MUJARRABI

Book 1 page 17&18

by @barista

MUJARRABI* 
   (Age is just a number)

By SAYYADA ✍️ Barrister Amanar Nimcy SARAUTA 👸🏻

***

Book 1 
PG 17&18

 Young talented writers Association YOTA 13 


 Ajiyar zuciya ya sauke da ƙarfi, idanuwan shi sun sauya kala, duk duniya ya tsani ganin yayar shi cikin tashin hankali ko cikin damuwa baya son ganin ɓacin rainta, shiyasa ya ɗau wa kanshi alkawarin samo mata farin ciki, ita ma taji daɗin rayuwa kamar yadda kowa keyi ta daina zubda ƙwalla, shi dai kawai hankalin shi bai kwanta da wannan mutumin ba, amma zai yi zurfi bincike akanshi, a hankali ya ɗago yana kallon ta ganin duk hankalin ta a tashe ya ce

"I'm sorry"

Ta sauke numfashi jikin ta ya yi sanyi ganin lokaci guda kuma ya dawo cikin hayyacin sa ta ce

Bana so, kada ka sake yi min haka, sannan ko ba komai shi babban mutum ne ya kamata ka girmama shi.

"Ina yin hakanne don farin cikin ki, bana so ki aure shi dan farin cikin Ammie na fi son ki yi aure cikin so da kuma ƙauna"

Ta sauke numfashi, na ji kuma na gode amma kasani dan kaina zan yi ba dan Ammie ba, dan haka ka maida hankali ga shirye shiryen tafiyan ka.

Ya sauke numfashi ya ce

To shikenan"

Ta fice ta fito compound na gidan ta tadda Alhaji Sama'ila har ya shige cikin mota, ta iso ya buɗe mata ta ciki ta shiga, a hankali ya tada motar sbd shi kaɗai yazo, shuru ya ratsa har suka fito daga layin unguwar su, mamaki ta ke irin na mujiyar da ƴan layinsu suka zubawa motar har suka ɓace. Sauke numfashi Alheri Sama'ila ya yi tare da cewa 

"A wacce Hospital ki ke aiki?"

AL'UMMA SPECIALIST HOSPITAL.

"Ok, kin san ba wani sanin kan garin na yi ba, sai kin taimakamin da kwatance"

Suna tafe tana nuna mishi hanyar da zai bi, har suka iso nan ya sauke ta cikin girmamawa ta mai godiya ta shige ciki. Office ta sanyawa key ta buɗe ta shige a nutse ta shirya komanta kamar yadda ta saba. Turo ƙofar Dr Mahmoud ya yi ya shigo tare da sallama, ta amsa ya zauna tare da cewa 

"Yau kam kin makara, in ce dai lafiya?"

Alhamdulillah.

Kawai ta ce, ta ɗauko white eyes glass nata ta saka tare da buɗe system nata tana duddubawa, ya yi murmushi ya ce

"Can we be friends?"

Ɗagowa tayi ta kalle shi tare da girgiza kanta ta ce

Friend's, how was that be possible, ni fa mace ce kai kuma na miji ta ya ya za muyi abota.

Ya yi murmushi ya ce 

"Ana yi ai, shi ya fi komai sauki"

Uhmm, ni bana yi.

Ya yi murmushi ya fice sbd ƙiran sallah da ake yi. Ta sauke numfashi ta miƙe ta shige toilet ta ɗauro alwala ta idar sannan ta fito ta wuce general ward, ta jima a cen sannan ta dawo. Tana zaune ita kaɗai ta ji wayar ta na ringing ta duba Abuja ne suka gaisa nan suka taɓa fira sannan sukayi sallama. Sai ƙiran OG ya shigo ta ɗauka cikin girmamawa ta ce

Barka da hutawa OG.

"Yauwa barka dai Dr Hamrah, ya ƙoƙari?"

Alhamdulillah.

