Book 1 page 15&16
by @barista
MUJARRABI
(Age is just a number)
By SAYYADA ✍️ Barrister Amanar Nimcy SARAUTA 👸🏻
***
PG 15&16
Young talented writers Association YOTA 13
tsit babu mai magana cikin motar, sai ƙamshi da sanyin AC dake ratsa dukkanin jikin su, ko da bata ɗago ta kalli inda yake ba ta san yana kallon ta saboda yadda ta jita bata cikin nutsuwa, haka kawai take jin mutumin na yi mata ƙwarji. A daidai ƙofar gidan su driver yayi parking hakan ya dawo da Hamrah daga tunanin da ta ke yi. Shatu ce ta fara fitowa driver ya taimaka mata suka sauke kayan, Hamrah na ƙoƙarin fitowa sai ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa
"Umm bani time na ki mana kaɗan muyi magana"
Ta sauke numfashi a hankali ta yi magana ba tare da ta kalleshi ba ta ce
Yamma tayi gashi sallah la'asar ma ta wuce mu, zamu je mu gabatar, amma ba ƙin tsayawa nayi ba.
Murmushi ya yi yana jinjina kanshi ya ce
"To ki ce da Malama nake tare to shikenan amma let's exchange our number"
Ta sauke numfashi tare da amsar wayar shi ta sanya number ta sannan ta fito ya ƙira ta yi saving da Abuja, sukai sallama suka shigo cikin gida shi kuma driver ya jashi suka tafi. Suna shiga ciki Shatu ta daka tsalle tana murna, daman gulma na cinta ta rasa yadda zatai tun ɗazu ta kagu ya tafi ta ce
"Wayyo ƙawata sanar dani good news Allah ya sa ya ce yana son ki"
Murmushi ta yi ta ce
"Ke to bai faɗa ba, ya so muyi magana amma kuma na ce dashi mun yi missing lokacin sallah la'asar za mu je mu gabatar, to shine fah ya karɓi number ta.
"Yeee Allah yasa ya ƙira muji alkhairi"
To in kuma wani zancen na dabanne fah.
"Kai ƙawata ai ga dukkan alamu ma ya kamu"
Dariya su kayi suka shige ciki, kasancewar Hamrah tana da night duty yasa suna idar da sallah ta hau shirin tafiya. Bayan sun fito ne Shatu ta wuce gida sbd kayan dake hannunta bata yiwa ƙawarta rakiya ba zuwa bakin titi. Hamrah ta iso bakin titi ta tari ɗan sahu ya kaita bakin Hospital ta shige ciki, kamar yadda ta saba ta ƙimtsa komanta kan teburi sannan ta kunna system ɗinta yau kam ta ɗan makara bata iso da wuri ba taji ana kiraye² sallah magrib ta tashi ta idar tana kan dardumar aka ƙira ishai nan ma ta idar sannan ta fito da niyyar tafiya general ward sai taji muryar Dr Mahmoud yana
"MD na neman ki yana cikin office nashi"
Kamar ba zata juyo ba amma jin MD yana nemanta shiyasa ta juyo ta dawo ƙofar office nashi har lokacin bai daina kallonta ba, ita kam ko kallon inda yake ba tayi ba tayi nocking ya bata izinin shigowa ta shiga, ta tadda shi zaune ya ɗaura ƙafarshi kan ɗaya ya kishingiɗe jikin kujera ya lumshe idanuwan shi.
Afternoon sir.
