MUJARRABI

Book 1 page 9&10

by @barista

*MUJARRABI* 
    (Age is just a number)

By SAYYADA ✍️ Barrister Amanar Nimcy SARAUTA 👸🏻

***
Book 1 
PG 9&10


 Young talented writers Association YOTA 13 


Tana tsaye har zuwa wannan lokacin tana kallon yanda ake fidda da kayayyakin dake office na Dr Aliyu, cikin wulakanci suke fiddawa shiyasa ma sauran kayan suke faɗuwa suke da farfashewa, lallai MD ya cika mara imani, duk da bata fahimci manufar shi ta yin hakan ba amma tasan da wata a ƙasa. Ba abu ne mai wuya ba ya ɗauke duk wanda yaga dama ya kaishi wani bangaren yanzun ma tasan wani ɓangare na daban zai kashi, shiyasa ake   kiran shi da transfer master sbd yadda yake juya Nurses kamar waina, a ce ba zaya bar ma'aikata su yi aiki cikin kwanciyar hankali ba kullum cikin farga suke. Ta sauke numfashi kamar zata juyo ta komo cikin office nata sai ta hango shi yana tahowa ya turo ƙaton tumbi sai bubbuɗawa yake yana hura hanci yana taunar goro ya iso ko kallon inda ta ke bayyi ba ya wuce cikin office na Dr Mahmoud, ta juyo ta shigo ta ɗau white coat nata ta sanya tare da sanya white eyes glass nata, ta fito tare da sawa office nata key, ta wuce general ward, a nutse ta ke duba patient na ta wacce ke fama da jiki, sai da ta kammala duba ta sannan ta juyo zata fice Dr zalihat ta ce 

"Dr Hamrah, neman ki ma nake, jira nake ki kammala ashe har kin kammalan kina shirin fita"

A hankali ta juyo tare da cire glass dake maƙale kan idanuwanta tana kallon Dr zalihat tare da murmushi ta ce

"Dr zalihat, sannu da aiki ya ƙoƙari, nema ta ki ke yi, to Allah yasa ba laifi nayi ba?"

Murmushi Dr zalihat ta yi daman akwai wasa a sakanin su ta ce

"A'a Dr Hamrah, ni a suwa, ai ku bakwa laifi, daman akan zancen ɗauke Dr Aliyu da a ka yi ne a wannan ɓangaren naga abin ba daɗi, sbd yana taimakawa sosai sannan babu ruwan shi harkar gaban shi ya ke y kuma nan ɗin ya fi dacewa dashi amma a ce MD ya dawo kusa da office naki, abin bai wani tsari ba"

Cike da mamaki Hamrah ke duban Dr zalihat, MD zai dawo office na Dr Aliyu akan wane dalili kenan, to menene amfanin shi wancan office nashi tabbas ruwa baya tsami banza amma ba zata yanke hukunci ba sbd zato zunubi ne ta ce

To ikon Allah, shi kuma Dr ALIYU ina aka kaishi?.

Eh to ɗazu nake jin nurse Laraba tana cewa wai cen bangaren yara aka kaishi kuma an yi mashi iyaka da wannan bangaren"

Sauke numfashi Hamrah tayi, tana jinjina maganar, iyaka da wannan bangaren akan 

 menene kenan there must be something under, ta ce

To Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.

"Ameen"

Ta fito ta tadda sauran nurses ɗin suna ta zance tayi wucewar ta, ta iso office na ta, a lokacin ake shigowa da sabbin kayayyakin MD, sai ganin Dr Mahmoud ta yi ya tsura mata idanuwa yana kallon ta ko kifta su baya yi, ta ɗauke kanta ta shige ciki.

Tana ciki har azahar, sai da ta gabatar da sallah sannan ta fito a lokacin babu har an kammala shigar da kayayyakin cikin office na MD an jera su sai ganin Dr Mahmoud ta sake yi  yi ya fito daga cikin office ɗin bata kulashi ba ta wuce cen wajen patients ta zauna sai la'asar ta dawo ta idar, tana zaune kan dardumar sallah ta ji alamun shigowar mutum tare da sallama cike da mamaki ta shafa addu'ar da take yi ta juyo sbd ta sake tabbatarwa shi ne ko kuma wani ne daban, ganin shi ɗinne yasa ta ɗauke kanta, murmushi ya yi da yake ɗan duniya ne ya yi kamar ba abin da ya haɗa su, kamar bayyi mata laifi ba, ya rage tsawon shi cikin sanyin murya ya ce 

"Hamrah, meyasa ki ke son zama ke kaɗai cikin.....

Dr Mahmoud, faɗi damuwar ka sbd ina da abin yi.

Murmushi yayi ya ce 

"HAMRA kenan, kamar kina gudu na....

