07
by @legendspen
Shafi na bakwai
(07)
A hankali na shiga takawa zuwa cikin gidan, yana tsaye yana kallona har na shige, kamar daga sama na ji muryarsa.
“Wane wannan?”
Shiru na yi bance ko ƙala ba, a fusace ya sake magana.
“Ba dake nake ba?”
Bakina na rawa na ce.
“Saurayina ne?”
Ya yi dariya sannan ya ce.
“Ba shine Sardauna ba? Fahad Ta ambo.”
“Fahad Ta ambo.”
Na faɗa kaina a ƙasa.
“Nana.”
Ya kira sunana amma yanzu muryarshi a hankali, na ɗago kai na kalleshi.
“Zo nan?”
Ya faɗa yana nuna kusa dashi, kamar mai ciwon jiki haka na taka na je.
“Kinsan waye shi? Su ɗin masu kuɗi ne sosai kuma kinsan duk irin waɗan nan masu kuɗin ba wani kirki ba ne dasu, kaɗan ne masu mutunci.”
“Nasani.”
Na faɗa a hankali, ya kalleni sannan ya ce.
“Nana ki sani kefa macece, rayuwarki tana da daraja ga iyayenki da ‘yan uwanki, ba wai dan baku da kuɗi yana nufin ku ɗin baku da daraja ba, nasani muna cikin wani zamani wanda duk mai wani abu shine mutum, amma duk da haka kada ka ta ɓa bari darajarka ta ragu ko ki nuna baki da ita, karki ta ɓa sa wa ranki alfarma zai yi miki ko yake yi miki, ke macece kuma mai daraja. Dan haka ka da nasake ganin abinda ya faru yanzu ya faru.”
Yana faɗin haka ya shige ɗaki, ya barni ina faman tunani, me ya gani? Me yake magana akai?.
Abu kamar wasa Fahad shiru, sati ɗaya sati biyu, idan na kirashi a wayar Hajiya ba ya ɗagawa, ta Malaika kam daman ya ja min kunne ya ce a wayar Hajiya kawai ya lamunce na kirashi.
Sai da aka yi sati uku baya ɗaga wayata kuma ba ya kirana, duk na bi na damu kuma na yi alƙwarin zanyi masa biyayya akan komai ya sani, tun da harshi ya ɗauki jahadin yi wa iyayensa magana akan yana son auren wacca ba ta kai ba, ni to me ya sa bazanyi ba.
Wata ranar laraba da yamma ina zaune a ɗaki na ɗauki wayar Hajiya na sake gwada lambarsa, ina kira ya katse ya kirani. Na ji wani mugun daɗi a raina, ina ɗagawa ya ce da ni.
“Ina bayan gidanku.”
Ba shiri na miƙi na zura hijabi na yi waje, Hajiya na tsakar gida tana kaɗa miya na ce da ita.
“Zani gidansu Amina.”
“Da yamman nan?”
“Eyh.”
Ina faɗin haka na fice zuwa bayan layi, yana jingine jikin farar motarsa, yana sanye da light blue ɗin shadda, ina ganin fuskarsa na ji wani sanyi ya mamaye zuciyata, wata irin nutsuwa ta shigeni, duk wata fargabar da nake ji ta tafi.
“Yanzu ma kin daina damuwa idan ban nemeki ba.”
Ya faɗa yana ƙare min kallo.
“Waya faɗa ma, wallahi na damu sosai da sosai.”
“Ban yarda ba, gashinan har wata ƙiba kika yi.”
“Ƙiba kuma?”
“Eyh, ya maganar mu? Me kika yanke?”
“Zanyi magana da Alhaji ta yadda zai fahimta.”
“Good girl.”
Ya faɗa yana buɗe motarsa, ya ɗauko leda ya miƙamin. Hannu nasa na amsa sannan na ce.
“Na mene?”
“Naki ne, na yi magana da Daddy ya amince amma Mom ce abun sai addu’a.”
Wani irin tausayinsa na ji ya ratsani, nasan irin wannan abun tabbas da wahala.
“Allah Ya sa ta amince itama.”
“Nana na sha wahala akan lamarinki, sai na ji kamar zan haƙura sai na ji bazan iya ba, amma ke babu ruwanki ɓata min rai kawai kike, maimakon ki nuna sakayyar soyayya amma naga babu abinda kike so sai ɓacin raina.”
A tsorace na ce.
“Ya zaayi naso ɓacin ranka?”
“Gashi ina gani.”
Da irin waɗannan abubuwan Fahad ya dinga amfani yana cusa min tausayinsa da wata iriyar soyayyarsa mai girma, wanda a kullum gani nake yana shan wahala a kaina, sai da fa na kasa tarar Alhaji ko Hajiya da maganar, duk son da nakewa Fahad bana jin ya kai tausayin da nake yi wa Alhaji ba.
