Book 1 page 43&44
by @barista
MUJARRABI
Book 1
PG 43&44
A hankali ta maida rinannun idanuwanta masu yi mata zafi da zugi ta rufe, jinsu take kamar an zuba mata ruwan borkono a ciki take ji, zazzaɓi mai zafi ya ratsa dukkanin jikinta, yunwa ciwon kai rashin ƙarfin jiki suka haddasa mata jin jiri duk da tana kwance ne kan bed amma tana jin duniyar na juyawa da ita. A hankali tayi yinƙurin tashi ta gagara ta koma ta kwanta ba tare da ta buɗe idanuwanta ba, sbd jin raɗaɗin da kasanta ke mata, buɗe idanuwanta tayi ta sake duban wannan ma'aikaciyar da take sanar da ita cewa mutumin da ya kama ɗakin ya rigada ya sake tun safe, to wa take nufi ne? Cikin rashin fahimta ta yi magana a hankali da ƙyar muryarta ke fitowa ta ce
"Ina ga ba wannan ɗakin bane aka turoki, wannan ɗakin mijina ne ya kama, ki duba maybe next room ne ko kuma room kafin wannan.
Sauke numfashi wannan ma'aikaciyar tayi tana mamakin abin da take cewa, ita dai tasan babu wasu mata da miji da suka shigo wannan hotel ɗin dan cin amarci, an kwan biyu gaskiya. Tayi magana tana mai sake kallon Hamrah ta ce
"Baiwar Allah ba ɓatan kai nayi ba wannan room ɗin ne aka sake wani ya kama har an biya kuɗin ma, manager ne ma da kanshi ya ce nazo na kimtsa shi. To amma ki kace da mijin ki kuka shigo ina mijin ki yake?"
Sai a lokacin kuma ta tuna rabonta da Alhaji Sama'ila tun daren jiya, to ina kuma ya tafi ba tare da ya sanar mata ba ko dai ya tafi sallaman bakinsa ne ya dawo su tafi cen Abujan. Ta dubeta cikin sanyin murya ta ce
"What the time now?.
"To 11:00am"
Cewar ma'aikaciyar, daram ƙirjin Hamrah ya buga har 11:00am yayi basu tafi ba to ina ya shiga ne?. A hankali ta sake cewa
"Please miƙa min wayata"
Ta nuna da hannu kan bed side.
Nan ma'aikaciyar ta nufo wajen ta sa hannu zata ɗauka sai tayi arba da wasiku guda biyu, ta dauki wayar tare da cewa
"Kin ga wasiku biyu a ajiye a kan bedside"
"Wasiku kuma?. Miƙo min su"
Ta miƙawa hamrah su, ƙaramar Hamrah ta buɗe arɓa da abin da ta gani ne a rubuce yasa ta saki kara a wajen ta sume nan take kan bed ɗin.
_3 hours left_
Da ƙyar ta buɗe dishashun idanuwanta a hankali tana bin ɗakin da kallo, idanuwanta suka sauka kan drip ɗin dake maƙale jikin window dake kusa da bed ɗin zuwa hannunta, tana son tuno me yasa aka sanya mata drip ne, mai kuma ya faru da ita?. ...
"Kin tashi sannu kinji"
Muryar da taji ne yasa ta juyo ta ɗayan ɓangaren ta kaleta, ma'aikaciyar hotel ɗin ne zaune kusa da ita tana kallon ta cikin tausayawa ta sake cewa
"Just rest you'll feel better soon"
A hankali ta fara tuna abin da ya faru da ita wasu zafaffun hawaye ne suka zubo mata, ta sauke nauyeyyen ajiyar zuciya tare da rumtse idanuwanta tana addu'ar Allah yasa mafarki take yi, duk wannan abin ba a zahiri ne yake faruwa ba a hankali ta buɗe idanuwanta ganin a zahiri ne yasa tabi jikinta da kallo ganin doguwar rigar ce irin na marasa lafiya a jikinta yasa tayi saurin kallon wannan ma'aikaciyar ta ce
"Bayan na suma meya faru dani?