Ya buɗe jajayen idanuwan shi ya zuba mata su ya ce
"Have a sit"
Ta zauna ta maida kallon ta gefe, mutum a gaida shi ba zai amsa ba wannan wane irin hali ne ya jima yana kallon ta sannan ya ce
"Dr Aliyu an mai dashi bangaren yara sbd ana bukatar irin shi gogagge ta fannin aiki a wajen, shine naga ya dace da ke da Dr Mahmoud kuyi aiki tare shine yanzu zai zamo messenger na sannan kuma PA nki ina so ku haɗa kai kuyi aiki tare, kamar yadda ku keyi da Dr Aliyu, Please i don't want to see or hear anything from both of you da ya shafi ƙoraf, muna bukatar ku haɗe kanku"
Sauke numfashi Hamrah ta yi ta juyo ta kalleshi kamar yadda yake kallon ta tace
Amma sir, in dai da mutunci ai yakamata ayi shawara dani akan wannan kafin a yanke hukunci, sannan ni na fi son aiki da Dr Aliyu ba a shawar ce ni ba aka ɗauke shi sannan kuma Dr zalihat ce wacce ta dace a haɗa mu ba wai Mahmoud ba, kai ma kasan aikin mu ba zai taɓa tafiya daidai ba kuma kasan halin shi sarai ba son zuwa aiki yake ba shine za a haɗani dashi sbd ni na ɗau nawin aikin shi, Please a kanza shi da Dr zalihat.
Shuru ya yi na wani lokaci sannan ya ce
"HAMRAH, you always challenged me at anything, kina nufin ban san me nake yi bane ke kin fini sani, kada kiga OG ya baki office ki ɗauka dani da ke kanmu ɗaya I'm bigger than you in everything yanzu ma na kiraki ne sbd na sanar dake ba wai shawarar ki nake nema ba.....
Turo ƙofar Dr Mahmoud ya yi ya shigo, yana ganin su ya tabbatar hali ya motsa, duk girman kai ne dasu ko wannensu yana son girma, shiyasa basa jituwa cikin tashi salon munafunci yace
"Ranka shidaɗe, an kammala duba patients ɗin ka"
MD ya washe baki ya ce
"Weldon Dr you are trying fa, thank you"
"Noted sir, ai in dai kai ne komai ma zan iya yi maka shi"
"Yauwa zauna ga Dr Hamrah nan muna magana akan aikin ku ne ku haɗe kai kuyi aiki tare"
"Ai ba komai ai in shaa Allahu.....
Akwai, ni ba zan yi shiru na cuci kaina ba, bana son aiki da kai Dr Mahmoud dan haka a sauya min shi da wata.
"Haba Dr Hamrah, i have changed fah wlh na kanza ba zaki sami matsala dani ba"
Uhm.
Kawai abin da ta ce, sai tayi maganin shi tun da ya ɓata mata suna a wajen Dr Aliyu sai ta sa ya yi regretting, ta miƙe tare da kallon wayar hannu ta lokaci ya ja gashi yau babu patients ɗin da ta duba, ta yi musu sai anjima ta fice, kai tsaye ta wuce general ward nan ta duba su sannan ta dawo ta kwanta, ta jima tana ta tunani kan rayuwa sannan ta kwanta. Gari na wayewa ta dawo gida.
_Bayan kwanaki biyu_
Kasancewar yau morning gareta hakan yasa tana dawowa daga wajen aiki ta faɗa toilet ta watsa ruwa ta shirya cikin doguwar riga mara nawi ta zauna Jin ana kiran sallah magrib yasa ta tashi ta idar har da ishai sannan ta kunna tv tana kallo Ammar ya shigo ya tadda ta zaune tayi zurfi cikin tunani har ya ajiye mata leda ya ɗauki remote ya kanza channel zuwa MBC Bollywood, ana film ɗin student of the year. Ya juyo tare da dan taɓa ƙafarta ta sauke numfashi tare da kallon shi, ya yi mata alamun na tane ta ɗauka. Ta dauko leder ta buɗe ta, roasted fish ne ya kawo mata da moltina sai kuma choculate kala biyu, ta kalleshi tare da cewa
"Na gode Ammar yau kuma har da choculate sai ka ce yarinya.
Murmushi ya yi kai Hamrah akwai son girma, ya ce
"Yarinya ce ke mana"
Hararar shi tayi, ya yi dariya sbd ta tsani wannan kalmar ta yarinya ta ce
Kada kasa na fasa cin abin da ka siyo.