Shi kuma a kullum faɗa min irin tashin hankali da suke yi da mahaifiyarsa da ‘yan uwansa a kaina, har cewa ya yi dani ya daina shiga sabgar sister ɗinshi, a ranar na yanke shawarar tunkarar Alhaji akan maganar.
09:15pm.
Alhaji na zaune a ɗakinsa ya bayan ya yi wanka yana sauraren radio na shigo cikin ɗakin.
“Barka da hutawa Alhaji.”
“Nana barka dai, akwai abinda kike buƙata ne? Ko kin shirya sanar dani damuwar da na ce tana damunki kike ɓoyewa.”
Gyaɗa kai na yi sannan na fara magana cikin rawar baki.
“Alhaji daman.. daman wani ne..”
Alhaji irin mutanen nan ne masu sauraron mutane, zai iya kwashe awa guda yana saurarenka ba zai katse ka ba, sannan kuma ba zai yanke ma hukuncin ba har sai ka kammala.
“Wani ne.. tun da daɗewa ya ce wai yana so ya turo iyayensa wajenka.”
Murmushi Alhaji ya yi sannan ya ce.
“Su yi mini me?”
“Wai yana sona zai aureni, kuma na faɗa masa kai bazaka aurar dani ba sai na yi karatu me zurfi na zama maaikaciya, ya ce wai ya ji ya gani zai barni na yi karatu duk wani waje da nake so.”
“Shi ɗin waye?”
“Sunansa Fahad Ta ambo.”
Wani murmushi Alhaji ya ƙarayi sannan ya ce.
“To ke me kika yanke, auren ko karatu Nana?”
Na yi shiru na rasa me zance. Allah Ya sani ina son Fahad ina tausayin halin da yake ciki a kaina, kuma bana son rasa shi, sannan kuma ina son cika burin mahaifina, amma kuma abu guda ɗaya da nake gani shine auren tun da Fahad zai barni na ci gaba da karatuna, domin a maganar mu ta ƙarshe da shi ya ce da ni.
‘Idan kika ga zaiƙi sai ki faɗa masa ni zan barki ki ci gaba da karatun naki.’
“Nana”
Alhaji ya kira suna na.
“Na baki kwana biyu kije ki yi shawara, duk hukuncin da kika yanke zan amsa tare da nawa sharaɗin akai.”
“Na gode Alhaji.”
Na faɗa tare da tashi na fice, ko da na shiga ɗaki na kwanta abubuwa suka yi ta faɗomin a rai, na saƙa wancan na kwance wancan.
“Kalli su Yaya Radiya, da Rumaisa sunyi aure kuma suna cikin rufin asiri, ga Rumaisa nan ma ta koma makaranta tana karantar harkar lafiya, ke me kike jira zaki zauna wani zama idan kika gama karatun girma ya kama ki tsaf sai ki rasa mijin auren.”
Zancen zucin da na wayi gari da shi kenan, haka na yi ta abubuwa komai sukuku, dan ma yanzu ba makaranta muke zuwa ba WAEC zamu fara nan da sati biyu, shi ya sa bamu cika wani zuwa ba. Bayan Alhaji ya fita na shirya na lallaɓa Hajiya akan ina son zuwa gidan Yaya Rumaisa da Yaya Radiya duka a rana ɗaya.
“Wai me zakije ki yi musu duka su biyun a rana ɗaya?”
Hajiya ta tambaya cike da mamaki, ganin tana neman hanane ya sa na ce.
“Alhaji ne fa ya ce na je dukkansu mu yi magana dasu.”
Kuɗi ta ɗauka ta bani tare da cewa.
“Kuma karki yi yamma.”
Ta gidan Yaya Rumaisa na fara, tun da shi yafi nisa, akan gidan Yaya Radiya. Shi ya sa na fara zuwa gidan Yaya Rumaisa, yanayin da na sameta ya yi matuƙar burgeni, ta yi ƙiba abunta duk da karatun da take yi ga yaranta kyawawa guda biyu Afra da Affan.
Bayan mun gaisa ne na kalleta sannan na ce.
“Yaya shawara nazo nema wajenki.”
“Ina saurarenki.”
Sai da na ɗan yi jim sannan na ce.
“Nasami Miji kuma dagaske aure na yake so ya yi, sannan ya yi min alƙwarin bari na na ci gaba da karatu da nuna masa Alhaji yana son karatun.”
“Rawasiya, kinyi magana da Alhaji.”
“Na yi, shi ya ce na yi shawara.”
Yaya Rumaisa ta gyara zama, ta kalli ni cikin idanu tare da kamo hannuna, sannan ta numfasa ta fara magana cike da nutsuwa.
“Nana zan gaya miki abubuwan da suke cikin aure na daɗi da rashin daɗi, idan na faɗa miki sai ki yi tunani da kanki, ki ga wanne kika zaɓa.”
