Chapter 7
Book 1
Chapter 7
Shigowa yayi kamar wanda bai san rahama ba a fuskarsa. Ko dan Firdausi bakuwa bai sa ya sassauta fuskar tasa ba. Haka ya shigo kamar wanda ba zai taka kasa ba. Firdausi ta miƙe tsaye tana kallon Zahra tace, “Zahra bari na tafi kawai.”
Zahra ta riƙe hannunta haɗi da zaunar da ita tace, “Ke kuma kawai sai ki wani tashi kice zaki tafi bayan muna kan magana?”
Wani banzan kallo Khalil ya watsa mata, sai da ya zo dab da ita sannan yace, “Ke wacece wannan?”
Wani kallo Zahra ta watsa masa tace, “Firdausi ce, yau zaka ce baka santa ba?”
Firdausi kam murmushi take yi tace, “Sannu da zuwa, ina wuni Ya Ibrahim.” Ta kare maganar tana ɗaukan jakkarta.
Ko amsa mata bai yi ba, still yana kallon cikin idon Zahra yace, “Bana son kina tara min mutane a cikin gida. Ya kamata ki sani nan ba dandali bane.”
Zahra ta miƙe zata yi magana amma Firdausi tayi saurin hana ta, sannan ta juya ta fita.
Tuni ya juya ya fara hawa stairs, ita kuma ta fara binsa a baya tace,
“Khalil wai wannan wani irin hali ne ka tsiro da shi? Abin naka ya fara yawa. Tun ya tashi akaina ya koma kan Yaya na, yanzu har kawaye na basu tsira ba. Ba zaka yi abin da at least mutane ba zasu zage ka ba? Gaskiya I'm tired of your bad attitude.”
Ya juya yana mata wani shegen kallo yace, “Okay, tunda kin gaji it's fine, zaki iya kwasan kayanki ki koma gidan ku.”
Mutuwar tsaye Zahra tayi a inda take tana kallon bayansa daya cigaba da hawa stairs har ya gama hayewa.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...” kawai ta iya furtawa.
Kukan ma da take son yi taji ba zata iya ba. Kawai ta juya ta wuce ɗakinta. A hankali ta zauna bakin gado tana sake narrating abin daya faru. Ita har sannan kamar a mafarki take ji. Me ta ma Khalil haka mai zafi? Yanzu abin nasa ya fara yawa.
Kifa kanta tayi wasu hawaye masu zafi suka zubo bayan ta tuna da abin da bata kaunar tunawa a rayuwarta.
Da daddare tana zaune a parlorn sama taji karar shigowarsa, kuma dama tana tunanin tun ɗazu daya zo bai fita ba sai sallah. Ita dai idonta na kan TV amma bata san me guda ɗaya ake yi ba.
Haka ya shigo ta gabanta ya wuce zuwa ɗakinsa. Ta ɗaga ido ta bishi da kallo. Can ya sake fitowa ya shigo ya zauna a hannun kujerar dake opposite ɗin nata.
Kai tsaye yace, “Zan yi tafiya gobe In Shaa Allah. Ba zan dawo ba sai bayan sati ɗaya. Wani aiki ne ya taso min shine zan tafi India.”
Tace, “Kai kaɗai zaka tafi ba tare da ni ba? Why not na shirya mana tunda sati ɗaya ne kawai zaka yi?”
Wani kallo ya watsa mata yace, “Idan da ke zan tafi ni ba zan sani bane ko ba zan faɗa miki bane? Tunda kinga ban ce tare zamu tafi ba, ki sani cewa wannan tafiyar ta wajen aiki ce.”
Ta sauke idanunta kasa ta kasa cewa komai.
Ya miƙe zai tafi tace, “Ina bukatar kuɗi toh”
Wani irin juyowa yayi yana kallonta yace, “Shi Yayan naki ba zai iya baki bane?”
Tsabar ɓacin rai Zahra bata san sanda tace, “Saboda Yayan nawa nake aure shiyasa kullum zan tambayesa kuɗi ai?”
Yace, “Ke kika sani. Ni yanzu tafiya ce a gabana. Kayan abinci kuma babu wanda babu a cikin gidan nan, dan haka wannan wasan da kika saba da kuɗi zaki dakata da shi.”
Ta miƙe tsaye tana kallonsa tace, “Ai ba haka na saba rayuwa a gidanmu ba.”
