08
by @legendspen
Shafi na takwas
(08)
Har dare ban iya ce da kowa komai ba, shiru kamar wacca ba ta da lafiya. Haka na kwana ina faman tunani har washe gari, gaba ɗaya ba mu haɗu da Alhaji ba shima kuma bai neme ni ba, har zuwa yamma lokacim da nasan Sardauna zai zo, Hijabi kawai na sanya na fita dan bana jin zan iya wata kwalliya a yanayin da nake, sai dai tambayar da nake yi wa kaina. ‘Wai shin me ya dame ni?.’
Kallo ɗaya Sardauna ya yi min ya gane yanayin da nake ciki, tambayar farko da ya yi min.
“Abban bai amince ba ne?.”
“A’a ya ce na je na yi tunani akan aure ko karatu?”
“To Nana me kike jira? Kinsan abinda na yi fama da shi yanzu kafin na fito?”
A hankali na buɗe baki na ce.
“Jiya da daddare muka yi maganar da shi, jira nake ya dawo na ce mai na amince.”
Ya yi wani murmushi sannan ya ce.
“Ko ke fa Hon.”
Nima na yi murmushi.
“Kinsan sunana?”
Na ɗago kai na kalleshi, ya gyaɗa mun kai.
“Wane suna?”
“Ban taɓa ji kin kira ba, shi ya sa na tambaya ko kin sani?”
Sai da na yi murmushi sannan na ce.
“Ya zaayi na kira sunan ka, ai babu ladabi.”
“To ai akwai sunan da nake so ki dinga faɗan.”
“Wannene?”
“SARDAUNA!”
Har cikin raina na ji daɗin sunan, sai da na maimaita a raina sannan na ce.
“Sunan ya yi daɗi.”
“Ina som sunan &akata ce ta samin shi, shi ya sa na ce shine sunan da mata zata dinga kira na, kuma a yanzu naga komai ya kusa kammala, shi ya sa na faɗa miki dan nima Mom ta fara amincewa.”
“Kai Alhamdulillah.”
Na faɗa a fili, shi kuma ya ce.
“Yanzu saura ke da Abba.”
Daga nan muka ɗan taɓa hira sannan ya tafi, abu ɗaya da na kasa sabawa da shi, shine duk sansa Sardauna ya zo wajena zai tafi sai na ji ba daɗi, nifa ko ba zamuyi magana ba ya dinga kallona da ido kaɗai ina kallonsa abun farin ciki ne. Daga nan gidansu Amina na shiga, abun mamaki na tarar da Fauziyya da Malaika duka a gidan.
“Da banzo ba da ba zama a nemeni ba kenan?”
Na faɗa ina kallonsu.
“To banza mun zo gidan naku aka ce kin fita, sai da muka zo Amina ta ce wai Fahad ne ya zo.”
“Eyh daga can nake.”
Na faɗa ina zama.
“Dagaske dai auren naki zai yi?”
Fauziyya ta tambaya, na kalleta sannan na ce.
“Eyh wallahi, a yanzu ma ‘yan gidansu so suke su zo, Alhaji ne har yanzu bai gama amincewa ba.”
“Kai ma sha Allah, muna da shagali a gabanmu, amma ya zancen karatunki?”
Amina ta tambaya, kafin na bata amsa Malaika ta bata amsa da cewa.
“Ke wai kin san gidan da zata shiga, to ƙila ma a ƙasar waje zata ƙarashe karatun na ta.”
“Kai Mailaka! Wai masu kuɗin gaske ne?”
Amina ta tambayeta.
“Wanne masu kuɗi kika sani kaf Jigawa?”
“Gidan gwamna.”
Amina ta bata amsa.
“Ai gwamna kuɗin jama’a ne, wannan magana ake kan masu kuɗin kan su, yarinya kin yi da ce za ki shiga cikin manyan mata masu aji.”
Ni dai jinsu nake har suka kammala hirar, na dawo gida. A bakin ƙofa na ga Yaya Ridwan yana kallona, ban kai ga shiga gidan ba na ji muryarsa na faɗin.
“Na ƙara ganin kin tsaya da wani ɗan iskan sai na ci uwarki.”
Daga haka ya shige nima na shige ciki, sai dare sannan Alhaji ya dawo, sai da na jira ya kammala komai ya shiga ciki sannan na shiga ɗakin na sa.
“Alhaji Barka da dare.”