Eh ina gudun ka, sbd dabi'un ka ba masu kyau ba ne, sannan ina sake gargaɗin ka a karo na ƙarshe ka fita cikin rayuwata kuma kada ka sake shigo min office is better for you to stay a side. 

"Uhmm HAMRA da an ganki za a ɗauka ke wata wayayya ce amma kuma da an bincika za a famin ci duhun kai gare ki, meyasa ba zaki bari na shigo cikin rayuwar ki ba na wani lokaci kinga za...

Tsawa daka masa cikin ɓacin rai ta ce

"Mahmoud, get out. I said get out, tun kan nayi maka rashin mutunci ka fita harka ta, 

wlh hawainiyar ka ta kiyayi ramata and this should be the last time da zaka shigo min office.

Kafeta ya yi da jajayen idanuwan shi, yana kallon ta yana kuma sakar mata da murmushi tare da kurawa coca cola shape nata idanun ba abin da yake muraɗi irin jikin ta, cikin sanyin murya ya ce 

"This is the beginning, yanzu ma na fara, kuma ban taɓa neman abu na rasa ba dan haka ina da tabbacin cewa sai na biya bukata dake, ki ka baiwa wasu gajoji ma ballantana handsome iri na, wanda mata ke mararin so amma nake kin kulasu shine ni zaki wulakanta to ki sani shi saurayin ki ma mun kaishi ƙasa balle ke da ki ke mace, ni zuba ido ki gani"

Yana gama faɗin haka ya yi ƙofar fita cikin ɓacin rai da tashin hankali ta ce

Kun cika marasa imani, sai Allah ya saka mashi  akan zaluncin da ku kayi mishi, amma kuma sai dai kun manta akwai Ubangiji kuma ya fiku shi zai ƙwato mashi hakkin shi. Sannan kasani ni Hamrah na fi ƙarfin ka, nesa ba kusa ba kuma ba zaka taɓa cin galaba a kai na ba, it will be the last not the beginning.

Murmushi ya juyo ya sakar mata irin na zancen ki ke so, sannan ya fice, ta daki teburin dake kusa da ita zuciyar ta nayi mata raɗaɗi, wannan wacce iyar rayuwa ce, meyasa duk inda take ake samun matsala, meyasa bata samun farin ciki sai bakin ciki, to yaushe zata jita cikin farin ciki kamar yadda kowa ke yi?. Ta sauke numfashi tare da rumtse idanuwanta wani tunani ne ya faɗo mata akan to ta bar wannan aikin mana, sai kuma ta sake sauya tunanin da cewa in kuma ta bari me zata yi, zaman gidan da Ammie bata so kuma tayi ta tunani ko kuma fita shan iska waje ƴan unguwarsu su sami abin faɗa a hankali ta furta

Nothing will happen in shaa Allahu.

Ganin time yaja yasa ta sauke nauyin ajiyar zuciya ciki sanyin jiki ta kammala shirya ko manta ta fito saboda tafiya gida ta tadda duk office na su a kulle ta fice ta iso bakin titi ta tari ɗan sahu ya kawo ta layin unguwar su, ta sauka tare da takowa zuwa cikin layin, jin  tsayuwar mota tayi an parker ta sannan aka fito bata kawo komai cikin ranta ba, ta cigaba da tafiyar ta.....

"Assalamu alaikum" 

Kamar ba zata juyo ba amma dan jin anyi mata sallama yasa ta ɗan juyo tare da amsawa ganin babban mutum ne kuma sanye yake da tufafi ta mutunci yasa ta ɗan saki ranta ta furta

Amin wa alaikassalam.

"Tambaya nake son yi miki in dai babu damuwa"

Ta ɗago tana kare masa kallo cike da mamaki, yana da tsawo sannan shi ba baki cen ba yayi shiga ta babbar riga wacce ake kira da gare, da kuma hula, shaddar dark green ce, ta sauke numfashi tare da cewa 

To ina jin ka Allah yasa na sani.

Ya sauke numfashi da yasa ta sake ɗagowa ta kalle shi, ganin haka ya ce

Ba ƙone ni sauka ta kenan daga airport nayo nan, wani gida nake nema gidan Alay SHAREEF wani ɗan siyasa mai neman takar house of reps, to na shigo ne kuma nake ta tantama kamar ba wannan ne layin ba, shine ganin ki yasa na ce da driver ya tsaya na tambaye ki"

Ta sauke numfashi ta juyo tana karewa layin su kallo ganin ga majalisu ga kuma shaguna a buɗe ana ta siyyayya bai tambayi kowa ba sai ita da mamaki ta sake juyowa tana kallon shi, dressing nashi sak na garin Maiduguri amma kuma baya shige ko kama da mutanen nan da alamu yarene, to meyasa ya zaɓi da ita yake son tambaya.....