Yace, “Ai ke ma kika ce gidan ku. Kinga nan ai ba gidan ku bane.”
Tace, “Wai Ibrahim ka manta sanda ka zo gidanmu kana roƙon a baka ni ne? Ka manta sanda kake roƙona don Allah na baka soyayyata? Ka manta sanda kake min alƙawuran zaka kula da ni ka bani dukkan farin ciki? Ka manta sanda kace ba zan taɓa buƙatar wani abu na rasa a gidan ka ba? Amma yanzu ina guda ɗaya a cikin waɗannan alƙawuran da ka cika? Ka tausaya min, kaji tsoron Allah. Ko hakkin alƙawari zai iya bin ka.”
Juyawa yayi ba tare daya ce mata uffan ba. Ita ma ta wuce nata ɗakin tana jin yadda zuciyarta ke ƙuna.
Bayan ta gama shirin bacci zata kwanta kenan taga alert na 1 million. Ganin sunan tayi dan duk tunaninta daga Khalil ne, amma sai taga akasin haka, daga Ya Umar ne. Kawai taji hawaye. Ashe naka ne ba zai taɓa gajiyawa da kai ba. Yau take jin dama bata yi wannan auren ba.
A hankali tasa hannu tayi dialing numbern Ya Umar.
Yana ɗagawa abu na farko daya fara furtawa, “Baby kiyi haƙuri da little abin dana baki. Ina expecting kuɗina cikin week ɗin nan zaki sake jina.”
Tace, “Thank you so much Yaya. A'a wannan ba little bane. Allah saka.”
Yace, “Ameen. Good night.”
Daga haka ya katse. Tana son basa hakuri amma tana tsorom ko yana cikin mutane, tayi deciding zuwa gida da kanya
Kiran Firdausi tayi. Tana ɗagawa bata barta tayi magana ba tace, “Please Firdausi kiyi haƙuri. Ni kaina bansan ashe haka Khalil yake ba.”
Firdausi tace, “Ba komai, amma tabbas abin ya fara bani tsoro. Sai kace ba mu bane muka zo ranan harda tsokarmu, sai kace ba mu bane yake roka mu taya sa samun ki. Ya Khalil dana sani yana fita da mu outing, har restaurant a school tare da mu, wai shine zai min haka? Tabbas yau na ƙara tsorata da maza. Amma please ki kwantar da hankalinki.”
Zahra tace, “Gobe zai yi tafiya. Please ki zo ina so muyi magana.”
Firdausi tace, “No, it's better mu haɗu a school tunda zaki shigo.”
Tace, “Toh shikenan. Ki ƙara haƙuri please.”
Tace, “Ba komai, sai da safe.”
Firdausi na kashe kiran ta kalli Mama tace, “Mama da gaske Zahra tausayi take bani.” Ta kare maganar tana share hawayen daya zubo mata.
Mama tace, “Itace ta kira yanzu?”
Firdausi tace, “Eh. Mama kuma kin san Zahra kwata-kwata bata gane mai sonta na gaskiya. Kin san yanayin rayuwar data taso, bata san wani abu wai shi wahala ba. Shiyasa yanzu take bani tausayi. Ni damuwata kar taje ta saka ma kanta hawan jini ne.”
Mama tace, “Idan abin nasa yayi yawa ta samu iyayensa farko kafin ta fara magana a gida. Amma yanzu ki bata shawarar ta same shi lokacin da yake cikin farin ciki ta tambayesa me ta aikata masa. Idan ma ya ƙi cewa komai ta basa haƙuri jikinsa zai yi sanyi.”
Firdausi tayi murmushi tace, “Mama baki ga yadda yayi min bane ɗazu? Ashe haka yayi yiwa Yayanta Umar?”
Mama tace, “Ikon Allah, aure tun bai tafi ko'ina ba? Toh ko dama ɗan iska ne ba'a sani ba.”
Firdausi tace, “Shiyasa tun farko bamu son sa, amma ganin tana son sa kuma ba mu zamu zauna da shi ba shiyasa muka ja bakinmu muka yi shiru.”
Duk shiru suka yi.
Firdausi ta ɗaura, “Mama baki ga yadda Zahra ta koma ba? Mace mai son kwalliya da ado amma gaba ɗaya yanzu babu wannan vibes ɗin tare da ita.”
