96
by @zahrabmrs02
Farhana tana shiga daki, ta ajiye jakar ta, sai wayarta ta fara rera muryar nishadi. Ganin sunan "Soul ❤️" ya sanya ta jin wani dadi ya ziyarci zuciyarta. Tana dagawa, muryar Farooq ta fito cikin wani irin shauki da damuwa.
"Baby girl... na shigo Nigeria jiya," Farooq ya fada, muryarsa tana dan rawa. "Amma wallahi hankalina ya ki kwanciya. Gani nake yi kamar Abdulkadir (AK) zai sake kwace min ke a karo na biyu. Farhana, wannan karon idan ya kwace ki, mutuwa zan yi murus."
Farhana ta lumshe ido, tana jin yadda bugun zuciyarsa yake ratsa wayar. "Babu wanda zai kwace ni Soul. We're meant to be this time around, Insha Allah. Ka kwantar da hankalinka, Maryam taka ce har abada."
Farooq ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce, "To yaushe kike so in shigo gidan? Domin tuni baba da waliyaina suka shirya, gobe Insha Allah zasu sauka a Abuja."
Farhana ta zaro ido saboda mamaki. "Gobe? Amma Soul... ba ka ganin kamar yayi sauri?"
"Babu wani sauri Baby girl," Farooq ya katse ta cikin zakuwa. "Ni so nake kawai a sa bikin nan nan da sati biyu. Na gaji da jiran ki. Zaman ki a Abuja ma ba tare da igiyar aurena ba risk ne a gare ni. So nake in ji kanki a gidana, sannan zan iya barin ki ki cigaba da tuka jirgin ki cikin kwanciyar hankali. Auren ki nake son yi
Farhana ta yi murmushi, fuskarta cike da kunya duk da cewa ba ya ganinta. "Sati biyu fa Soul? To Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Zan gaya wa Abbi da Diddi."
Bayan sun gama waya, Farhana ta fito palo ta iske Diddi tana gyara wasu kaya. Ta zauna kusa da ita, muryarta a sanyaye.
"Diddi... Farooq ne ya kira. Ya ce gobe waliyansa zasu zo Abuja ganin Abbi. Kuma... yana so a sa auren nan nan da sati biyu."
Diddi ta ajiye kayan hannunta, ta kalli Farhana da murmushi. "Sati biyu? Lallai Farooq . Amma gaskiya ne, zaman ki a haka yana damun sa, musamman yadda Abdulkadir yake ta kai-da-komawa a gidan nan. Bari Abbi ya dawo mu tattauna, , Allah ya sanya alkhairi."
Sajid dake gefe yana sauraren su, ya kyalkyale da dariya. "Wato Farooq bada wasa yazo ba. Ya san cewa idan bai yi sauri ba, mutanen Matazu (su Nene) zasu iya dagula masa lissafi. Maryam, ki fara shiri kawai, domin satin nan Abuja zata rude da maganar auren Captain
Ba tare da an sanar da Nene ba, waliyan Farooq suka sauka a Abuja. Abbi da Hamma Fahad ne suka tarbe su cikin girmamawa. Yarjejeniya ta tabbata, inda waliyan Farooq suka ijiye Naira Miliyan Uku a matsayin sadaki da kudin sa rana.
Abbi da Hamma Fahad sun dan tsorata da yawan kudin. "Gaskiya wannan kudin sun yi yawa," Abbi ya fada. Amma waliyan Farooq suka nace, "Ai Farooq ya ce wannan kadan ne ga darajar Farhana." A karshe dai aka tsaida sati biyu a matsayin ranar daurin aure.
Farhana ta fara shirye-shiryen ta a boye. Domin guje wa sa-idon Nene da kalaman ta, Farhana takan sulale ta tafi gidan Adda Sabrina don yin gyaran jiki na musamman. Kamshin daka da turaren wuta ya fara ratsa fatar ta, duk da tana kokarin boyewa.
Sati daya ya rage biki, Farooq ya riga ya buga katin gayyata na alfarma.
"Soul, yanzu ni da girma na za a yi wasu events a Kaduna?" Farhana ta tambaya ta waya, tana tunanin nauyin taron.
Farooq ya yi dariya, "Duka nawa kike Farhana? Kin manta da wuri kika yi auren fari? You're 25 fa. Kawayen ki da yawa ma ko auren farko ba su yi ba. Wannan shi ne aurena na fari, don haka dole mu yi murna."
Su Husna da Safina (yayun Farooq) suka iso Abuja dauke da akwati guda goma sha biyu (12). Lefen ya kasance na gani na fada, cike da leshi da da kayan ado na alfarma. Sun yi watsi da maganar wata Khairi da suka so su hada shi da ita a baya, domin sun ga yadda Farooq yake son Farhana
Bayan sun tafi, akwatunan suna jere a falo, sai ga Nene ta fito tana dingisa kafa , ta zaro ido
"Wai ni zaku fada min lefen waye wannan ko kuwa shiru zaku yi min?" Nene ta tambaya cikin fada.