Ajiyar zuciya da ya sauke ne yasa ta sudda kai kasa, ya ce

"Menene, kina mamaki ne sbd na tambaye ban tambayi mutan da suke layin ba"

Ta yi saurin ɗagowa tana mamakin ya aka yi yasan abin da take tunani kenan...

"Abin da yasa na tambaye ki shine, bana son shiga cikin mutane sbd wani dalili na, amma da fatan hakan bai bata miki rai ba"

Ta sauke numfashi ta ɗago tare da cewa 

Gidan Alay SHAREEF ba a wannan layin yake ba yana layin baya gida na biyar kofa milk color painting jikin gidan coffee brown ne.

"Na gode sosai, kin san yawanci old GRA layin na kama shiyasa kuma ni bako ne ma'ana mata fiyi, da wannan zuwana na uku kenan garin Maiduguri, ina jin labarin karamcin ku ban taɓa yarda ba sai da ki ka nuna min"

This time ta yi murmushi ta ce

Wannan ba komai bane.

Ta juya ta soma tafiya ta ji ya ce

"Ko zan iya sannin sunar mallamar, saboda ko wata rana zamu iya haɗuwa na sake gode miki"

Hamrah na ke.

"Masha Allah, HAMRAH, nice name, i Alhaji Sama'ila by name from Abuja state"

Ta sauke numfashi tare da jinjina kai tayi wucewar ta sbd na mujiya da ƴan majalisan matasa da suka zuba mata shikenan yau da chapter ta za a kare zama, ta iso kofar gida ba tare da ta juyo ba, bata san ko mutum ya tafi ba ko kuma yana tsaye ba sai ta taji horn na mota, ta juyo sai ganin motar Ammar ce ke mata horn ya ɗaga mata hannu alamun ta buɗe masa, ta ce

Kai da wannan motar ta ka one door ka ke min mulki, to baza a buɗe ba.

Dariya ya yi sbd yana jin abin da ta ta ce, wani yaro ne da gudu ya yi cikin gida ya boɗe mashi ya shiga ya yi parking ya fito yana

"Likita kada ki damu da zaran na dawo daga ABGANISTAN za ki ga na siyo dan kareriyar mota"

Uhm Ammar kenan ce maka a kayi da ga dawowa za kayi kuɗi ai sai ka ci kwakwa tukuna.

Ya yi murmushi ya ce

Ai ni da kafar dama na shiga kin san ina da babban kwali kuma certificate biyu gare ni na nan da kuma na out side kada ki yi mamaki na samu genaral"

Dariya ta yi tana nufo kofar palour tana 

Su genaral manya.

Ya yi murmushi ya biyo bayan ta yana

"In shaa Allahu, duk abin da aka ce Allah an gama komai"

To Allah ya sa.

"Ameen"


 ta wuce ɗakin Ammie, shi kuma ya wuce dakin shi. Tana shiga ta tadda Daddyn su na zaune ta gaida shi yake tambayar ta wajen aikin su ta ce dashi Alhamdulillah, ya ce

"Kamar na ji tsayuwar motar Ammar"

Eh Daddy ya dawo yana ɗakin shi.

To madalla ya yi kyau, shima yanzu fama  yake da jama'a kin san kasuwanci sai an jure saboda har ka ce ta mutane amma kuma yana complain a kan su"

Uhm hakane Daddy sai anyi hakuri, to in ma ba abin UMAR ai harkar jama'a sai an yi hakuri balle kuma customers sai da lallaɓa"

Daddyn su ya yi dariya ya ce

"Wa Ammar ne zai lallaɓa customers ai ko cewa ya ke in dai tsari ka zo yi ka sara ko kuma kayi gaba, baya ɗukan nonsense"

Uhm gashi kuma sun kusa tafiya training.

"Eh na kammala haɗa masa duk abin da zai bukata kuɗin shi ma yana account"

Masha Allah Daddyn mun gode.

Ba damuwa ai....

Ammie ce ta shigo ta zauna Hamra ta gaidata ta amsa sannan ta wuce ɗakin ta.

Faɗawa toilet ta yi ta watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala ta fito ta shiryar ta gabatar da sallah magrib tana kan dardumar sallah ta na lazimi aka kira ishai ta tashi ta idar yunwa ta ke ji, ta fito ta shige kitchen yau ko ruwan zafin haɗa tea ɗin ma nata dashi tana kan ɗaura ruwan zafi cikin electric cattle ne AMMAR ya shigo, ta juyo tana duba me zata dafa cikin ƴan mintina ta rasa ya ce

"Likita nima yunwa na ke ji a dafa dani"

Ba tare da ta juyo ba ta ce

To ai abin da zan girka ne ma ban sani ba.

