06
by @legendspen
(06)
Bai ko kalleni ba ya shige mota ya tafi, na kusa minti biyu a tsaye sannan na juya ga su Malaika.
“Ku zo mu tafi.”
“Wallahi Nana ban yarda saurayinki ba ne sai yanzu.”
Fauziyya ta faɗa bayan sun ƙaraso inda nake.
“Ni har yanzu ma mamaki nake, kinsan su waye familyn Ta Ambo kuwa? Kaf jihar jigawa suna cikin manyan masu kuɗi guda biyar, ‘yan kasuwa ne na gaske masu arziƙi, duk a turai suke rayuwarsu baki ɗaya, wannan ma kina ganinshi kinsan ba rayuwar nan ba ne, gashi duk ‘ya’yan attajirai suke aure.”
Tin da Malaika ta fara magana har ta dire idanuna na kanta, domin nasan gaskiyya take faɗa zalla ma kuwa.
“Idan kuwa hakane tabbas wannan yafi ƙarfinki Nana, ina baki shawarar karki ɗaurawa kanki abinda bazai ɗaure ba, kizo ki sha wahala a banza.”
Fauziyya ta faɗa tana dafa ka faɗa ta, ni basu san abinda ke damuna ba wannan ba ne, fushin da ya yi ya tafi ya barni yafi komai ɗaga min hankali.
‘Yanzu yaushe zan sake ganinsa?’
Na tambayi kaina sai dai ba mai bani amsa, tsoro na ɗaya kar ya yi dogon fushi, fata na dai Allah Ya kawo shi da wuri, sai dai fatan ba ai amso ba dan haka aka yi sati ɗaya babu shi babu alamunsa, duk na damu gashi ni irin mutanen na ce da ba su iya faɗar damuwarsu wa wani ba, sai dai na bar abu a zuciyata ya yi ta cina, ni kam sai dai aga ina ta rama duk na zagwanye. Haka kuwa aka yi na yi ta faman rashin lafiya a tsaye babu zazzaɓi sai ciwon kai sama sama, tari da kuma ɗacin maƙwogwaro, haka na yi ta fama sati ɗaya sati biyu har sati uku, hankali Hajiya da Alhaji duka ya tashi, kowa yasan akwai abinda ke damuna amma nakasa faɗa.
Haka su Malaika ko da yaushe sai sun tambayeni saurayina, kuma a ko yaushe sai sun nusar dani cewar yafi ƙarfina, tun ban fiya sa abun a rai ba har na yardarwa kaina Fahad yafi ƙarfina, har na fara jin cewa ya gane yafi ƙarfina ne shi ya sa ya tafi bai sake zuwa ba.
Abu kamar wasa Fahad ya yi wata ɗaya, ya yi wata biyu, ya yi wata uku. Ta dole na haƙura da Fahad na fara tunanin cireshi a raina, sai dai hakan ya gagara duk ranar da na fita da sa ran ganinsa nake fita, haka zan ta ganin masu kama da shi a hanya.
Wata ranar juma’a cikin wata na huɗu da rabuwarmu da shi, ranar ma daƙyar na iya fita makaranta sai da Hajiya ta yi min jan ido sannan ma na fita, ko a cikin aji ma haka Malaika ta isheni da surutu.
“Daman na faɗa miki Fahad ba tsarar aurenki ba ne, bikin Cousin brother ɗinsa ake yi yanzu haka komai a Abuja aka yi sai jiya su ka dawo Jigawa ɗaurin aure zaayi yau ɗinnan sai kuma wani event ɗin anan dutse da zaayi gobe Asabar, ‘yar gidan ministan man fetur yake aure.”
“To yanzu ni mene alaƙa da hakan?.”
Na faɗa ina kallonta, wayarta ta zaro ta shiga dubawa, tana faɗin bari ki ga. Duk cikinmu daman ita kaɗaice mai waya, duk tafi mu waye sabida gidansu tsantsar ‘yan boko ne gaske.
“Kinganshi.”
