Chapter 1
by @fatyafreen1
*DANGIN MIJINA*
*BOOK 1*
WhatsApp ---***
BY FATY AFREEN
(Oum Ra'eed)
Wattpad- fatyafreen1
Arewapen- Fatyafreen1
*Idan kunada buqatar cigaban wannan labarin ku tintibeni ta WhatsApp numberna ta akan farashi qalilan 500naira*
Bismillah_____✍️
Page-1
Inna zaune a bakin qofar shagon chemist da nake aiki Inna shan iska, kasan cewar yayin yau da zafi, hankalina yana kan wayata, dagowar da zanyi naga wata 406 Ash colour tayi parkin, tashi nayi nashiga shagon saboda inna tunanin magani akazo siya, wanda nagani ya fitoh daga motar ne yasani sakin murmushi tare da fadin
"Dama ana ganinku ai kunzama manya ynzu"
Dariya yayi yace "Harkina da bakin magana".. Dariya nayi daidai lokacin ya qaraso inda nake gaisawa mukayi sosai kasan cewar tin da nataso nake crushing akansa,
"Ummu-salma kenan"ya fada Yana murmushi Wanda ya bayyanar da dimple din dake fuskarsa kansancewar shidin black beauty ne tinda muka taso nake crushing akansa,
Sunansa Abubakar Adam Shu'aibu, haifafen garin katsina (Dutsin-ma), Ya karanci civil engineering a FUDMA University dake cikin Dutsin-ma, amma ynzu currently yana aiki a Kaduna...
Sunana ummu-salma Ibrahim Abdullahi Nakasance nima yar garin Dutsin-ma dake cikin jihar katsina,,, anguwar mu data da Abubakar anguwar 'yan daka....
Dangina da nasa sunkasance suna zumunci,tinda muka tashi tare muka gansu,Abubakar yakanzo gidanmu sosai yayi hira haka nima nakanje gidansu nayi hira dan kanwarsa Maryam tare muka taso komai tare mukeyi da ita, ataqaice dai kamar qawa take agurina dan dik wata shawara tare mukeyinta ita.. Tinda ya graduate ya samu aiki ban Kuma sashi a ido ba yau kusan 2years kenan saboda aikin daya samu a kaduna
Abubakar yanada yaya mace (Hauwa'u) se qannensa uku, mata biyu da namiji(Maryam) ita take binsa sai (Umar) saikuma Autarsu(Zainab)...
Sunan ma haifiyarsu Hadiza amma suna cemata Ummee...Mahaifinsu mal.Adam Yana da provision store babba Wanda dashi yake kula da gidansa har Allah ya bama yaronsa aiki... Yayarsa watoh tanada Yara biyu dikka maza, tana auren wani babban me kudi acikin garin katsina hakan yasa takeji da kanta sosai,
Gefena Kuma mu biyu ne agun iyayenmu nida Dan qanina (Ishaq) sunan mahaifiyata Khadija amma Muna kiranta da (Umma) mahaifina babban Dan kasuwa ne.watoh mal.ibrahim...
*Cigaban labari*
Haba "Yaya ai da dauka ka manta damu ne, yaushe Ka dawo" murmushi yayi yace tin jiya dadddare
"Allah sarki sannu da zuwa ba fada Inna qoqarin tattare kayana ganin haka yasa yafara fadin "tafiya zakiyi ne?" Gyada Kai nayi Inna fadin eh lokacin tashi na yayi, sallamar hafiza mukaji waccan dama ita zata karbeni da misalin karfe 2pm..
Gaisawa sukayi da ita ta kalleni tana kashemun ido daya Dariya nayi dan na gano me take nufi.
Komawa yayi ya tsaya jikin motarsa, cikin qasa da murya hafiza take cewa "ya kinyi sabon catch ne?" Zaro ido nayi Inna "Yaya Abubakar nefa Yaya Maryam" itama zaro ido tayi, tana fadin "haba ,kyayawane wallahi" banko kulata ba nadau jakata na nufin inda yake, "muje insaukeki agida" yafada yana juyawa zuwa motarsa.
Inna shiga motar wani kamshi me dadi ya daki hancina daidai sanda wayarsa tafara ringing, dauka yayi tare da sakin murmushi a fuskarsa, niko na tsaya kallonsa wanda hakan yasa ya dan daga mun girrar sa nayi saurin kawar da kaina daga kallonsa dan motarsa yayi yanacigaba da wayarsa...
Tinda muka hau hanya yake waya har muka Kai qofar gidanmu , muryar mace nake jiwo shidai bawata maganar kirki yakeyi ba dik ita take surutun , yana yin parkin "yace toh naji" zankiraki batare daya jira yaji mezatace ba ya katse wayar..
Niko narasa meyasa nakeji wani baccin rai azuciyata , "Nagode Yaya" nafada tare da bude murfin motar... Murmushi yayi Yana fadin "kigaida umma" bance masa komai ba na fice daga motar na shige gida...
Innajin wani iri azuciyata...
Inna shiga gida Maryam na tarar tana zaune a Palo murmushi nayi Inna fadin, "kinshigo kenan, ynzu muka rabu da yaya ashe ya dawo"
Tabe baki Tayi tana fadin "ya dawo Dan drama ba" ajiye jakata nayi na baje akasa Inna cewar meyafaru
"Chapter suketa sha shida ummee akan yarinyar dayakeso ya aura, Ummee Kuma bata sonta" yafada yana danna wayarta.. miqewa zaune nayi da sauri tsoro dik ya cikamun zuciya Wanda bansan na meye ba..
*Idan kinaso kuwa kasance dani acikin littafinan turomun da saqo a WhatsApp numberna ***
Akan farashi 500naira kacal👌
*Oum Ra'eed*