Mama tace, “In Shaa Allah ko dan kyawawan halayenta Allah ba zai barta cikin wannan damuwar ba. Tunda ita mutum ce mai son cire mutane a damuwa, wannan jarabawarta ce. Allah shiryesa shi kuma.”
Ta amsa da, “Ameen.”
Wasa gaske har ƙarfe uku bacci ya gagara ɗaukan Zahra. Ta miƙe zaune ta wuce toilet. Alwala tayi ta fito tayi raka'a biyu. Bayan ta sallame, ta daɗe tana addu'a. Daga ƙarshe ta ɗauki Qur'ani ta fara karatu. A haka har aka yi sallar Asuba. Bayan ta idar ne, data kwanta nan da nan bacci ya kwashe ta.
Wajen ƙarfe 8:40am ta farka. Data miƙe taji wani irin jiri yana shirin ɗibarta, da sauri ta dafe bango ta zauna. Ta daɗe tana zaune a wajen, can daya yi sauƙi ta miƙe ta wuce toilet. Brush tayi, tayi wanka sannan ta fito tasa kaya ta wuce dining. Cornflakes kawai tasha dan bata jin zata iya girki. Already ma tasan tayi late before ta tafi.
Tana gama sha ta kai cup ɗin kitchen ta wanke sannan taje ta ɗauki school bag ɗinta tare da keyn motar. Da ƙyar ta tada motar don yadda take ji a jikinta. Bata son ta zauna a gida tunani ya addabeta, da ba zata school ba.
Parking motarta tayi a bakin department sannan ta sauka ta wuce ciki. Tun daga yadda ta kalli wajen babu mutane sosai tasan cewa sun fara lectures. Ta shiga ta back door.
Bayan 3 hours lectures suka gama. Suhaima, Asiya da Firdausi suka ƙaraso inda take dan a baya ta zauna.
Asiya tace, “SubhanAllah, amma baki da lafiya ne Zahra?”
Murmushi ta mata kawai.
Suhaima tace, “Ko ɗan Baba ne ya fara baki wahala tun yanzu?”
Tace, “Wai ku ɗauka kuka yi ciki gareni? Lallai baku shirya ba ma.”
Class rep ne ya ƙaraso wajenta yana mata kirari. Tayi murmushi tace, “Kai dai Class Rep ba'a rasa ka da tsokana.”
Yace, “Ba haka bane Hajjaju. Nace ko zamu je ki kalli practical ɗinki ne? An gama cire result yanzu saura miki chapter 5 a project. Ina gama haɗawa zan turo miki sai ki bawa supervisor ɗinki ya duba miki, idan da gyara mu gyara.”
Tayi murmushi tace, “Class Rep bana jin daɗi. Duk yadda kayi yayi dai-dai. Nagode sosai. Opay ne ko First Bank?”
Yana murmushi yace, “Opay ne Hajiya.”
Kai ta gyaɗa masa. Ya juya ya fita yana godiya.
Shiga mobile app ɗinta tayi, nan take ta masa transfer ɗin 50k sannan ta jefa wayar cikin jaka ta ɗago tana kallonsu tace, “Ya muke ciki yanzu?”
Suhaima tace, “an gama lectures na yau fa, dan kamar Prof ne kawai yace zai yi lectures yau.”
Ta miƙe tace, “Firdausi ko zamu wuce off camp kafin mu tafi gida? Ko da akwai abin da zaki yi ne a gidan yanzu?”
Tace, “Nope, mu tafi mana.”
Haka suka fita dukkansu direct wajen motarta suka nufa. Daga nan ta jasu zuwa University Villa, wannan gidan sai 'ya'yan wane da wane suke kama wa. Nan Zahra take kama musu ita da friends ɗinta tun suna 100 level.
Shiga cikin estate ɗin tayi da motar har dab da room ɗinsu sannan tayi parking. Duk suka sauka. Asiya ta buɗe musu ƙofa duk suka shiga cikin ɗakin
Zahra tayi murmushi tace, “Wai rabona da nan har na manta.”
Dariya suka yi. Ta wuce ta kwanta kan gado.
Suhaima tace, “Zahra me zaki ci sai mu dafa?”
Tace, “Anything please.”
