LULLUƁIN BIRI

32

by @halimahz

Boɗejo zaune kan kujera a babban parlon Mai Martaba ta ce,"Ah tou ni ɗin dai na gama magana. Idan kuma kun lalace ne to sai na ji, amma batun auren Ilham da Ɗan'uwanta wancan kumburarren babu wanda ya isa ya hana sai dai ko bayan raina, sai in kuma ikon mai sama".

Mai Martaba ya sauke numfashi ya ce,"Amma Hajjah...". Da sauri ta katse shi,"Hashim kai kaɗai ne mau shegen taurin kan da ba zaka tuba ka daina kirana da Hajja ba ko? Kasan Allah kar ka bari raina ya ɓaci akanka, ya na zo ina batun haɗa yara aure kana ce min ba haka ba, yanzu kuma kana ƙara kirana da sunan da ka san bana so".

Cikin kwantar da murya Mai Martaba ya ce,"ki yi haƙuri". 

Boɗejo ta ƙara haɗe rai ta ce,"Ka riƙe haƙurinka. Mu yi batun da ya kawo ni wajenka, ba tun yau nake faɗa ba sai dai zan ƙara nanatawa ina so ku haɗa Muhammadu da Rumana aure, in kuma ban isa ba sai in ji". 

Baffa ya ɗago kai ya kalleta ya ce,"Balle ma kin isa Boɗejo, sai dai kawai ya kamata ayi duba a lamarin, tun da bamu san ba ko su yaran nan za su so haɗa su auren da za ai".

Mai Martaba ya ce,"Abin da nake so ki fahimta kenan Mama, zamanin yanzu ba ɗaya bane da na da, yanzu ba'a haɗa yara aure gudun abin da ka iya zuwa ya dawo a zamantakewar ta su muddin babu soyayyar junansu, amma kuma idan aka tabbatar da yaran nan suna son junansu shikenan salamun alaikum, mu kanmu ba ƙaramin farinciki zamu yi da hakan ba".

Boɗejo ta tafa hannu tana salati kafin ta ce,"Na shiga uku, Hashim yanzu al'adar tamu zaka rushe? Kai kasan a yadda aka yi aurena da ubanku kuwa? Tabɗijam, to da kasan ta yanda aka laliƙa min ubanka na aura da baka zo min da wannan ƙabali da ba'adin ba. Shashashan sarki kawai, kai idan akai hakan ma ba ƙarfafa zumunci aka yi ba, amma kana batun wani idan ba sa son junansu, a'a to da ƙiyayyar junansu suke yi? Ko an faɗa muku su irin ƴan'uwan mahaifinku ne kafin su tuba, kai gaskiya Hashim kana da gurɓataccen tunani, wai idan basa son junansu! Maganar nan na ka har ga Allah ya yi min zafi, to kar ka ƙara wallahi, don ni dai kaf jinina babu mai mugun hali, kowa son ɗan'uwansa yake yi. Tsakani da Allah ina Turaki zai ce baya son Ilham ƴar'uwarsa? Kuma itama ta ina zata ce bata sonsa yarinyar da kullum zancenta akansa yake, babu fitowar rana da faɗuwarta da ba zata ambaci sunansa ba, dan ma dai waccan uwar tata mai baƙin hali da mugun nufi na hanata zumunci da shi, to a gaskiya indai ana so aga dai-dai abi umarnina kawai, auren nan yinsa za'ai babu wani zaman tuntuɓe-tuntuɓe balle asa min ɓacin rai".

Mai Martaba zai yi magana ta ɗaga masa hannu,"A'a dakata, dakata ba sai ka ce komai ba. Ɗaga waya kawai ka kira min Hakimi ya zo yanzun nan, ban sani ba ko haɗe kanku ku ka yi kuke so ku nuna min kune kuka haifi yaran nan, ni banda wani hurumi da su, in haka ne kuwa sai in kama gabana na barku da halin bijirewa maganata".

Baffa ya tausasa murya ya ce,"Ba bijire miki zamu yi ba Boɗejo, zamani muke so ki duba. Kuma mu ma fa bamu ce ba za a yi hakan ba, ce muka yi a fara jin ta bakinsu tukunna, idan sun amince da junansu mu abin farinciki ne a wurinmu wallahi".