Ta faɗa tana miƙomini wayar, idanuna suka saukan akan kyakyawar fuskarsa. Yana sanye da wani baƙin men lace da aka yi masa babbar rigar, yasa baƙar hula da baƙin takalmi haka baƙin agogo, wayanda suka ƙara haska farar fatarsa.
Ji nai zuciyata ta yi wani irin bugu da ƙarfi, na yi saurin runtse idona sai ga ƙwalla zir zir.
‘Ashe haka na yi kewarsa? Ashe haka nake son sa?.’
Na shiga tambayar kaina.
“Ke mene haka? Lallai iska na wahalal da mai kayan kara, chaɓ.”
Na ji muryar Malaika na faɗa, ban ko kulata ba na miƙa mata wayarta, na kifa kaina da benci na shiga kuka a hankali marar sauti.
Ina wannan yanayin har aka tashi, na ɗakko jakata na fito banko tsaya su ba, sai dai ina fitowa bakin gate na ji ƙirjina ya fara wani irin bugu, na shiga waige waige.
“Me kuma kike dubawa ne?”
Fauziyya ta faɗa, ban ko kula ta ba nasake waigawa. Yau daga can nesa ya tsaya, dan bana iya hango fuskarsa sosai sai dai na tabbatar da shi ne, baƙaƙen kaya ne a jikinsa sai dai na yau yadi ne, kuma motar ta sa yau ma baƙa ce. Basan lokacin da na fara ɗaga ƙafafuna ba ina bin hanya zuwa inda yake sai da na daina jiyo hayaniyar ‘yan makaranta sannan na waiga baya, ashe na yi nisa ma.
Haka na ci gaba da takawa har inda yake, bansan na yi kewarsa ba sai da na ƙaraso inda yake, na yi ƙasa da kaina na fara zubar da hawaye.
“Nana! Nana ɗago mana.”
Ya faɗa cikin sassanyar muryarsa, kasa ɗagowa na yi sai da yaji shasheƙar kuka ne, sannan ya ce.
“Subhanallahi! Nana kuka kuma?”
Ɗagowa na yi na kalleshi, idanuna ne suka sanar dashi halin da zuciya da gangar jikina suke ciki. A hankali ya ce.
“I’m sorry Nana, kwana biyu da haɗuwar na tafi chaina, and daman zuwan da na yi nazo ma faɗa miki tafiyar ne, last week na dawo kuma Abuja na sauka sabida bikin brother na Aliyu, jiya muka dawo nan kuma jirgin dare ne, yau ko breakfast banyi ba na tawo nan, tun 9 nake wajen nan gashi har 12:30.”
Gaba ɗaya sai na ji wa’yannan ƙwayoyin kalmomin da ya faɗa sun goge duka wani ɗaci da ɓacin raina na wattanni, kalmar da ya faɗa ta. ‘Ko breakfast banyi ba na tawo nan, tun 9 nake wajen nan gashi har 12:30.’ Ta haifar min da wani zazzafan tausayinsa a cikin zuciyata, sai na ji dama nima banyi breakfast ba na tawo.
“Nana! Ki yi haƙuri dan Allah, baran sake irin haka ba.”
Sai da na ja numfashi sannan na ce.
“Na yi ta rashin lafiya sosai, har da low Bp.”
Ya gwalalo ido waje cike fa mamaki ya ce.
“Low Bp Nana? Akan me?”
“Ka tafi kana ta fushi da ni, gash bansake ganinka ba wajen kwana ɗari da uku.”
“Nana duk akaina haka? Ki yi haƙuri bansan zaki damu ba kwata kwata wallahi.”
“Uhm.” Na faɗa tare da niyar waigawa baya, sai dai da sauri na dakatar da hakan sabida bana son ma ganin ko sunan ko ba sa nan dan duk halin da na shiga sune suka ja min.
“Kawayenki?”
Ya tambaya, da sauri na girgiza kai sannan na ce.
“A’a basu ba?.”
Ya yi murmushi sannan ya ce.
“Suna nan tsaye.”
“Uhm su yi ta tsayawar, kasan me suke cewa?”
“A’a sai kin faɗa.”