Yauwa haɗamin file ɗin da ki ke haɗamin da sauran document ɗin zan shigo on Monday around 10:00am akwai abubuwan da zan yi"

In shaa Allahu, zan haɗa su OG Allah ya nuna mana jibin.

"Good, ameen"

Su kayi sallama.

Ta miƙe ta fara haɗa su, daman haka ta keyi duk record yana office nata, shiyasa ido yake kanta, kuma akwai sirri a sskaninta da OG shiyasa yake ɗaura ta kan ragamar komai, bata da yawan magana, kuma bata wasa da aikinta, ta kammala haɗasu ta ajiye su cikin loker ta sanya key, sannan ta kwanta. 

WASHEGARI a nutse ta haɗa kayanta ta fito babu mutane da yawa sbd Sunday ne yawan ci ƴan visiting ne a farfajiyar Hospital ɗin ta fito ta tari ɗan sahu ta dawo gida, a filin gida ta tadda Daddyn su ta iso gareshi, cikin girmamawa ta duka ƙasa ta gaida shi

Barka da safiya Daddy

Ya ɗago daga danna wayar shi da ya keyi da alama sako yake son turawa ya ce

"Likita barka dai, kin dawo?"

Eh Daddy na dawo.

"To madalla a huta gajiya"

Na gode Daddy.

"Yauwa likita Ammie ta faɗa min da akwai wanda yazo jiya kuma yana son ya turo magabatan shi, to anjima da daddare ki sameni sai mu yi magana"

Jikin Hamrah ya yi sanyi, anya Ammie bata yi saurin sanar da Daddy ba, da ta bari sun ɗan fahimci juna dashi, amma daga zuwan farko. 

Ta sauke numfashi tare da cewa 

To Daddy Allah ya kai mu.

"Ameen"

Ta miƙe ta shigo ta wuce side na Ammie ta taddata kwance nan ta gaidata ta amsa 

"Lafiya"

Har zata miƙe kuma ta ji muryar ta 

"Nayi magana da Daddyn ku ya ce za ki iya ce masa ya turo magabatan shi"

To.

Shine abin da ta ce sannan ta fito ta tadda Ammar yana shirin fitowa cikin sanyin jiki ya kalleta tare da cewa 

"Kin dawo?"

Eh na dawo, fita za kayi?"

"Uhm magana Daddy ke son yi dani akan tafiyar mu, an matso dashi nan da satin sama zamu tafi" 

Ta ɗan yi murmushi ganin yana magana yana kallon gefe ta ce 

Ina so zamu yi magana anjima ni da kai.

Ya sauke numfashi tare da cewa 

To.

Ya fice ta dawo ɗakinta duk jikinta a mace ta watsa ruwa ta sanya riga da wondo na material sannan ta hau kan bed nata ta kwanta, bata jima ba bacci ya ɗauke ta, ta jima tana bacci ta ji alamun an taɓata buɗe idanuwan da tayi ne ta sauke su kan namecynta ta sakar mata da murmushi tare da miƙa mata hannu, ta riƙe ta janyota kan bed suka kwanta, Little Hamrah ta ce

"Good morning"

Hamrah ta shafa kanta tare da cewa 

Morning cutie, da Mom ki kazo?.

Ta gyaɗa kai alamun eh.

Suka ji sallaman su Nazeer suka shigo suna gaidata ta amsa musu nan ta hau raba musu choculate daman bata rabuwa dashi, suna murna suka fita itama ta fito ta dawo ɗakin da suke sauka, tana shiga ko duk suna nan, ta zauna Maryama na ganin ta shigo ta fice Zeenat ce ta ce

"Yaya Hamrah duk da ina fushi dake amma bazan ƙi gaida ki ba, ina kwana"

Murmushi Hamrah ta yi ta ce

Amin afuwa duk da bansan laifin da na yi ba, lafiya ta kalau.

"Kin ƙini baƙi ɗaya, ko ƙira ballantana ziyara gani da tsohon ciki ƙafata ɗaya a duniya ɗaya a lahira"

Oh sorry Zeenatu na, kin san Allah kina raina tun last week na ke son biya ta gidan ki amma Allah bai nufah ba, ya kuke ina uwar gidan ki?.

