HADIN KADDARA

Chapter 18

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                     By

         AyshaNalado 


Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍


BOOK 1


Page  18


Sosai Mother ta yi busy a kitchen, hakan yasa ba ta ji shigowar su Suraj ba. Zama AA ya yi a ɗaya daga cikin kujerun falon ya lumshe idanu tare da dafe kansa da ke sara masa, ganin haka yasa Suraj jiki ba kwari ya yi kitchen domin kiranta, duk wani karsashi da murnar ganin Yayan nasa na juyewa zuwa damuwa, saboda damuwar da ya gani a tattare da shi. Motsin shigowarsa kitchen ɗin ya janyo hankalinta, ganinsa hannu sake,  nan take fuskarta ya canza “Oh Allah! Ba a dace ba ko?” ya gyaɗa kai “ Ai duk laifinka ne Surajudeen, yanzu ya kake so na yi da Bunayya?”  Ta  karshe maganar tana jifansa da harara, ƙasa ƙasa ya ce “Yau ni dai na shiga uku, na taɓa ajiyar ɗan gwal.”  “ Me ka ce?” Ta tambaya tana matsowa da cokalin miya ta roba a hannunta, da sauri ya yi baya yana ƴar dariya, “Inna ta ce fa za ta aiko miki, yanzu take yi, ta ma kusa gamawa.”  Ajiyar zuciya ta sauke, tana nuna shi da cokalin ta ce, “Allah yaso ka.” ta yi ƙwafa ta juya ta ci gaba da aikinta. “Ya B ɗin ma  ya iso fa.” Juyowa ta yi “Yana ina?”  “Falo, ina ganin kamar baya jin daɗi, very upset da shi.” gabanta ya ɗan faɗi, dama ta zargin haka, gas ta rage, ta ajiye cokalin suka fito falon tare da Suraj. Har ta zauna gefensa ba shi da labari, “Bunayya.” Ta kira sunansa a hankali cikin taushi, amma shiru, hakan yasa ta ɗan kara ɗaga sauti. A hankali ya ɗago ya zuba mata idanunsa da suka sauya launi. 
“Na'am Mother.” “Mene ne?” Ya girgiza kai ƙadan kafin ya ce, “Babu.” “Akwai.” ta bashi amsa kai tsaye tana kallosa cikin ido, Dauke kai ya yi daga kallon titsiyen da take yi masa, ya ce. “Ina jin yunwa Mother, a bani fura.” Sai da ta juyo ta wullawa Suraj dake zaune yana kallonsu kamar ya samu TV kallon ka gani ko, kafin ta sauke ajiyar zuciya, ta ce “Babu fura a ƙasa Bunayya, na aika yanzu ake yi, ka yi hakuri, ban san za ka zo da wuri ba, amma bari na hada maka tea ka sha kafin na ƙarasa maka girki.” Sai da ya lumshe ido ya bude kafin ya girgiza kai ya ce, “ No furan kawai nake buƙata zan jira.” da kai ta amsa masa. Sai kawai ya miƙe ya yi sama zuwa ɗakinsa ba tare da ya sake cewa komai ba.  Kallon juna Suraj da Mother su ka yi,  “Mother me yake damunsa?” “Ban sani ba Suraj, gabana na faɗuwa,  ina jin tsoron wani abu.”  Da sauri ya ce “Mene ne?”  “Sanin naka ba shi da amfani.” Sai kuma ta mike ta wuce kitchen don ci gaba don girkinta. Zamewa Suraj ya yi ya kwanta a 3 sita, yana jin zuciyarsa babu daɗi, gafe daya kuma  yana jiran karsawowar su Salman dake hanya, ya so yau ya gabatar da Salmah a wajen Ya B da Mother, ya so kwarai ranar da Salmah za ta fara taka ƙafa cikin gidansu ya yi mata tarba ta musamman, sai dai yanayin Ya B ya rusa masa tsari, Ya B ba kawai Yaya bane a garesa, rabin jikinsa ne, damuwarsa tasa ce haka farin cikinsa nasa ne, yana jinsa a ransa fiye da duk wani hasashe, shi ya raine shi da hannuwansa, a tsakanin kafaɗa da kirjinsa ya bude ido har ya fahimci wanene shi, akan Ya B ya fara sanin soyayya da daɗinta.



