MUJARRABI

Book 1 page 41&42

by @barista

MUJARRABI 

Book 1 
Page 41&42
***

Kallonta Hamrah keyi tun da ta shigo ta ganta ta soma bala'i bata ce komai ba sai dai tayi mamaki a ina taji zancen za tayi auren, ita Hamrah ba wasu ƙawaye ne da ita ba ballantana zancen aure ya bayyana kuma ba wasu ƙannene da ita ba waɗanda za a ce su suka yaɗa sbd yarinta, ƙannenta duk sun yi aure kuma ba masu yawan yawace² bane. Bata so ƴar gold ta san da zancen aurenta ba tafi son ayi sa cikin sirri har ta kammala abin da take so cikin kwanaki kaɗan amma ba komai ko a hakan ma ta san za tayi nasara ko ba a jima ba zasu gano gaskiya su dawo kan turɓa madaidaiciya. Ta sauke numfashi a daidai lokacin da ƴar gold ta ƙaraso ta zauna ta tsareta da idanuwanta ita a dole anci amanar ta, murmushi Hamrah tayi ta ce 

"Ƴar gold, sannun ki da gajiya ban ma jima ba da shigowa, Rahama ke faɗa min kina hanya....

"Dakata Hamrah ki fara bani amsar tambaya ta wai shin da gaske this week za a Daura aurenki?"

Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce 

"Eh Hauwa'u abin da ma ya kawo ni kenan...

"Ba wani pretty daman cen da wata manufa a ƙasa, yaudarar mu ki ke son yi, in ma ita ce to ki sani ko da auren kinne ma za ki ci gaba da wannan harkar"

Uhm.

Cewar Hamrah, Zee ta ce 

"To ai daman ta san da hakan kawai dai auren da za tayi a matsayin kariya ce daga idon al'umma"

Rahama zaune duk jikin ta yayi mata sanyi da abinda Hamrah ta faɗi mata, a hankali ta ce

"Ai aure ba matsala bane muma ai yana kanmu kuma muke harkar, zata iya fitowa ayi da ita kawai a bata sati dan cin amanar ci tana gamawa sai ta fito"

"To na ji wannan shawarar amma tun da taji sirrin mu ya zama dole ta zauna ayi harkar tare amma cewa zata bari ba zata ga daidai ba"

Cewar Hauwa'u Jibrin, ita dai Hamrah bata ce komai ba, bata jima ba ta fito ta dawo gida, a ƙofar gida ta tadda Alhaji Sama'ila a tsaye a kofar gida yana jingine cike da mamaki ta iso inda yake yana ganinta ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce

"Wayar ki bata shiga duk na damu, tun ɗazu nake nan na rasa wanda zan aika shi cikin gidan ya kiramin ke"

Ajiyar zuciya Hamrah ta sauke tare da ciro wayar ganin network ne ya ɗauke ta ce

Wayar a kunne take service ne ya ɗauke.

"Ok shigo mota"

Ta zagaya ta shiga suka zauna jikinta duk yayi sanyi ta zauna cikin sanyin murya ta ce 

Amma lafiya ko?.

Ya juyo sosai yana kallon ta na wani lokaci sannan ya ce 

"Em nazo ne na baki kuɗaɗen da zasu isheki, sannan kuma kin san ba a garin nan zamu zauna ba a cen Abuja ne, dan haka bana son ƴan rakiya dake kaɗai zamu tafi kuma bana son tarkacen kaya ina da komai cikin gidana"

Ta sauke numfashi cikin sanyin murya ta ce 

*To zan je muyi shawara da yan'uwana duk yadda mu kayi sai na sanar maka....

