HADIN KADDARA

Chapter 19

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                     By

         AyshaNalado 


Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍


BOOK 1


Page  19


Lokaci ɗaya Inna  ta fita daga hayyacinta, ta shiga sauke numfashi dakyar, tana sakin ajiyar zuciya mai karfi lokaci bayan lokaci, kana kallon fuskarta zaka fahimci halin da zuciyarsa ke ciki na tsananin damuwa. Sosai hankalin  Maamah  ya tashi, sai lokacin ta dawo hayyacinta ta gane katoɓarar da ta yi, ta yi dana sanin sanar da ita wannan maganar yafi cikin carɓi, ko bata tambaya ba tasan ciwonta ne ke son tashi na hawan jini, wanda  ta yi imanin idan da abinda ke saurin tado mata shi, to zancen Adda Shatou ne, kuma  bata da tantama akan ta dalilinta ta samu larurar. Har yau da ake neman shekara  tara da faruwar abinda ya faru, ta kasa sabo da rashin Shatou, wannan  na ɗaya daga cikin dalilin da ya sanya daga Baffa har ita babu mai  ambaton sunanta ko wani abu daya  shafe ta a gabanta, saboda irin wannan  yanayin da take shiga. Ko da ta taimaka mata ta kaita ɗaki bata kwantar da ita ba, sai da ta  ɓalla  magungunanta  ta bata ta sha.  Kwanciya Inna ta yi ta lumshe ido, zuciyarta cike da bege da kewar ɗiyar tata mai tsanani, tana jin idan har ta mutu ba ta yi ido biyu da Shatou ta nemi yafiyarta ba, to tabbas Ubangiji zai tuhumeta kuma zai hukuntata a kan hakkinta, har yau laifin kanta kaɗai take gani akan abin da ya faru, kullum tuhumar kanta take yi a kan me yasa bata saurare ta ba , a lokacin da take kuks tana rungumar  ƙafafunta? Me yasa bata jata a jiki ta ji damuwar ta ba? Me yasa ta kasa yi mata uzuri, ta kasa sarrafa fushinta  akan yar tata a lokacin da kowa ya gaza fahimtarta, a matsayin ta na uwa, itama sai ta saje da sauran mutane,  itama sai idanunta su ka rufe har ta mance da irin tarbiya da nutsuwar Aysha, ta kasa tantance  abinda zata iya aikata da kuma aikin kaddara wanda ya riga fata. A hankali ta shiga motsa bakinta ba tare da ta buɗe idanu ba, “Ya Allah ka tsare min ita a duk inda take, eɗe e nder kene, eɗe waɗa mo e laawol moƴƴol, ka kare min mutuncinta, wonaa sabu mo mi waɗi, ya Rabbi.” Jin irin addu'ar da take yi ya sanya Maamah saurin ficewa ɗaga ɗakin  zuciyarta na rawa, kai tsaye ɗakinta ta nufa ta faɗa kan godo ta saki wani irin kuka mai cin rai, kukan da suka kwashe shekaru suna rairawa ita da iyayenta, a fili da zuciya, tabbas Ubangiji sai ya yi musu sakayya, hakika an cutar da su...

