace komai ba 
Yace 
"bari na barki ki ƙarasa karatun ki nasan gobe ma zaki je kiyi making ɗina proud,"
Jinjina mishi kai tayi kawai kamar yana gabanta 
Yace 
"What of your speech agobenne ko se yaushe?"
Girgiza mishi kai tai tana faɗin 
"se ranar Thursday"
 yace 
"okay Allah ya kaimu, I'll be there in sha Allah "
Tace,
"Ameen ya rabb"
Yace 
"have a peaceful night my lady, see yah"
ahankali tace 
"Goodnight yah Mu'allim" 
Yace 
"take care of yourself for me"
Aciki ciki tace
"you too"
Tana katse wayar komawa tayi ta cigaba da answer pass q ɗinta gaba ɗaya yau she's moody saboda sunyi waya da Daddy yace mata baze samu damar zuwa speech ɗinsu ba.

kwankwasa kofar ɗakin taji anayi,
tamiƙe tana faɗin 
"shigo"
Da sallama Rayyan ya shigo yana rufe ƙofar 
Yace 
"hope banyi distracting naki ba"
 haɗa takardun ta tashiga yi ta jinjina masa kai alamar a'ah 
Yace 
"Natasha is trying to rob me fa,
 kinga lissafin datamin wai dress din speech da zaku siya hardasu kwalliya da abubuwa,
Gaskiya Unique sunyi tsada ku samu designer me sauƙi ku siya,"
Jinjina masa kai kawai tai don duk graduation ɗin ya fita aranta jin Daddy baze zoba,
Ta miƙe ta nufi inda zata ajje kayan karatunta zama yayi gefen bed ɗin harta ajje ta dawo,
ta zauna akusa dashi yace 
"menene?
 ko kema haushina kikaji don nace arage kuɗin Unique?
toh yi hakuri kuyi yadda kuke so kawai I'll send you the money,"
 da sauri ta girgiza kai tana ce masa 
"ba haka bane yaya ni kasan ko kayana zan iya sawa naje kawai dai..."
setai shiru kuma tana wasa da yatsunta ahankali ya gyara zama yana faɗin "meyafaru?
tell me akwai damuwa a voice ɗinki,
Ko kayan basu miki ba?"
Girgiza kai tai kwalla na biyowa idonta tace "Daddy ne,"
Da mamaki yace 
"Daddy kuma meya miki meya haɗa ku?" fashewa tai da kuka dan har ranta takejin ɗacin rashin kasancewar tasa tare dasu sabda tayi matuƙar kewarsa tasaka ran zata ganshi tace 
"yace wai baze zo speech ɗinmu ba,"
Rayyan riƙo kafaɗarta yayi ya shiga lallashin ta yana mamakin meyasa Daddy zeƙi zuwa yasan Daddy is not like that yana kasancewa aduk wani abu me mahimmanci nasu sedai idan abune me mahimmanci ya tare shi,
Yace 
"kiyi hakuri Unique dan Allah ba gani ba, kuma kinsan Mummy ma zatazo,
ga Hajiya,
 we will all be here for you, Daddy ƙila akwai abinda yake da mahimmanci ya keyi acan shiyasa yace baze zoba,
Please calm down kisaki ranki,"
Ahankali tace 
"I understand yaya it just hurt,
I want to see him, I miss him so much yaya"
 tafaɗa tana dafe kirjinta yace 
"i know Imsal ki daure kinji nasan daddyn ki shine favourite person ɗinki, we will try ko bamu miki duk abinda yake miki ba zamu ƙoƙarta yar gidan daddy, we will be there for you kinji,"
jinjina mishi kai tai cikin tsokana ya raɗa mata 
"and your boyfriend will be there too,
 kinga zakiji daɗin soyayya dashi,
without jin kunyar daddy"
 da sauri ta miƙe daga inda yake tana rufe fuska murmushi Rayyan yayi ganin ambaton Abdullah da yayi kawai yayi lightening mood ɗinta 
Yace
"so dukkan mu potatoes ne,
nace duk zamu zo baki murna ba seda nace Bin Suhail ko,"
Wurin press ɗinta ta nufa duk da babu abinda zata ɗauka ta buɗe ta shiga bincikawa keeping herself busy don kada Rayyan ya cigaba da tsokanar ta gashi duk ya bata kunya.

Bata san sanda ya ƙara so ba
 se jinsa tai abayanta yace 
"toh lover girl,
zansaka miki kuɗin a account ɗinki kuje tare ke zaki payment ɗin a ajjemin canjina, idan akwai ban yarda ba,
Natasha ba zata iya yimin sama da faɗi da kuɗi,"
Se alokacin Imsal ta fara dariya tace 
"yaya hakane fa kuɗin ba abinda taƙara" yace 
"ohh haɗin bakine ma za'a min yau,
ai shikenan tunda ɗan albashin nawa zaku kwashe ni na tafi zakiji alert,"
juyawa yayi ya fice se da taji rufe ƙofarsa ta juyo, ta nufi toilet wanka tayi ta saka kayan barcinta, already tayi sallar isha'i ta kashe wuta ta kwanta.

