LULLUƁIN BIRI

30

by @halimahz

Ilham ta shigo parlon Yarima Abbas bakinta ɗauke da sallama da wani irin emotions a tare da ita. Tun shigowarta kanta ke sunkuye a ƙasa kamar ta shiga fadar Mai Martaba. 
Ta ƙarasa gaban table ɗin da ke tsakiyar su Yarima Abbas, ta ajiye ƙaramin tray da ke hannunta, bayan ta ajiye ta ɗago ido ta kalli ɓangaren da ta san anan ne zata yi tozali da Turaki, tun da from there hancinta ke jiyo mata ƙamshinsa, wannan ƙamshin turaren da ita ta basa kyautarsa har ya zama choice ɗinsa.

Idonsa da nata suka haɗu wuri ɗaya, kuma ba tare da ƙwayar idonsu ta fita ata junansu ba suka saki wani sanyayyan murmushi wa juna. Wanda hakan ya wanzar da jin kunya a tare da ita, Turaki kuma da har sannan murmushin bai ɗauke masa ba ya ce,"Zo ta nan".

Yarima Abbas cike da jin girma na izza ya ce,"Ka fi kowa sanin bana son yara suke zuwar min sashina ko, amma duk sanda ka zo sai ka dinƙa wani kiransu suna shigo min da dattin ƙafafu".

Ba tare da Turaki ya dube shi ba ya ce,"Da wa kake?". 

Rai ɓace Yarima Abbas ya ce,"Yaushe wannan rainin hankalin zai bar jininka Turaki?".

Turaki ya ɗauke idonsa akansa yayi masa banza bai tanka masa ba.

Ilham ta zauna akan hannun kujerar da Turaki yake zaune, ya kamo hannunta ya riƙe yana cewa,"Wai ni wannan Kunyar ta wa da kike yi tun da kika dawo ta mene?". 

Kanta na ƙasa ta ce,"kunya kuma Hammah?". 

Ya ce,"Ehh mana, kuma ni ban haihu ba, balle na ce ɗana kike wa ƴarki kamu".

Take fuskanta yayi turning zuwa na shagwaɓaɓɓu tana ɗan dukan ƙafa a ƙasa ta ce,"To ai sai mu haɗa zumunci ko."

Murmushi kawai ya yi yana shafa beard ɗinsa. Idonsa na kan tray ɗin da ta aje, ya ce,"What is this?"
Ta ce,"Your favorite. Tun safe na dafa shi idan zan tafi na kawo maka."

Sai ya katse ta da cewa,"Have you forgotten?"

Sai ta ɗan ɓata fuska ta ce,"Ban manta ba, but ai na ga ada ne."

Ya gyara zamansa yana faɗin,"Ba iya da bane har yanzu Ilham. Girkin Maama da Zaytun kawai."

Wani irin rashin jin daɗi ya ziyarci Ilham, fuskarta ta nuna hakan, Turaki ya kalleta ya ce,"Fushi?".

Ta girgiza kanta da sauri,"A'a". 

Ya ce,"To saki fuskan". 

Ba tare da ta yi hakan ba ta ce,"To har girkin matarka ma ba zaka ke ci ba Hammah?". 

Ya ce,"Dalilin da ya sa zanyi aure na zauna a kusa da Maama kenan". 

Ta ce,"Amma Hammah akwai...". 

Ya tari numfashinta da faɗin,"Akwai mutuwa ko? Na san da hakan. Na kasa sabawa da girkin kowa ne har yanzu. Ki taya ni addu'ar na riga Maama mutuwa ba na ga tata ba".

Ilham ta ce,"To Allah ya ƙara mata lafiya ya kuma bata tsawancin kwana me albarka". 

Ya amsa da,"Amin Lelen Boɗejo". Ya sauke numfashi sannan ya sake cewa,"Ina gyalenki?".

Ta ce,"Na barosa kan bed ɗin Mami saboda ka ce na hanzarta". 

Hannunsa akan fuskarta ya ce,"Je ki ɗauko ki dawo, ki faɗawa Mami zaki min rakiya".

Fuskarta ta washe da murmushi tana tambayarsa,"Ina zamu je?". Ya shafo wuyansa sannan ya bata amsa,"Perfume zamu sayo".

Idonta ya ƙanƙance tana kallonsa. "Ƙarewa ya yi? In ɗauko maka nawa?".

Ya ce,"A'a wani zan sauya". 

Idonta na ƙara ƙanƙancewa da matuƙar mamakinsa, ta ce,"Canjawa kuma? Perfume na ka ɗin Hammah? Your best choice fa?".