Kamar yadda Inna ta yi alkawari, bayan fitar Suraj cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala haɗa, lafiayyar furarta dakan hannu da ta ji kayan ƙamshi, ta  cura da yawa ta zuba a tsabtabbiyar roba mai murfi, sannan ta kwalawa Maamah dake tsakar gida tana wankin fararen uniform ɗinta na school of midwife kira.  “Hee inna.“  ta amsa “ki zo ki kaiwa Umman Surajo furan nan.” “ Hee Inna, mi ɗo.”  ta faɗa tana cire hannu a ruwan wankin, ta dauraye tare da miƙewa, baƙin hijabinta dake kan igiyar shanya ta ja ta saka, ta shiga ɗaki ta karɓi robar furar ta tafi.

Yana shiga ɗakin, kai tsaye fridge ya nufa, ya buɗe ya dauki ruwa mai sanyi, ya lalubi bakin gado ya zauna, ya ɓalle murfin goron ya kafa kai ya shanye,  wurgi ya yi da goron, kafin ya koma da baya ya kwanta  daga zaune da yake kafafunsa a ƙasa yana kallon saman ɗakin, kirjinsa ya yi zafi, zuciyarsa kamar zata kama da wuta, zai iya jurar komai, banda abu ɗaya, zai iya yin biyayya a komai banda abu ɗaya, bai taɓa yin jayayya da umarnin Abba ba, tun da ya mallakin hankalin kansa, kuma baya so ya fara a yanzu, zazzafar  huci ya furzar sannan cikin raunatacciyar murya ya furta. “Abba… why? Abba me yasa kake son shiga gonar NURIE? Abba ka yi haƙuri, ban taɓa gaya maka ba, my heart belongs to someone else, the girl that’s so, so, so special… beautiful, rare, and impossible to forget.” lumshe idanu ya yi, lokaci guda kuma wata irin haɗaɗɗiyar murmushi wanda kana gani kasan kai tsaye daga zuciyarsa take, ta suɓuce masa. “Na tsane ka!”  kamar saukar aradu muryar yarinyar ya ratsa kunnuwansa, babu shiri wa ware idanu lokaci guda murmushin fuskarta ta ɓace ɓat,  "koɗaɗɗiyar fuskata yanzu ka fara ganinta, ba zan kyale ka ba har sai na ga bayan ka, na yi maka alkawarin sai na rusa dukkan farin cikin ka, mugu kawai, na tsane ka, na tsane ka, na tsare ka!…" Haka kalmar ya dinga amsa kuwwa a kunnuwansa, take jikinsa ya dauƙi rawa,  ya toshe kunnuwansa tare da rintse ido da ƙarfi,  amma ina babu abinda ya ragu, domin sautin daga zuciyarsa take fitowa kai tsaye tana zarcewa ƙwaƙwalwarsa. Ya fi mintuna biyar a haka kafin, ringing ɗin wayarsa ta dawo da shi hayyacinsa, ɗaga wa ya yi kai tsaye ba tare da ya duba ko wanene ba, daga ɗaya bangaren, ya ji muryar da ya sanya shi ware idanu, “Alhmdlh Maigida akwai kyakkyawar albishir, ina bukatar haduwa da kai da gaggawa idan babu damuwa.”  zaune ya karkare miƙewa, muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Giɗaɗo, an same su ne?.”  “A'a amma da yiwuwar samun nasu nan da ko wanne lokaci.” Sai da ya sauke wani irin ajiyar zuciya, kafin ya ce, “ Mu haɗu yanzu a palace.” yana katse wayar ya miƙe tare da wurgata a aljihu, kai tsaye ya fice daga ɗakin da sassarfa. Daidai wannan lokacin Maamah ta sake rangaɗa sallama a bakin falon Mother, jin ba a amsata ba a karo na biyu ya sa ta shigo kan ta tsaye da tunanin ko basa ƙasan ne, tunda gidan ba baƙonta ba ne.

