the humiliation
by @surayyahms
18..🦋🦋🦋
TALES OF THE WAZEERIS....
tun kafin su karaso wajen zaman students a pavilion din wajen ya riga yadauka da wata kalar hayaniya
kowanne group na ta shigowa da plastic chairs suna zama a layi layi wasu na dariya wasu kuma na hira cikin walwala dfrent girls clique anata daukan selfies cikin farin ciki.
duk da ana camp ne amma yau kowa ya dau wanka andan saki jiki saboda birthday din mr abdul wanda yake tamkar favourite din kowa.
a hankali ushna take tafiya gefen ziyada hannunta dauke da bag inta da gift din yake ciki,fuskarta babu wani annuri dan tun bayan rikicin dasukayi da deeja zuciyarta ya ke mata wani irin nauyi da bata iya fassarawa.
ita kanta batasan dalilin daya saka ta hakura ta siya gift din ba ma, hala saboda kalaman deeja sun shiga ranta ne fiye da yadda take zato ko maybe saboda bata son rasa mutanen data taso dasu ne tun tana karama tanajin kamar ita din ba irin mutanen nan bane da suke iya rike fushi na lokaci mai tsawo.
suna karasowa wajen zama idanunta suka dan zazzaro waje ganin yadda wajen ya cika da mutane harda wasu lecturers da matrons suma suna zaune a gaba suna dan hira an jera chairs ne kawai cikin simple setting na camp meeting bawani taro ne babba ba.
a tsakiya kuma aka tanadi dan table inda students suka aje mishi birthday cake
karfe 9.30 am dede mr abdul ya iso da sport car dinsa, sanye yake cikin wani fitted black shirt da grey pants masu matukar fidda shape din jikinsa yana sauka da mota kamr local champion yake daga hannu sama yana murmushin tare da amsa gaisuwar students kamar perfect gentleman. yan mata da yawa na ta kallonsa suna dariya da rade rade akan irin kyan da yayi“oh my gosh he looks so good today.this man is illegally handsome.
ushna ta dauke kai tana jin wani iri aranta kana ganinta kasan she doesnt even want to be here dan a karo na farko kenan ta dan fahimci cewa ashe mr abdul din nasu ba ordinary instructor ba ne shine general senior supervisor na entire LSE bootcamp prgram din gaba daya wato kusan kowa dake wajen yau saboda shi yazo.
a gefe guda kuwa kawarta deeja dake zaune kusa da wasu yan mata tanata satat kallon ushna ta gefen idonta wani boyayyen murmushi ne kwance akan lips dinta dan har cikin ranta take jiran lokacin da gifts zasu isa hannun mr abdul agabn mutane dan a tunaninta yau ne ranar da za’a wulakanta ushna a gaban kowa ranar da wannan perfect image dinta zai rushe gabaki daya.
kai tsaye ya nufi wajen zamansa yanamai sakin sanyin murmushi saidai a karkashin wnn calm face dinsan wani irin mugun shiri ne ke yawo cikin zuciyarsa.
tunda ya zauna kwayr idanunsa suke yawo akan ushna dake zaune can can baya.
for sometine ya tsaya yana kallonta sai kuma gefen bakinsa ya dan motsa ahankli almost like someone who already knows exactly what is going to happen.
bayan an zazzauna ahankali daya daga cikin white senior instructors yamike tsaye yana gyaran wine glass dinsa kafin yace“okay students, i think zamu iya fara abunda ya kawo mu nan kafin rana yayi sosai., nan take wajen ya dauka da shiru mr abdul ya dan sunkuyar da kansa kasa yanata murmushi kmar wanda bashida wani matsala a duniyar nan.
nan mutumin ya rike mic ya cigaba da cewa “first of all, behalf of the final year LSE bootcamp committee muna appreciating mr abdul for his hardwork, patience nd cooperation with students. honestly within few days mun samu reports akansa masu kyau sosai from almost all groups.
nan take wajen ya kaure da tafi mai kara
yan mata da yawa ma harda ihu, ushna dai bata tafa ba bare tay wani kwakwkarn motsi kawai zama tayi idonta na kallon gefe.
ta dago kai kenan zata gyara zama suka hade ido da deeja sai taga deejan ta murmusa tana mata wani irin kallo kfin nan ta tabe baki cikin yanayin rainin hankali kafin nan ta maida hankalinta gaba.