Ya yi murmushi ya ce
"Allah baki hakuri babbar yaya"
Nan ta yi murmushi ta soma ci sai ta ji wayar ta na ringing tana dubawa ta ga mutumin da tayi saving da Abuja ne, sai da ta sinke ya sake ƙira ta ɗauka cikin sanyayar muryar ta tayi sallama, har tana jin yadda yake suke numfashi ya amsa tare da cewa
"Ranki shidaɗe, Allah yasa ba bacci ki keyi ba na tada ki"
Ta sauke numfashi cikin sanyin murya ta ce
A'a na kusa amma.
"To ashe dai ban yi laifi ba, daman na ƙirane mu gaisa kuma na nemi alfarmar ko zuwa gobe ne nazo sai muyi magana"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Eh to da yake ina fita aiki kuma gobe ina da morning duty sai yamma zan tashi.
"Wow, fantastic! Do you mean ke likita ce?"
Yes of course.
"Masha Allah, that's good, ki ce nima ina dab da warkewa"
Baka da lafiya ne?.
Eh.
Ya faɗa, sannan ya ce
"To zuwa yaushe ki ke gida sai nazo"
Jibi.
Ok Allah ya kaimu"
Ameen.
Sukai sallama, ta sauke wayar ta ɗan ɗago ta kalli Ammar wanda ya zuba mata na mujiya tun da yaji da na miji ta ke wayar ta sauke numfashi tare da cewa
Menene?
"Waye ne?"
Me ka ke nufi.
Kai tsaye ya ce
"Wa ya ƙiraki, me yake nufi da wannan kiran?"
All questions for me, ban isa a ƙirani bane yaya Ammar?.
"Da gaske nake fah, kamar da na miji ki ke magana, kuma kina ce dashi yazo jibi me zai kawo shi?"
Ta tattare ledan ta saka a dustbin sannan ta wuce toilet ta wanke hannunta ta fito, ta sameshi ya yi tagumi a hankali ta ce
Sunan shi Alhaji Sama'ila daga Abuja yake, to mun haɗu ne ranan na yi mishi kwatancen gidan Alay SHAREEF mai nema takaran House of reps, shine kuma kwanaki biyu da suka wuce muka haɗu a wajen shopping shine ya kawo ni gida, yanzu kuma cewa ya yi yana so yazo akwai abin da ya ke son muyi magana akai.
Sauke numfashi Ammar ya yi ya ce
"To yazo muji da me yake tafe, amma kuma daga jin sunan shi tsoho ne, in kuma da gaske hakan ne gaskiya ya yi gaba"
Murmushi tayi ta ce
To cewa fa ya yi magana zamu yi, ba wai so na yake ba.
Bayyi magana ba ya ci gaba da kollon shi, ta yi murmushi ta ce
To ai naga son na yi aure kowa ya ke to menene kuma na waɗannan tambayoyin?.
Ya sauke numfashi tare da cewa
"Haka ne muna so ki yi aure amma kuma mun fi son kiyi auren kwanciyar hankali, shiyasa sai mun tantance wanda zaki aura"
Dariya ta yi ta ce
Ƙanina na kaina, kada ka damu da yardan Ubangiji zan yi dace.
Sun jima suna fira sannan ya yi mata sai da safe ya fice, ta yi addu'an bacci ta kwanta.
Washegari bayan ta kammala shirinta, ta fito tayiwa Ammie sai ta dawo bata kulata ba ta fice zuwa wajen aiki, tana isowa sai ga motar Dr Aliyu ta shigo har ya yi parking ya fito yana kallon ta, ta shige ciki ta buɗe, bayan ta kammala jera komata ta zauna tare da sauke numfashi, turo ƙofar ya yi tare da sallama yana isowa ya zauna tare da cewa
"Good morning my partner"
Bata ɗago ba ta ci gaba da danne² a wayar ta, ya ce
Nazo ne mu tattauna akan abubuwan da zamu gudanar wunin yau"
Ai ni tun kan na fito na ke gama daily plan ɗina.