Sautin taƙun da ta juyo daga stainrcase, yasa kai tsaye nan idanunta ya sauka. Wani irin wuntsilawa ƙirjinta ya yi lokacin da idanunta ya sauka a kan mutumin da ke saukowa daga kan stainrs ɗin,  da sauri ta yi  baya ta saki robar furar tana zare ido, tare da kiran sunan Allah,  sandarewa ta yi a wajen ta rasa abin yi, sai kuma ta juya ta kwasa da wani irin gudu kamar  zararriya, ta fice daga gidan, tana waige.

Yanayin da yake ciki ya sanya Mother kasa yi masa musu, lokacin da yake bata uzirinsa na kiran gaggawar da aka yi masa, da sassarfa ya fice daga falon Suraj ya biyo bayansa,  suna fitowa waje, motar Salman na kutso kai cikin gidan, tun daga nesa ta hangesa, gabanta ya yi mummunar faɗuwar, shigar nan tasa ta ɓadda kama, ta yi imanin tafi kowa ganesa da shi. Suraj ya hango su, amma uzurin yayan nasa ya hanasa karasowa, sai da ya tabbatar ya shiga motarsa ya tayar, sannan ya nufo su cike da farin ciki, sun na tsattsaye bakin motar,  dauke kai Salmah ta yi ta sha mur don sai da aka kai ruwa rana tsakaninta da Salman kamin ta amince ta biyo su,  Aysha kam gaba ɗaya hankalinta na kan motar AA dake kokarin ficewa daga harabar gidan.

Gaba ɗaya hankalinsu ya yi gaba domin Suraj har ya kama hannun Salman sun yi ciki Salmah ta bi bayansu, taba harare harare, hakan yasa ta juya ta fice da gudu ta bi bayan motar tasa. Burinta bai wuce ta sake nuna masa koɗɗaɗɗiyar fuskarta,  kamar yadda ta yi masa alkawari, sai dai  cikin rashin sa'a bai juyo ba balle yasan da zamanta, ciza yatsa ta yi, cike da takaici lokacin guda zuciyarta na ƙara  tunzurata, tana jin har idan ta bari wannan damar ya wuce mata ta yi babbar asara, “Ba za ka taɓa tsare min ba, wallahi  sai ka ga koɗaɗɗiyar fuskar wacce za ta zama ajalinka Babangida.”  Cikin ɓacin rai da rufewar ido, ta miƙa hannu ta tari mai adadaita sawun dake wucewa, ta fara yi masa nuni da motar A A da ta fara yi musu nisa tana basa umarnin bin bayansa.