Ya ɗaga gira ɗaya,"Yes, bana son ƙamshinsa yanzu". Tayi knodding kanta sannan ta miƙe ta fita, tana mai cike da mamakin canjin ra'ayinsa, da wani ne ya ce mata Turaki ba ya son ƙamshin turarensa yanzu, da ta ƙaryata.

Yarima Abbas ya rakata da harara, Turaki ya tsayar da ƙwayar idonsa akanta har ta fice, bai san dalilin da yasa yake tausayin yarinyar ba, ko dan ta kasance ita ɗaya a wurin mahaifiyarta ne? 
Ba hakan ba ne, hakan kuma ba zai zama dalili ba. Yana son Ilham kamar yadda ya ke son Nihal, Samha da kuma Zaytun. Yana ƙara sonta da burin faranta mata saboda yadda itama ta ke sonsa tun yarintarta, take masa kallon jininta fiye da yadda take kallon su Yarima Abbas. 

Ya sauke gauron numfashi yana jinginar da kansa jikin kujera tare da rufe idanuwansa, ba ya manta alkhairi a rayuwarsa ko da ace daga baya zaka saka masa da sharri, wannan alkhairin naka garesa zai mantar da shi girman sharrin da kayi masa. Sai dai har yanzu ya kasa mantawa da sharrin da Mami ta yi masa, tsawon shekaru da yawa har yau neman dalili yake na ƙala masa sharrin sata da Fulani Azima tayi. 

Idan ya tuna cewa bayan da mahaifiyarsu ta tafi ta barsu, a cire Hajiya Madina a gefe, babu wata mace da ta nuna musu ƙauna tsurarta gami da tausayi tare da kyautatawa irin Fulani Azima. Ta so shi shi da Zaytun kamar zata haɗiye su, ta yi sa'insa da Mai Martaba duk a kansu. 
Ya faɗa rijiya Fulani ta kusa binsa cikin rijiyar a ɗauko su tare, a matsayinta na matar Mai Martaba ta zubar da gwiwoyinta gaban mahaifinsa tana roƙonsa akan ya bata Turaki zata kula da shi fiye da yadda zata kula da ɗan cikinta har zuwa ranar da Ramla zata dawo. 

To amma sai dai me? A lokacin da ya shaƙu da ita, ya saba da ita, ya shaƙu da ƴarta, yake ganin ta zamar masa uwa, sai Fulani ta rikiɗe ta koma kalar wata mace ta daban, mace me cike da tuggu da makirci, ta shiga muzguna masa tana goranta masa akan zaman da yake yi acikin masarautar, alhalin ita ta rabosa da Hajiya Madina, ba wani ya ɗaukosa ya kawosa ba.
Ta ƙala masa sharrin satar gwal a lokacin da bai ji ba, bai gani ba, ta ƙara da faɗin ya satar mata kuɗaɗe, kuma ba tare da wani tunani ko bincike ba Mai Martaba ya yanke masa hukunci daidai da abin da ya aikata.

Hukuncin da Hajiya Madina ta yi tsalle ta dire agaban Mai Martaba ta ce muddin aka ga an saka ɗanta a prison to wallahi sai dai idan bata numfashi. Ta kuma fuskanci Baffa gaba da gaba ta ce ya sani, idan har matsayinsa na alƙali bai yi hukuncin gaskiya ba, to lallai shari'a ita da zuriyarsa sai inda ƙarfinta ya ƙare. Kuma zata kwashi su Turaki ta tafi da su ta barshi, ko da zai dinƙa yankar naman jikinta yana goranta mata ba ita ta haife su ba.

Asalin samo gaba mai ƙarfin gaske kenan da ta shiga tsakanin Hajiya Madina da Fulani, har tsawon shekaru ma su yawa, har sai lokacin da Turaki ya kammala degree ɗinsa na biyu sannan gabar ta su ta ƙare, bayan Hajiya Madina ta tambayi Turaki ya faɗi kyautar da yake so tayi masa ya ce mata yana so ta daina gaba da Fulani, domin gaba abar ƙyama ce Allah baya so, kuma ma'aikin Allah ya ce kar mutum ya rama sharri da sharri dan haka ta bar batun ɗaukar fansa da ta ce zata yi akan abin da Fulani ta yi masa, ta yafe mata kamar yadda shima ya yafe mata. 

A duk sanda ya nemi abu a wurin Hajiya Madina take a wurin take yi masa ba tare da ɓata lokaci ba muddin bai fi ƙarfinta ba, amma a wannan roƙon da yayi mata sai da ta ɗauki tsawon kwana biyu shi kansa ba ta shiga sabgarsa ba, wai sunan shawara take ta yi da zuciyarta, taga idan zata iya yafewa wanda ya ƙalawa ɗanta sharrin sata. 
Daga baya kuma sai komai ya warware tun da suka ƙara tausarta shi da Khalil da Bello, daga nan kuma Hajiya Madina ta sauko ta ci gaba da bawa Fulani girmanta na matsayin da take da shi.