Ƙarfe huɗu daidai ta tashi kamar yadda ta saba tayi na filfilinta da addu'o'in ta har zuwa lokacin sallar asuba seda tai sallar asuba ta fara karatun ƙur'ani,
Har rana ta fara fitowa,
ganin haka yasa ta kammala izifin tai addu'o ta haye saman bed da niyar komawa barci don jarrabawar tasu ta rana ce yau,
Notification taji ya shigo wayarta ta jawo tana buɗe wa ta shiga karanta saƙon daya turo mata 
"Good morning, Ya umri
Today’s your last paper… just go and handle it like you always do. I’m proud of you already, no matter what happens. Don’t stress yourself too much, just breathe and write.
I’ll be waiting for you after it’s done."
Murmushi tai tashiga typing masa reply
"Morning Ua hubb umri 
I’ll try my best. Thank you."
Ajje wayar tai tana murmushi me sanyi ta lumshe ido nan danan barci mai daɗi ya ɗauke ta.

Ringing ɗin wayar ta ne ya tasheta daga barcin da ya ɗauke ta, ta miƙe ahankali rabin idanuwanta arufe taja wayar tana ɗagawa takara a kunnenta, don tinaninta Abdullah ne,
Anitse tace 
"Assalamu alaikum,"
Daga ɗayan bangaren ansawa yayi cikin deep masculine husky voice ɗinsa yace 
"Ameen Wa Alaikummussalam,"
Aɗan firgice ta tashi jin strange voice,
ba sassanyar muryar Ya Mu'allim ɗinta data sabaji cikin kunnenta ba,
ta raba wayar da kunnenta tana kallon number data kira ta bata santaba,
ganin har lokacin kiran na reading yasa ta maida wayar kunnenta batace komai ba tana jiran jin waye ne, jin tayi shiru yasa yace
“Good morning, Lulu.”
Ware idonta tai sosai don ta tina wannan mutumin Mummy ɗinne daya haɗasu faɗa, jitai ranta ya ɗan ɓaci saboda katse mata barci da yayi tana sane tace
“Wa ke magana?” 
Tana jin tashin sautin dariyar sa daga ɗaya ɓangaren kafin yace 
“I don’t like repeating myself,” 
Jin batace komai ba yasa yace 
 “But I’ll make an exception today.”
Kai tsaye yace mata
“Umar Farouq your future husband.” 
Wani irin bugawa taji ƙirjinta yayi batasan sanda tace masa,
“Me… me kake so?
Murmushi taji yayi yana faɗin 
"Wow I like how straight forward you are,
You sound so much like our Mummy, I like that energy, and regarding what I want we will discuss that in person,"
Jitai kamar ta kashe wayar baki ɗaya jin ya cika ta da magana, amman tinawa da ze iya sake haɗata da Mummy yasa tace mishi 
"Why are you calling?"
farouq da yake ɗaya bangaren ɗan ɗage gira yayi yanajin yadda yar ƙaramar muryarta ke sounding very bossy irin batason rainin nan ji yayi ta sake burgeshi sosai, daga gani zatai tsiwa
Ahankali yace
“Today, is your last paper right.” 
da
"eh"
ta amsa masa 
A hankali yace 
“I want you to go in there and write like you belong to success… because you do, .”
Taɓe baki tayi, tace mishi 
"Okay, se anjima,"
Tana katse wayar, gefe ta ajjeta tana tinanin yadda zatai blocking ɗinsa ba tareda Mummy ta sani ba.

Wani kiran ne ya sake shigowa kamar tai ignoring se kuma ta ɗaga tana sawa a speaker ta miƙe tafara gyara gadonta jitai yace 
"Ba'a katse ma Farouq waya, da wani ne bakeba ba lallai ya kwana da ransa yau"
Kallon wayar ta shigayi tana tsayawa da abinda take yi,
Yace 
"Lulu ba dake nake magana ba"
jiyayi ta mai banza kamar ba bata wurin,
Yace
"Lulu say something"
Ahankali tace 
"sunana Imsal banji ka kirani ba ai,
i thought your talking to someone else"
 ita kanta batasan sanda tace masa hakan ba don ya kawota wiya besan haushinsa take jiba kaɗan ba.
Da wata irin gadara da kausashshiyar murya yace 
"I know your name banga damar faɗa bane, I'll call you with whatever I like and you'll answer it, I'm I clear"
Wani murmushin takaici Imsal tayi tana ɗaukar wayar tace 
"excuse me Malam,
 I don't even know you, kada ka sake ma kiran wayana daga yau se yau,
and don't you raise your voice at me again I'm not your daughter,
darajar Mummy na ma kaci har na tsaya ina sauraron ka,"

Tana ƙarasa maganar ta kashe wayar,
Alert ɗin kuɗin da Rayyan ya saka musu ta gani ta duba se ta sakata a Flight mode gaba ɗaya ta jefar tana turo baki cikeda jin haushi ta wuce toilet.
wanke bakinta tayi tai wanka ta fito ta saka simple doguwar riga da hula ta sakko ƙasa.

