Book 1 page 25&26
by @barista
*MUJARRABI*
(Age is just a number)
By SAYYADA ✍️ Barrister Amanar Nimcy SARAUTA 👸🏻
***
Book 1
PG 25&26
Young talented writers Association YOTA 13
Ganin ya rufe min baki yasa na waro idanuwana ina kallonsa sbd fargaba da tashin hankali cikin kankani lokaci na haɗa uban gumi a lokacin da na yi la'akari da ganin babu kaya a jikin shi sai gajeren wondo, ya sake janyo ni jikin shi na haɗe da ƙaton tumbi shi ya yi magana cikin dashesheyar murya tare da zaro min idanuwan shi alamun gargaɗi da kuma tsoratarwa ya ce
"Kada ki kuskura ki min gardama dan za ki sha baƙar wahala kuma ba kyaleki zanyi ba, dan haka is better for to accept me for the hours, bazamu jima ba amma kin kin bini yadda na ke so in kuma ba haka ba zan aikata miki abin da har ki mutu ba zaki dawo daidai ba"
Zuciyata taci gaba da bugawa na tsorata at the time na saduda dan na sadaukar babu mai ceto na a wancan ranar, jikina na rawa, sai zazzaro idanuwana nake sbd rufemin baki da ya yi babu yadda zanyi nayi magana balle kuma nayi mashi magiya, ganin babu sarki sai Allah na soma karanta duk adduar da tazo cikin zuciyata, ina neman tsari daga azzalumin mijin mahaifiyata.....
Fincikoni ya yi ya tadani zaune tare da yaga min rigar dake jikina daman doguwar riga ce, ganin haka yasa na kurma ihu ina rokon sa da ya kyaleni amma kuma sai ya yi kamar baijiba ya hankaɗe ni na faɗi ta baya kan bed ɗin ya danneni yana huce ya ce
"Kinci sa'a kina period ni kuma ina ƙyanƙyamin mace wacce ta ke cikin al'ada, amma ba komai zamu gamu nan da kwanaki"
Ya miƙe ya fice, na sauke numfashi na sake fashewa da kuka cikin ƙuna da takaici ace mijin mahaifiyata yaga jikina, wannan wane irin ƙazamin mutum ne mara imani da tsoron Ubangiji, sam ya manta da cewa akwai mutuwa. Na jima ina kuka sannan na miƙe na faɗa toilet na watsa ruwa na sauya kaya a daidai lokacin Mommy ta dawo gida, na fito palour duk na ka sa nutsuwa, ya fito ya tadda mu a zaune ya dubeni tare da cewa na kawo mashi tea na saka suger kaɗan a ciki. Da farko na ƙi amma kuma ganin Mommy ta bata fuska sbd ganin naƙi tashi yasa na miƙe na wuce kitchen na haɗa, tun daga wannan ranar ya sanya min ido duk motsina a kan idanuwan shi ko me yake dubawa oho, sai dai kuma indai ya aike ni ɗakinshi bana zuwa, da ya fuskanci hakan shine ya ƙirƙiro cewa yana meeting a guest House nashi dan haka Mommy ta dinga aika mashi abinci, a tunanin sa ni zata dinga aika amma kuma sai yaga driver ne yake kaiwa, ranan ya yi waya akan ta turoni da kulolin abincin akan na zanyi serving baƙin, da farko naƙi amma ganin Mommy ta ɓata fuska yasa nabi driver na tafi, a lokacin da muka iso sai ya sallame driver ya rage daga ni sai shi, rarrabe idanuwa nakeyi ko zanga baƙin amma kuma babu kowa, shuru banji motsin shi ba na soma tafiya, na iso kofar palour na murɗa handle door amma sai najisa gam a rufe, nayi² na buɗe yaƙi sai naji motsin fitowa na juya muka haɗa 4eyes da da daddy ɗaure yake da towel a kugun shi, cikin tsoro da firgice na fiddo ita waje ganin yana yimin murmushin mugunta, a tsorace na ci gaba da murɗa handle door ko zai buɗe dan na fahimci plan ya hada amma yaƙi, cikin sauri ya finciko ni na faɗai kasan tyles na buga kaina nan ta ke ya fashe bai ko tausaya min ba ya janyoni a hakan ina zubda jini yana jana har ta kusa ƙofar ɗakin shi muka jiyo an danna door bell, cike da mamaki yake dubana ina cikin mawuyacin hali bazan iya tashi ba balle kuma nayi magana, ya wuce baƙin ƙofar ya leƙa ta maleƙa ganin wacce ya gano ne yasa ya yo kaina a guje cikin tashin hankali ya yi cikin ɗakinshi tare da ɗauko wani kyalle ya ɗaure min bakina baibi ta jinin dake malale kan fuskata ba ya buɗe ɗan wani karamin ƙofar ya sakani cikin sannan ya wrgani ya fice bayan ya ɗaure min hannayena, ina jin motsin shigewar sa ɗakinsa da kuma goge inda jinin ya ɓata, sannan ya buɗe ƙofar palour sai jin muryar Mommy nayi tana
"Ikon Allah, ya naga gidan shiru ina ɓakin ne?"
