Book 1 page 5&6
by @barista
*MUJARRABI*
(Age is just a number)
By SAYYADA ✍️ Barrister Amanar Nimcy SARAUTA 👸🏻
***
Book 1
PG 5&6
Young talented writers Association YOTA 13
Buɗe idanuwanta tayi a hankali a daidai lokacin da ake kiran assalatu ta asubar farko a nan masallacin dake layin unguwar su, da ƙyar ta sauko daga kan bed duk tsawon baccin da tayi amma ji take bai isheta ba duk jikinta yana mata ciwo, sbd gajiyar tafiya da dawowa ta wajen aiki da take yi. Tana shiga cikin toilet ta watsa ruwa bayan ta yi brush ta ɗauro alwala ta fito ta sanya doguwar riga da dogon hijabi ta idar da raka'a biyu na nafila sannan tayi raka'a biyu na farillah, ta jima tana miƙa kukanta ga Ubangiji sannan tayi azkhar na safe ta ɗan taɓa karatun Alkur'ani sannan ta shigo kitchen, ta tadda Ammie na kitchen tana haɗa karin kumallo hakan ya tabbatar mata cewa Daddyn su zai yi fitan safe saboda a duk lokacin da Ammie in dai da kanta ta shigo kitchen to hakan na tabbatar wa da breakfast zata haɗawa Daddyn su dan shi in ba dole ba baya cin abinci masu aiki sai dai ko su yaran su dafa shima sama² yake ci, HAMRA tana taimakonta amma tun ranar da wannan al'amarin ya faru a sakanin su Ammie ta dakatar da ita daga duk abin da take yi, HAMRA na da gudun ɓacin ran Ammie shiyasa ta ke taka tsantsan da abin da zai jawo ta bata mata rai. Ƙarasowa ta yi kusa da ita cikin girmamawa ta ce
Ammie, ina kwana?.
"Alhamdulillah"
Kawai abin da ta faɗa ta ci gaba da haɗa souce ɗin kayan ciki, Hamrah jiki a sanyaye ta wuce cikin store dan dubo ko da akwai abin da zata girka cikin sauki, mutumin ta tayi tozali da shi Doya, a jibge gefe guda a store ɗin da alamu jiya da daddare mai kawowa Daddyn ya kawo musu, kai fitanta aiki yasa bata sanin wasu abubuwan saɓanin a da ita ke duba ƙarewar abin store ta sanar, ɗauko ɗaya ta yi ta maida hankali ta fere doyar ta sannan tafasa shi ta soya da kwai ba tare da tayi souce ba ta zuba yaji akan plate ɗin da ta zuba soyayyar doyar ta fito, dan tasan bata isa ta taɓa wanda Ammie ta girka ba, to ina ma fuskar balle ta taɓa haka ta tattaro ta dawo ɗakinta ta haɗa black tea ta sha tare da cin doyar sannan ta shirya ta fito tafiya kada ta makara. Ta shige ɗakin Ammie ta tadda Daddyn su ya shirya yana breakfast da alamu fita zayyi da ya kammala ta gaida shi ya amsa cikin kulawa
Good morning Daddy.
"Morning likita, har an fito, to Allah ya taimaka"
Ameen Daddy, eh na fito ina sauri ma kada na makara.
"Gaskiya kam yanzu lokacin gudu yake kan ka ankare ka makara"
Eh fah Daddy,
Ammie anjima da na tashi zan wuce gidan Ayshe.
"To"
Kawai Ammie ta ce, taci gaba da cin abincinta, Daddy ne ma ya ce
"Ah madallah ki gaida min da jikokai na, ko zaki jira na sauke ki ne?"
Zasu ji, a'a Daddy zan wuce ...