A dining ta samu Hajiya tana breakfast tai joining ɗinta sukaci abinda zasu ci suka koma ɗakinta suna fira.
Seda taga sha biyu ta kusa sannan ta koma ɗakin ta tai shirin school, tana saka socks Natasha ta shigo da uniform ɗinta niƙi niƙi set set tana tambayar ta wanne yafi kyau saboda sign out da zasuyi.
Da tausashshiyar murya tace
"Natasha da kin haƙura da sign out ɗinnan ki kawo akwai yarinyar data cemin tanason kayana yar gidan Maman nan me saida ruwan sanyi,
se na kaimata harda naki kinga zataji daɗi sosai, ta amfana dashi, karkiyi almubazzaranci bakyau,
 sign out ɗinnan duk shirmene zasu lalace ne abanza,"
Natasha riƙe ƙugu tayi tana faɗin 
"wai kala ɗayan dazan ɗauka muyi celebrating kike complain please ni ki barmin maganar nan just show me wanda yafi kyau,"
wani tsoho Imsal ta nuna mata tana dariya tace 
"ki ɓata wannan kinga sababbin nan semu kaimata duka,"
hararar ta Natasha tai ta dire tsohon tana faɗin 
"toh wallahi bazan sashi ba"
ta ɗakko wanda akai musu term ɗinnan tace 
"shi zansa sedai ki yi,"
tafice aɗakin Imsal kawai ta bita d kallo ɗaukar waɗanda ta ajje tayi, ta samo leda ta haɗa da nata kayan duka ta ajje agefe yarinyar tace mata zatazo har gida ta karɓa saboda tanajin kunyar ma ta kaimata school yan ajinsu sugani afara mata wulaƙanci,
iyayenta basu da ƙarfi harta da school fees ba biya take ba scholar ce, Maman ta ruwa take siyarwa a school din kuma itace nanny ɗin junior section.

Sakkowa tayi da yake yau General paper zasuyi civic education tare da Natasha suka wuce, tunda suka hau napep take waya da ƙawayenta don ko bikin ta za'ayi se haka tsabar yadda take zumuɗi.

Suna daf da ƙarasawa makarantar ta kammala wayoyin nata ta kalli Imsal tana faɗin 
"kinga harsu Babba sun amso nasu kayan nifa idan be turo mana ba zan kira mummy kawai na faɗa mata ta saka mana,
haba wai kuɗin har nawa ne da yake ta ja mana rai haka,"
Imsal tace
"Toh ya turo sarkin ƙorafi,"
Natasha da mamaki tace 
"really"
jinjina mata kai tayi tana murmushi,
Tace 
"nawa ya saka"
"Nawa kikace yasa"
 Imsal ta bata ansa 
Taɓe baki natasha tayi tana faɗin 
"shi ko ɗan ƙarin nan be iya ba ya ɗan ɗora wani abu akai nasaka kati haba"
Ta faɗa cike da ƙorafi kafin tace 
"kin faɗawa saurayin ki yau zamuyi final kuwa?"
Banza Imsal tayi mata amman hakan besa  tadena maganar ba tace
"Gwara dai ya sani ɗan gift din soyayyar nan ahaɗo akawo mana,"

Girgiza kai kawai Imsal tai daidai Malam Garba na tsayawa a kofar school Imsal ce ta fara fata fitowa seda ta ƙarasa ƙofar gate ta cire niƙab dinta ta saka a handbag ɗinta tabi bayan Natasha da already har tayi gaba.

Acikin hall ɗaya suka zauna, har aka kawo jarrabawar clique ɗinsu Natasha basu dena surutu ba seda aka shigo aka tsawatar musu sannan sukai focusing akan exams ɗin,
 da yake civic ce batai wani wiya ba, basu jimaba suka kammala baki ɗaya tundaga ƙofar hall ɗin aka fara celebrating ganin sunfara damun na ciki da basu gama ba yasa aka korasu can school compound, Imsal seda ta kammala anitse lokacin befi saura su huɗu a jinba duk sauran sun fice sungama antafi celebration tai submitting ta fito.
kusan cin karo sukai da malamin Chemistry ɗinsu wani igbo guy ɗan guntu dama suna ɗasawa da Imsal, cike da tsokana yake ce mata 
"a'ah our valedictorian is out finally,"
Murmushi tayi kanta aƙasa don bata da yawan surutu inba mugun sabawa tai da mutum ba indai bama agidansu kake ba ba lallai kasan tana magana,
Ahankali yace mata 
"congratulations my dear, 
nasan bright future nanan tana jiran ki,
when you become someone successful don't forget with me ooo, or when you marry someone rich cause beautiful ladies like you ehnnn, basa barin poor men like us musamu"
Murmushi kawai Imsal tayi
Yace 
"Allah ya bada Sa'a yakawo kyakkyawan sakamako"
 tace 
"Ameen ya hayyu ya qayyum,
thank you Sir "
Ya amsa da
" your welcome,
my dear your welcome, 
greet your father for me, I'll see him during your speech right, "
Girgiza masa kai tayi alamar a'ah,
Gyara zaman takardun daya maƙala ahammata yayi yana faɗin 
"a'ah why nah?
 is he not coming?"
jinjina masa kai tayi 
Ganin kamar batason maganar yasa yace "alright I'll see you there then,
bye bye,"
Yana bata hanyar wucewa da sauri tayi gaba tana ɗaga mishi hannu.

inda suke ajje jakar su ta nufa taje suka gaisa da malamar dake gurin ta ƙarbi jakarta.
ta ciro wayoyin ta,
dama tasaka tata wayar a Flight mode tasan bame kira ta Ya Mu'allim kuma misscall dinsa biyu ta gani thirty minute ago tafiya tafarayi tana ƙoƙarin kiransa.