Sauke numfashi wannan ma'aikaciyar tayi ta ɗan dafe jikin bed ɗin da dukkanin hannunyenta cikin tausayawa tace
"Sunana Hadiza Aliyu, ma'aikaciyar a nan hotel ɗin na jima ina aiki cikin wannan hotel ɗin, nasan duk wani shige da fice na wannan hotel ɗin, nasha cin karo da ire-iren abin da ya same ki sai dai banbancin naki da nasu shine ke da aurenki akayi miki hakan, na tausaya miki fiye da yadda ki ke tunani, mutumin da ki ke magana akan shi shine wanda ya kama wannan room ɗin sbd bayan kin suma ne na fita da gudu zuwa reception na tadda manager nan nayi masa bayani cikin tashin hankali, cikin sauri ya biyo ni muka shigo yaga abin da yake faruwa he feel so bad. Hankalin shi ya tashi nan ya kira wata likita ya mata bayanin abin da yake faruwa kuma da alama kamar an sadu dake, jin haka yasa tace mu fita muka fita. Nan ta duba ki ita da kanta ta shirya ki da ta fito ne take sanar damu cewa kin sami buɗewa ta kasanki tayi miki ɗinki, amma kina bukatar drip, aka turani na siyo na kawo ta sanya miki, sannan ta tafi. Abin da nake so dake yanzu shine kiyi hakuri ki kira gidanku ki sanar dasu ga abin da yake faruwa dake sai suzo su tafi dake gida amma maganar gaskiya ya sake ɗakin dan mun duba sunan wanda ya kama ɗakin kuma mun samu shine wanda ya sake kuma yayi tafiyar sa shi da wasu mutane ne ma suka fice"
Tunda ta fara magana Hamrah ke kallonta bata ko kifta su ba, jin ta take kamar ma bata cikin duniyar baki ɗaya anya itace kuwa, to me yake shirin faruwa da ita ne me wannan Alhajin ke nufi da yin hakan ne, meyasa ya kashe mata kuɗaɗe in dai sbd ya kwanta da ita na dare ɗaya meyasa yayi mata haka menene tayi masa shin daman ba aurenta yake son yi bane tun asali?. Rashin samun amshoshin wanɗanan tambayoyin da tayiwa kanta ne yasa tasa hannu ta cire drip a hankali ta tashi da ƙyar ta zauna cikin tashin hankali take bin ɗakin da kallo idanuwanta suka sauka kan wayarta ta ɗauka missed calls ya kai 50 ta gani cikin sanyin ciki ta kunna wayar tana kallon waɗanda suka kirata, Ammie 20 missed calls, Daddyn 10 missed, Ammar 15 missed calls, Ayshe 3 missed calls Zeenat 2 miss calls ta sauke nauyeyyen ajiyar zuciya tayi tare da kumshe idanuwanata da suka ciko da kwallah rumtse su da tayi ne yasa suka karasa zubewa, zuciyar ta nayi mata zugi da kuma ƙona, ta yaya zata koma cikin gida ta sanar dasu abin da ke faruwa, mema zata ce dasu tace Alhaji Sama'ila da aka ɗaura aurenta dashi jiya j ya gudu ya barta, ta ina ma wannan maganar zata shige su. Sannan tayi yaya da mutanen dake gidan innalillahi wa inna ilaihi rajiun shine kaɗai abin da take ita faɗi cikin ranta....
"Kiyi hakuri ƴar'uwa ki kuma kwantar da hankalinki ki sami nutsuwa ki bar zubar da kwallah"
Cewar Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ɗin, a lokacin da ta dafata
Uhm.