Da ƙyar na miƙe ina bin jikin garu na leƙa ta wani rami ina hango su, gani nayi ya tsosa keyarsa ya ce
"Ai cewa su kayi sai yamma zasu iso"
"To ina kuma Shatu tayi gashi bata nan ɗin ma?"
"Ai bai jima ba ta tafi gida"
"No driver kaɗai na gani na tambaye shi yace ya barota anan, to daman miyar kuɓewar ce ta tuwan shinkafar suka manta shine na fito dashi daman unguwa zan wuce"
"Ai Shatu bai jima ba ta fice, nayi mamaki ma da baku haɗu ba"
"To daman wucewa zanyi ga miyar nan"
Ta ajiye ta juya da niyyar tafiya kuma ta tsaya tare da cewa
Jini........
Ringing na wayar Hamrah ce ta katse labarin da Shatu ke bata, ta kalleta tare dayi mata alamun bari na ɗaga, Daddyn su ne ta ɗauka cikin girmamawa ta gaida shi ya amsa yake tambayar ta, ya su kayi bikin, ta amsa da komai lafiya sannan su kayi sallama, ta kalli Shatu dake zaune dirsham kan carpet sai a wannan lokacin tayi la'akari da ciwon dake goshinta ta sauke numfashi tare da riƙe hannun Shatu ta ce
So sorry bestie ashe kina cikin mawuyacin hali banne meki ba, meyafaru bayan Mommyn ki ta kalli jini?.
Sauke numfashi Shatu tayi tare da share hawayen dake kan fuskar zatayi magana sai suka jiyo an turo ƙofa an shigo, Zeenat ce suka gaisa ta ce
"Yaya Hamrah dangin mijin Ayshe sun shigo injita wai ki tarɓesu"
Ajiyar zuciya Hamrah tayi tare da cewa
Ina fitowa.
Zeenat ta fice, Hamrah ta ce da Shatu
Ƙawata ina zuwa ɗan bani muntuna bazan.....
Wayar Shatu ta hau ruri ta ɗauka tare da cewa
"An gama kenan zan iya tahowa?"
Ba tare da Hamrah taji mai aka ce ba sai jin Shatu tayi ta ce
"Ok on my way"
Ta katse wayar tare da kallon Hamrah wacce itama ita ta ke kallo ta ce
"Lawyer na ne ya ƙirani, zan tafi, zuwa gobe zan tafi gidan ku na ƙarashe miki labarin"
Lawyer kuma?.
Cewar Hamrah tana takewa Shatu baya suka fito ganin jama'ar dake palour yasa Shatu ficewa ba tare da sunyi sallama ba, Hamrah ta hau hidima dasu sai bayan la'asar ta huta shima a lokacin ake shirye shiryen shigowa da Amarya wajen uwar gida ta shige ɗaki ta kwanta sbd kanta dake tsara mata, lallai Shatu na cikin bala'i wannan wane irin tashin hankali ne, sai 4:30pm aka shigo da Amarya sukayi buɗan kai sannan aka watse.
8:00pm ta kammala shirin tafiya gida suka fito ita da Zeenat da kuma Maryama, Ayshe tayi² su sake kwana amma suka ce zasu tafi Hamrah kuma tana da morning duty gobe kuma Monday ne sai ta koma gida ta shirya Ba zayyu ta kwana anan ba da safe ta wuce, a haka ta hakura suka fito Maryama mijinta ne yazo ɗaukanta ita kuma Zeenat driver ya tura, Hamrah na ƙoƙarin fitowa bakin layin unguwar su Ayshe taga call na Abuja kamar bazata dauka ba ta ɗauka cikin sanyayyar tayi sallama ya amsa tare da cewa
"Baby nah, kwatantamin unguwar da kike yanzu zan iso"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Oh yanzu haka na fito zan koma gida.
"Ba damuwa gani nama iso faɗa min layin?"