Murmushi ya yi ya ce
"Amma kin san yanzu ni PA kine so, we will work together, kuma dole nasan duk wani abin da za kiyi"
Ta juyo tana kallon shi, shima ita yanke kallo, ta ce
Bai zama dole kasan komai na ba, do you work.
Ya sauke numfashi ya ce
"Dr Hamrah let's work together, bazan sake yi miki abin da baki so ba, na canja fa"
To Allah yasa ba tuban muzuru ka yi ba.
Ya yi murmushi ya ce
To dame zamu fara?"
Akwai patients a VIP rooms dukkanin su maza ne kai za kaji dasu yau, nima kuma zan duba mata a general ward.
Dariya ya yi sosai ya ce
"What that means?"
Kawai.
Ya jima yana kallon ta sannan ya yi murmushi ya fice, ta yi ajiyar zuciya, shi Dr Mahmoud ya yi amfani da Dr Aliyu wajen neman kusanci da ita shi kuma MD yana so ya yi amfani da Dr Mahmoud wajen tattaro bayana daga wajenta, uhmm tayi ajiyar zuciya.
5:00pm na yi ta tattaro yanata² ta yo hanyar gidan, sai dai kuma wani tunani ya bata ta shiga gidan su Shatu su gaisa a tsai tsaye ko ba komai ita tana zuwa mata amma ita bata da time na kanta ma ballantana ziyara, tana shiga a daidai lokacin kuma Alhaji Yusuf yana ƙoƙarin fitowa Mommyn shatu tana yi mai rakiya cikin girmamawa ta gaida su ya yiwa Hamrah kuri da idanu har ta shige ta girgiza kai a ranta ta ce Allah ya shirya. A palour ta tadda shatu aiko tana ganinta cikin murna ta ce
"Ƙawata kamar kin san ko kina raina daman cewa na yi koman dare zan shigo"
Murmushi Hamrah ta yi tare da cewa,
Aiko ba zan ma jima ba a gajiye na ke zan wuce, daman mu gaisa ne.
"Duk da haka sai na shafa miki labarin"
A lokacin Mommyn ta tashigo tare da cewa
"Hamrah ki zauna mana"
A'a Mommy daga wajen aiki na ke zan wuce ma.
To Shatu yi mata rakiya ko.
Shatu ta miƙe suka fito, Hamrah ta ce
Kamar Mommy ta sauko kin yi yadda muka tsara ne?.
Eh na yi tun washegarin ranar na baiwa Mommyn hakuri dashi kuma Daddyn sai dai jikin shiya yi sanyi amma bai fahimci komai ba"
Ai ba zai fahimta ba sai nan gaba.
Dariya sukai suna fira har ta rako Hamrah kusan gidan su Hamrah ta ce
Yauwa ƙawata wannan mutumin na Abuja mun yi dashi gobe zaizo.
"Kai amma na ji daɗi ki ce na shigo mu haɗa beta na taran baƙo"
Ke rufani ki sayani, a da ma da nayi yarinta ke ɗibata yanzu kam ba wanda zan mai wata beta in ya yi mutunci na bashi ruwa, ballema shi wani abun ne zai kawo shi innayi beta ma sai yaga rashin hankalina.
Nan sukai dariya sannan suka rabu, Hamrah ta shigo gida a lokacin ma Ammar ya dawo yana tsaye yana waya ganinta yasa ya katse ya ce
"Ashe baki shigo ba sai yanzu, na yi tunanin kina ciki ai"
Murmushi ta yi ta ce
Gidan su Shatu na shiga, me akwai ne naga kamar da labari.
Murmushi ya yi ya ce
Muje ki girka mana abincin ki mai daɗi.
Ta ɗan buge shi a kadaɗa tare da cewa
A gajiye na ke yau sai dai ka siyo mana a bin taɓawa a waje.
"To ƙanwata kada ki damu harda choculate ma zan siyo"
Hararar shi ta yi ta ce
Ko mutum zayyi ya ya dai girma an fi shi.