 kiɗan da yake tashi daga school compound yasa ta toshe kunnenta ɗaya tana sauraron yadda wayar ke ringing beyi picking ba, ganin haka yasa ta maida wayar jaka, 
tana tafiya har zuwa compound din school na farko,
anan masu celebrating suke, anata rawa sun kunna speakers ana sign out 
atsakiya ta hango Natasha uniform ɗinta already yayi kaca kaca da signing ɗin mutane da spray paint, 
batama yi yunƙurin kulata ba tasan tace zata dakatar da Natasha daga wannan celebration ɗin da taci buri tashin hankali za suyi.

gefe can bakin gate ta tsaya tana jiran zuwan Malam Garba tayi shiru,
Wata ƙawar Natasha samina ce ta ƙaraso inda take tana haki tace 
"Imsal ungo yimin signing"
tana bata permanent marker girgiza kai tayi tace mata
"banayi"
kawai ba tare da ta karɓa ba,
 samina tace 
"come on Imsal,
 nifa ba yi miki zanyi ba,
signing ɗinki kawai nake so dan Allah yimin, Please Please,"
Jin tace mata dan Allah yasa ta karɓa kawai tana faɗin 
"bazaki minba kin yarda?"
tana dariya tace 
"eh naji bazan yimiki ba,"
gefen hijab ɗinta Imsal ta kama ta shiga yi mata signing ɗinta gently tana gamawa samina ta karɓa tana fadin 
"yes na karya record
na karya record jama'a 
"ta koma ciki da gudu tana basu labarin ai Imsal Umar ta mata signing"
Natasha jin haka yasa tai saurin fitowa tana nufar Imsal tace 
"dama zakiyi signing shine ni ƙanwarki kika kasaimin se wata bare"
 Imsal folding hannunta tai aƙirjinta tana kallon rigima irin ta Natasha tace 
"kince nai mikine and beside itama kannai mata I told her baza tamin ba ke kuma nasan ba yadda zakiyi ba,"
Tace 
"nice nace miki haka,
 ungo toh yimin"
karɓa tayi don gudun rigima kawai ta juya bayanta tai mata, 
Natasha tace 
"thank you,"
Imsal tace 
"naga har yanzun Malam Garba be zoba ko ya manta lokacinne"
dariya Natasha ta farayi tace 
"nice nace yatafi,
 se anjima zamu dawo,
tunɗazun yazo kina exam,"
"What?"
 Imsal ta faɗa tana kallon Natasha datai baya tana dariya ta ciro spray paint tana faɗin 
"chill yah Imsal,
celebrate a bit"
ta jijjiga, dasauri Imsal ta rufe fuskar ta tana faɗin 
"don't do that Nats,
 banaso na faɗa miki banso"
 dariya tayi tana ce mata
"Allah sena fesa miki,
Bari ma kiga"
ta shiga matsowa,
"Kina fesa mata sena kakkarya ƙafarki acikin makarantar nan yau"
taji Muryar sa daga bayanta yana faɗa da sauri ta juya cikin mamaki tana kallon sa, ta fara rarraba ido,
 Imsal da itama taji muryar tasa buɗe ido tayi tana jin hankalinta ya kwanta ganin sa.

Natasha da sauri tace 
'wasafa nake mata daman...."
tana ɗan sosa kai cikeda jin kunya,
Fuskarsa ahaɗe ya nuna mata gate yace "wuce muje,"
raurau tai da ido tana kallon Imsal don tinaninta itace ta kirashi,
Tace 
"yaya Allah bazan fesa mataba,
Bafa agamaba,"
bema juya yakalli inda ake kade kaɗenba yace 
"kinfison na barki anan kuyita kwasarwa kanku zunubi kunabin gangar dujal ko, anhaɗu mata da maza ana shashanci"
Natasha kallon Imsal tai irin tasa baki ɗinnan batace ƙala ba sema gaba da tayi irin ba ruwan tannan, 
shima bin bayanta yayi Natasha ta tsaya tanajin dana sanin fitowa gurin Imsal da tai kawai ta juya tab bayansu don tasan idan ya tafi batareda itaba akwai matsala.

Sanda ta ƙarasa harya buɗe ma Imsal gidan gaba ta shiga ko kallon inda take beyi ba dakanta ta bude gidan baya ta shiga,
Se asannan shima ya buɗe gidan baya ya ciro wasu red roses a gefen da Natasha ta zauna, yana daukowa ya rufe.

Ya bude driver sit ya shiga yana ajjema Imsal roses ɗin asaman lap ɗinta yace "congratulations ya umri,"
Murmushi tai tana ɗaukar rose ɗin ta shiga shinshinata wani irin kamshi take me daɗi ta lumshe ido tana faɗin 
"thank you Ya hubb umri,"
Wani irin taɓe baki Natasha tayi tanajin dukkansu sungama da ita sun hanata ƙarasa sign out ɗinta, su kuma sunzo suna soyayyar su.