Ammar ne ya shigo tare da sallama bayan ya gaida Daddy da Ammie ya ce
"Ah na manta ashe kin koma morning, to tashi na sauke ki, nima fita zan yi"
HAMRA ta sauke numfashi SBD rashin sakin fuskar da Ammie ba tayi mata ba, kuma amsawar da ta yi shima saboda Daddyn su dake wajen ne a hankali ta kalli AMMAR ta ce
"To tashi mu tafi kada na makara"
A tare suka fito, sun ɗanyi tafiya jim kaɗan ya ce
"Afwan bari na kira a amshi sako minti biyu Please"
HAMRAH ta soke fuska ta ja numfashi ta sauke ta ce
Kaga irinta ko, ni dama bari na kayi na hau ɗan sahu hankali na kwance, amma kawai kasa mutum ya makara.
Murmushi yayi ya ɗau waya ya yi ƙira, ya sanar da mai shi ya iso. ya juyo ya ce
"Ayi hakuri likita, ban yi bayani ba tun farko"
Bata ce komai ba ta maida kallon ga bakin titi tana kallon yadda mutane ke sintiri.
Suna nan zaune cikin motar Hamrah taji muryar mace tana
"Young Roheet how fah"
Ta ɗago ta kalleta, fara ce sol ƙirar Yaruba, tana ganin HAMRA ta ce
"Is she your sister, kuna kama sosai, hey barka da safiya?"
Hamra ta sake fuskantar ta amsa da
Yauwa, barka dai.
Ammar ya ce
"Yeah, uhm Furera ga sakon ki, tun jiya fa nake son kawo miki amma abubuwa sun sha min kaina. Ya mika mata ta karɓa tayi masa sai anjima ta tafi ya tada motar su kayo hanyar Hospital, Hamra ta ce
Young Roheet, yaushe kayi sabon suna?.
Murmushi ya yi ya ce
"Tun sunan da suka saka min jss, shine har ya bini"
To, ikon Allah wato kai fans na Roheet ne na India shine suke kiran ka da sunan shi.
"Uhm wai muna kama suke cewa"
Ta taɓe baki ta ce
Uhm ya yi kyau. To AMMAR da alamu bikin Yaruba zamu yi kenan?.
Ya sauke numfashi a daidai lokacin da yayi parking bakin gate na Hospital ɗin ya ce
"Ni bani da wata budurwa wannan itama tana cikin waɗanda zamu tafi training ne kuma tare muka kammala secondary skul namu"
Uhm to waya san muku yaran yanzu.
Murmushi yayi ya ce
"To babbar yaya sai kin dawo"
Thanks.
Ta faɗa ta shige ciki a daidai lokacin da MD shima yake parking. Kai tsaye office nata ta nufa ta buɗe ta shirya duk abin da zata buƙata sannan ta sanya white coat ta fito, taci karo da Nurse Laraba cikin sauri ta iso kusa da ita ta ce
Dr HAMRAH, yau kina morning kenan?"
Kallon ta HAMRAH tayi sam bata son shishigi da kwainene irin da abokan aikinta to in ma ba abin Laraba ba, da bata morning duty ai ba zata ganta ba, ta ce
Eh Laraba, da akwai wani abu ne?.
"No, ba wani abu bane, daman tun jiya nake son yi miki magana ashe kina night duty shine na bari yanzu kuma na ga hango ki shine na ce bari mu gaisa kuma naji ana cewa kun sami matsala da MD wai akan ya ce.....
Sauke numfashi HAMRA ta yi cikin takaici ta ce
Laraba, mind your business. Wannan ba hali bane to menene naki a ciki in ma ya faru ai sakanina da shine.
Tana faɗin haka ta shige cikin general ward, tana mamakin gulmar ma'aikatan wannan Hospital ɗin musamman ita wannan Nurse mai suna Laraba akwai kai kawo sakanin ma'aikata. A nutse take gaisawa da patients ɗin ta jima a wajen su, sannan ta dawo office nata, Dr Aliyu ya shigo tare da sallama yana
"Good morning special Doctor"
Cikin sakin fuska ta ce
Morning doctor Aliyu, ya ƙoƙari?.
"Sai godiya kam"
Da akwai abin da kake buƙata ne?.