Ta yi hanyar ciki ya yi dariya ya bi bayanta. Ɗakin Ammie ta shige ta gaidata amma bata kulata ba ta wuce ɗakin ta har dare tana kwance, Ammar ya shigo masu da kayan ciye² ya ajiye tare da kunna tv suka soma ci sai suna fira sai da suka kammala sannan ya tafi ɗakin shi. Wannan ɗabi an tun suna yara su keyinta har suka girma basu daina ta ba, shiyasa akwai kyakkyawar fahimta a sakaninsu kuma basa ɓoyewa junan su sirrin su.
_WASHEGARI_
A hankali ta buɗe idanuwan ta tare da ƙurawa farin slink ido, tunowa da tayi yau Friday ne yasa ta sauke numfashi ta miƙe ta gabatar da sallah asubah ta ɗan taɓa karatun Alkur'ani sannan ta koma bacci bata farga ba sai wajen 10:00am da ƙyar ta iya tashi ta ƙimtsa dakinta sannan ta wuce kitchen ta dafa indomie ta zauna a kitchen ta ci, ta wuce ɗakin Ammie ta zauna a lokacin Daddyn su yana shirin fita, suka gaisa ya fice ta kalli Ammie a hankali ta ce
Ammie, anjima akwai baƙon da zaizo ya ce yana son magana dani.
Ga mamakinta sai taga Ammie ta saki fuskar har da ƴar murmushinta ta ce
"To saura ki yi sake kamar yadda ki ka yiwa sauran suka tafi"
Kanta a ƙasa ta ce
Ammie ba saurayina bane, haɗuwa mu kayi ya ce yana so muyi magana.
"Ah in ba abinki ba haka kurum ai bazai ce zaizo ba, ni dai na faɗa miki kisan irin tarɓar da zaki yi mashi"
To Ammie na gode.
_____ cikin nutsuwa ta ke shiryawa ta sanya riga da skart ta lace mai background pitch da kuma ratsi blue ya yi dai dai da shape nata ta yi normal ɗauri ta fashe Jikinta da turaruka masu ƙamsha tare da yane jikinta da gyalle ta dau wayarta dake ruri ta yi sallama ya ce
"Na iso"
Ok ka shigo ba damuwa.
To.
Ya faɗa ya kashe wayar.
Ta juyo zata fito sai ganin Ammar ta yi a tsaye yana kallon ta, ta ƙaraso ta ce
Meyasa ba kayi sallama ba, kuma kasan bana son hakan.
Haɗe fuska ya yi ya ce
"Ya yi tsufa da yawa, please kada ki bashi fuska wannan kwalliyar ma ki sauyata"
Sosai ta ke kallon shi cikin ɓacin rai ta ce
Ina ruwan ka da sufan shi sannan ma ce maka ya yi yana so na ne?.
Sauke numfashi ya yi ya ce
"Da gaske na ke ni kwata kwata bai kwanta min ba"
Ta raɓe ta gefen shi ta wuce ɗakin Ammie ta sanar da ita yazo, sannan ta fito.
Tun da ta fito Alhaji Sama'ila ya saki baki da hanci yana kallonta har ta iso cikin sanyayar muryarta ta ce
Sorry, na jima ba.
"A'a ai girman kujerar ki ne"
Ya faɗa yana tsosa keyar shi, ta janyo farar kujerar zama ta ajiye mashi ya zauna sannan ta ce ina zuwa, ta shige ciki, ta ɗauko mashi gorar swan water ta fito ganin Ammar ta yi yana yi mashi magana bata ƙaraso ba ta ɗanyi jim kaɗan sannan ta ƙaraso ya bar wajen ta ajiye mashi tare da cewa
Sannunka da zuwa.
"Yauwa"
Duk jikin shi ya yi sanyi ba kamar ɗazu ba ya ce
"Waye wannan wanda yanzu ya fice"
Ta sauke numfashi a hankali ta ce
Ƙanina ne shi.
"Ƙani?"