Boɗejo ta jijjiga kai ta harɗe ƙafafu ta ce,"To bara ka ji Dikko, tun da uwata ta haife ni ban taɓa ganin Ubanku ba sai a ranar da aka kira ni aka yi min zancen aurenmu da shi. Ina zaune lafiya daga zuwa na gaida mahaifiyata zanyi kwana uku a wurinta sai Kakanku yasa Babana ya doka min kira wai in je fada ana nemana, kai kasan tashin hankalin da mahaifiyata ta shiga a dalilin wannan kiran kuwa? Saboda kiran fada bai cika zama alkhairi ba, ina zuwa ga Babana Waziri ga Mai Martaba ga Ubanku a zaune aka ce ga mijin da aka yi min, kuma a gobe za'a ɗaura mana aure. Yo da ike ni mai biyayya ce ban bijire ba daga ni har shi uban na ku, hasalima shi tausata yake yana cewa mu yi haƙuri mu bi umarnin iyaye zamu ga ribar hakan, to da na aure shi Dikko mutuwa na yi ko me ya same ni? Ga shi nan dai ku huɗu na haifa jeras tare da shi, idan bana sonsa zan bari a haife ku ne?. Sai akan ƴaƴanku za ku ce ba haka ba, Turakin ma da wancan algungumar Azimar ta raine shi, Turaki fa har goya Ilham ya yi, to banda dai rashin tsoron Allah irin na ku ina ku ina cewa ba ya sonta?
Ku dai ku ke kyautata zato akan abu, ba wai kowa yake hasashe mara kyau ba. Na tabbata babu abin da zai sa yaran nan suƙi amincewa muddin kun nuna musu kuna so, banƙi ba shi ɗan naka ya iya botsarewa, to amma shima na san na ƴan mintina ne tun da yana da ladabi, kana cewa haka ka ke so ba zai ja ba zai ce ya amince, sai dai idan kuma a munafurce ni a hure musu kunne".

Daga Baffa har Mai Martaba babu wanda ya ƙara yin magana, Boɗejo ta tafa hannu wani bafade ya shigo parlon yana zubewa a ƙasa.

Ta ce,"Maza kira min sarkin gida". Fitarsa babu jimawa sai ga sarkin gida ya shigo, ya zube a gaban Boɗejo ta ce,"Ɗau waya ka kira min Hakimi".

Sarkin gida ya kira wayar Hakimi da wayar Mai Martaba, bugu ɗaya biyu ya ɗaga. Ya yi saurin miƙawa Boɗejo. Ta karɓa tasa a kunne, bayan sun gama gaisawa ta ce,"Ka na jina?".

A ladabce ya ce,"Ina jinki ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon rai". 

Ta ce,"Amin, Allah ya yi maka albarka. Dama magana zanyi da kai".

Kamar yana gabanta saboda tsananin ladabi ya ce,"Tom shikenan, ɗazu an ce min kin fita, gidan Dikko zan zo ko fada?".

Ta ce,"A'a yi zamanka akan kujerarka. Dama batu ne na aure na zo maka da shi, ina so a haɗa auren Turaki da Ilham, ba kuma na so ya wuce wata guda, wata gudan ma saboda zan gyara jikata ne banda haka cikin sati ɗaya za'ai komai a gama".

Hakimi ya ce,"Tom shikenan ranki ya daɗe, za'a yi yadda kika ce. Allah ya tabbatar da alkhairi".

Ta ce,"Amin ya Allah". Da haka suka yi sallama, da yake a handsfree ta saka duk conversation ɗinsu su Mai Martaba sun ji.

"Da akwai wanda zai ja ne?". Ta faɗa tana kallon su duka. A tare suka haɗa baki wajen faɗin,"A'a, Allah yasa albarka ya kuma tabbatar da alkhairi". Tana nuna musu fushinta na gardarma da suka yi mata a farko ta ce,"Kai Dikko ka kira min Falmata yanzu a waya".

Baffa ya ɗau wayarsa ya kira Falmata ya miƙawa Boɗejo, sallamar Falmata kawai ta amsa ta ce da ita,"Anjima za'a kawo Ilham gidanki, ki gyarata gyara na ban mamaki Falmata, gyaran da ba zai sa Turaki ƙara kallon wata mace da sunan sha'awa ba har mutuwarsa, irin gyaran da ba zai so Ilham ta matsa a kusa da shi ba".

Inna Falmata ta amsa da,"Tom ranki ya daɗe".

Boɗejo ta dubi Mai Martaba bayan gama wayar ta ce,"Sai kuma me?".

Ya rissinar da kansa ya ce,"Ya kamata a sanar da Fulani Azima da kuma Madina". 

Boɗejo ta haɗe rai ta ce,"Ashe ma ba so na ke auren ya tabbata ba. Gwara ma in Madina ka ce, amma wace wata Fulani Azima?. To maganar aure dai cikin sirri na yi ta, ko yaran ba za su sani ba sai ranar ɗaurin aurensu, magana daga ni sai ku na yi ta, idan na ji ta a wani waje kuma wallahi tallahi akwai Allah".

Tana gama faɗar hakan ta miƙe. "Dikko tashi mu je gidanka zan wuce".