Sit belt ya saka ya kalli Natasha ta mirror gently yace mata 
"na dauka kinyi hankali,
ashe har yanzun da saura,
yanzun da banzo ba spray paint ɗin da zaki zuba mata, kinsan cewar ita can trigger her asthma and give her the worse attack ever, there's aerosol there ko baki sani ba?" da sauri ta shiga girgiza kai alamar bata sani ba.
Yace 
"be careful next time I won't be this calm, her health should always be your first priority,"
Jinjina kai Natasha tayi tana faɗin 
"bazan ƙara ba, yah Imsal I'm sorry," murmushi Imsal tayi tana kallonsa yadda ya wani yi kicin kicin yana wa Natasha faɗa leƙa fuskarsa tayi tace 
"yah Mu'allim nah,
tace sorry, I know bata sani ba so let's forgive her pleaseeeeee"
ta ƙarasa tana jan Please ɗin juyowa yayi suka haɗa ido,
Yace 
"Bane should we?"
Jinjina masa kai tayi alamar eh,
Wani irin murmushi ya saki wanda Natasha bama tasan ya iya shiba yace mata 
"your pardoned kinci darajarta,"
Shida Imsal dariya suka fara saboda yadda yayi maganar Natasha jitai kamar ta shaƙesu don bataga abin dariya ba taƙulu over sunsata agaba sun maidata clown.

 Imsal ganin yadda tai zuru zuru yasa ta kara juyowa tana dariya, Natasha ƙwafa tai bata kula taba irin zasu haɗunnan susu biyu.

Haka ya tada motar susu biyu suke hiransu yawanci akan karatune Natasha ta lumshe ido tana jinsu bata tanka musu ba har seda suka ƙaraso gida.

afusace ta buɗe ƙofar bata kula kowa cikin suba tayi cikin gida,
Imsal ɗan kallonsa tayi tana karkatar dakai tace 
"thank you for the ride,"
Ahankali yace 
"is my pleasure your highness, 
take care of yourself for me,"
Ahankali tace 
"kaima haka"
kanta aƙasa yace 
"me kikace?"
girgiza kai tayi tana buɗe ƙofa da sauri rungume da roses ɗinta ta fito shima fitowar yayi yana jingina jikin motar yace "tafiya zakiyi ki barni ko."
Gyada mishi kai tayi yace 
"zo kiji banfa gama hirar ba,"
maƙale mishi wiya tai alamar a'ah, ya nuna kansa yace 
"niko?"
 rufe idonta tayi tana giggling ear to ear tana jujjuya kanta.
Shima murmushin yake kafin yace 
"alright 
I'll come later, 
prepare something nice for me,"
ɗan buɗe idonta tai tace 
"really"
 yace 
"yes but not food, something sweet like telling me you love me ko babe,"
Turo baki tayi tasa roses ɗin tana rufe fuska,
Yace 
"Allah nidai se ance ana sona kwanan nan karnaje ni kadyai nake abuna fa,"
 ɗan leƙowa tayi ta gefen roses ɗin tana kallonsa yace 
"I can see those angelic eyes behind the roses"
 da sauri ta rufe fuskar duka tace 
"byebye"
tana ɗaga mishi yan hannayenta,
daidai ana zuge gate ɗin gidan ganin wata prado ce fara ta shigo cikin gidan, 
Imsal ta tsaya tana kallon motar don tana so ta tabbatar da zarginta,
 juyawa tai tana kallon garage din gidan dake abuɗe alamar tabbas ta gidance itace aka fitar da ita,
 