Yana zaune cikin tunanin abubuwan da su ka faru a baya, Ilham ta dawo, sai da ta taɓasa tukunna ya buɗe idonsa ya sauke a kanta. Ta yi kyau a cikin shigar da ta sauya na sky blue ɗin code less me shegen tsada, ya miƙe yana ɗaukar key ɗinsa ya kalli Abbas ya ce,"Babban Yarima zan wuce".

Ba tare da Yarima Abbas ya ɗago daga operating laptop na sa ba ya ce,"Ka gaida Maama da Zaytun".

Fitowarsu daga sashin Yarima Abbas su ka ci karo da Fulani Azima ta fito daga turakarta kuyangu uku na biye da ita. Haka kawai Turaki ya ji gabansa ya faɗi da ganinta, lokaci ɗaya kuma ƙwaƙwalwarsa ta shiga karanto wasu ayoyi na kariya da ke cikin alƙur'ani, ba wai yana nufinta da mugun abu bane, a'a haka kawai tun a ranar da ta je asibiti duba shi ya ji zuciyarsa ta kasa kwanciya da ita, kuma yana ta ƙoƙarin yakice abin da zuciyarsa ke raya masa akanta amma hakan ya ci tura, in yayi ƙoƙarin watsarwa sai maganar Fullo ta dinƙa dawowa cikin kansa na batun asirin da ta ce ta ɗauke akansa.

*ASIRI!* Har yau kalmar nan tsaye take a cikin ransa. Kenan inda Allah bai shigo da Fullo cikin rayuwarsa ba shikenan duk kalar asirin da yaji ta ɗauke akansa sai ya kama shi?.

Ya rufe ido ya buɗe yana kawar da wani tunani da ke shiga sashen tunaninsa.
Fulani Azima ta tsaya da tafiya tana kallon Turaki da Ilham suna tafiya, wai Turaki ne tare da ƴarta?. 
Lokaci ɗaya zuciyarta ta yi wani mugun matsewa. Ta ji kanta ya sara mata, lallai bata ga ta zama ba, sai ta sake sabon shiri, dole ne ma ta koma wurin boka, zata faɗa masa ya sauya tsarin aikinsa, sannan kuma ya yi mata duba akan duk shegen da ke lalata mata aiki.
A harzuƙe ta juya ta koma ta fasa zuwa inda ta nufa.

Cikin motar Turaki da ke tafiya akan titin zuwa PERKY FRAGRANCE STORE, wayarsa wacca ke hannun Ilham ta yi ringing a karo na huɗu, kuma a karo na huɗun ta ƙara ce masa,"Hamma ya kamata ka yi picking call ɗin nan". 

Shima a karo na huɗun ya ƙara bata amsa da cewar,"Picking ɗin ba ya da wani amfani".

A karo na biyar da kiran ya ƙara shigowa Ilham ta tsaya tana kallon lambar da babu suna a jiki. Kasancewar kiran ba huruminta bane dalilin da yasa tun farko bata bi ta kan lambar ba, sai a yanzu da idanuwanta ke kallon lambar cikin kanta kuma na karanto mata lamabar ƙawarta Gimbiya Aisha.

Har kiran ya katse Ilham bata bar kallon lambar ba, haka ɗaya sai ta ji kamar an soketa da kibiya a ƙirjinta. Kenan dama da gaske Aisha take yi mata. 
Conversation ɗin su na last haɗuwarsu ya shiga yawo a cikin kanta. Ranar buɗe company ɗin su Turaki, ranar da Turaki yayi kwalliyar da babu macen da zata kalle shi bata kwaɗaitu da ya zama mallakinta ba. Kuma a sannan Aisha ke bata labarin ta taɓa ganinsa a asibiti ta je duba wata cousin sister ɗinta, ta so ta yi masa wulaƙanci irin wanda kare ba zai shinshina ba, amma sai ya juya ya tafi ya barta da zummar zai je ya dawo ya bata haƙuri, ashe juyawa ya yi ya tafi da zuciyarta.

Ya tafi da dukkan nutsuwarta da tunaninta, don haka a ranar buɗe company da ta ƙara ganinsa ba zata yi saken da zai suɓuce mata ba. A lokacin Ilham faɗa mata ta yi kai tsaye cewar indai Hammah Turaki ne ba zai sota ba, hasalima ko kulata ba zai yi ba talkless of batun soyayya har ta kai su ga aure. Ta faɗa mata bai taɓa soyayya da wata mace ba.

