FARASHIN IZZAH

Chapter 6

by @hauwajaywrites

Ta daɗe tana zaune a wajen. Tabbas maganganun Firdausi gaskiya ne, amma anya za ta iya? Share hawayenta tayi ta miƙe tsaye, kamar mahaukaciya haka ta ɗaura hannu a kanta ta saki ihu, sai kuma ta durƙusa kan gwiwowinta tana kuka.

“Khalil me na maka da zafi har haka da za ka saka min ta wannan hanya? Ko dama haka soyayya take? Dama haka zaman aure yake, ko nata ne daban?”

Aure ko wata ɗaya bai gama cikawa ba. Ta sake fashewa da kuka tana nanata Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Ji take kamar ta cakkawa kirjinta wuƙa kawai ta huta. Ambaton Allah da take yi ne ya fara daidaita mata nutsuwarta.

A hankali ta sauka ƙasa ta wuce kitchen. Buɗe fridge tayi ko za ta ga abin da za ta girka, amma sai taji ba za ta iya girki ba a halin yanzu. Kawai ta fita ta wuce ɗakinta. Ta shiga toilet tayi wanka, ta fito ta shirya cikin blue lace. Ba ƙaramin kyau tayi ba. Ta ɗauki handbag ɗinta da keyn mota ta sauka ƙasa.

Kitchen ta wuce ta ɗauki wani warmer mai kyau. Bayan ta kulle ko’ina, ta nufi motarta. Ta saka kulolin a back seat, ta koma front seat ta shiga sannan ta tada motar ta fita bayan mai gadi ya buɗe mata gate ɗin.

Ba ita ta tsaya ba sai a wani eatery. Ta sauka ta shiga ciki tare da kulolin a hannunta. Bayan ta sayi abincin ta fito ta ci gaba da tafiya. Gaba ɗaya tukin da take yi kamar kwakwalwarta ce kawai tayi recording ɗin inda za ta tafi. Amma idan ba haka ba, ita kanta bata san a wacce duniyar take ba. Ta faɗa duniyar tunani har idanunta suka canza.

Bayan tafiyar kusan minti ashirin ta isa wani babban gida. Duk da cewa gidan bai kai gidan mahaifinta ba, amma shima ya gaji da haɗuwa. Horn tayi, mai gadi ya leƙo ganin ita ce ya koma da sauri ya buɗe gate ɗin. Shiga da motar tayi tayi parking sannan ta sauka ta ɗauki basket ɗin kulolin ta shiga da shi.

A babban parlorn gidan tayi sallama sannan ta shiga. Wata matashiyar dattijuwa ce zaune a parlorn ana mata pedicure. Ta ƙarasa har cikin parlorn. Matar ta ɗan ɗaga kai ta kalli wacce ke shigowa sannan ta ɗauke kai ta mayar kan TV.

Bayan ta ƙarasa wajensu ta ɗan durƙusa kaɗan a jikin sofa tace, “Mama, barka da warhaka.”

Matar ta juyo, sai sannan ta sake fuskantarta tace, “Yauwa.”

Ta ce, “Ina wuni Mama, fatan na same ku lafiya?”

Tace, “Lafiya ƙalau. Ashe kina tafe?”

Ta ce, “Eh Mama, dama ina so nazo amma saboda school yasa komai sai a hankali.”

Tace, “Ai nasan struggles ɗin final year, balle ma yanzu da kike da aure, not like before da kike off camp da zama. Sai dai kawai Allah yasa a gama lafiya, shine addu’ar.”

Tace, “Ameen, nagode Mama.”

Matar dake ma Mama pedicure ce ta ɗago kai tace, “Sannu da zuwa Hajiya.”

Zahra na murmushi tace, “Nagode, ina wuni?”

Tace, “Lafiya ƙalau.”

Daga haka suka yi shiru. Mama sai kallon Zahra take yi wanda yasa ta zama uncomfortable. Ta saci kallon Mama suka haɗa ido sai tace, “Mama ga abincin da na kawo miki, nakai dining ne?”

Tace, “Har da wahala haka ke da baki da lokaci yanzu? Toh nagode Zahra, Allah yayi albarka. Ɗauki ki kai min dining ɗin.”

Ta miƙe a hankali ta ɗauka ta wuce dining ta ajiye. Bayan ta dawo parlorn taga gaba ɗaya hankalin Mama na kan waya.

A hankali tace, “Mama bari na tafi, dama ina da school ne shine nace bari na biya ta nan.”

Tace, “Ayyah, toh nagode.”

Daga haka ta mata sallama ta fita. Sosai taji wani relief. Bayan ta hau kan titi tana tuki, tunanin direction ɗin da za ta yi ta fara. Kawai tayi deciding ta koma gida. Taji ko ta koma school ba lallai bane ta iya gane komai.

Bayan ta isa gida tayi parking ta sauka ta wuce ciki. A main parlorn na nan ƙasa kawai ta zauna. Ta ɗauki wayarta tayi dialing numbern sa. Ji tayi kawai ta kira duk da tasan ba wai sun tashi bane, amma zai iya zama sun tashi sallah. Sai kuma ta ajiye wayar nata.