Shine kaɗai a bin da Hamrah ta iya cewa dan wannan tashin hankalin bata san da meyayi kama ba ita ko a tarihi bata taɓa jin abin da ya faru da ita ya faru da wata ba, sannan duk cikin labaran da ta jisu daga bakin waɗanda suka faɗa cikin jarrabawa ma bata ji makamancin irin nata ba, komawa tayi ta kwanta tana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Ta jima a kwance ta rasa mafita a hankali ta sake duban wayarta ta shiga contacts ta rasa wa zata fara kira, wani tunani ya faɗo mata ta kira Shatu mana suyi magana ko zata sami mafita, wata zuciyar kuma ta ta bari ba yanzu ba. Cen kuma ta ce ko ta kira Ayshe ne ta sanar da ita halin da take ciki, cen kuma ta ce ko Ammie ko kuma Daddyn su, tana ta wannan tunanin ne Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ta sake cewa
"Ki tashi ki gabatar da sallah azahar lokacin ma ya wuce la'asar ma ta kawo kai"
Sauke numfashi tayi tare da juyowa ta kalleta ita sabar tashin hankali ma ta ma manta da ita a zaune. Ba tare da tayi magana ba ta mike ta shige toilet da ƙyar take iya takawa ta tadda akwai na'urar dafa ruwan zafi ta kunna ta dumama ruwa ta shiga ciki ta jima a cikin sai da taji ta ɗan dama² sannan ta ɗaura alwala ta fito ta sanya kayanta na lace da ke jikinta jiya ta yafa mayafin ta gabatar da sallah. Ma'aikaciyar ta fice dan haka tana sallame wa ta dawo kan bed ɗin ta zauna ganin message ya shigo ne ta duba kuɗi ne daga Alhaji Sama'ila Naira miliyan 10, sai da ta sake dubawa da kyau ta kula ashe tun safe ya tura mata. Tayi saurin kiran layinshi kuma a kashe, ta sauke numfashi ta kira number Ayshe kira na farko ta ɗauka tare da cewa
"Amarya ran gida tun jiya nake ta kewar ki aure ya rabamu, amma meyasa ake ta kiran number ki baki ɗaukawa duk hankalin mu ya tashi musamman ma Daddy tun jiya ya kasa cin abinci, haka ma yaya Ammar"
Sauke numfashi hamrah tayi ta haɗiye abu mai zafi cikin ranta tare da haɗiye kukanta ta ce
Ayshe bacci ne ya kwashe mu, bayan na farka kuma na koma sai yanzu na tashi, ina Ammie?"
Dariya Ayshe tayi ta ce
"Madallah yaya Hamrah kin shiga system ɗin, ai daga yanzu ko zaki fara rama bacci. Ammie tana nan, tun safe duk ta damu ƴan rakiyar ki sun shirya amma kuma shuru ba a ji komai daga gareku ba"
Daram ƙirjinta ya buga, wai tashin hankali yanzu ya za tayi kuma ta san dole sai ƴan rakiyar nan sun rakata hasbunallahu wa ni'imal waƙil, Allah yakawu mata mafita shine abin da take faɗi cikin ranta, a hankali ta ce
Ki hau online muyi video call.
"To yaya Hamrah yanzu ma ko"
Dukkanin su suka hau online Hamrah sosai ta ɓoye damuwarta ta kirkiro murmushi amma ana iya hango damuwa ƙarara kan fuskar da dakuma idanuwanta, cewa Ayshe tayi ta dinga yawo da wayar tana son ganin mutan gida, Ayshe ko ta dinga yawo dashi gida ko cike yake maƙil da mutane, sai kaiwa da komowa suke, wasu a zaune wasu kuma a kwance ana ta fira ana raha ta iso inda Ammie take tana tsaye tana haɗa kayan Hamrah wanda za a tafi dasu ta mota katse video call ɗin tayi ta fashe da kuka, sosai taci kuka jin ringing da wayarta keyi ne yasa ta share hawayenta ta ɗauka ganin sunan Zeenat ta kara a kunne tare da sallama Zeenat ta amsa ta ce
"Yaya Hamrah barka da rana, yanzu Ayshe ke sanar dani kunyi waya na ce bari na kiraki mu gaisa"
Da ƙyar Hamrah ta ita iya yin magana
Eh hakane inna shirin kiranki ma kika kira ya gajiyanku?.