“Barka dai Nana.”
Ya amsa yana saurarena, sai dai na yu shiru na kasa magana.
“Nana ya aka yi? Kin yi shwarar ne?”
Na gyaɗa kai a hankali, ba tare da na yi maganar ba.
“Faɗi mana, ki yi magana ina sauraren kinji.”
“Al Haji.. da ma.. Daman Alhaji na gama ne.”
Na faɗa a rarrabe, ya ɗago kai ya kalleni sannan ya mayar da kansa ga abinda yake.
“Kinga me?”
A hankali na ce. “Shwarar.” Muryar na ba ta fito sasai ba.
“Tom me kika yanke, ina saurare.”
“Auren.”
Ya ɗago kai ya kalleni kusan minti biyar sannan ya mai da kai ƙasa.
“Wannan ita ce shawarar taki?”
“Eyh Abba.”
Abba ya sauke numfashi bayan ya gama sauraro na, ya kalle ni da idanuwan da suka nuna damuwa amma kuma cike da soyayya, sannan ya fara magana
"Nana, na ji abin da kika zaɓa. Kuma a matsayina na mahaifinki, ba zan taɓa tilasta miki abin da zuciyarki ba ta so ba, domin aure ya fi ƙarfin dole. To amma, kafin mu kai ga mataki na gaba, akwai wasu abubuwa da nake so ki sani, kuma akwai sharuɗɗan da zan gina aurenki a kansu nasan kinsan Aure, Nana, ba wasa ba ne. Mutuncinki shi ne mabuɗin darajarki a gidan miji. Ina so ki sani cewa kowace mace ita ce take gina mutuncinta ko ta ruguza shi. Ki zama mai hakuri, mai biyayya, kuma mai kiyaye sirrin mijinki. Amma kuma, ki sani cewa Allah ya ba ki daraja a matsayinki na mace, kada ki bari wani ya take miki mutunci. Kamar yadda kika sani, burina ne ki karanta ilimin likitanci ko wani fanni da zai amfani al'umma. Tunda kin zaɓi aure yanzu, to zan bar ki ki yi auren, amma a kan sharɗi guda Lallai sai kin ci gaba da karatunki a gidan mijinki. Ba zan yarda ilimin ki ya tsaya a nan ba. Ilimi shi ne gatanki, shi ne haskenki, kuma shi ne zai ba ki ‘yanci koda bayan raina. Sannan, ina so in ga wanda ya sace zuciyar ‘yata har ta zaɓi barin karatu a yanzu. Dole ne in ganshi, in tattauna da shi, kuma in fahimci wane ne shi, daga wane gida yake, kuma wane irin hali yake da shi. Ba zan ba da ke ga mutumin da ban yarda da asalin sa da addininsa ba."
Gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, soyayyar da mahaifina yake yi min babba ce ba ƙarama ba, kuma in sha Allahi sai na cika masa wannan burin nasa, nasan Sardauna yana sona kuma zai so abinda nake so.
“Abba na yi maka alkwarin zan tsaya kai da fata akan karatuna, zan zama ‘yar da zaka yi alfahari da ita.”
Na faɗa muryata tana fitar da wani irin sauti, kamar mai kuka. Alhaji ya yi murmushi sannan ya ce.
“A kullum ina alfahari dake da dukkan ‘yan uwanki Nana, Allah Ya yi miki albarka.”
“Amin Abba.”
Na faɗa tare da ta shi na fice, ko da naje ɗaki ban wani iya bacci sosai ba, bawai ina cikin yanayin farin ciki ba ne da amincewar Abba ba, ba wai kuma ina cikin damuwa ba ne, kawai wata iriyar soyayyar Alhaji ce ke ratsa zuciyata, ina son Abbana so mai girma.
Washe gari.
A wayar Hajiya na kira Sardauna na faɗa masa yadda muka yi da Alhaji, maimakon naji farin ciki a muryar Sardauna sai tsoro.
“Hon ina jin tsora gaskiyya, ba zan iya tunkararsa ba sai dai kawai na turu.”
“Alhaji fa ba shi da matsala, kuma ba wani abu zai ce da kai ba kawai tattaunawa zakuyi ku yi hira da shi.”
“A’a Honey pls.”
Nasan dole aiki ne babba akaina, na lallaɓa Sardauna ya zo wajen Alhaji, cikin sanyin murya na ce dashi.
“Ko zaka zo yau mu haɗu.”