Duk abinda ke faruwa, akan idanun Ussy da Jarumi yaran A'A da suka yi masa tsakiyar sirri  dake zaune cikin mota, suna jira ya yi ɗan nisa su rufa masa baya kamar yadda suka saba,  Ussy ya ce, “ Wannan yarinyar victim ce, Maigida take bibiya.” “ Da wanne ta zo.” cewar Jarumi, “ Ban sani ba, amma bana tunanin ita ma  kamar sauran ƴan matan ne, duba da yanayinta.” Ussy ya amsa masa idanunsa akan Aysha, “ Hakkinmu mu kare lafiyar Megida, domin don haka ake biyanmu.” Jarumi ya yi maganar tare da kama handle ɗin motar zai fita, “Dakata kasan baya son duk wata harka data shafi mace, mu fara tuntubarsa first.”  “Ka yi kyan kai.“  daidai lokacin napep din ya fara tafiya bayan ta shiga, take Ussy ya tada motar su ka fara bin bayansu, yayinda Jarumi ya shiga lalubar A'A a waya, cikin sa'a ya ɗaga, ba tare da kwana-kwana ba, ya sanar masa abinda ke faruwa, kai tsaye zuciyarsa ya bashi yarinyar ce, “ Ku zo da ita.” shine kawai umarnin da ya ba su ya kashe wayar.  Ci gaba da bin gefensu  suka yi har sai da suka daidaici wajen da babu mutanen kafin suka sha gabansu, babu ɓata lokaci Jarumi ya fito ya nufo napep ɗin bayan ya daure rabin fuskarsa da hankicif, ya kwama bakin madubi, duk da gardama da kafiya irinta Aysha ganin bindiga yau muraran yasa ta yi laushi, sai zare ido take yi tana ambaton Allah a zuciya, ƙirjinta kuwa kamar zai fashe tsabar bugu. Lokacin da ya bata umarnin fitowa ta shiga motarsu ne, ta so tirjewa, sai da ya yi mata jan ido, da kan shi ya saka hannu ya ficikota daga keken, ya wurgata bayan motarsu ya rufe, ya shiga gaba, Ussy ya taka da gudu suka bar wajen bayan sun baɗe mai keke da ƙura.

Yadda ta shigo gidan a gigice tana hali yasa Inna dake zaune tana tsintar shinkafa miƙewa, ta saki tiren ba tare da ta shirya ba.  Kai tsaye a kanta Maamah  ta faɗa tana wani irin haki tare da nuna bayanta, tana yi mata bebenci.  Jijjigata Inna ta shiga yi hankalinta a matukar tashe, “Innalillahi wa Inna ilaihi! Maryam, Maryama, Mero, Maryoji. Mi waɗi a boni! Me  ya same ki ? Ko ɗume waɗata? “ Na ganshi. Inna na ganshi.”  “ Mi waɗi a boni, to Maryoji heɓi gamo!, Allah ka shiga lamarinmu.”  sai kuma ta hau tofeta da addu'a.  Sake shigewa jikin Inna Maamah ta yi, ta rike hannunwanta ta ce “ Da gaske na yi gamo, Inna ki yi min addu'a, ki karanta min Ayatul kursiyyu da falaki da nasi.” Jin haka yasa Inna ta ƙara kaimi, tun tana yi a zuciya har ta koma  f yi a bayyane. A hankali nutsuwa ya fara saukar mata, ta lumshe ido ta shi shiru tana sauraren kira'ar Inna da harshenta daya karye da yarenta na fulfulde, kusan mintuna goma sha biyar su ka yi a haka, kafin ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, kamar me ƙurji a baki, ta ce, “Inna!” Dakatawa Inna ta yi ta amsa da “ Na'am Maryama.” Ɗan jim ta yi kafin ta sake cewa, “ Hamma na gani.”  “ Wani Hamman?” Da sauri Inna ta tambaya gabanta na ɗan faɗuwa. “Hamma Babangida.” “ Wane ne haka kuma Mero?” ta sake tambaya cikin yanayin ruɗu da tashin hankalin  da ya kasa ɓoyuwa a tattare da ita, duk da iya bakin kokarinta da ta yi wajen dannewar. “ Inna Hamma Babangida na Adda Shatou.” Cak Inna ta dakata, wutar numfashinta ya dauƙe na wucin gadi, kafin ta yi namijin kokarin janyo shi da karfin tsiya, ta saki wani irin kakkauran ajiyar zuciya, wanda ya sanya Maamah sauri sakinta, sai kuma ta rikota ganin kamar tana shirin silalewa ta kwanta a wajen, “Ya Salam! Sannu inna.”  ta gyaɗa kai dakyar alamar amsawa, kafin ta ce, “ Ki kaini ɗaki Maryam zan kwanta.”