"Ni dai ba zan hakura ba har sai kin je min, uwar gida tana nan fah, sai abin da ya ƙaru a halinta yau ma nazo ki bani shawara"

Hamrah ta sauke numfashi tare da cewa 

Ikon Allah, ita bata sanin ta girma, to Allah shi kyauta.

Ameen.

Ayshe ta ce 

"Zeenat ki yi wa Yaya Hamrah uzuri ko dan irin aikin ta, Yaya Hamrah barka da safiya?. Bata ma bari mun gaisa ba"

Lafiya ta lau uwar gida, ya shirye shirye?.

"Alhamdulillah suna yi, dan ni ko kallo basu isheni ba"

Hamrah ta yi murmushi kishi ya motsa ta ce

Kuna yi dai ba suna yi ba.

"Uhm ke dai bari ashe haka ake ji in za ayi wa mutum kishiya kai abin sai an daure, fisabilillahi duk yadda muke da ƴan uwan shi amma suka juya min baya suka koma gindin Amaryar tun basu shigo ba"
Ayshe ki nutsu ki kwantar da hankalin duk wannan ɗokin na wani lokaci ne amma da kansu zasu dawo gare ki.

"Kai ki bari a wannan satin kam sai na durza bakin ƙanwarshe fiddausi"

Ayshe har yanzu hakuri zan baki, ina nan ina kan shiri nan da kwana biyu zan je na zauna miki in ba danna ƙirji nayi miki ba abin ba zayyi kyau ba.

Zeenat ta ce

"Gaskiya kin kyauta ki je cen ɗin yanzu ma da na biya ta gidan ta ƙadan ta mari Yayar shi, muna zaune ta shigo wai ko anƙi ko anso sai ankawo Amaryar mubi duk bokan da muka daman bi, tamu ba ta Allah ba"

Uhm gwada da baku tanka musu ba, ina yaran ne?.

Ayshe ta sauke numfashi tare da cewa 

"Sun bi Yaya Ammar zuwa waje, ni fah nazo da Abinci ko ci ban nutsu nayi ba muje ɗakin ki Yaya Hamrah mu ci na kwanta ko naji 
sanyi"

A tare suka fito zuwa ɗakin Hamrah, suna shiga suka mimmiƙe Hamrah ta fito zuwa kitchen anan aka ajiye abincin, ta tadda Maryama tana zuba abinci Hamrah ta soma zuba nasu a babban trey jollof rice ne wacce ta ji kayan spices, sai dandarun jan nama, ganin irin rainin dake kan Maryama yasa ta ce

Maryama, kina bani mamaki ta yadda rayuwar duniya ke rud'an ki, wannan halin da kika ɗaurawa kanki wallahi babu inda zai kai ki, bansan meyake sanya ki fuzgar kai ba, amma ina mai baki shawara ki bi duniya a sannu.

Turo baki da kuma ɗaga hanci tayi ta ce

"Ai kinfi kowa sanin dalilin da yasa nake haka in kema baki sauya daga ƙiyayyar da ki ke nunawa habibina nima bazan daina abin da na keyi ba, kin nuna banbanci sakanina da Zeenat bacci ni dake mun fi kusanci....

Ya isa, Maryama kada kiga ina biye miki ki ɗauka tsoron ki nake ji, a'a tausayi ki ke bani sbd kin ɗauki dala ba gamo ne, shi Alay Shatteema ne ya ce dake bana son shi ko kuma ke ce ki ke ganin hakan? To ki sani shi rashin mutunci riga ce kowa ma yana iya arota ya sanya ta kuma ya yi, amma kuma ganin rigar ba mai kyau bace shiyasa ake gudun sanya ta, amma in ba haka ba Maryama kin yi kaɗan kimin na ɗauka.