"A'a Hamrah bana son hakan shiyasa tun farko na faɗawa maneman auren cewa bana buƙatar komai daga wajenku sbd bana son yawan magana ne kawai muyi maganar nan a sakanin mu, ke ba yarinya bace da zamu tsaya muna cece kuce kawai maganar ta zauna a haka"

Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce 

"Gaskiya, maganar gaskiya wannan ba al'adar Maiduguri bace kamar yaya zan yanke hukunci da kaina, bayan bani ce zan aurar da kaina ba, zancen akaini babu kayama bai taso ba dole sai an min duk abin da ake yiwa ko wacce amarya. In yaso ko daga baya ne sai akai min cen ɗin. Amma menene dalilinka na son na tafi babu kaya kuma babu ƴan rakiya?.

Ganin ranta ya tsoma ɓaci yasa ya rage murya ya ce

"Shikenan ayi miki kayan, amma daga baya sai a kawo miki, bani account number ki sai na tura miki kuɗi"

To.

Ta faɗa ta bashi sannan ta shigo cikin gida bayan sun yi sallama, mai Alhaji Sama'ila ke nufi ne. Har ta shigo cikin nan ta tadda Ammie a palour tana zaune tana ta shirya kayayyakin da tasa a kawo. Zama Hamrah tayi cikin sanyin murya ta gaida ta 

"Ammie barka da yammaci?"

"Barka dai Hamrah kinga yanzu babanninki suka tafi kalli abin arziki da suka kawo min nan, kai amma sunyi ƙoƙari sosai"

Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce 

Ammie, yanzu Alhaji Sama'ila ya tafi.

"Ah to madalla"

"Amma fah ya ce wai baya son a haɗani da kayayyaki komai akwai acen, kuma babu ƴan rakiya, Ammie na fara jin tsoro"

Murmushi Ammie tayi tare da cewa 

"Ke zolaya ce, giyar wake muke sha da za ace a kai ki babu komai shima kawai faɗa yayi ai sai anje anga masaukinki"

A hankali Hamrah ta sauke numfashi jin abin da Ammie ta ce, dan haka ta miƙe ta shige cikin ɗakinta, ta watsa ruwa ta gabatar da sallah magrib tana kan dardumar sallah har aka kira ishai ta idar ta kwanta. Cikin dare ta farka duk tayi gumi taba sauke numfashi zuciyar ta nata harɓawa sbd mummunar mafarkin da tayi, ganinta tayi cikin daji ita kaɗai dajin naci da wuta babu kowa tana ta neman masu cetonta amma babu har wutar ta kusa dab da isowa inda take shine ta farka ta sauke nauyin ajiyar zuciya. A hankali ta furta

"Mafarki ba gaskiya bane"

Ta tashi ta ɗaura alwala tayi addu'ar bacci ta kwanta.

Washegari tun da ta tashi ta idar da sallah asubah ta koma bacci. cikin bacci taji ana tattaɓata ta buɗe ido little Hamrah ce ke zaune kusa da ita da murmushi ta rike hannunta tare da cewa 

"Namesake saukar yaushe?"

Turo baki little Hamrah tayi ta ce

"Da Mommy na muka zo tana ɗakin granny"

Turo ƙofar da sallama Ayshe tayi ta shigo ganin little Hamrah ta ce

"Au nan ki ka shigo ina ta duba ki"

Hamrah dake kwance ta miƙe ta zauna cikin sanyin murya ta ce 

Aiko ita ta tadani da ko yanzu ina ta bacci. 

"Kema ki shirya yaya Hamrah ki fito mai gyaran jiki ta iso zaku fara tun kan rana tayi zafi"

"Uhm kai Ayshe wane gyaran jiki kuma, ai bikin da saura"

"Wane da saura this coming Saturday nefa yau kuma Sunday please get ready, muna cen baya sai kin fito"

Ayshe ta ɗauki little Hamrah suka fice. Hamrah ta shige toilet ta yi brush sannan ta fito tayi inda suke. Anan suka wuni akaiwa Hamrah gyaran jiki wuni daya tayi matukar kyau sai sokanata suke tana murmushi har suka watse. Biki saura kwanaki uku duk ƙannena ta suka tare a gida, gida kam cike yake da baki kamar aranar ce za a daura ƴan kauye ma duk sun hallara. Hamrah tayi matukar kyau kamar ba ita ba Ayshe ce tayi mata rakiya zuwa saloon aka gyara mata gashin kanta sbd ba zai kitsu ba yana da yawa da tsawo da kuma tsantsi. Ana washe gari biki akayi mata kunshi da kuma lalle tayi matukar kyau. 