ai batai wata wataba ta ruga aguje tunkan mota ta tsaya ta ƙarasa daidai tana tsayawa tana haki sosai cike da murna,
Ƙoƙarin buɗe bayan motar takeyi kawai ta hangosa yafito ta  front sit ta ɗayan side ɗin da wani irin gudu ta zagaya, ta faɗa jikinsa tana maƙalƙaleshi tana haki da dariya se kuma ta fashe masa da kuka duk lokaci ɗaya wani irin murmushi ne me sanyi yake fita daga fuskarsa ya shiga shafa bayan ta jin hakin nata yaƙi tsayawa cikeda kulawa yana faɗin 
"calm down
is me,
I'm here please be careful, na hanaki gudu banason gudannan adena yinsa"
Sunkai minti uku ahaka seda taji numfashinta yadawo daidai taɗago tana kallonsa cikeda shagwaɓa ta ƙara rungume shi tana kuka tace
"kace kuma bazaka zoba Daddy,
I was so sad, I cried alot, I miss you Daddy yaushe ka dawo daddy meyasa baka faɗa minba?
Daddy are you hungry?
dariya ya farayi yace 
"Stop crying first"
Yaƙarasa yana goge mata hawayen da hannunta dasuke zubowa kamar famfo seda kyar suka tsaya,
Tace 
"Daddy tell me everything"
Yace 
"Toh Imsal wanne zan amsa cikin tambayoyin naki haka"
 sakinsa tayi tana kama hannayensa tace "duka Daddy na,"
 Rayyan daya fito riƙe da key ɗin motar ahannunsa don shine yaɗauko su daga airport yace 
"aifa shikenan munshige su daddy ya dawo zamu ga iyayi kala kala da wariyar launin fata,"
Mummy da ta fito daga gidan baya, cikin ɗan faɗan wasa take faɗin 
"idan yarinyar nan taga Doctor makancewa takeyi koni dana haifeta mantawa take dani kaikuma asuwa,"
 se alokacin Imsal ta juya tana washe baki ta saki Daddy ta ƙarasa gurin Mummy zata rungumeta tace 
"don't touch me,"
 cikin wasa tana hararar 
"ai seda kika gama da babanki gani nai kwantai shine zakimin oyoyo ina yata nima nasan zatai murnar ganina nan matsamin natafi wurinta,"
 Imsal dariya ta farayi ta cukuikuye Mummy tana faɗin 
"Mummy na kinsan your my favourite ko, aibanganki bane bansan dake aka dawoba," Mummy tace 
"toh cikani karkimin squeezing ɗin ta ainima dama bansan kina gidan ba,"
 Daddy kallo faɗan nasu yake yana murmushi shi kaɗai se alokacin ya lura da Abdullah daya ƙaraso kansa a ƙasa yana kasa haɗa ido da Daddy ya durƙusa yana faɗin 
"barka da dawowa Abba"
 don haka yake ce masa,
Da sauri Daddy ya riƙoshi yana faɗin 
"my son ashe kana nan"
 ya rungumeshi yana faɗin 
"kun haɗa baki kun gudo kun barni ina shan sanyi koh,"
 murmushi Abdullah yayi yana ɗan sosa keyar jin kunya,
Daddy ya sake shi yana dafashi yana tambayarsa 
"ya suke ina yar uwarsa,"
Yace masa 
"tana nan lpy alhmdlh,"
Juyawa yayi yace ma Mummy 
"Barrister nikuwa yaushe rabon da naga Mubeena gaskiya ya kamata tazo mu gaisa kafin na koma,"
tace 
"tana nan itama ta zanƙale kamar imsal,
Zaka ganta kuwa kasan duk tare suka gama yau duka dandai ba makarantar su ɗaya ba,"
Yace 
"Masha Allah,
Allah yasa albarka yaran namu dai duk sun girma,"
Mummy da se alokacin ta lura da ros5e ɗin dake hannun Imsal ta ɗan taɓasu jin natural roses ne taɗan taɓe baki tana faɗin "ke kuma waya baki red rose kina yawo niƙi niƙi dashi,"
Wani irin bugawa ƙirjin Imsal yayi tana rasa amsar da zata bayar attention ɗin daddy ne ya dawo kansu shikansa Abdullah seda yaji ƙirjinsa ya buga,
Rayyan ne yayi saurin cewa,
"Ke rose dinne har yanzu baki ajjeba da kuka gama hotunan,"
Irin shiya siya ɗinnan ɗan kallonsa tai,
Ta jinjina masa kai tana ƙin yarda idonta ya haɗu dana daddy don ze iya ganewa intayi ƙarya.
 Mummy ta karɓi roses ɗin tana faɗin 
"lallai Imsal kinci gwal ke kaɗai kike iya cin kuɗin yaronnan kirasa me yake da kuɗi ni kaina babarshi pencil be taɓa siyamin na neman albarka ba,"
Da sauri Rayyan ya ce
"Mummy I'm planning something big for you, nasan chicken change money ɗina ba abinda ze miki, villa nakeso na gina miki wacca tafi ta shugaban ƙasa"
Kallon Abdullah tana faɗin 
"Kaji ko haka take kullum se daɗin baki,
ka ringa mishi faɗa mutuwa dai akeyi idan ya tara kuɗi ya mutu cinyewa zamuyi," murmushi Abdullah yayi kawai don dama ba wani shirin kirki tsakaninsu da Mummy ɗin don yadda zata zauna taima Rayyan tas inyayi abu haka take zama tamai musamman yadda taga yasa Hajiya Nafisa agaba kan bayason siyasar da take yi shiyasa basa ma zaman guri ɗaya, yanzu ma yayi mamaki data sashi cikin maganar ta.
 Daddy dafo imsal tayi yana faɗin 
"muje ciki I have something nice for you" haka ya jasu ciki Abdullah agefen haggunsa Imsal a damansa bema bashi damar cewa ze tafi ba.
A parlour suka tarar da Natasha tana bawa Hajiya labarin abinda Imsal da Abdullah suka mata yau cike da takaici jin sallama da al umma dayawa yasa ta juyo,
tsayawa tai da labarin ta ƙame kamar statue tana kallonsu,
kafin ta wani yi ihu tana daka tsalle tai kan Daddy itama tana cukuikuye shi,
Mummy riƙe ƙugu tayi ganin Rayyan da Imsal suna mata dariyar tsokana saboda yadda ta gama kuri akan Natasha seta watsa mata ƙasa a ido itama,
Sakinta daddy yayi yana kallon uniform ɗinta yace
" ke me yasameki haka?
Me yasami uniform ɗinki duk wani zane zane har fuskarki meya faru?"
Rayyan da sauri yace 
"yauwa daddy gara da Allah yasa kai kagani inda wani ne ya gani ya faɗa zatace anmata sharri sign out ta tsaya yi gashinan harda su spray paint duk jikinta don batasan ciwan kanta ba tana kallon yar uwarta ta ta dawo lafiya ba wanda ya mata komai ajiki,"
Turo baki natasha tai tana faɗin 
"Daddy is just sign out fa, abin kwana ɗaya,"
Rayyan cikeda kumbura bala'i yace 
"ki rantse matane kawai suka miki signing ajiki nafasan halinki,"
ganin daddy yayi kicin kicin yana jiran amsar ta yasa ta juya gurin Mummy tana faɗin 
"Mummy kin ganshi ko?"
 Mummy ɗaga hannayenta tai alamar babu ruwanta tace 
"ai doctor kika sani shi ya shigar miki karma kizo inda nake"
ta ƙarasa tana zama gefen Hajiya tana gaidata, amsawa tayi fuskarta ba yabo ba fallasa.
Natasha sakin Daddy tai ta ƙaraso tana wani maƙalewa Mummy tana faɗin "Mummy sorry kinsan shi na daɗe banganshi ba shiyasa,
amman aikinsan kece number one favourite dina ko Mummy kiwa yaya magana,"
"tashi ajikina karna mareki zaki batamin jiki da wannan painting ɗin"
 miƙewa Natasha tai cikin jin haushi tana ɓata fuska ganin Imsal da Rayyan na mata dariya ta shiga bubbuga ƙafa tana komawa wurin Daddy da fata yayi suka ƙarasa zama ciki falon ya shiga yi mata nasiha kan rashin jin da take yi akan duk yana samun labari daman kuma yanason ta dena imba so take suyi faɗa ba, haka dai tajishi tace mai tadena.
Se alokacin yaran suka sakeshi ya gaisa da Hajiya ta shiga tambayar sa
"saukar yaushe ya hanya"
 yace 
"ai ko awa ɗaya da sauka basuyi ba hanya alhmdlh,"
Takalli Mummy tana faɗin 
"Ashe tafe kuke da A'isha ko Abujar ka biya mata kan kazo,"
girgiza kai yayi kafin ya kalli Mummy cike da soyayyar ta da bata ɓoyuwa a idonsa yace 
"taje canne ɗan hutu shine muka dawo tare"
 taɓe baki Hajiya tayi tana fadin
" toh yayi kuje ku huta bari na saka zuhra tayi muku abinci kafin ku gama,"
miƙewa mummy tayi tana kallon Daddy tace 
"Doctor muje ko,"
Ɗan kallon Hajiya yayi yana jin kunyarta sosai.