"To ki dafa indomie mana"

Kai baya raina, kuma dole ke sa na ci, bari na duba cikin store ko na samu abin da zai kwanta min a rai sai na dafa shi.

Ta shige cikin store ta duba ganin tayi kwana biyu bata ci macaroni ba yasa ta dauko shi ta dawo dashi nan ta soma haɗashi jollof na shi, ta soma pa_boilling nashi ta zuba shi cikin matsiyaya sbd ruwan jikin ya tsami sannan ta soma haɗa souce ya ɗan ji wuta sannan ta zuba kifi da nama a ciki sannan ta juyi macaroni a kai ta yi ta juya shi komai ya haɗe ta kashe gas tana kammala  shi ta juye ruwan zafin cikin tea flask ta miƙawa Ammar wanda ke tsaye yana ta santi tun kan ya ci ta abin cikin cikin food flask su ka dawo ɗakin ta, nan ya zauna suka soma ci, yana santi ya ce

"Kai da zayyu da sai ki bini mu tafi ABGANISTAN wlh"

Dariya ta yi ta ce

Kai Ammar naje nayi menene a cen.

"Uhm ki yi ta dafa min irin wannan"

Tayi murmushi, ta ce

Uhm Ammar kenan, yanzu akan abinci sai na bika cen da yake ni ce ƴar fari ko.

Dariya ya yi sosai ya ce

"Yes babbar yaya"

Ya haɗa musu tea suna sha suna fira ya tashi ya kunna tv sai suka ji ana  nocking, Ammar ne ya miƙe ya buɗe, ganin ƙawar Hamra yasa shi cewa

Shatu ki shigo mana"

Ta shigo Hamra na ganinta ta sakar mata da murmushin nayi kewar ki, ta ƙaraso ta zauna nan Ammar ya fice bayan sun gaisa. Hamra ta haɗa mata tea tare da zuba mata abinci tana

Ƙawata saukar yaushe haka, shiru babu labarin ki.

"Yau na dawo, na tambayi Nura mai shago ko yaga giftawar zuwa wajen aiki ya ce eh kin fice, shine na ce sai zuwa dare zan shigo, ji na shuru da kika yi wata ce ta sami matsala shiyasa na rasa number ki"

Ayya Shatu so sorry, ya Mama?.

"Tana nan tare muka dawo ai, da bazan zo ba ma da ƙyar aka shawo kaina"

Subhanallah! Me kuma ya faru?.

"Uhm pretty ke dai bari, abubuwa a kullum sake taɓarɓare min suke, wlh da wannan rayuwar ƙuncin da nake ciki gwamma na mutu, i hate this life, menene daɗin duniyar ma.....

Shatu.

Cewar Hamrah, tare da dafa ta ce

In dai akan jinkirin auren ki ke irin waɗannan kalaman to ki sani wannan babu kyau, kina ja ne da jarrawabar da Ubangiji ya yi miki, kuma ba a so bawa sbd yana cikin tsanani ya dinga furta irin wannan kalaman, sannan irin su ke cire mutum cikin musulunci, musulmi an fiso ya yarda da KADDARAR mai kyau ko mara kyau, sannan Ubangiji yana jarraba bawan shi ne sbd ya gwada imanin shi, amma da addu'a, hakuri da juriya sai ki ga ya yaye mana damuwar mu kamar ba a taɓa yi ba, abin da nake so dake shine ki daure ki ci gaba da addu'a Allah zai kawo mafita.

"Hamrah pretty na gode da karfafa min gwiwa, wlh matsalar da nake cikin ta, tafi ƙarfin kai na, abin ya wuce tunanin mai tunani, in taƙaita miki saura ƙiris na sami matsalar brain, sbd tunani da kuma tashin hankali"

Jikin Hamra ya yi matukar sanyi ta gyara zaman ta cikin sanyin murya ta ce 

Shatu kina nufin bayan matsalar da na sani kina fama da ita akwai wacce ta fita?.

"Eh hakana nake nufi akwai wacce ta fita amma kuma kusan ita wancan ɗin ta rashin auren ce ta haifar da wannan ɗin, zan faɗa miki komai amma sai ranar da baki da aikin wuni zan shigo na sanar dake"

Sauke numfashi Hamrah tayi cikin sanyin murya ta ce 

To shikenan ƙawata gobe ma night duty gareni, babu inda zan je sai kin shigo.

Sun ɗan taɓa fira sannan Shatu ta tafi, Hamrah ta dawo ta rufe ƙofarta, ta haye kan bed ta yi addu'an bacci sannan ta kwanta.





Comments and share fisabilillah