“Wai daman kaima kasan ba tsarana ba ne, shi ya sa ka daina zuwa.”
“Nana bana son sake jin wannan maganar abarta dan Allah.”
“Tom.” Na faɗa tare da fara wasa da yatsuna.
“Kizo na kaiki gida.”
“Yanzu ka dawo daga can ɗin gaba ɗaya kenan?”
“A’a, zanyi one week anan sannan na je na yi 3weeks acan, shikenan.”
Tun daga wannan ranar kullum sai Fahad Ta’ambo ya zo wajena, soyayya da shaƙuwa ta shiga tsakanina da shi ba tare da kowa ya sani a gida ba, har ya yi satinsa ya koma.
Bayan tafiyarshi ma, munyi waya sau ɗaya a wayar Hajiya da na ɗauka na kirashi, sai kuma wata rana da na je gidan Yaya Radiya.
Ranar da ya cika sati uku cif ranar ya dawo kuwa, da na kirashi a wayar Hajiya ya ce dani ya dawo kuma zai zo har ƙofar gidanmu. Tun da ya sanar da na shiga tashin hankali, dan ko a hirar mu ta ƙarshe da Alhaji sai da ya tunasar dani akan course ɗin da yake so na karanta da kuma amfaninsa.
Afujajan na fice gidansu Amina Aminu, dan a cikin ƙwayenmu ta ɗan fi sirri, Fauziyya ma bata da matsala sai da yawan surutu marar amfani. Tana zaune a tsakar gida tana daka na shigo. Kallo ɗaya ta yi min ta gane ba lafiya ba.
“Nana me ya faru?”
“Muje soro dan Allah.”
Na faɗa ina fitowa, ta tashi ta biyo bayana.
“Amin wai Fahad ne zai zo kuma wai gidanmu.”
Na faɗa kamar zanyi kuka.
“To ke mene a ciki, ba son shi kike ba kuma duk wanda ya ce zai zo gidanku ai aure ne zai kawo shi, ji dai Abdul ɗin Fauziyya yanzu har magana ta tsaya.”
“Ba haka ba Amina, kinsan ko ranan Alhaji ya ce da ni so yake na karanci ko Mass communication ko Law.”
“Kai Nana, Fahad ai me ilimi ne kuma da wayewa, kina tunanin zai iya hanaki karatun boko? Gaskiyya ba alama.”
“Nufinki zai ce zai jira nagama karatu? Mussamam Law wajen shekara goma.”
“Alhaji ba zai iya bari ki yi karatun a gidan mijinki ba, yanzu fa ke damuwarki kawai Alhaji ne, kuma idan kika matsa tsaf zai barki ki yi a gidan mijinki.”
Daga haka tai ta bani shawarwari kala kala, daga nan na koma gida na fara shiri. Ina zaune cikin ɗaki Hajiya ta shigo.
“Hajiya ina zaki?”
Na faɗa ganin irin shirin da ta yi.
“Ki shirya ki taso muje, Hajjace zata tsallaka titi mashin ya bugeta ta yi tsagewar ƙashi.”
“Allah Ya bata lafiya, amma ba inda zani.”
Na faɗa ina kwanciya.
“Bazaki tashi ba?”
“Uhm”
Na faɗa tare da rufe idona, haka ta ƙaraci faɗan ta ta fita, tana fita na miƙe tsaye tare da daka uban tsalle ina faɗin.
“Alhamdu Lillah.”
Ban ɓata lokaci ba na hau shiryawa, ƙarfe 05:30 daidai na ji yaro ya shigo wai ana kiran Nana a waje. A raina na ce. ‘Yanzu da Hajiya tana nan haka zaiyi mini chaɓ?.’
Ina shirin fita na ga Yaya Ridwan ya fito, kallo ɗaya ya yi min ya ɗauke kai ya fice. Nasan dai bazai taɓa yi masa magana ba dan ba halinsa ba ne, amma kallon da ya yi min tabbas ya bani tsoro.
Da yake gidan namu yana da girman compound kafin ka kai ga shiga cikin gidan ya sa na sauke anan, wajen yana da faɗi dan har mota biyu zasu iya tsayawa.