A haka bacci mai nauyi ya ɗauke ta. Can a cikin baccinta taji ana knocking na ƙofar parlorn. Da sauri ta miƙe ta kalli ƙarfe biyu da rabi. Wani murmushi tayi ganin yau yazo gida. Da sauri tayi bakin ƙofar ta buɗe.

Tana buɗewa taga Ya Umar ne. Kasa magana ma tayi. Ya sakar mata murmushi ya kai hannunsa fusakarta kamar zai taɓa mata ido yace, “Ya haka? Ko baki son gani na ne?”

Murmushi tayi ta rungume shi, yayi saurin janye ta.

Tace, “Nayi mana Yaya, kawai murna ne yasa kaga na kasa magana.”

Ta ja hannunsa suka shiga parlorn. Ya zauna a kan kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, ita kuma ta wuce kitchen ta ɗauko masa ruwa da snacks ta ajiye a gabansa.

Ta ce, “Ya Umar me za ka ci?”

Yace, “A’a, a ƙoshe nake fa.”

Tace, “Ya gida? Ya jikin Abbah na? Ya kuma Mami da Mummy na?”

Yayi dariya yace, “Shine sai duk kin jero min wannan tambayar lokaci guda Baby?”

Murmushi kawai tayi. Shi dai kallonta kawai yake yi. Wannan shagwaɓan babu.

Ya ce, “Duk lafiyarsu ƙalau.”

Tayi shiru tana kallon wani waje, shi kuma studying ɗinta yake yi. Can ya ce, “Baby...”

Ta juya ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace, “Ina Antyn na?”

Yace, “She’s fine. Baby meke damunki?”

Ta ware ido tace, “Wai wani abu ke damuna?”

Ya ce, “Ban sani ba, ina tambayarki kina tambayata.”

Sai data ɗan tsorata ganin yadda lokaci guda ya canza tone ɗinsa, dan ba kasafai ransa ke ɓaci ba. Ta sauke idonta ƙasa tace, “Babu komai fa Yaya, kawai stress ɗin school ne.”

Yace, “School ɗin da kika fara fita jiya shine ya saka miki duk wani irin canjin da kika zama tun farkon auren nan ko?”

Tayi shiru tana kallon wani waje. Ya ɗan sassauta muryarsa yace, “Don’t hide it from me Baby, ki faɗa min gaskiya akwai wani abu dake damunki ne?”

Ta girgiza masa kai.

Yace, “Toh damuwar ta mecece?”

Tace, “Yaya bana cikin damuwa fa.”

Wani kallo ya watsa mata yace, “Shikenan Allah yasa. Ba zan saka miki magana a bakinki ba, amma kiyi tunani sosai, kar ki yarda wani abu ya kashe mana ke. Duk abin dake damunki ki tausaya mana ki faɗa min, ko da kuwa a gida ba zasu ji ba.”

Ta gyada kai sai kuma tace, “Amma Ya Umar meyasa kace ina damuwa?”

Dariya yayi yace, “Zahra tun kina ƙarama nake tare da ke. Babu wani halinki da ban sani ba, babu wani walwalarki da kuma akasin hakan da ban sani ba. Yadda kika zo gida ranan da yadda mijinki ma yazo, and the way you both ignored each other, ya tabbatar min akwai wani abu. Amma zan baki space, nima bana fatan ya zama akwai matsala. Sai dai yanzu babban abin da ya tsaya min a rai shine yadda kika rame, kika yi wani iri har abin tausayi.”

Ta kasa cewa komai. Ya miƙe tsaye yace, “Kina buƙatar wani abu ne?”

Ta girgiza masa kai tace, “A’a.”

Yace, “Sure?”

Sai kuma tayi dariya tace, “Sai dai idan za ka ƙara min wani abu a account ɗina, ba zan ƙi ba.”

Yayi dariya yace, “Alright toh, idan na nutsu zuwa anjima zaki ji ni.”

Tace, “Nagode Yaya.”

Ya juya zai fita, tayi saurin cewa, “Yaya baka sa komai a bakinka ba fa?”

Yace, “I’m full.”

Tace, “Tohm Yaya, ya maganar Firdausi ne?”

Sai sannan ya juyo yana kallonta yace, “Ban gane ba?”

Ta ce, “Yaya wallahi she’s so nice, kuma tana da kyau. Baka ga yadda Abbah da su Mummy ke yaba mata ba? Please ka so ta, Allah suna wahala.”

Yace, “Zahra! So fa ba’a masa dole. Za dai muyi magana anjima.”

Buɗe ƙofar aka yi, duk suka juya suna kallonsa. Haka ya shigo parlorn kamar wani boss. Wani kallo shi da Ya Umar suka ma juna sannan ya ɗauke kai ya nufi hanyar stairs, shi kuma Ya Umar ya wuce ya fita.

Zahra tayi tagumi. A hankali tace, “Wannan wani kalan mutum ne? At least ko magana ba zai yi wa Ya Umar ba?”