Firdausi sai kallonta take yi, musamman idanunta wanda kallo ɗaya zaka mata kasan ko kuka tayi ko rashin bacci.
Tana kwanciya nan da nan bacci ya kwashe ta. Can wajen Azahar ta farka, nan ma sanadiyyar kiran wayarta da ake yi ne. Ta ɗaga taga Abbah ne.
Da murmushi a bakinta tace, “Abba na.”
Yace, “Na'am Baby na, duk da ma Baby ta manta da Babanta.”
Dariya tayi tace, “Abba ba haka bane fa. Ba zaka gane bane Abba amma kullum kana raina.”
Yace, “School ɗin ne?”
Tace, “Eh Abba, yanzu haka ma ina school.”
Yace, “Allah taimaka. Bari sai kin koma gida, just concentrate.”
Tace, “Thank you.”
Yana kashewa ta miƙe ta wuce toilet. Bayan ta fito da alwala zata yi sallah Asiya tace, “Na saka miki abinci yanzu kafin ki idar?”
Tace, “Eh, amma ki haɗa da tea please.”
Suhaima tace, “Sai dai kije ki saya sugar a waje dan ƙarshen na sha ɗazu”
Asiya tace, “Alright.”
Kafin ta idar da sallah har Asiya ta shigo ta saka mata abincin. Bayan nan basu wani daɗe ba suka tafi.
A hanya Firdausi tace, “How far, yayi tafiyar ne?”
Tace, “Ina zan san masa? Dan wulakanci ko sallama bai min ba.”
Firdausi tace, “Call him now. Ki tambaya ya isa lafiya dan wannan hakki ne a kanki.”
Tace, “Okay.”
Kiran sa tayi while tana tuki. Yana fara ringing ya ɗaga.
Tace, “Noory...”
Yace, “Uhum.”
Ta ce, “Tafiya ba sallama?”
Yace, “Naga kamar ranki a bace yake ai jiya.”
Tace, “Amma at least koma menene na tafi idan ka faɗa min ai da daɗi.”
Yace, “Enough! Bana son wannan unnecessary drama naki.”
Tayi shiru kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace, “Ka isa lafiya?”
Yace, “Lafiya kalau.”
Tace, “Toh Ma Shaa Allah, dama na kira naji ne.”
Yace, “Alright.”
Daga haka ta kashe kiran ta juya ta kalli Firdausi.
Firdausi tace, “Zahra no matter what kar ki daina sauke haƙƙinki a kansa. Ki ci gaba da haka. Kinga yanzu shine right time da zaki yi gyara kafin ya zo.”
Tace, “Kinsan Allah ko saboda mugun halinsa ji nake kamar na fasa. Yanzu ya fara fita min a rai wallahi.”
Firdausi ta gagara cewa komai.
Ta wuce taje tayi dropping ɗinta a ƙofar gidansu sannan ta ja motar zuwa nasu gidan. Bayan tayi parking ta sauka sai ga Ya Umar ya fito zai fita Batoul a bayansa.
Tayi saurin riƙe masa hannu tace, “Yaya minti ɗaya mana.”
Yana kallonta da kamar ba zai ce komai ba sai ya matsa gefe, ita ma ta bishi.
Tace, “Ya sorry da abin daya faru. Ba zan iya ce maka sorry a waya bane amma dan Allah kayi haƙuri.”
Ya ɗaga mata gira ɗaya yace, “Akwai abin daya faru ne?”
Tace, “Haba Yaya, abin daya faru jiya mana, kai da Khalil.”
Yayi murmushi yace, “Zahra ban san yaushe kika fara ɓoye min abu ba. Ni nasan kin san cewa nasan kina cikin damuwa amma kika zaɓi shiru. Yes, it's good kin fara haƙuri, amma ki sani ba zan yarda wannan banzan ya cutar da ke ba. Ki je kiyi tunani if you're ready to voice it out. Ni damuwata bana son ganin wannan damuwar a tattare da ke Zahra. I can't take it anymore, naga wani yana cutar mana da ke.”
Ta sauke idanunta kasa tace, “Nagode. Sai kun dawo naga fita zaku yi da Ya Batoul.”
Daga haka ta fara tafiya tace, “Ya Batoul ina wuni?”
Ba tare data ɗaga kanta daga wayar da take daddannawa ba tace, “Lafiya.”
#Jiddatulkhayr writes
#***