daga nan aka fara kiran students daya bayan daya suna kai gifts dinsu wasu na bashi har da desgnr perfumes wasu har da watches. harma akwai wata yar india data bashi handwritten poem da akasa ta karanta agaban kowa wajen ya dauka ihu da tsokana mr abdul kuwa sai murmushi yake yana acting all emotional nd humble.
duk sanda students suka bashi gift zakaga ya tashi ya tsaya dan yayi appreciating dinsu softly kamar wani me hanklin gaske, har saida aka gama da dika grps snn aka kira
group B students,nan take deeja ta mike da sauri sauri tana gyara zaman rigarta,ziyada ta mike itama ushna tana mikewa tsaye taji zuciyarta na buguwa da karfi sai ta basar da tunanin kodan bata son abun ne aranta ya saka zuciyarta yake bugu uncontrably
cikin dedeto makanta nitsuwa ta mike slowly tabi bayansu zuwa can gaba nan suka fara aje gifts din akan table.
jin datay kamr ana kallonta yasaka ta dago kai suka hade ido da mr abdul ya dago ido ya kalleta tare da sakar mata smile din nan nasa mai sanyi sai
ita kuma bata mayar masa ba kawai ta dauke kanta.
yarinyar dake bayanta tafara chuckling tace 'girl, ure cold as always ushna bata wani kula su ba daga cikin girls din wasu suka bige da dariya. ushna taji wani irin abu ya tsaya mata a kirjinta amma haka ta daure bata nuna komai ba suka tsaya suna jira mr abdl ya taso ya fara budewa
nan instructor din yace
“okay mr abdul, i think you should open group B gifts. lets cut the cake.
calmly yace “sure. nan take deeja ta dan matso kurkusa kadan idonta cike da wani irin boyayyen excitement dan batajin dandanin guilt aranta gani take zata lalata ma ushna rayuwa ita kuma nata rayuwar zaiyi kyau daga yanxu tunda mr abdl zai kara aminta da ita sosai kuma zai aureta ne nan bada jimawa ba
kai tsaye mr abdul yafara bude gifts din daya bayan daya yana murmushi yana kiran sunan each student yana godewa duka students ana masa tafi.
har zuwa lokacin daya kai hannunsa kan gift wrap din ushna daya zamto shine 2nd to the last, gabanta ne ya dan fadi kadan batare da tasan dalili ba nan mr abdul ya dago kwayr idanunsa ya kalleta briefly kafin yafara bude wrapping din ahankli.
deeja ta wani matse hannunta cikin jin tsananin farin ciki
ziyada kuma tana ta murmushi batare data san komai ba.
haka kawai ushna taji jikinta yayi wani irin sanyi tafarajin kma zuciyarta na kkarin gaya mata something is terribly wrong.
ahankali mr abdul ya cire wrapping paper din duka nan take farar rigar calvin klein din ta bayyana.
...CK..nicee,wasu yan maza suka fada suna tafa hannu
mr abdul ya daga farar rigar sama kadan yana dan mrmshi ahnkli yace wow…this is my favorite Designer.
deeja ta dan sunkuyar da kanta kasa tana boye wani irin shuumin murmushi da tunanin duk shirinsa ne
ushna na tsaye hannunta nade a gaba tanata kallon yadda yake duban gift din sai kace nata yafi na kowa
sai can kafin ya dan saka hannu cikin gift bag din kmr wanda yasan akwai wani abu a ciki after few scnds
sai ya ciro hanky wnda tun bai gama rikewa da kyau ba condoms din suka warwaro suka fado kasa rolls of 4.
atake wajen yayi shiru irin dead silence innan wani irin sanyi ya ratsa jikin ushna daga tskar kanta har kasa lokaci daya idanunta suka fito waje kirjinta na bugawa da karfi kuma in shock tace “what the hell…?
kafin kace wani abu daga cikin sashen maza dariya ya wani kwace nan take wajen ya kara kaurewa da hayaniya.
yan mata wasu suka rike baki wasu suka fara ihu, matrons suka dan hada rai wasu kuma suka mike tsaye sbd mamaki.
mr abdul sai ya tsaya yana kallon abunda hannunsa ke rike dashi kamar shi kansa is in shock sai kuma ya ciro folded note din dake manne agefen gift din.
deeja ta wani hade hannuwanta a kirjinta zuciyarta na wani irin harbawa da mugun farin ciki.
nan mr abdul ya bude note din very slow idanunsa suka bi kan rubutun, da karfi yace ma student hold on... nan take kuwa akayi shiruuuu
sai ya dan hade gira kamar wanda yake cikin matukar mamaki.
wata white matron me zafin rai data kasa hakuri cikin daure fuska tace “excuse me sir, what is written ther?
da wani irin confusion ushna ta kallesa da sauri muryanta na rawa rawa tace “sir i…i dont think this is mine
yace okay, i will...“read it.”lets all find out who wrote it
atake wajen yayi tsit gaba daya.
tsabar karfin bugun zuciyar ushna sai data farajinsa acikin dodon kunnuwanta.
mr abdul ya dago ido ya kalleta briefly. sai ya sauke numfashi ahnkli kafin yafara karantawa cikin murya me sanyi.