Tun da mike tsaye yake ƙare min kallo sai can ya ce.
“Na ga ma fa ke yarinya ce, anya za a aurar dake yanzu?.”
Na yo dariya sannan na ce.
“To ka jira na girma kawai, kafin nan na ƙarasa karatu na.”
“Ina bazai yu ba, ki girma kuma? Ai ba amfani.”
“Mene ba amfani?”
“Girman mana, bakisan mace tana ƙarama tafi daɗin zama ba, shi kanshi miji yafi son ya aureki kina ƙarama.”
Na yi dariya sannan na ce.
“Alhaji dai ya ce Karatu zanyi.”
“Dagaske ko wasa?”
Ya faɗa da alamar damuwa, ni kuma kai tsaye na faɗa masa gaskiyya.
“Kuma ba zai taɓa bari ki yi aure ba, sai kinyi karatun?”
“A’a zai iya bari na na yi mana idan mijin zai barni.”
“Nana!”
Ya kira sunana cikin wani irin yanayi.
“Na’am!”
“Nana, ina sonki dagaske, kuma aurenki nake son yi, bazan iya rayuwa ina kallonki a haka ba a matsayin matata ba, Nana ina da mugun kishi akanki sosai wallahi.”
Gaba ɗaya na ji tsigar jikina ta tashi, daidai lokacin kuma Yaya Ridwan ya shigo, kallo ɗaya ya yi mana ya ɗauke kai ya shige ciki.
“Nana wannam yayanki ne?”
“Eyh shi nake bi.”
“Okay, amma baya ganin mutane ne?”
Sai da na yi dariya sannan na ce.
“Ai haka yake, shi ko Abban mu ya gani a hanya ko Hajiya zai iya ɗauke kai.”
“Uhm.”
Ya faɗa yana zaro wayarsa, sannan ya ce.
“To yanzu mene mafita?”
“Game da me?”
“Kin manta?”
“A’a ban manta ba, amma maganganun da muka yi da yawa bansan akan wacce kake magana ba.”
“Zancen aure, Nana kina sona?”
Wani irin abu na ji a zuciyata, “wai ina sonsa?”
“Eyh Nana?”
Sai da na ɗago na kalleshi sannan na ce.
“Mugun so ma?”
Ya yi dariya sannan ya ce.
“Wane iri ne mugun son?”
Ƙasa na yi da kaina na fara wasa da yatsuna.
“Nana akwai wata matsala a gida, bansan ta yadda zan samu iyayena da maganar ina sonki ba, sabida mu family ɗin mu gaba ɗaya Rich Family suke aure.”
Gabana ne ya faɗi, maganarsu Malaika ta fito da suke cewa yafi ƙarfina, a Royal family suke aure ko ‘ya’yan manya.
“Nana wannan ba matsala ba ne, ni zanyi ƙoƙari da gida kema ina so ki yi koƙari anaku gidan ki tabbatar Abbanku ya ce zai miki aure.”
Shiru na yi gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, ta ina zan fara tunkarar Abba da zancen ya yi min aure?
“Kinyi shiru, wannam fa aiki ne babba muka ɗauka Nana, kina sona ina sonki, kuma kowa akwai matsala a ɓangarensa, naki ɓangaren ba yanzu za su yi miki aure ba, nawa ɓangaren ‘ya’yan masu kuɗi suke su.”
“Yanzu ni ta ina zan fara, wannan aikin babbane.”
Na faɗa kamar zanyi kuka.
“Ta ina da zan fara, look Nana idan bakya sona ne ki fito ki faɗan.”
“Ina sonka mana.”
“Banga alama ba.”
Ya faɗa tare da kaɗa kai zai fice.
“Ka yi haƙuri dan Allah, zan yi musu magana Allah.”
Banza ya yi ya sa kai ya fice.
“Shikenan na sake ɓata masa rai.”
Na faɗa tare da juyowa idanuna suka faɗa cikin na Yaya Ridwan, yana tsaye yana kallona.
Legendspen
***