"Sai godiya, amma ya kamar kina kuka?"
Uhm a'a Zeenat ba kuka nake yi ba.
"Kai yaya Hamrah gashi naji har muryarki ta dishe, kada ki damu kaɗaici ne ke damunki kuma zai wuce kewace muma duk munyi irinta kina kaiwa sati ɗaya za ki saba da rashinmu"
Haka ne Zeenat thank you.
"Yauwa ga Ammie nan ku gaisa tana ma son magana dake"
Ta sauke numfashi ta ce
To ki bata.
Ta mikawa Ammie cikin masifa Ammie ta ce
"Haba Hamrah abin da ki kayi bai dace ba yaya za ku shanya mutane tun safe suna jiran ku a ɗau hanya amma sai ku sharesu haka ake yi ne, wallahi banji daɗin hakan ba, yanzu ya za ayi ne goben ne tafiya tun da yau an ɗaga ko kuma kun tafi ne?"
Wani kuka ne ya zuwa Hamrah kamar ta ɗaura hannu a kai ta saka ihu amma ta jure ta danne ta ce
"Ammie ya gajiya eh tafiyan sai gobe in Allah ya kaimu da man sunyi magana da wasu ne akan ɗiban kayayyakin to ban san ya abin zai kasance ba, bari muga goben.
"To ki kira ki sanar dani da wuri dan ko da ƙyar na tsaida babanninki wai zasu tafi, to in kinga tafiya ba ta gobe bace sai su tafi kada mu ɓata musu lokaci ba"
To Ammie.
Shine abin da Hamrah ta iya furtawa. Ammie ta kashe wayar nan Hamrah ta rushe da kuka kamar ranta zai fita ta soma furta kalmar
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Ya Allah ka kawo min ɗauki Allah na tuba ka yafe mini, Allah ina cikin tashin hankali na rasa mafita Ubangiji kai dayane zaka taimakeni Allah ka dubi lamurana ka rufa min asiri ka taimaka min taimako ka kaɗai nake nema.
Sosai take kuka, har lokacin da Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ɗin ta shigo ta taddata tare da Manager suka shigo, nan ta dinga rarrashinta tare da ban baki da ƙyar Hamrah tayi shiru sannan manager yayi magana
"Ba abin da zan iya cewa akan wannan abin da ya faru ya riga da ya faru sai dai na baki hakuri, ki ɗauki hakan a matsayin kaddararki Allah shine MUJARRABI yana jarabtan bawansa ta ko wacce siga musamman irin sigar da bawan ke yaƙi da ita yaga ko in abin ya samesa zai jure ne kamar yadda yake son wasu su jure to ban sani ba ko kina ɗaya daga cikin su. Yanzu dai duba da halin da ki ke ciki yasa na dauke miki kwana ɗaya zuwa biyu a nan dakin sbd wanda yake da niyyar kamawan ma na sauya masa da wani dan haka zaki iya zama nan da zuwa jibi in kin sami lafiya da kuma nutsuwa sai ki koma gida ki sanar dasu halin da ki ke ciki"
Hamrah dai kanta a ƙasa ta rasa bakin magana sai zubda ƙwalla take tabbas maganar wannan manager abin dubawa ne tayu sbd da tana wayar da kan wasu akan kada su kaucewa tsarin musulunci su jure wa duk wani halin da suka sinci kansu a ciki shine Ubangiji ya jarrabe ta yaga ko ya ita za tayi a hankali ta furta
Astagfirullah.