Ta miƙe itama zata wuce sama ɗakinta. Bata ji zata yarda su haɗu da shi ba. A corridor suka haɗu. Wani kallo ya mata yace, “Ke ya kike kawo min gardawa cikin gida?”

Tace, “Kila baka gani, Ya Umar ɗin ne gardi?”

Yace, “Idan ba gardi bane mace ne shi ɗin?”

Tace, “Amma kar ka manta cewa Ya Umar shine mutum na farko daya fara accepting ɗinka. Sannan shine ya fara supporting ɗina akan aurenka. Idan za ka canza min halinka bai kamata ka nuna masa ba. Hakan zai saka masa shakku kamar muna samun matsala ne.”

Wani dariya yayi yace, “This should be the first and last time da zan sake ganin wannan mutumin a gidan nan.”

Sosai ya bata mamaki. Ta ja baya da sauri tace, “What? Yayan nawa?”

“Toh ai kuwa idan har kanwarsa tana cikin gidan nan da aure dole yazo.”

Yace, “Shikenan, ya ci gaba da zuwa zaku sha mamaki.”

Daga haka ya wuce ta ya sauka ƙasa.

“Ya Allah...” ta furta da ƙarfi.

Ta wuce ɗakinta. Da ba dan baccin da yake ɗaukanta kwanakin nan ba ba tare da shiri ba, ji take da jininta zai hau saboda tunani da damuwa.

Can yamma ta fita compound tana kallon flowers dake wajen, amma a baɗini tunaninta baya tare da ita. Wayarta ce ta fara ringing. Ganin Firdausi yasa ta ɗaga ta kai kunne.

Firdausi tace, “Gani a cikin gidan ki, ki zo ki buɗe min.”

“Toh,” ta amsa mata sannan ta kashe wayar ta koma wajen main entrance.

Tana ƙarasa wajen taga Firdausi. Rungume ta tayi tace, “Har an tashi a school?”

Ta ce, “Eh fa.”

Shiga parlorn suka yi. Firdausi tace, “Ban so ba da baki zo school yau ba.”

Tace, “Sorry, bana jin zan iya ne”

Tace, “Kin je gidan nasu ne?”

Tace, “Eh, kuma Maman taji daɗi.”

Tace, “Good. Ita zaki fara siya kafin ki gane kansa.”

Wani dogon ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalli Firdausi tace, “Firdausi ya zama ke kaɗai nake faɗawa magana dan na samu salama. Dan Allah ki riƙe min wannan amanar. Ko da wasa kar ki faɗa ma wani, duk da nasan halinki.”

Tace, “Haba Zahra, ai faɗan sirrinki tamkar nawa ne.”

Tace, “Nagode.”

Sai tayi shiru tana kallonta, can ta ci gaba.

“Firdausi, inaga Ibrahim yana neman mata.”

Haka taji maganar ya dake ta.

Tace, “Ban gane ba? Wannan wani irin magana ne Zahra? A’a no, kar ki fara kawo irin wannan zargin a zamantakewar aurenku saboda hakan zai zama mabuɗin mutuwar aurenku.”

Dariya kawai Zahra tayi tace, “Kin san da safe yau an kira shi, na ɗauka kuma mace naji tana magana.”

Nan ta faɗawa Firdausi yadda abin ya faru. Ba kaɗan ba Firdausi ta jijjiga da jin maganar.

Tace, “Kuma kin masa magana akai?”

Tace, “Me zan ce masa bayan na faɗa miki reaction ɗinsa? Nace miki ko ɗan ɗarr yaji saboda na ɗauka amma ko a kulansa, har da cewa hakan shine maganin masu ɗaukan wayar miji. Can you imagine?”

Firdausi tace, “Zahra akwai aiki a gabanki sosai. Dole sai kin tashi kin tsaya. Bacci ba naki bane yanzu. Ki dukufa sallahr dare da miƙawa Ubangiji kukanki, dan shine kaɗai zai share miki hawaye. Ni ma zan taya ki da addu’a.”

Zahra tace, “In Shaa Allah. Baki san yadda nake ji ba. Firdausi kin fi kowa sanin ina da kishi, amma ace na faɗa irin wannan halin ina tsoron kar na aikata laifin da zanyi dana sani.”

Firdausi tace, “Calm down please, kar ki aikata komai. Amma kuma naga Zahra tunda har abin yazo haka, anya ba zaki sake gyara ba? Kiyi haƙuri da abin da zan faɗa, ko dai ba yadda yake buƙata yake samu daga gare ki ba?”

Zahra tace, “Ina zan sani Firdausi? Toh idan gyara ne please ki haɗa ni da wanda zasu min gyara. Kinga dazu ai yazo har haɗu da Ya Umar, amma ko minti arba’in bai yi ba ya sake fita. Ni da ganin sa kuma sai asuba.”

Tace, “Ya tabbata Zahra gyara zamu sake miki.”

Tace, “Ki taimaka min please.”

Buɗe ƙofar aka yi wanda yasa dukansu suka juya zuwa ga ƙofar...


A dinga voting Please, kuma a saka a Library tare da following ɗina saboda duk sanda na sake update ku samu, thank you.