Ya faɗa yana kare mata kallo, ya sauke numfashi, ta ce
"Eh girman jiki gareshi amma yaro ne"
Ajiyar zuciya ya yi ya ce
"Hamrah bazan ɓoye miki, ina son ki kuma da aure, tun a ranar da na hango ki har na tsayar dake muka gaisa na kamo da sonki, in har kin amince min nan da karshen wata zan turo magabata na a sanya ranar biki, kin san ni ba mazaunin nan bane wasu abubuwan ne suke kawo ni amma kuma hakan ba zai hana na tsaya ayi komai dani ba"
Jikin Hamrah ya yi matukar sanyi ta ɗago ta kalleshi kwarjinin shi yasa zuciyar ta harɓawa, bashi da wani abin da za a koshe shi sai dai girma da kuma girman jikin da yake dashi ne ba kowacce mace bace zata amince ya aureta. Ta sauke numfashi ta ce
To zan yi shawara tukuna, bani nan da kwanaki biyu.
Murmushi ya yi ya ce
Ko dai ganin na fara tsufa ne?"
Ta yi murmushi tare da cewa
A'a.
Ya ce
"To ba matsala zan jira amma kada ki ja lokacin ya yi tsawo"
To.
Sun ɗan taɓa fira ta ce dashi zata wuce wajen aiki, ya ce ta fito ya sauke ta, taƙi amma ya dage hakan yasa ta shige ciki ganin Ammie ta yi zaune a palour tana ganin Hamrah ta ce
"Da me yazo"
Jikin Hamrah ya yi sanyi kuma amma yadda Ammie ta sake fuskarta yasa taji sanyi ta ce
Ammie cewa ya yi da aure ya ke so na.
"Alhamdulillah me ki ka ce dashi?"
A hankali ta ce
Na ce zan yi shawara.
"Ba ga irinta ba hamrah wannan halin naki shine ya sanya saura gudawa, wacce shawara da ta wuce ki amince"
Eh Ammie daman wai muyi magana ne.....
"Ammie gaskiya basu dace ba, kin gan shi kuwa sai ka ce Daddyn...
"Ammar ka ci gidanku, manya na magana kana saka baki, tshoholo ko shi ya kawa tsufa duniya tunda ya ce yana so angama"
Ya turo baki ya shige cikin ɗakin shi. Hamrah ta ce
Ammie zan shirya na wuce wajen aiki.
"To Hamrah a dawo lafiya"
Ta ɗago ta kalli Ammie sbd rabonta da taji ta faɗi hakan a kanta ta manta, ta wuce dakinta ta dauko jakarta ta fito ta shige ɗakin Ammar ta taddashi ya cika sai batsewa ya ke a dole Alhaji Sama'ila bayi mishi ba ta ce
AMMAR.
Ya kalleta da jajayen idanuwan shi bai ce komai ba ya ɗauke kanshi. Ta yi murmushi a ranta tace su Umar hali ya motsa ta zauna kusa dashi tare da cewa
Ammar, dama ce ta sameni bai kamata mu bari ta kubuce min ba, baka ga yadda Ammie ta saki fuska muna magana ba, sannan menene in na aure shi ai ba wani matsala ni ma ai na tsufa.
Ya sauke numfashi ya fisgar da iska ya ce
"Na yi mai tambayoyi daga dukkanin alamu bashi da gaskiya....
Kai Ammar, shiyasa ya ke tambaya ta wanene kai a gareni ashe da abin da ka faɗa mashi, Please tell me me ka faɗa mishi?.
Ban ce komai ba kawai tambayar shi na yi waye shi, menene sana'ar shi sannan menene taka mammen abin da ya keyi anan...
Ammar wannan ba hurumin ka bane, kabar manya su yi magana, stay out of this, abin da ka keyiwa sauran suke gujemin shine abin da ka ke so kayiwa wannan ko kana tunanin ban sani bane, to ka sani muddin ka zama dalilin tafiyar wannan mutumin to babu ni babu kai.........
Comments and share fisabilillah