A bangaren su Salmah kuwa, har suka ƙarasa cikin tamfatsetsen falon Mother, ba su kula da rashin Aysha a tare da su ba. Mother dake zaune a ɗaya daga cikin kujerun falon , ta dago da fara'a tana kallonsu, kai tsaye Salman gabanta ya nufa, ya risina yana gaisheta cikin yanayin da ke nuni da tsantsar sabon da su ka yi da juna. Suraj dake tsaye ya juyo ya saci  kalon mutuniyar tasa  da ta coge daga  bakin kujera, ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, har ya kasa dauke ido daga kanta, zuciyarsa  na wani buɗawa saboda nishaɗin ganinta a kusa da shi da yake yi, Allah ya sani yana kaunar Salmah so mara iyaka, wanda yake jin a shirye yake da aikata komai domin mallakarta, kuma idan za a saka masa bindiga ba zai ce ga abinda ke daukar hankalinsa gareta ba, kawai so ne sadidan minal lahi, wanda ya fara shi tun daga gani na farko da ya yi mata, tun yana daukar abin wasa har ya fahimci da gaske fa sonta yake so irin na aure so irin na rayuwa a tare har abadan da'iman. Duk da ɓacin ran da take ciki hakan bai hanata gaisar da Mother  a mutunce cike da tsantsar ladabi ba, sai dai fuskarta a tamke babu alamar Rahama “Lafiya ƙalau Salmah, karaso ciki mana mu gaisa da kyau.” Mother ta faɗa  tana miƙa mata hannu karasawa ta yi zata zube a gabanta, ta janyo ta ta zaunar kusa da ita, tana ci gaba da faɗin,  “Tabarkallah masha Allah, yau dai naga ƴata Salmah, to ya kike ya Ammienku.” “Tana Lafiya.”  “Ma sha Allah, haka a ke so. Am Suraj kawo wa baƙuwa ruwa, don dai shi Salman ɗan gida ne.” Mother ta faɗa tare da sauke idanunta a kansa, tsananin shagaltar da ya yi a bagen Salmah yasa bai san ta yi maganar ba, sosai mamaki ya cika Mother ganin irin kallon da yake binta da shi, abinda ta karanta a cikin kwayar idanuwansa, ya sanya bata san sanda ta kira sunansa da karfi ba “Surajudeen!” Firgigit ya juyo, suna haɗa idanu ya yi ƙasa da kai, sai kuma ya dake  ya ɗago ya kalleta tuna a gaban Salmah suke kar ya yi abinda za a yarfa shi, Salmah ta sake raina shi “ Na'am Mother.“ ya amsa da wata kamillayar murya mai  cike da nutsuwa, wacce Mother bata san shi da shi ba, yana wani kame fuska. Zancen da za ta yi ne ta nema ta rasa saboda mamaki “Ikon Allah sai kallo.” Mother ta faɗa a ranta tana riƙe haɓa, sai kuma ta mike ta yi kitchen ɗin  da kanta. Tana tashi Suraj ya zauna kusa da Salmah, da tunda ta shiga ko gefen da yake bata kalla ba, tana nan a kan bakanta na alkawarin da ta yi na daina sake mai fuska don taga rainin nasa na neman wuce gona.
“Welcome Salmahtah.” Ya furta ƙasa ƙasa, yi ta yi kamar ba ta ji ba, hankalinta na kan wayarta sai da ta kwashe kusan sakan talatin kafin ta  dago ta yi masa wata shegiyar kallo na tsantsar raini kafin ta ce, “ Thank you.” ba tare da kallesa ba. Murmushi ya saki mai taushi, don hakan da ta yi ba ƙaramin tafiya da shi ta yi ba. Dogon tsaki Salman da ke binsu da kallo ya ja cike da takaici kafin ya ce, “Ku wai ina Aysha?”  sai lokacin gaba ɗaya hankalinsu ya kai ga rashinta, Salmah ta yi tsammanin ta ɗan tsaya wani abu kamar amsa call haka shi yasa bata biyo su ba, kasancewar kuma tana fushi da ita akan dan hatsaniyar da suka yi a hanya, yada bata koma ta jira ba ta yi shigowarta. Sai dai yanzu da Salman ya yi magana hankalinta ya rabu, domin koma mai ta tsaya yi zuwa yanzu ya ci ace ta shigo ai. “Bata shigo ba, ban san me ya tsayar da ita har yanzu ba, ko zaka duba.” “Wace ce?” Mother da ta dawo dauke da tiren ruwa da drinks, ta tambaya. “ Aysha yar uwarmu ce tare muke, kuma mun ga har yanzu bata shigo ba.” “ Ah ahh, maza dubo ta Suraj ko lafiya.”  kafin ma ta gama maganar Salman ya mike don haka suka fice tare da Suraj ɗin.
Fitarsu kamar da minti shida, su ka dawo, da damuwa a fuskokinsu, Salmah ce kadai a falon don Mother data ajiye tiren ta koma kitchen, “Ba mu ganta ba fa.” Salman ya fada yana kallon Salmah, “ Kamar ya? ” “ Kamar yadda ki ka ji, kuma har megadi mun tambaya.” Murmushi ta yi Irin na an raina ma mutum wayon nan,  ganin hakan yasa Salman ya kara cin serious ya ce, “ Ke wallahi da gaske fa na ke yi.” wannan karon Dukansu suna ɗunguma duka sake komawa wajen don sake dubata.


A daidai wannan lokacin ne, motar su Ussy ta faka a tsakiyar farfajiyar katafariyar gidan AA dake by pass. Jarumi ne ya fito kamar ɗazu ya bude bayan motar, ya watsa mata idanunsa masu ban tsoro kafin da dakakkiyar muryarsa ta garada ya ce, “Fito.” idanunta da suka rine suka juye lokaci guda daya dai babu ɗigon hawaye a cikinsu ta watsa mai, a daidai wannan lokacin tabbas da za a tsaka jikinta za a iya ganinsa a bushe babu jini saboda matsanancin Firgici da tashin hankalin da take ciki, zuciyarta kuwa kamar zata faso kirji, amma saboda karfin hali fuskarta a bushe, ko ƙadan yanayinta bai nuna hakan a zahiri ba...



Ku yi hakuri babu yawa, yau na fita, da kamar ma ba zan yi ba, na ce dai bari na daure ko yaya ce, mu tara gobe da yardar Allah.