Zaune suke bayan sallar la'asar suna fira su Ayshe sai sokananta suke wai ta Alhajin Abuja mai komai dozen, ita dai sai murmushi take yi, suka ji daga waje ana marhaban mutanen Afghanistan. Aiko su Ayshe, Zeenat da Maryama suka fice daga ɗakin Hamrah sbd yiwa yayansu oyoyo sai da da fitarsu suka dakata tare da tsayawa kallon shi, sbd yadda yayi wani haske da kiɓa kamar wani Balarabe ko ba India ya koma tamkar jarumannan na indiawa masu faffaɗan ƙirji da shanyeyen ciki, sanye yake da riga read da kuma ba Black trouser sai kuma bakin agogo, fuskar nan ta fito rau da kwantaccen saje da size box, gashin kannan yasha gyara kamar na larabawa. Murmushi ya sakarwa kannensa ganin yadda suka tsura masa idanuwa suna tantama shine ko ba shi ɗin bane. A hankali cikin silent voice ya ce

"Ina amaryarmu take?"

Suka ƙaraso tare da cewa 

"Ya Ammar tana ciki"

Suna tayi masa sannu da zuwa kai tsaye ya shige ɗakin Hamrah ya tadda tana zaune kasan carpet ganin shigowar sa yasa ta sake baki tana kallon sa irin kallon nan na saukar yaushe. Murmushi yayi ya iso ya zauna kan kujerar gaban mirror ya ce

"A jinki ba zanzo bikinki bane ai ko in bana nan baza a ma daura ba sai na zo"

Dariya tayi ta ce

To alwalina, tunda kazo barka. Ya hanya?.

"Alhamdulillah, ya shirye shiryen biki kuma?"

Anayi.

Sun ɗan taɓa fira ya miƙe ya wuce ɗakin sa ya watsa ruwa sannan ya fito ya wuce wajen Daddyn shi sbd tattaunawa kan yadda zasu tsara gidan sbd taron da za ayi na ɗaurin auren.

Har dare su Ayshe na ta sokanar Hamrah abin da ya basu mamaki shine yadda gidan ya cika makil da mutane har da wasu ƴan uwan su da basu taɓa gani ba, Hamrah tun tana gaisawa dasu har ta gaji duk tayi laushi, ta zame jikinta ta dawo ɗakinta ta zauna. Ammar ne ya turo ƙofar ya shigo ganin sa yasa ta tashi ta zauna. Zama yayi bakin bed tare da cewa 

"Baki kwanta ba ashe, nima sai yanzu na shigo ina cen wajen Daddy wani abu naji wai meke faruwa ne me wannan Alhaji yake nufi da wai baya buƙata ƴan rakiya ya turo wani dattijo wai gobe da yamma za a tafi dake masaukinsa kuma wai baya buƙata ƴan rakiya a ina aka taɓa yin hakan?"

Sauke numfashi Hamrah tayi tare da cewa 

Ya turo da wani kuma Ammar?.

"Eh Hamrah, ba kuyi magana bane"

Ta sauke numfashi ta rasa gane kan Alhaji Sama'ila meyasa baya buƙatar ƴan rakiya me kuma na cewa ita kaɗai zata je masaukinsa wane masaukin kenan yake nufi shin ya tanada mata inda zai ajiye tane ko kuma menene...

"Ya kinyi shiru?"