“happy birthday mr abdul…”...consider this condoms, as my way of asking for a private moment with you after the lights go out…”
nan take aka fara dariya ushna taji jikinta yafara rawa sosaiii wani hajijiyar bazata na son waina ta kmr zata yanki jiki ta fadi hayaniya ya kara tashi.
ziyada tay saurin riketa tana cewa..oh my Goddd. no wayyy...
mr abdul ya cigaba da cewa “just you, me… and whatever tension we’ve both been pretending not to feel…
dede nan ya tsaya ya dan hadiye yawu snan yace “from…ushna.”
tamkar sauƙar tsawa
haka ushna taji sunan ta ya fara tashiacikin wajen lkci guda idanun mutane gaba daya suka dawo kanta.
ziyada dake rike da ita tazaro ido waje atake ushna taji kafafuwanta sun kasa daukarta.
dakyar ta daga kai ta kallesa idanunta cike da rudani da ruwwan hawaye tace ..“No! no no i..ii didnt write that!. is not mine pls sir....
daya daga cikin matrons mata cikin tsawa tace miss ushna are you serious right now? kafin ushna ta hadiye hawayenta ta budi baki wani gaye daga baya ya kwace da dariya yace damnnn topper girl got desires too huh? wajen ya sake kaurewa da surutu aka fara dariya wasu na kallonta da tsananin mamaki wasu mata kuma tuni suka fara cece kuce..
i knew she liked him, so she was just pretending? so stupid, classy outside, a sex freak inside..
ushna taji duniyar na juya mata yuuuuuu ta dago ido cikin rawar murya tana kallon ziyada da wani irin rauni ya kama nakasa ta zatay magana knn kuka me karfi da rauni ya kwace mata tace ziyada pls…tell them is not mine wnn abun ba nawa bane i swear to GOD.
ziyada dake hawaye itama duk saitaji ta rude ta rasa me zatayi she looks so shocked nd disappointed nan take zuciyar ushna ta kara karyewa sosai tafara kuka ahankli
dede nan mr abdul ya dunkule note din ahankli yana girgiza kai kamar wanda yaji ciwon abun matuka. ya karbi mic din ahnkli yace..honestly i dont know what to say.
da yaudararen yanayin nan tasa ta matured gentleman ya tsaya sai kuma ya sauke ajiyar zuciya ahankli kafin nan ya mayar da note din cikin aljihunsa sai baice komai ba kawai ya girgiza kai kadan..
can yace i think…i need a minute..
...daga haka ya juya da sauri sauri ya fice daga pavilion din tareda note dintan ahannunsa
nan take wajen ya kara kacamewa da surutu anata jin tausayinsa kamr me, wasunsu har suna na daga murya suna cewa this is crazy. i cant believe ushna did this.
ushna dake tsaye cak jikinta na rawa hawaye na zuba akan fuskarta bata sake iya daga kai ba dan batamasan me takeji na tsananin rauni da kunya ajikinta ba
nan daya daga cikin matrons tamike tsaye da fuska a harde tace
miss ushna to the head office now.
da sauri ziyada tace
but ma’am maybe its a misunderstanding pls ushna will neva eva do this
da tsawa matar tace
ohhh just sit down nd shut up miss ziyada or else u will get your suspension too.
nan take wajen yayi tsit ziyada ta nemi waje ta zauna tanata kuka abun tausayi dan ita kanta bakaramin rudewa tay ba.
haka kowa ya zuba wa ushna ido har tabi bayan matrons din zuwa disciplinary office.
suna shiga atake office din ya cika da senior camp staffs aka tsayar da ushna a tsakiya
fuskarta duk ya jike da ruwan hawaye jikinta har yanxu bai dena rawa ba
daya daga cikin manyn lnstructor ya hade rai yace is this how you people behave in LSE now? how cud you of all ppl write such a shameless content to your snior supervisor?
wata mata tace..and condoms too sriously?
ushna ta girgiza kai da sauri tana kuka sosai
“sir…i didnt write him anything. dat wasnt mine i swear.
matron din data kawo ta tace “but the note carried your name.
ahnkli cikin kuka ushna tace “i know ma’am but dat was not mine.
tsaki taja tace classic excuse miss ushna, are you denying the entire gift too?
tace “no…the shirt is mine...only the shirt.