“So kike na zo ki haɗani da shi?”
“A’a magana zamu yi da kai.”
“Tam zan zo.”
Ya faɗa tare da kashe wayar, haka na mayarwa da Hajiya a barta, ni dai gaba ɗaya wani sukuku haka nake, tunanin yadda zan fara fahimtar da Sardauna muhimmamcin zuwa wajen Alhaji kawai nake.
Ra’is ne ya buɗe labulen ɗakin.
“Wai daman baki mutu ba?”
Na watsa mai harara sannan na ce.
“Sakar mini labule ka fita.”
“Naƙiya, wai me kike yi a ɗaki kwana biyu?”
“Ra’is ka sakar min labule ka fita kafin na yi ma rashin mutunci.”
“Karki fasa.”
Ya faɗa yana shigowa ya zauna gefen gadon ɗakin.
“Wai na ji aure zaki yi?”
A razane na juyo na kalleshi sannan na ce.
“Waya faɗa maka?”
“Duk abinda ake ɓoyewa ai mun sani, mun yi waya da Yaya Rumaisa ta faɗan, sannan ta ce na zo na baki shawara.”
Shiru na yi ban ce komai ba, shi kuma ya ɗora da cewa.
“Wallahi indai saurayinki yana sonki, kin yarda da soyayyar da yake miki, to ki yi aurenki me zaki zauna ki yi a gidan? Ke mace fa, ba ‘yar zama ba ce, akwai lokacin da mace take samin samari cike har da na aure, da ta yi wasa ta ƙara girma shikenan zasu tsiyaye kamar hawaye su tafi.”
Kallon Ra’is na yi a raina na ce.
“Shi kuma kalal tashi shawarar kenan.” A fili kuma na ce.
“Alhaji yana so na yi karatu”
“To ai a gidan mijin ma zaki iya ci gaba da abinki, wannan fa a ganina ba matsala ba ce.”
Haka Ra’is ya yi ta bani nasa shawarwarin, bayan ya tafi na zauna na haɗe komai na cakuɗa a kwalwalwata, na yi ta faman kwashewa da ɗebewa har zuwa yamma.
Wajen ƙarfe biyar na tashi na fito tsakar gida lokacin Hajiya na shara, kallona ta yi sannan ta ce.
“Kwana biyu iskancin zaman ɗaki kika ɗaukarwa kanki ko Nana?”
“A’a Hajiya, bani da lafiya ne fa.”
“Baki da lafiya shine bazaki sanar ba.”
Yaya Ridwan ne ya leƙo daga ɗakinsa sannan ya ce.
“Hajiya ƙyaleta kawai.”
Ni a raina na rasa me yasa Yaya Ridwan baya sona da Sardauna, ina tuna lokacin bikin su Yaya Radiya duk da bai yi magana ba amma yanayinsa ya nuna yana farin ciki da hakan, amma ni ya fito ya nuna baya farin ciki da hakan, dan ko jiya da daddare sai da ya sake min magana akan Sardauna.
Wayar Hajiya na ɗauka na shiga ɗaki, ina shiga na kira wayar Sardauna, ya katse bai ɗaga ba can kuma ya yi min text.
“Ki fito.”
Abinda ya rubuta kenan, na rasa me yasa duk lokacin da Sardauna ya shigo unguwarmu sai na ji a jikina.
“Ina zaki ke da ba lafiya?”
Hajiya ta faɗa ganin ina shirin fita.
“Abu zan amso a waje.”
“Wajen wa a waje?”
“Ɗan ajinmu ne.”
Sai da ta kalleni sossi sannan ta ce. “Idan kinga dama ki zauna a wajen.” Sannan ta ci gaba da abunda take, ni kuma na fice.
Yau a barandarmu na sameshi, ya tsaya ya harɗe hannunsa a ka faɗa. Kamar ko yaushe dai cikin kyakyawar shiga yake.
“Ke baki damu bama da kiran da Alhajin yake min ko?”
Abinda ya fara faɗa kenan, bayan na ƙaraso inda yake. Na rasa me ya sa Sardauna yake ce min ni bandamu ba, ko so yake ya ga damuwar ƙarara a fuskata?
“Ba fa wani abu ba ne Allah.”
Na faɗa bayan na ƙaraso inda yake.
“Nana ajikina nake jin Abba bazai ban aurenki ba, ni dai idan kina da wata hanyar kawai ki faɗan.”