"Ai ko shi Alay Shatteema bai faɗa ba ni ai kin min na gani, kina ɗaya daga cikin waɗanda basu son aurena dashi ko kin manta ne da abin da ya faru a wancan lokacin, sannan haka still ya sake faruwa a ranar sunan Waleed, dan haka duk wanda ya ce baya son mijina to nima bazan yi dashi ba"

Murmushi Hamrah ta yi su sai ta ce

Au sai yanzu na fahimta wato dai kin fi son mijin ki da danginki to ya yi amma ki sani ba a takama da gidan miji amma anayi da na uba, ki yi indai zai miki kyau Allah bada sa'a.

Tana kaiwa nan ta ɗauko abincin ta nufi dakinta dashi tana jinjina lamarin, lallai Maryama ta na dab da zubar da hawayen dana sani in dai akan Alay Shatteema ne. Allah shi kyauta.

Nan suka zauna suka soma ci, yaran sun dawo ma ɗakin Ammar suka wuce dan fita ya yi dasu su kayo siyayya. Bayan sun kammala cin abinci ne Zeenat ta kalli Hamrah tare da cewa 

"Yaya Hamrah na rasa gane kan uwar gida ta, ta hanani sakat a gidan ke numfashi ma so ta ke ta hanani, shima kanshi Alay Gana kamar tsoronta yake da ta ƙirashi har rawar jiki yake duk ya kiɗime"

Uhm Zeenat, daman duk wacce tazo a mace ta biyu a gidan miji sai tayi hakuri, duk abin da za tayi ki kau da kai in kince sai kinyi magana babu wanda zai goya miki baya cewa za ayi kin sameta a gidan dole kice za kiyi hakuri.

Zeenat ta sauke numfashi ta ce

To ai Allah ne ya ƙaddara sai na auri mijinta, dan meyasa zata ja da hukuncin Ubangiji abin da ma zai baki haushi shine tana da ɗiya a gidan miji yadda na ji ma ta kusa haihuwa amma ta ke takuramin"

Ayshe da tayi shiru tun ɗazu ta ke jin nata takaicin ta ce

"Ai ya zame muku dole ki bi tsarin da muka ɗaura mazajen mu akai ta yaya zaku shigo ku mulke mu, ai ba zayyu ba wallahi"

To fah sun rabawa Hamrah kai abin ya koma kowa so ta ke a goyi bayan ta da ƙyar Hamrah ta shawo kan zancen aka sauyata zuwa kayan da zasu ɗinka na fitar bikin  nan da kwanaki biyar, sun zazzaɓa akan Ayshe zata karɓo sai ta kaiwa telan ta, nan Hamrah ta sanar dasu zuwan Alhaji Sama'ila, ai ko suka saka murna suna Alhamdulillah Allah ya ƙarɓi addu'ar su, su kayi ta bata shawa akan ta amince mashi su sha biki. Fira ta sauya an koma na bikin hamrah, ita dai bata ce komai ba sai binsu ta ke da kallo, a haka har suka wuni sai yamma lis suka tafi da yaran baƙi ɗaya aka bar Hamrah da kaɗaici, ta dawo ta zauna jin ana kiran sallah magrib yasa ta miƙe ta shige toilet ta ɗauro alwala ta fito ta idar ta jima tana addu'a akan in Alhaji Sama'ila alkhairi ne gareta Allah ya tabbatar in kuma ba alkhairi bane Allah ya sauya mata da mafificin alkhairi har aka kira sallah ishai ta idar sannan ta fito zuwa wajen Daddyn ta dake zaune a farfajiyar gida tana isowa ta zauna kusa dashi tare da yi mashi barka da dare, ya amsa tare da cewa 

"Da man akan batun wannan mutumin ne, wanda Mommyn ku ta faɗa min akan shi ne zaɓinki a matsayin wanda zai aure ki, shin ɗan ina ne kuma a wacce unguwar ya ke menene sana'ar shi, waye iyayen shi?"