Ganin haka yasa Rayyan ya kalli Abdullah yace 
"bari muwuce Daddy anjima zamu shigo can ɗin,"
Daddy ya kalli Abdullah yana faɗin 
"ka gaishemin da mamanka"
yace 
"zataji in sha Allah,"
Yace 
"kar amanta atahomin da Mubeena anjima,"
Yace 
"insha Allah Abba semun dawo"
ficewa sukayi daga falon,
Imsal ma sumsum ta nufi sama tana ƙerawa Natasha tataso,
ganin kamar akwai tension tsakanin Hajiya da iyayen nasu funfurun Natasha tayi mata ta ƙara gyara zama saman kujera.

Mummy ganin Daddy be miƙe ba yasa ta ɗan kalleshi ciked a ƙosawa tace 

"Kona wuce railway ne?"
ahankali Daddy ya miƙe yace ma Hajiya,
"Uhmmm..ahmmm zamuje can tal'udu ne kamar yafi space, 
karmu zauna anan kuma ga yara duka zamu ta kura miki koh Hajiya,"
Murmushi kawai Hajiya tai dama tasan za'a rina indai yazo A'isha na garinnan ba zata taɓa barinsa ya zauna a inda take ba, tace "toh Allah ya kiyaye hanya amman dai kunsa anyi muku shara ko,"
Ɗan kallon Mummy yayi,
Takalli Hajiya tana murmushi cikeda kissa tace 
"nayi hiring wani cleaning company tun inacan nafisa tayi guiding dinsu sunyi duk abinda ya kamata tun shekaranjiya mama," jinjina kai Hajiya tai tana faɗin 
"adawo lafiya"
da sauri Natasha ta miƙe tana faɗin "Mummy nima zanbiki,"
Mummy ɗan kallon Hajiya tai kafin ta basar duk da yadda takeson kwashe ƴaƴanta tajisu kusa da ita kafin ta koma musamman Imsal se batace komai ba.

Daddy yace
" kije ina ɗin babu inda zaki je, 
kwana nawa zamuyi dududu kiyi zamanki anan zamu ringa zuwa dubaku,"
Awani shagwaɓe Natasha ta ƙarasa gurin Mummy tana faɗin 
"nidai Mummy dan Allah kicema Daddy zan biku ai munyi graduation kuma islamiyyar mu ma tafi kusa da can gidan,"
Kallon Daddy Mummy tayi kafin ta kalli Hajiya tace 
"niba ruwana sakeni ki tambayi kakar ki da baban ku,"
Hajiya tace 
"Aka raka taki gona dama banice nakawo kuba kuwuce, 
Ke harda Imsal ɗinma sekun tafi,"
Ta Kwalawa Imsal kira tana falon sama da sauri ta sakko tana faɗin 
"na'am Hajiya,"
Tace 
"kema haɗo kayanki kibi iyayenki dan nasan kinma fita nacinsu,
 idan suka ƙara tafiya gantalin sukai gaba seku dawo nima naji kunnena zobe,
 dama Rayyan ne ɗan gidana ku.tafi abinku,"
Imsal ɗagowa tai tana langaɓe kai tace "ayyah nima Hajiya anan zan zauna ba inda zanje na barki, sede kitaho muje tare,"
Riƙe baki Hajiya tayi tana faɗin 
"ba dani za'ai lalatar zama agidan ɗaba zaki haɗo kayanki ki wuce ko sena ɓata miki rai"
tuni Natasha tai sama dan ɗibo kayanta,.
Imsal tace 
"Hajiya Please...."
Mummy ce tatari numfashinta tace 
"yazaki ringa sa'insa da ita Imsal wuce kije kiyi abinda ta saki karna sake jin bakinki"
Imsal badan ta soba ta hau sama haɗo kayanta.
Hajiya ta miƙe tana nufar ɗakinta,
Daddy kallon Mummy yayi yace mata 
"ina zuwa"
 yabi bayan mahaifiyarsa Mummy ta taɓe baki tabi gidan Hajiya da wani shegen kallon ƙasƙanci tana ya tsine fuska.