"Eh Dr Hamrah akwai patients nawa taƙi na duba ta shine na ce ko zaki duɓa min ita, kin san yawanci mata in ba a dole ba ba sa son maza su duba su, ita ma wannan haka taƙi"
A hankali ta katse abin da take yi a system nata ta ɗago, ta ce
A wane ward take?.
"Tana vip 3"
Ok ba matsala a tare suka fito, Dr Mahmoud yana daga bakin ƙofar office na shi ya kura musu idanu ganin su tare kuma su biyu yasa ya haɗe rai har suka ɓace wa ganin sa. Dr Hamrah ta wuce vip shi kuma ya wuce wani bangaren, tana shiga ta tadda patient ɗin ta dubata sannan ta fito ta iso office nata. Dr Mahmoud da kuma MD suna tsaye suna tattaunawa har ta iso ba tare da tayi magana ba ta buɗe office ta shige ta zauna, ta kunna system nata ta ci gaba da aikin ta. Taji an turo kofar a hankali ta ɗago MD ne ya ƙaraso ya tsaya yana karewa cikin office ɗin kallo cike da mamaki ta kallon shi mutum ko sallama ba zayyi ba da girmansa....
"Hamrah who are you?"
Ta sauke numfashi, bata yi mamakin wannan tambayar ba dan indai bak'ar magana ce ya iya yinta kuma duk yanda yaso haka yake yinta ta ce
I'm human like everyone.
"Saboda jiya nayi miki magana shine kika ɗau gaba dani?"
Ta sake kashe system nata ta ce
Subhanallah gaba kuma MD, a'a ni bana riƙe kowa a raina kuma mema zai sa na yi gaba da kai?.
Eh wato duk iya shegen sa akwai wacce ta fi shi, murmushi yayi har jajayen hakwaransa suka bayyana ya cire glass na idon shi ya ce
"To me yasa da kika ganni da Dr Mahmoud ki ka wuce ko gaishe ni bakiyi ba?"
Ta sauke numfashi ta ce
Oh i got it, nayi tunanin kuna tattaunawa ne shiyasa bana son katse ku.
Nan ma ya ce
"Hamrah i need to know more about you"
This time murmushi ta yi ta ce
I'm nobody but I'm somebody.
"What that means"
Uhm sir, nothing.
Mamaki yake yi tabbas akwai abin da take takama da shi, koma menene zai bincika ya gani sannan kuma nan da kwanaki biyu zata gane kuren ta.
Ya juyo ya fice ta ci gaba da aikin ta. Ita sam taki jinin yawan magana musamman ma akan abin da bai da muhimmanci shiyasa sai suke ganin kamar girman kai gareta, amma she's so simple sai dai ba zata juri wulakanci ba, sannan tana girmama duk wanda ya kama girman shi.
5:00pm nayi ta fito, bayan ta kulle office nata, cikin nutuwa ta iso bakin gate na Hospital ta samu ɗan sahu ta mai kwatancen unguwar Ayshe amma ta ce dashi ya tsaya tayi shopping a bakin babban titi. Nan tayi siyayyar tsaraban yaran sannan ya kaita ta sallame sa.Turo gate ɗin tayi ta shigo ta hango yaran suna wasa a compound na gidan hankalin su kwance sai wasan su suke jin ƙarar turo ƙofar ne yasa suka juyo aiko suna ganin ta su kayo inda take suna
"Oyoyo Mommy Hamrah"
Cikin farin ciki ta rungume su tana cewa
Oyoyo, ya kuke?
Nazeer, shine ɗan fari a wajen ƙanwarta Ayshe ya ce
"Mommy Hamrah muna lafiya, ina grandma and pa?"
Tayi murmushi ta dafa kan nazeer ta ce
Suna lafiya kalau suka ce a gaida ku.