"Ammar mun yi magana amma na ce dashi ba zayyu ace babu ƴan rakiya ba shine ina ga ya tura wani"

"Gobe zan yi mashi magana kamin a ɗaura auren"

Sun jima suna fira sannan ya fice zuwa ɗakin shi.

 _WASHEGARI_ 

Gida ya kauraye da hayaniyar hidiman biki sai kaiwa da komowa ake yi su Ayshe kam sai rawar jiki suke ana auren babbar yaya, an kashe Naira iya Naira bikine wanda ba a taɓayi ba Daddy ya buɗe bakin aljihunsa yana zubda Naira karfe 11:00 am aka ɗaura auren Hamrah da kuma Alhaji Sama'ila, akan sadaki 15 million, wuni akayi ana hidima har 4:00 pm aka kawo kayan akwatin Hamrah dozen biyu dukkanin su cike da kayayyaki na gani na faɗa da key mota a cikin kid na dankunnayen gold nan akayi ta murna ana ta sanya albarka. Sai dab magrib motar tazo kwalli ɗaya wai anzo ɗaukan amarya nan hankalin kowa ya tashi akace ba zayyu ba sai anga inda zai ajiye ta, aka kirasa ya ce a hotel zasu kwana da safe zasu hau jirgi su wuce Abuja amma akace ba zayyu ba da ƙyar aka amince masa shima sbd yace da safe masu rakiya su shirya sai azo a ɗauke su. Hamrah kuka kaman ranta zai fita Ammie ce ke rarrashinta tare da banbaki, ganin Ammie ta sanya baki yasa ta ɗan sagaita kuka ta shirya aka fito da ita aka sanyata cikin motar abin da ta bata mamaki shine babu kowa a cikin motar sai driver kawai tana shiga ya tada motar kai tsaye sai a hotel ya direta ta baya yayi mata jagora suka shige ta tadda Alhaji Sama'ila zaune cikin manyan kaya sai ƙamshi yake yana ganin ta ya miƙe ya riko hannun ta zuwa bakin bed ta sudda kai ƙasa tana wasa da zoben gold ɗin dake hannunta ya rike hannunta tare da ɗago dashi ya ƙurawa lallen ido yana jujjuya tare da shafawa. Ta sauke numfashi a lokacin da ya janyo ta cikin jikin shi tare da ɗago da habarta ya kura mata idanuwa, a hankali ta sauke nata idanun sbd ba zata iya jure ganin nashi jajayen nan ba duk a tsorace take. Babban yatsan hannun sa yakai kan bakinta yana shafawa a hankali, ta ɗago ta kallesa zuciyarta na harbawa, idanuwanta sun ciko da kwallah kamar za tayi kuka murmushi ya sakar mata tare da cewa 

"I'm sorry dear"

Bata fahimci mai yake nufi da kalmar ba a hankali tana ƙoƙarin zamewa daga jikinsa ya sake riketa gam tare da zame mata ɗankwalin lace ɗin kanta, bayyanar gashin ganta da yayi yasa ya sauke numfashi tare da bin gashin yana shafawa hannunsa ya soma rawa abin da bai taɓa yi masa ba. Gaskiya wannan lady special ce, ƙoƙari zuge mata zip na rigar ta da yake yi ne yasa ta rike hannun sa tare da yin magana muryarta na rawa ta ce

Ba muyi sallah ba kamar yadda ake yi.

Lumshe idanuwan sa yayi ya buɗe tare da sakar mata da murmushi ya shafi gefen fuskar ta yayi jin laushinsa yasa ya sauke numfashi tare da cewa 

"Yanzu na idar da sallah kuma na sanya ki cikin addu'a so no need sai mun sake yi"