Ahankali Daddy ya tura ƙofar ɗakin Hajiya harta zauna saman gadonta ta jawo Radio ɗinta tsabar yadda yake shakkarta a ƙofa ya tsaya yace 
"Maama in shigo?"
 ajje radio tayi ta gyada mishi kai ya ƙarasa ciki ya zauna aƙasan carpet gefenta yace
"Base sun bimu ba Allah,
muɗinma indai ɗakinmu na nan agyare yake zanyi mata magana semu zauna anan kawai,"
Murmushi Hajiya tayi tana shafa kansa
tace 
"Ummaru bazan takura maka ba, 
nasan ka daɗe ba tareda iyalinka ba kana bukatar ƙebewa guri guda dasu,
Sannan kasan zamana da A'isha baze taɓa haifar da ɗa me ido cikin gidannan ba, shiyasa ma ban ji haushi ba,
dan kace zaka bi matarka sedai inason ku tsaya ku kula da tarbiyyar yarannan da kyau kamar yadda nakeyi anan ɗin musamman Natasha har zaman ku ya ƙare"
ɗan jinjina kai yayi kafin yace 
"dan Allah kiyi haƙuri ma'ana"
 tace 
"Ummaru ba abinda kaimin tashi kaje Allah yayi maka albarka, yasa albarka cikin zuriyarka"
se a lokacin yaji zuciyarsa tayi sanyi ya miƙe yana mata sallama ya fice ta bishi da kallo.

A parlour ya samu Mummy da Natasha dako sauya kayan jikin ta batai ba ta haɗo kaya trolley guda, yace 
"ke kuma ina zakije da waɗannan kayan? ce miki akayi dundundun zaki koma can ɗin,"
girgiza kai tai tana rarraba ido daidai Imsal na sakkowa,
awata babbar jakar goyo tazubo kayanta.

Ya kalli Natasha yana faɗin 
"wuce ki sanja kayannan na jikinki sannan ki rage kayan da kika zuba aiba garin zaki bariba,"
da sauri Mummy tace 
"Doctor da munje can duk se tayi,
wallahi nagaji ƙafata duk ciwo takeyi kasan yanzun inkace taje sama wani zaman zata samu yi,"
Kallon Natasha yayi ganin tayi ƙifi-ƙifi da ido bata motsa daga inda takeba.
Yace 
"ba magana nayi miki ba"
 da sauri ta ja trolley da tama fi ƙarfin ta tayi sama.
 Mummy kawai ta juya ta fice yasan haushi taji ba'a bi yadda takeso ba.
Karɓar jakar hannun Imsal yayi yana dafota ganin duk mood dinta is off yasa yace 
'ya dai ƙawar Daddy meya faru?"
Ahankali tace 
"zamu bar Hajiya ita kaɗai fa,"
Yace 
"karki damu Rayyan will be here kinji,"
jinjina kai kawai tayi, yace 
"ya exams hope you aced it,"
Jinjina mishi kai tayi alamar eh,
Yace 
"Rayyan yafaɗamin duk kunci jamb ita 210 ke 280 ko,"
Murmushi tai tace 
"eh Daddy,"
Yace
" yanzun se admission ko,"
Girgiza kai tayi tace 
"Daddy se anyi post utme"
 yace 
"again?
wani exams din?"
 jinjina masa kai tayi yace
"karatun ƙasarnan gaba ɗaya wahalane, Unique da badan nasaka kuɗina awancan aikin ba Harvard zan kaiki
Kiyi karatu inda mukayi duka"
murmushi tayi tace 
"Daddy hakanma mungode Allah your trying your best and I really really appreciate it,"
Murmushi yayi yace 
"you always know the right things to say ko,"
Murmushi tayi tace 
"Daddy aikaine ka koya min,"
Girgiza kai yayi yana faɗin 
"I'm not wise when I was your age, 
da I'm wise enough like you bazan auri mamanku ba,"
da sauri ta kalli ƙofa inda Mummy ta fita ta rufe baki tana dariya ƙasa kasa tace 
"karka bari taji baruwana,"
Shima dariyar ya shiga yi yana faɗin 
"I'm just stating a fact fa, A was blinded by love and I'm still blinded by it, I love her way too much, gashi kullum cikin samun issue nake da mahaifiyarta because of that,"
Murmushi kawai Imsal tayi saboda tasan gaskiya yake faɗa 
"Mummy ta mugun latsa Hajiya inkaga tayi mata mutunci toh agaban Daddy ne na ganin ido yana barin wurin ko sabgarta bata bi takanta tsakaninsu iyakaci gaisuwa,"
"Be wise when choosing a life partner,"
Taji Daddy ya faɗa yana shafa kanta,
Ƙasa dakanta kawai tayi batace komai ba.

Daidai nan Natasha ta sakko da jakarta irin ta Imsal ta sako doguwar riga itama irinta imsal sak donma kartasa wata ace tayi wani laifin,
wucewa sukai suka fito, Daddy ne yayi driving motar tasa, Mummy agefensa agaba itada Natasha abaya.


It's fatoumspassion  IMSAL 
Don't forget to 
Share
Comment 
Like
Vote