Sameena dake gefe tana kallo, ta kada kai ta ce, "Lefen Adda Farhana ne Nene."
Nene ta taba baki, "Au, shi Abdulkadir din har wani lefen ya kara mata? Lallai ya matsu ya mayar da ita."
Sameena ta yi dariya, "Bafa shi zata aura ba Nene. Wannan lefen daga wajen Farooq yake."
Nene ta saki robar hannuta , ta koma ta zauna a kujera tana salati. "Farooq? Wane Farooq din? Wato Ibrahim ya gama magana da ni ya je ya bada auren yarinyar nan ba tare da na sani ba? Kuma shi Abdulkadir din ya sani?"
Diddi ta fito daga daki, ta kalli Nene cikin natsuwa. "Nene, lokaci ya yi da zaki bar Maryam ta huta. Wannan auren na Allah ne, kuma gashi nan cikin girmamawa aka kawo lefe. Ba kamar na AK ba ne."kuma dan Allah kar ki sanar da Ak maganar auren nan sameena tace a gefe guda
Nene ta daka tsawa, "To wallahi sai na sanar da shi Abdulkadir din! Ba za a yi wannan cin amana da ni ba!"
dauke wayar nene sameena tayi inda nene ta dinga tofin ala tsine akan wayarta zata kira Ak dashi
Falo ya rude da guda, Sameena da kawayen Farhana suna ta faman murna. Farhana tana daki, tana sanye da wata lallausar laffaya, jikinta duk ya yi sanyi saboda nauyin kalmar "Aure" da ta sake dawowa kanta. Tana cikin wannan tunanin, wayarta ta fara kiran "Soul ❤️".
Ta daga wayar, amma shiru... kowa ya kasa magana na tsawon wasu dakiku. Daga karshe, Farooq ya sauke wani nannauyan ajiyar zuciya wanda ya ratsa ta cikin wayar.
Farooq: "Baby Girl... ko ince Mrs. Farooq?"
Muryarsa ta fito a dishe, cike da wani irin shauki dake nuna cewa har kuka ya kusa yi saboda farin ciki.
Farhana: (Muryarta tana rawa) "Soul... har yanzu na kasa yarda
"Wallahi ni ma Maryam. Tsorona daya ne tun safe, kar in farka in iske ashe mafarki ne. Amma an daura , na tabbatar Allah ya karbi addu'ata. Farhana, kin san me hakan yake nufi? Daga yau, babu wani mutum dake da iko akanki sai ni. Babu wani AK da zai sake nuna miki isa ko ya tursasa ki. Ke tawa ce yanzu."
Insha Allah Soul. Na gode da baka taba barina ba, koda a lokacin da na fada cikin ramin duhu."
A'a Maryam, ni zan gode miki da kika ba ni damar in zama mijinki. Ina so ki sani, ba zan taba zama kamar yadda kika sani a baya ba. Zan zama garkuwar ki, zan zama babban masoyin ki, kuma zan rinka alfahari da ke a matsayin Captain dina. I love you more than words can say, My Wife."
Hawayen dadi ne suka wanke fuskar Farhana. Wannan kiran ya wanke dukkan dacin da take ji na zancen Nene da tsoron AK.
Gidan su Farhana ya cika da mutane kadan, 'yan uwa da abokan arziki na kusa kamar su Fateeha, Precious, da Hamma Fahad. Farhana tana zaune cikin adon ta na amarya, tana tunanin yadda zata koma Boston ta ba su Isabella da Hailey labarin auren ta da Farooq.
Ba zato ba tsammani, sai ga Farooq ya shigo dakin da wani irin murmushi mai ma'ana. A bayan sa kuwa, wasu fuskoki ne wadanda Farhana ba ta taba tsammanin gani a Najeriya ba a wannan lokacin.
Farhana ta mike tsaye, ta kasa rufe bakinta saboda tsananin mamaki. Isabella, Hailey, da Zayd ne a tsaye, suna ta faman fara'a. Harda Kevin!
"Surprise!" Isabella ta fada da karfi, tana ware hannayenta.
Farhana ta kasa magana, kawai sai ta ji hawayen dadi suna zuba a fuskarta. Da gudu Isabella da Hailey suka rungume ta, suna murnar ganin kawarsu ta zama amarya.
"We couldn't let you do this alone, Captain!" Hailey ta rada mata tana dariya. "Farooq ya shirya komai, ya ce dole mu zo mu shaida wannan rana."