“Wace irim hanya?”
“Wacca zamu bi a fasa zuwa wajensa.”
“Maganar makaranta kawai zai yi ma fa, Alhaji ba zai janye maganar karatu ba fa, kuma Alhaji idan yana ce akan magana babu mai sauye sai Hajjansa ita kaɗai.”
“Wace Hajja?”
“Kakarmu fa.”
“Aina take?”
“Dutse Gadawur.”
“Kina ganin ba zanje na gaishe ta ba yau, sai na ce mata nine saurayinki?”
Taɓe baki na yi tare da cewa.
“Ni ban wani cika shiga al’amuranta ba, hasali ma ba ta son mu.”
Murmushi ya yi sannan ya ce.
“Zata so ku, bani address kawai.”
Ba shi cikakken address na yi na gidan, bai wani jima ba ya tafi, na shiga gida. Ina kallon wani irin kallo da Yaya Ridwan yake min, ni narasa na mene haka?.
Ko da dare da Alhaji ya dawo bai yi min maganar ba, sai ma sanar damu da ya yi ansa bikin Isah Nadabo sati biyu, ya sami mata a jihar kano.
Na ji daɗi sosai a raina tare da yi masa fatan alheri, nasan dai bikine zamu sha dan a gidanmu zaayi komai daga farko har ƙarshe, dan iyayensa ba anan suke ba ‘yan Gumel ne.
Kwata kwata ba muyi magana da Sardauna ba har washe gari, sai da safe ya kirani muka sha soyayya kuma a yanayinssa babu wannan fargabar, nima kuma ban tambayeshi ba.
Wajen ƙarfe tara da rabi, ina zaune bakin rariya ina wanke wanke, Hajiya na ɗakin Alhaji yana shiryawa, Ra’is kuma na sharar tsakar gida muka jiyo baloƙoƙon Hajja.
Gabana ya yanke ya faɗi. ‘Me ya kawo matar nan gidan nan kuma?.’ Na faɗa a raina, sabida daman a tsarin Hajja sai ta gama baloƙoƙo kafin take shigowa gidan. Hajiya da Alhaji duk sun fito tsakar gida suna jiran ta shigo, ita kuma tana can ta tagar ɗakinsu Yaya Ridwan ta baranda tana faman yi masa sababi.
“Ni dai kaf zuri’a ta a kanku a gama tabbatattu, ga dai farin jini Allah Ya yi muku amma sai baƙar zuciya, wacca nasan wajen uwarku kuka gado, yo daman fulanin jeji ina zuciyar arziƙi a tare da su, Allah Ya kyauta dai.”
Abinda ta shigo da shi cikin tsakar gidan kenan a bakinta, Alhaji ne ya fara tarar da faɗin.
“Hajja Barka da safiya, sannu da zuwa.”
“Yawwa sannu.”
Ta faɗa tana kauda ido, Hajiya ma ta ce.
“Hajja sannu da zuwa, ina kwana.”
“Lafiya.”
Ta amsa a daƙile, Ra’is ma ya ce.
“Sannu da zuwa.”
Banza ta yi da shi, nima na ce.
“Sannu da zuwa.”
Aikuwa ta washe haƙora tare da faɗin.
“ ‘yar arziƙi ke nake ta baza idanun ganin, kinsan idanun ba kowanne ke da kyau ba, gashi ke ba zuwa kike ba uwar mai mugun nufi ta hanaki.”
“Ikon Allah sai kallo, yau rikicin tsufan nan ya kawo ta kenan.”
Ra’is ya faɗa yana daga inda yake, ni kaina nasan rikicin tsufa ne, dan ina ga ma Yaya Radiya take magana akai, tin da ita ce ta auri jikan da take so.
“Kina ina ne, matso na shafiki, na shafi arziƙi.”
Ta sake faɗa, kamar wacca ƙwai ya fashewa a ciki haka na taka na je idan take.
“Sannu mai ƙashin arziƙi! Sannu ‘yar nan.”
Ta faɗa tana riƙe hannu, sannan ta juya ga Alhaji.
“Sannu tabbatacce, kai yanzu ace yarinyar nan tana da wanda yake sonta daga gidan arziƙi irin haka kamar gidan Ta ambo, amma ka ɓoye min, sai yaron da kansa ya nemeni ya kawo min kayan arziƙi, ka ji tsoron Allah.”
Legendspen
***