Ta sanar dashi, aiko babu jimawa sai gashi ya iso da kansa yake tuka motar yayi parking a kusa da ita ya fito tare da sanya mata kayanta cikin boot na motar ya buɗe mata ta shige ta zauna, sanyi da ƙamshin dake cikin motar yasa ta lumshe idanuwanta tare da sauke numfashi, ya shigo ya tada motar suka fito daga layin sai dai kuma sai taga ya ɗau wata hanyar ba inda ta ke tunanin za taje ba, cikin sauri ta kallesa ya sakar mata da murmushi ya ce
"Yi hakuri baby zan bada saƙo ne sai na maidaki gida"
Ta ɗan sauke numfashi ba ta ce komai ba suka wuce Hotel ya yi parking a bakin gate ɗin ya kalleta tare da cewa
"Baby nah yi min rakiya na bada saƙo sai mu fito"
Kai tsaye ta ce
A'a ka shiga ka fito.
Ya yi murmushi ya ce
"Kamar kina shakka a kaina, na yi tunanin yadda na yarda dake haka kema ki ka yarda dani, amma ba komai jirani na shiga na fito"
Ya fice, tana zaune tana kallon yadda ake shigowa da ƴan mata da kuma fita dasu tana mamakin meyasa Alhaji Sama'ila ya sauka a hotel, kuma ace duk faɗin garin Maiduguri yarasa masauki....
"Sorry baby na jima ko?"
Ta kalleshi bata ce komai ba har ya tada motar ya kawo ta ƙofar gida, zata fito ya yi saurin cewa
"Baby nah kamar kina fushi dani, Please faɗamin laifina sai na bada hakuri"
Tayi ajiyar zuciya tare da cewa
Ina so muyi magana amma ba yanzu ba duk na gaji ina so na huta, sai dai ko gobe.
Murmushi ya yi yana mamakin irin kaifin brain nata ya ce
"Ba damuwa gobe zan zo da yamma ko kuma bayan ishai sai muyi magana"
To Allah ya kaimu.
"Amen"
Ya faɗa tare da saukowa ya cire mata kayayyakin ta sai ganin Ammar ya yi ya zuba masa na mujiya ya ɗaga masa hannu tare da cewa
"Ɗan saurayi taho mana ka taimakawa yayarka"
Ammar ya cika ya yi tam kamar ya haɗiyi zuciya, kut lallai wannan mutumin.....
Ammar zo ka taimaka min kaji.
Ba zaiƙi taimakawa yayar shi ba ya iso ba tare da ya kalli inda Alhaji Sama'ila yake ba ya ja luggage na Hamrah ya yi ciki dashi, ta bi bayansa yana ganin ta shigo ya kalleta ya ce
"Hamrah ki jawa wannan tsohon kunne ya fita cikin harkata ya kuma iya bakin sa dan kin bashi dama bazayyu ya yi duk yadda yake so ba damu"
Murmushi tayi ta ce
Ammar mijin da zan aurane so yana da daman ya aiki ƙanina sanan kaima ai ƙanine gareshi.
"Kai ina wannan tsohon ya yi ɗa dani wallahi, kina gani duk ya kusa sheƙewa"
Bata kulashi ba ta wuce ciki ta barshi yana ta huci, ɗakin Ammie ta shige ta ajiye mata sakon da Ayshe ta ce a bata, ta amsa tare da yi mata tambaya akan komai ya tafi daidai ta bata amsa da eh Alhamdulillah, sannan ta wuce ɗakinta tadda Ammar zaune ya kunna tv yana kallo ta ajiye jakar hannunta ta faɗa toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta shirya ta zauna bakin bed ta kalli Ammar ta yi murmushi ta ce
Ammar jibi warhaka baka nan.
"In shaa Allahu, ina cen Afghanistan ina shan snow"
Murmushi tayi ta ce
Zanyi kewarka zan kasance ni kaɗai cikin gidan nan.
Jikin shi ya yi sanyi ya juyo ya ce
Ai zan dawo, kuma zamu dinga waya.
Hakane kam.
Sun jima suna fira ya tashi ta fice ita kuma ta kwanta bacci. Washegari tunda ta tashi ta shirya ta fice kada ta makara, ta iso a daidai lokacin ƴan night duty sun fara tafiya ta buɗe office nata ta shige ta shirya komanta ta sanya white coat nata da kuma white eyes glass nata tana ƙoƙarin fitowa Dr Aliyu ya shigo ya gaidata babu yabo babu fallasa ta amsa ta ce zata wuce general ward nan ya bi bayanta, sun jima acen yana taimaka mata sannan suka dawo. 5:00pm na yi ta shirya ya fito ta dawo gida, ta wuce ɗakin Ammie ta gaidata tare da sanar da ita akan Alhaji Sama'ila zaizo anjima, amma harda murmushi ta ce
"To sai kije ki shirya mashi snacks ko, to Allah yayi albarka"
Amen.