....then who did the condoms nd the letter?
shiru tayi sbda ita kanta batasan waye ba hawaye sunakan kara zubo mata sai can tace“i dont know…”
daya daga cikin manyan matrons cikin tsawa tace look at me when am talking to you young lady, idan baki gaya mana gaskiya ba yanxun nan zamu kira iyayenki suzo snn a dauki mataki me tsauri akanki.
nan take ushna ta dago kanta da sauri tana kuka sosai tace
ma’am please please please dont involve my parents in this..i beg you...
kafin wani ya kara budan baki aka turo kofar office din ahnkli
mr abdul ne ya shigo ciki duk idanu suka koma kansa fuskar nan tasa dauke da wata calmness kamar wanda baya son tashin hankali
ya kalli ushna dake kuka sosai kmr ranta zai fita na dan wani lkaci sai ya juya wajen malaman cikin sanyin murya yace…i think we should calm down a bit. atake wani matron yace“mr abdul this is clearly inappropriate.”
cikin nutsuwa yace “i understand sir, but since she is denying it, a good handwriting is der, i think it would be unfair if we suspend her rashly without proper verification.
matrons suka kalli junansu daya daga ciki tace okay let cary out some handwriting comparison.
murmushi yay kadan kamar wanda baya son ganin an zalunci wani..cikin son gamsar dasu yace all am saying is students are emotional sometimes. maybe somebody is framing her, maybe not. but i think we should investigate this case properly.
ushna ta dago kwayar idanunta dake cike da hawaye tadan kalleshi akaro na farko dataji yadan burgeta har lkcn kuma bata san cewa shima yana cikin yan wasan ba..
har cikin ransa yasan cewa he design all these traps ne just to gain her FULL trust...
can waje akace taje ta tsaya ta jirasu kafin nan suka dan tattauna tsakaninsu daga baya daya daga cikinsu yace fine then lets summon all group B students back.
after almost twenty minute aka sake tara duka students din camp din a pavilion
wajen yayi tsit sosai babu irin hayaniyar farko aka tsayar da ushna a gaba fuskarta ya haura ya kumbura saboda tsabar kuka dataci..
kowa da irin kallon dayake mata awajen
deeja tana ganin an dawo gabanta ya fara faduwa dan batasan me zai biyo baya ba.
nan daya daga cikin matrons ta mike tsaye tace all group B camp students should bring out their camp jotters now.
nan take suka fara ciro camp jotter dinsu har deeja ma hakan tayin she have no idea what is going to happen
nan aka baza jotter din one by one fara duba handwritings anakan camparng da na letter din daya bayan daya.
ushna na tsaye kawai hawaye ne ke gangaro mata tana sharewa dan tasan maganar nan na zuwa kunnen babanta a gidansu ta gama karatu kenan a ryuwarta har abada
mr abdul bai shige cikinsu ba shide yana gefe hannunsa cikin aljihu fuskar nan tasa dauke da wata fake deep concern
sai da aka kai jotter din deeja matron din ta tsaya cak takara kallon leter dake hannunta sannan ta sake kallon rubutun jotter din deeja
fuskar ta canza atake
wani lecturer ya matsa kusa da ita yace“what is it?matron din tadago ahankali idonta na akan deeja sai tace
…this is the same handwriting with the same ink...
mutumin yana dubawa yace miss khadeeja maroki..please come foward!!!
nan take gaban deeja yay wani irin dukan tara tara tsananin tsoro ya gumeta cos this wasnt part of the plan tana daga ido kuwa taga wayam mr abdul baya kan stage din..
kafafunta na rawa rawa kirjinta na bugu fat fat ta karaso gaba..
SURAYYAHMS
ME KUKE HARSASHEN ZAI FARU da deeja, ushna da kuma mr abdul akan wannn case din?????
what secret game did u think mr abdul yay playing akansu duka??
hassada bata san sabo ba,kina ganin childhood friend dinki zata iya miki irin haka??
inkece a matsayin ushna shin ta zakiyi?
kubiyo ni acikin littfin 👇🏻
TALES OF THE WAZEERIS
by surayyahms
***