Buɗar bakin Gimbiya Aisha ce mata ta yi,"Ilham, ni kuma ki rubuta ki ajiye, zan sauke duk wani jin kai da ke kansa, zai so ni, zai nemi aurena, zai aure ni a lokacin da ya gama haukacewa akaina".

Ilham ta ce mata,"Asirce min ɗan'uwa za ki yi?". 

Gimbiya Aisha na murmushi ta ce,"Ba na fatan wata rana ta zo da zan aikata saɓon ubangiji Ilham, amma ki sani, zan haukata ɗan'uwanki ne kawai da salon soyayyata mai zafi, irin wacca zai hanaku sakat har sai kun zo kun ɗaukar masa ni kun kai masa gidansa. Da gaske na ke miki Ilham ina son Brothernki sosai wallahi, kuma ina addu'ar Allah yasa ya zama mallakina, na san kuma zan samu tun da dai har sarauta ce ta haɗu da sarauta".

Ilham ta rumtse idonta sosai tana jin wani iri a ƙasan zuciyarta wanda ta rasa dalilin hakan. Ta wutsiyar ido take kallon Turaki da ke driving cikin ƙwarewa, yana bin karatun ƙur'anin da ya kunna. Ta mayar da murfin idonta ta rufe tana jin kamar zata yi kuka.
Turaki ya kai sanyayyan hannunsa ya taɓa goshinta, lokacin ta buɗe ido tana gyara zamanta.

Ya ce da ita,"Did anything happen?"

Ta girgiza masa kai ta ce,"Ba komai Hammah."

"Kuma kika yi shiru bayan na san wannan bakin naki baya rabuwa da labari."

Ta yi murmushi tukunna ta ce,"To ai na ga kana bin karatu ne."

Turaki ya kai hannu ya kashe karatun sannan ya ce,"Ina jin ki, bani labari."

"Wanne iri to?"

Ya ce,"Irin fitinar da kika riƙa yi kina yarinya bayan na koma Europe wurin Granny."

Ta sa hannu ta rufe fuskarta tana cewa, "To ai ka san wannan time ɗin, kaga babu batun a ba ka labari."

Ya ɗan waigo ya kalle ta yana cewa,"Shikenan Give me my phone."

Ta miƙa masa, ya yi dialling number ɗin Zaytuna ya kira.
Sai da kiran ya kusa katsewa sannan ta yi picking. Bayan ta ɗaga kiran, shiru ya yi bai ce mata komai ba. Sai ita ce ta yi murmushi daga inda take, tana duban Fullo da ke bacci hankali kwance a kan gado ta ce,"Ba ta tashi ba."

Turaki ya ce,"Up till now? Lafiya kuwa?"

Zaytuna ta ce,"Lafiya lau. Rashin bacci ne ba ta yi ba jiya."

"Why is that?"

Ta ce,"Na je wurin Kaka na ce mata ko da za ta ji shiru Fullo ba ta dawo ba, za ta kwana a wurina, saboda na ga kamar ba ta jin daɗi tun ɗazu, tana ta bacci. So Kakan sai take ce min ai jiya ma kwana ta yi ba ta rumtsa ba, tana ta kuka. Kuma ta yi tambayar me ke damunta, ba ta sanar mata ba, ta dai bar hakan a rigimarta kawai. Da na dawo kuma na ji jikinta da zafi. Kukan da ta yi ma zai iya sa mata zazzaɓi."

Turaki ya ja numfashi ba tare da ya ce mata komai ba. Hakan ya sa Zaytuna ta kwantar da murya ta ce,"I will prescribe some drugs, sai ka taho da su saboda ciwon yatsanta. Like akwai fever ma a jikinta."

Ya ce,"Okay, send it to me right now via message."

Sai kuma ya ce,"Bello fa?"

Zaytuna ta yi dariyar da ta bayyana haƙoranta ta ce,"He left since. Da ƙyar na taushe shi wai sai ya je wurin Maama ayi wacce za a yi."

Tsakin Turaki ya fita da ƙarfi yana cewa,"Mahaukaci ne ai… don’t pick up his calls again. Na san zai yi ta kiranka".

Zaytuna na murmushi ta ce,"Na hannun daman naka Hammah?"

Ya ce,"Eh, shi." Ya faɗa yana katse wayar.

Ya kashe kiran yana parking a ƙofar store ɗin da suka zo. Suka fito tare da Ilham, wacce ya zagaya yana tambayarta dalilin sauyawar mood ɗinta, alhali ba a haka suka fito ba.