Daram ƙirjinta ya buga me yake nufi, ita dai tasan ana yin raka'a biyu na godewa Ubangiji kafin a kwanta amma meyasa Alhaji Sama'ila yaƙi suyi, ba tayi aune ba taji ya zuge zif na rigar ta tare da sanya hannu ya cire mata rigar da kuma kunce zanin. Jikinta ya tsoma rawa yayi saurin kai bakinsa kan labbanta ya soma tsosa kamar tsohon maye. Tsoro da fargaba yasa jikinta rawa, ga yunwar dake addabar ta wunin ranar ba abinda ta saka abaki anyi² taci abinci ta kasa ci. Sosai yake sarrafa ta ita dai banda rawar da jikinta keyi ba abinda tayi. Ya miƙe ya barta kwance ya cire dukkanin kayan jikinsa ya tsaya yana kallon ta duk ta tashi hankalin ta ganin ƙaton tumbinsa da kuma manyan nonuwansa kamar mai shayarwa yasa ta fara zubda ƙwalla a tunanin ta zai kashe wutar ɗakin ne amma taga ya hayo kan bed ɗin ya kai mata danƙa kamar an old hungry Lion, a hankali bakinta na rawa ta ce

"Dan Allah, kayi min a hankali ban taɓa yi ba wallahi tsoro nake.....

Kan ta karasa ya rufe bakinsa da nata yana masa shan rake a tunaninta horo man ne yana so ya zuƙi jininta. Nan ta fara ƙoƙarin kwatar kanta a hankali ya zame bakinsa ya kalleta da jajayen idanuwan sa ya ce

"Hamrah wai meye haka ne?. kinsan dogon lokaci da na na ɗauka ina jiran wannan ranar, bana son haka ki barni na dirji kuɗina in kuma ki kayi gaddama ke jikinki zai gayawa"

Bakinta na rawa ta ce

Dan Allah...

Amma yaki saurara mata, yana dab da shigar ta kuma hakan yazo daidai da kusan ta shiɗe sai taji ya dakata ya ɗanyi shuru na wani lokaci sannan ya ɗago da fuskar ta yana mata kallon mamaki tare da yin magana cikin rawar murya ya ce


"Are you a virgin?"

Kirjinta ya kara bugawa daman me ya ɗauketa cikin sanyin jiki tare da rawar murya ta kaɗa masa kai alamun eh. Ya sauke numfashi tare da cewa 

"I'm really sorry"

Daga nan bata sake sanin inda take ba sbd sumar da tayi.

Washegari 

10:00am, a hankali taji kamar ana tattaɓata ta buɗe idanuwanta da su kayi mata nawi da ƙyar tana bin inda take da kollo a hankali komai ya dawo mata, ta ɗan juyo taga Alhajin da yake ƙoƙarin tada ta kuma sai taga akasin haka, ta sauke idanuwan ta kan wata ƴar budurwa sanye take da jan riga polo da kuma bakin skit sai face cap. Da alamu ma'aikaciya ce a wannan hotel ɗin a hankali tayi magana sbd yadda zazzaɓi ya rufe ta da kuma ciwon kai da yunwa ta ce

"Kina son abu ne?"

"A'a turoni aka yi na gyara wannan room ɗin sbd akwai wanda ya kama zuwa yamma zai iso"

Cewar wannan ma'aikaciyar. Cike da mamaki Hamrah ta sake waro idanuwanta tana kallonta ta ce

Ina ga ba nan bane, dan da mijina nake, ki bari ya shigo ina ga ya ɗan fita ne in yazo sai kuyi magana.

Gyara tsayuwar ta ma'aikaciyar tayi cike da mamaki ta ce 

"Baiwar Allah miji kuma, ai wanda ya kama ɗakin  tun safe ya sake daman kuɗin dare ɗaya ya bada, yanzu ma manager ne ya turoni na gyara ganin ki kwance kuma yasa nayi mamaki.........

_________________________
Alhamdulillah yanzu aka fara wasan. Daman nace tun daga farkon PG ɗin zuwa PG kafin wannan shimfida ne to yanzu labarin ya soma.

Ayi hakuri da typing errors bana samun time na gyarawa ne.







Comments and share fisabilillah