“Tom Yaya.”
“Nana, aure ba kawai canza gida ba ne ko samun wanda zai riƙa lura da ke. Aure ibada ne, kuma makaranta ce da ba a yaye ɗalibi har sai mutuwa ta raba. Idan kika ga mace a cikin jin daɗin gidam aure, to dole akwai matakan da ta bi waɗanda suka kai ta ga wannan matsayin jindaɗin. Nana abinda zaki fara sani a farkom farko shine, mene ne Aure kuma yaya Rayuwarsa take?
Aure haɗaka ce ta rayuka biyu. Manzon Allah (SAW) ya ce a cikin Hadisin Al-Baihaqi Idan bawa ya yi aure, to tabbas ya cika rabin addininsa.... Don haka, rayuwar aure tana buƙatar haƙuri da juriya. Za ki ga daɗi, za ki ga wuya. Amma mabuɗin shi ne Biyayya da Fahimta. Sannan kisani akwai Abubuwan da ake so Mace mai aure ta yi, duk da suna da yawa amma bari na baki wasu daga ciki. Nana na farko akwai Biyayya. Ki sani Nana, biyayyar miji tana kai mace Aljanna. Amma fa muddin bai sanya ki saɓon Allah ba. Na biyu akwai Kwalliya da Tsafta, Nana ki zama kullum idon mijinki yana ganin abin da zai faru da shi, hancinsa ya riƙa shaƙar ƙamshi mai daɗi. Sannan kuma akwai riƙe sirri. Kada ki yarda sirrin gidanki ya fita waje, koda ga mu ‘yan uwanki ne, muddin ba neman shawara ta lalura ba ne. Bayan wayannan akwai abubuwan da ba a so Mace ta yi. Misali Gasar Iko, Kada ki riƙa nuna wa mijinki ke ma kina da iko kamar sa. Shi ne shugaban gida, don haka ki ba shi matsayinsa. Sannan Yawan ƙorafi Kada ki zama mace mai yawan gunaguni a kan kowane ƙaramin abu. Sai kuma wani abu da muke yawan yi shine ƙaryata Alkhairi. Manzon Allah (SAW) ya nuna cewa yawancin mata suna shiga wuta saboda rashin godiya ga mazajensu. Don haka, ko kaɗan ne ya yi miki, ki ce 'Na gode'."
Ta ɗago ta kalleni yadda jikina ya yi sanyi, sannan ta ce.
“Nana aure kala biyu ne, ko na ce zaman aure kala biyu ne, na farko akwai farin cikin aure idan aka yi dace. Nana, idan kika samu miji na gari, miji mai tsoron Allah kamar nawa, to za ki ji kamar kina Aljanna a duniya. Za ki samu abokin shawara, wanda zai kiyaye miki mutuncinki, ya kare miki rayuwarki, kuma ya zama silar ƙarin kusancinki da Allah. Za ki ji wani sanyi a zuciyarki wanda ba shi da misali. Na biyun kuma shine akasin haka Idan ba a yi dace ba, Idan kuma aka samu rashin da ce wanda Allah Ya kare mu, to aure yakan koma kurkuku. Idan miji ya zama mara tsoron Allah, mai son kansa kawai, to zai riƙa amfani da ikon da Allah ya ba shi yana zaluntar mace. Zai iya raba ta da mutuncinta, ya raba ta da danginta, ya kuma mayar da ita tamkar baiwa a gidansa. Shi ya sa nake ba ki shawara Nana; Kada ki yi gaggawar aure don kawai kina son yin sa, ki yi shi don kin samu wanda ya dace, kuma ki tabbatar ba za ki daina karatun ki ba domin ilimi shi ne gatanki."
Jikina ya yi sanyi, ya mutu baki ɗaya. Tabbas duk wata shawara da nake nema nasame ta wajen Yaya Rumaisa, kuma dole na zauna na yi zurfun tunani akai sosai da sosai.
“Nana karki yanke hukunci cikin gaggawa, ki sami lokaco ki nutsu, ki duba halayen saurayin naki Nana ki ga nagartacce ne ko akasin haka.”
“Shikenan Yaya Na gode sosai.”
Daga nan na yi mata sallama na wuce gida, ban ma je gidan Yaya Radiya ba, ko da Hajiya ta tambayi ya na dawo da wuri sai na ce da ita.
“Iya gidan Yaya Rumaisa na je.”
Da ta cika ni da tambayar ya take ya gidan, kawai na tashi ma shige ɗaki. Kwata kwata ma bana son magana, so nake na nutsu na saurari zuciyata me take ce min, me ta hanga a tare da Fahad, sai dai fa ko mene ina matuƙar ƙaunar Fahad, rabuwa da shi da wuya.
Legendpen
***