Hamrah ta miƙe cikin farin cikin ganin Ammie ta saki fuska, ta faɗa toilet ta watsa ruwa kamar yadda ta saba ta shirya ta gabatar da sallah tana kan dardumar sallah har aka kira ishai ta idar Alhaji Sama'ila ya kirata akan ya iso ta sanya hijabinta ta fito taci karo da Ammar dake ƙoƙarin shigowa ɗauke da niƙe² kaya ya ce
"Ya kamata yau muyi fira dan gobe zan tafi"
To Ammar na yi baƙo sai na shigo.
Ya haɗe fuska ya wuce ciki, ta fito ta taddashi zaune, ta yi masa sannu da zuwa ya amsa tare da kura mata idanuwa ko ruwa bata kawo mashi ba ballantana snack tasan ba ci zayyi ba ya ce
"Ranki shidaɗe na iso ina sauraronki, da fatan ba laifi na yi ba?"
Ta sauke numfashi tare da cewa
A'a ko kusa ba laifi kayi ba, daman so nake nasan waye kai, tunda kasan ba zayyu mu gina rayuwa cikin duhu ba.
"Alhamdulillah hakan yana nufin kin amince dani, to na gode da wannan karamcin. Sunana Alhaji Sama'ila kamar yadda ki ka sani, mazaunin garin Abuja kuma ni ɗan siyasa ne kuma ita ke kawoni nan Maiduguri, ina da mata ɗaya da kuma ƴaƴar 7 ina so ne na aureki sbd na yaba da hankalinki kuma naji inason na haɗa zuria dake"
Ganin ya yi shuru yasa ta ɗago, ya sakar mata da murmushi ya ce
"Is that enough?"
Ta sauke numfashi ta ce
Eh.
Daddyn ta ne ya shigo ya yi parking, ganin haka yasa Hamrah miƙewa tsaye tana sudda kai, ya iso inda suke cikin girmamawa Alhaji Sama'ila ya gaida shi nan ya ce ta shiga ciki za suyi magana, ta wuce ciki, sai ganin Ammie ta yi a tsaye a palour ta ce da ita "Ya na ganshi da Daddyn ku?"
Eh Ammie magana zasu yi.
"To madalla abu ya yi kyau"
Umm Ammie ina so muyi magana.
"To bismillah zauna mana"
Hamrah ta zauna tare da cewa
Daman akan Alhaji Sama'ila ne, bakon nawa akwai abin da ya ɗaure min kai game da shi.
"To menene kuma?"
Ammie a hotel ya sauka kuma ya ce dani yana da mata ɗaya da ƴaƴa 7 sannan shi ɗan siyasa ne, to amma ni zaman hotel ɗin ne bai kwanta min ba....
"To sannu ƴar iya, tun da mu bamu sani ba ke ce masaniyar komai ko to ki sani aure babu fashi bari Daddyn ku ya shigo naji ya su kayi zan sake tabbatar mashi da cewa wannan karon dole sai anyi in yaso da kunyi aure ya dafa ki ya cinye ki, mutum ya tako ya bar iyalin shi ya taho domin neman aurenki amma ki ce wai kina tantama shi baice yana tantama a kanki ba da ki ke kwana wajen aiki sai ke. To ki sani wannan karon ba zan lamunta ba, ya zama dole ki amince"
Jikin Hamrah ya yi sanyi ta ce
"Ki yi hakuri Ammie"
Ammie ta shige ciki, cikin fushi Hamrah na zaune ta shiga zurfin tunani ta ji muryar Daddyn su na cewa
"Hamrah jeki baƙonƙi na jiranki kuyi sallama"
Jiki a sanyaye tare da jin kunya ta miƙe ta fito ta tadda shi yana tsaye ta ce
Zaka wuce ko?
"Au korata ma ki ke to ki sani yanzu na zama ɗan wannan ahalin ne"
Murmushi ta yi ta ce
"To da wuri haka"
"Yes Daddy ya ce na turo da manyana"
Daddyn kenan, to ya yi kyau.
Ta mai rakiya ya tafi ta dawo ciki ta wuce ɗakin Ammar, yana zaune yana shirya katanshi ya ki kallonta, ta fahimci fushi ya ke ta zauna kusa dashi tare da sanya hannu tana maimaka mashi suna shiryawa tare ta ce
Fushi ka keyi?
"Eh kinsan daga gobe ba zamu sake zama muyi fira ba har sai na je na dawo shine ki ka jima"
Murmushi tayi ta ce
Daddy yazo ya tadda ni da Alhaji Sama'ila sun tattauna kuma ya ce ya turo magabatan shi.....
"What?"
Cewar Ammar yana zaro idanuwana waje..........
Comments and share fisabilillah