Cikin murna suka rakota ciki, a hanyar ta shigowa ciki ne ta hango sabuwar mota dal anyi parking nata a area park. Suka shigo ciki tana sallama tayi trus ganin an kanza komai na palour, tana ƙarewa wajen kallo yaran kuma su kayi ciki da gudu suna kiran sunan maman su cewa Mommy Hamrah ta shigo. Mamaki take ya a kayi Ayshe ta samu ta kanza set nata bayan sunyi magana da ita, ta ce bata da halin kanzawa. Zubawa sabon show glass din idanu tayi yadda aka jera kwalaben turaren wuta da humaira da culacham a ciki yayi tsari, ikon Allah duk wannan a 2days a kayi shi, sai kuma babban plasma ta dake kan tv stand saɓanin nata da kwanaki ƙarami dake manne jikin garu, tabi kujerun da kallo sunyi kyau cikin yadi golden color....
"Yaya Hamrah"
Ta ɗago ta kalli Ayshe dake ɗauke da murmushi kan fuskar ta, ga dukkan alamu tana cikin farin ciki, itama murmushin ta yi ta ce
Bakuwa babu sanarwa ko?.
Murmushi Ayshe ta yi ta ce
"A'a ai nan gidan ki ne zaki iya shigowa a duk lokacin da ki ka ga dama"
Murmushi HAMRA tayi taji daɗin abinda Ayshe ta faɗa mata ko ba komai ta mutunta ta shiyasa tasu tafi zuwa ɗaya ta ce
Nayi kewar yarana ne naga a weekend amin rowar su.
"Uhum kin ganni nan kwana biyu ban zauna ba yanzu hake ke nake bi a raina, ina ta son na kiraki kuma ina tunanin kina Hospital shine na bari in kin koma gida muyi waya, sai ko gaki ƴar halak"
Nima haka fa, tun jiya nake son kiranki amman ban samu na kira ba na ce kawai inna tashi wajen aiki sai na biyo na duba ki na shigo kuma naga abin duniya.
Dariya Ayshe ta yi ta ce
"Uhmm ke dai bari ƴar'uwa, bari na fara baki ruwa ki sha"
Ayshe ta shige ciki, yaran kuma suka fito suna sake mata sannu da zuwa so biyar ne ƙaramar cikin ita ce takwarar HAMRA suna kiranta da UKHTY ( ƴar'uwa), HAMRA ta rike hannunta tare da zaunar da namecynta kan cinyarta tare da ciro musu da tsara ta basu sai murna suke, ta ce da namecynta
Takwarata, how was skul?.
"So good"
Ta faɗa cikin siririyar muryar ta, yarinyar ce ƴar shekara 3 kyakkyawa da ita kamar HAMRA ce ta haife ta saboda kamanninta ta ɗauko, HAMRA ta sake ce mata
Da anyi hutu zan aiko Uncle AMMAR yazo ya taho dake kinji?.
Cikin murna ta ce
"To"
Suka shige ciki tare da tsarabar su suna murna, Ayshe ta shirya abincin kan Dining table dake Dining area ta dawo palour wajen yayar ta. Zama tayi ta ce to kinga an fara kiraye² sallah magrib mu idar tukuna"
Murmushi HAMRA ta yi sosai rabonta da taga ƙanwarta cikin wannan farin cikin har ta manta, ta ce
Ayshe na kagu naji menene dalilin wannan farin ciki haka.
Itama Ayshe tayi dariya ta ce
"Aiko zaki ji, muje bedroom mu idar da sallah tukuna"
A tare suka shige cikin, Ayshe ta ce da ita ta shige toilet ta ɗauro alwala, HAMRA ta shige ta ɗauro ta fito itama Ayshe ta shiga. Kusan lokaci guda suka idar, amma Ayshe taki bata labarin ta ce su ci abinci tukuna, HAMRA dai ta taɓe baki suka fito tana ganin mulki, sun kammala cin abinci su ne suka dawo palour suka zauna, a lokacin mijin Ayshe ya shigo tare da sallama ganin Hamra zaune yasa jikin shi sanyi ya ɗan tsaya jim kamar ya koma kuma sai ya yi wani tunani ya karaso ya zauna, murmushi Hamra ta yi da taga abin da ya yi, ta san ya san cewa ta sami labarin ƙarin auren da zayyi shine yake jin nauyinta, ta ce
Ina wuni Babana?.