Jikin Hamrah ya yi sanyi sosai ta rasa ta inda zata fara amsa tambayoyin nan ita kanta bata san a salin labarin shi ba kawai dai Ammie ta yi saurin sanar da shi ne , a hankali ta ce 

Sunan shi Alhaji Sama'ila, ba mazaunin nan garin Maiduguri bane wasu ayyuka ne suke kawo shi, a Abuja state yake da zama.

Sauke numfashi Daddyn su ya yi tare da cewa 

"To ke likita ya za kiyi ki aure mutumin da baki san asalin shi ba, shin ma har tsawon yaushe haka ku ke tare har yasa baki san sana'ar shi ba?" 

Kanta na ƙasa a hankali ta ce

Daddy bamu jima da haɗuwa ba baifi sati biyu ba jiyane dai yazo nan ya ke sanar dani cewa yana so ya turo magabatan shi.

"Kayya! Wannan ai bai nuna ba har yanzu zancen danyene ace daga zuwan shi na dauke ki na bashi ce mashi akayi ke kaya ce, ko ko mun gaji da ke a'a ba zayyu ba sai nayi bincike kanshi, kada ki yi gaggawa kema kin ji ko in shi ba zai jira ba ya tafi Allah zai kawo miki wani"

Sauke numfashi Hamrah ta yi to yanzu Ammie zata ce bakin ta ɗaya da Daddyn ta ya zata yi kenan, a hankali ta ce 

To Daddy na gode.

Ta miƙe ta shigo ciki nan ta tadda Mommyn ta a tsaye tana jiran shigowar ta, aiko tana ganinta ta jeho mata da tambayar ya suka yi nan Hamrah ta sanar da ita amma ina ranta ya matukar ɓaci ta ce

Ban gane ba sai kun fahimci juna yanzu mutum ya taso daga wata uwa duniya yazo shine za a ce ba mutumin kirki ba sai anyi bincike to shikenan sai ki zauna muyi ta gogan kafaɗar juna cikin gidan"

Ita dai Hamrah bata ce komai ba kanta a kasa sai ga Daddyn su ya shigo ya tare shi da zancen ya kalleta ya ce

"Hajjiya Batula ni kam me wannan yarinyar ta tare miki ne, yarinya da ko magana bata yi kuma da ta fita tun safe sai yamma ta ke dawowa ko kuma ta fita da yamma ta dawo da safe, to wai ma sbd ta jima bata yi aure ba shikenan daga zuwan shi sai mu bashi ita ba tare da mun san shi ba, ni na faɗa bazan mata auren gaggawa ba, in zai jira zuwa wani lokaci sai a sanya ranar amma daga zuwa ya ce wai har ya yanke lokaci ba tare da ya zauna dani ba ko mun zauna da mutanen shi ba"

Ammie ta birƙice musu lokaci guda da ya sanya Hamrah sorata ta miƙe da sauri zata bar wajen ta ji ta ce

"Na gaji Alhaji, na gaji ka fito kawai ka faɗamin cewa akwai wata manufa a ƙasa shiyasa, yarinya shekaru sun ja manema sun fito amma kuma kace sai ka zaɓa ka ɗirce is she a diamond, ina itama kamar sauran ta ke haihuwar ta akayi, to muddin tana son mu zauna lafiya ta fidda miji ta yi aure, in dai ba wata manufa ta daban cen ba....

"Hajjiya Batula, meya kawo wannan zancen, me ki ke nufi da wannan Hamrah ɗiyata ce ba zan taɓa barin a cutar min da ita ba shiyasa na ke son na aura mata mutumin da zai riƙemin ita da amana, dan haka sai na duba na tantance kuma magana ta zauna, in kuma kin shirya son rashin zaman lafiya cikin gidan to shikenan"

Sauri Hamrah ta yi ta faɗa kan bed ta fashe da kuka me Ammie ke nufi ne...

In ba wata manufa ba, to me hakan ya ke nufi kenan? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun......





Comments and share fisabilillah