Manager da Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ɗin suka fita basu jima da fita ba ta shigowa Hamra da abin da zata sanya a cikin ta, ta ajiye wa Hamrah ganin ko kallon abinci batayi ba yasa ta haɗa mata tea mai kauri ta bata tasha, kaɗan ta sha ta ajiye ta kwanta. Har dare tana kwance ta rasa mafita tayi tunanin duniyar nan ta rasa mafita ta rasa wanda zata kira suyi shawara ya taimaka mata cen sai wata zuciyar ta ce AMMAR nan ko sai hankalinta ya kwanta da ta tuna dashi a hankali ta ɗauki wayar kira ɗaya ya ɗauka tare da cewa
"Ni har nayi fushi dan kinyi aure shine har kika manta dani na kira baki ɗauka ba na ce to su amarsu"
Uhm Ammar, ai ban isa na manta da kai ba, bana jin daɗin jikina ne yasa na kasa amsar wayar.
"Subhanallahi, meke damunki, ya naji muryar ki haka ince dai lafiya?"
A hankali ta ce
Zan tura maka address na hotel ɗin da nake Please be hurry ina jiranka.
"Hamrah is something wrong, are you alright?"
Uhm just come now Ammar.
Ta kashe wayar. Ta tura masa address na hotel ɗin da take ta kuma faɗa masa room number da kuma sunan wacce zai je wajenta Hadiza Aliyu tayi masa jagora zuwa inda take. Ta miƙe ta daura alwala ta idar da sallah ishai tana kan dardumar sallah taji turowar kofar ta shafa addu'ar da take yi ta juyo ta kalli bakin kofar Ammar ta gani a tsaye yana karewa ɗakin kallo idanuwansa suka sauka kan roban drip ɗin dake bedside da kuma tulin magungunan dake wajen, ya sake juyowa ya kalleta cikin sanyin jiki ya ƙaraso inda take kallo ɗaya yayi mata ya fahimci akwai matsala ya rage tsawonsa ya zuba mata idanuwan shi yana sake karantar yanayi ta, a hankali yayi magana
"Kada ki ɓoyemin komai Hamrah idanuwanki sun nuna min akwai abin da ya faru, kuma yanayin ki ma ya nuna? Ina Alhaji Sama'ila?"
A hankali hawaye ya zubo mata ganin Ammar yasa ta danji sanyi a hankali ta ce
Nima ban san inda yake ba.
A take numfashi sa ya soma hawa yana kallon ta irin kallon nan na me ki ke nufi, bakin ta na rawa ta ce
Tun da na farka da safe ban sake ganin shi ba har yanzu.
"Ah bangane ba ina ya tafi baki kira number shi ba ne?"
Na kira baya shiga, amma manager hotel ɗin ya ce wai tun safe ya sake ɗakin ya basu key ya fice.
A take idanuwan Ammar suka kaɗa su kayi jajir numfashin sa ma na sizin, ya ce
"Ya sake ɗakin ya tafi gidan ubanwa ya tafi ya barki me yake nufi da mu ne?. Yaudarar mu zayyi ko kuma yaya?"
Ita dai sai hawaye ta rasa abin cewa ta nuna mashi wasikun da ya bari da hannu, ya miƙe ya iso wajen ya buɗe karamar nan take jikinsa ya soma rawa shatin jijiyoyin jikinsa suka bayyaa tun daga kansa zuwa hannayen sa ya dunkula hannu ya daki jikin garu take hannunsa ya fidda jini yana fuzgar da iska ya ce
"What?. Mu za a yaudara, to in ya saba yiwa wasu mu ba zayyi mana mu kyaleshi ba, yana nufin taron da mu kayi ya tashi a banza ya maida mu shashashu kenan taron iska mu kayi, to bai isa ba yayi kaɗan kuma sai ya gane kurensa yayi kuskure da yayi AUREN HARAMCI dake.........
_________________________
Alhamdulillah ala kulli halin. Masu min addu'oi ina godiya matukar. Akwai masu cewa labarin ya sauya ban sauya labarin ba asali ma PG kafin wannan shine PG 1 wannan kuma PG 2 to duba da yadda nake son sakon ya isa kafin abin da ya sami ita Hamrah ta cikin labarin shine na kawo labaran wadanda suke dauke da jarrabawa daban daban SBD in tata jarrabawar tazo a fahimci abin.
Ayi hakuri da typing errors
Comments and share fisabilillah