Daman sunan da take kiran shi da shi tun ranar da ya saka mata takwara.
"Lafiya kalau, ya kwana biyu, na ke tambayar mamar ta ki kin ɓuya kwana biyu, ta ke ce min aiki ne ya ɓoye ki"
Sauke numfashi ta yi ta ce
Eh fah ai Sunday ne kaɗai nake hutawa, shiyasa fita unguwar ma bana samun yi yanzun ma na ce zan yi squizing time nawa na biyu na duba yaran.
Ah aiko kin kyauta, ai sha'anin aiki sai an jure abin ba a cewa komai, yana magana yana sunkuyar da kanshi ƙasa, ita dai sai murmushi take to menene yake wani abu so gulty to dan zayyi aure ai babu mai hana shi.
Abin da yasa yake jin nauyinta sbd ya sha wahala kamin aka ba shi Ayshe kusan hauka ya dinga yi musu, HAMRA ce ta shige ma shi gaba wajen Daddyn su aka ba shi hakan ma sai da ta haɗa da wani aminin Daddyn su sannan Daddyn na su ya amince saboda shi Daddyn a lokacin akwai wanda babu ya ya kawo kuɗin aure sannan a zo da wani zance ya ce baza a mai dashi ƙaramin mutum ba, to haka dai Hamra ta yi ta rokon sa da ƙyar ya maida musu kuɗin auren da suka kawo, saboda shima yaga tijarar da Alay Bukar yayi har fa kwana yayi a ƙofar gidan su, kuma anyi ruwa a wancan daren yayi mishi duka har sai da ya kwanta a Hospital, daga karshe dai aka bashi ita sosai ya riƙe sunyi soyayyar da sai da kaf familyn su suka sani suke sha'awar su, har ta kaiga ya saka mata takwara, saboda sake kulla zumunci, ranar suna ko anyi bidirin da ba a taɓa yin irin sa ba dan Hamra tayi wasan Naira. Sauke
numfashi Hamra ta yi ta ce
Amma a hutu zan aiko da Ammar ya ɗauko min takwarata.
"Babu komai ai, sai yazo ɗin in ma bai samu zuwa ba da kaina zan kai miki ita"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Na gode.
Cikin sanyin murya ya ce
"Yaya HAMRA"
Sunan da yake kiranta dashi a lokacin da yake cikin giyar son ƙanwarta duk da ya girme ta amma yake bata girma a matsayinta ta yar matar sa, cikin sanyin murya ta ce
Na'am Alay Bukar.
Daman Allah ya ƙaddara zan sake wani auren, kin san rabo babu yadda ka iya dashi, wai aka ce rabo ajali, to a takaice dai next week za a ɗaura min aure"
HAMRA ta so tayi dariya da wannan dogon zancen da ya ɗebo tun da dai aure ba fashi ai ba wani ɓoye² ta ce
Masha Allah, to Allah ya sanya alkhairi ya baka ikon yin adalci a sakanin su.
Ya washe baki yana
"Ameen wlh Daughter"
Uhm maza kenan halin su sai su. Wato fa in sun ce sai sun yi to sai sun yi ɗin. Ya miƙe ya shige ciki ya bata da zancen zuci, sai da suka idar da sallah ishai sannan ya fice ya basu waje Hamra daman a ɗaki suke HAMRA ta ce ta bata labarin wannan farin cikin, murmushi Ayshe ta yi ta ce
"To yanzu ko zaki ji........
_______________________
(Sakanin mata da miji sai Allah) To sai ku biyo ni dan jin wasu hanyoyi Ayshe ta bi har wannan Alay Bukar nata ya kanza mata set. To uwar gida taho, biyo ni da gudu zuwa next pg dan jin wannan sirrin. Na san wata zata harare ni ta ce ba set ba koma menene za a kanza ba zata yarda a yi mata kishiya ba💃🤣
Allah yasa dai ana fahimtar littafin MUJARRABI 😃
Comments and share fisabilillah