98
by @zahrabmrs02
Ayarin motocin sun ɗauki hanyar Kaduna cikin natsuwa. Su Isabella da Hailey suna maƙale a jikin windows na motar, idanunsu cike da sha'awa. Duk lokacin da suka wuce wani ƙauye (village), sai su fito da wayoyinsu suna bidiyo.
"Maryam, look at those houses! They are made of red mud! It's so beautiful and artistic," Isabella ta faɗa cikin zumuɗi yayin da take kallon gidajen ƙasa na wasu ƙauyukan da suka wuce.
Farhana ta yi murmushi, tana ba su bayanin cewa waɗannan gidajen sune asalin gine-ginen gargajiya waɗanda suke sanya sanyi a lokacin zafi.
A ɗayan motar kuwa, Zayd da ne tare da su Hamma Fahad . Zayd, wanda ya saba da gine-ginen zamani na Dubai da Amurka, ya zuba ido yana kallon yadda rayuwar ƙauye take gudana a Najeriya. Ganin yadda mutane suke gudanar da kasuwanci a bakin hanya da yadda yara suke wasa a cikin gidajen ƙasa ya ba shi mamaki ƙwarai.
"The soil is so rich," Zayd ya faɗa wa Hamma Fahad. "And the people look so energetic despite the heat."
Suna isa Kaduna, aka wuce da su zuwa wani babban masauki (guest house) na alfarma wanda Farooq ya kama musu. Masaukin ya cika da duk wani abun jin daɗi, inda aka ware wa su Isabella ɓangarensu, su kuma maza ɓangarensu.
Karfe 2:00 na Rana:
Kowa ya fara shiri domin taron Kamu da za a fara da ƙarfe 4:00. Adda Sabrina da Precious suka shigo da masu makeup
"Oya, maza-maza amarya da kawayen amarya! Lokaci yana tafiya," Precious ta fada tana zama a kujerar makeup din
Taron Kamu ya kankama a cikin babban dakin taron (hall) da aka kawata shi da launuka masu kyau da ratsin purple Su Isabella da Hailey sun bude baki suna kallon yadda aka tsara wurin.yadda aka jera kumbo manya manya
"The decoration is top-notch! I’ve never seen anything like this," Isabella ta fada tana zare ido.
Aka sa kida mai ratsa zuciya. Adda Sabrina da Hailey ne suka rike Farhana a tsakiya, wadda aka rufe fuskarta da wani siririn mayafi na net mai kyalli. Takunta daya-bayan-daya yana nuna kwarjini da natsuwa har zuwa sit dinta .
Mamma (mahaifiyar Farooq) ta karaso cikin fara’a, ta biya kudin "bude fuska" kamar yadda al'ada ta tanada. Sanda aka yaye mayafin, Mamma ta kalli fuskara Farhana, sai ta ji wani irin dadi ya ziyarci zuciyarta.
"Masha Allah! Maryam din Lamido, Allah ya yi miki albarka," Mamma ta fada, ta kasa rufe bakinta saboda murnar ganin kyan da Allah ya ba surukarta. Auren ya kasance tamkar na budurwa, domin daukakar ta sanya kowa mantawa da cewa wannan ne auren Farhana na biyu.
Bayan an zauna, aka fara raba abincin Najeriya kala-kala. Su Isabella basu yi kasa a gwiwa ba, suka fara dandana pounded yam da egushi ,masa kunun aya zobo harda fura da nono , da kuma shinkafa da hanta.
"Wow, this spicy rice is everything!" Hailey ta fada tana share gumin dadi.
Farhana tana tsaka nishadi ta sai ta ji an dafa kafadarta a hankali. Ta juyo da sauri, idanunta suka sauka a kan wata kyakkyawar mace dake dauke da wani kyakkyawan jariri a hannunta.
Nusaiba!. Ganin ta da jariri a hannu ya sanya Farhana mikewa tsaye cikin mamaki da murna.inda ta bar sit din amarya ta ja ta gefe ,already dama hankalin mutane na kan abinci a hall din
"Nusaiba? Ke ce?" Farhana ta fada muryarta na rawa.
Su Fateeha da Precious suka rugo da gudu sanda suka gane wacece. wajan ya rude da murnar haduwar kawaye. Nusaiba ta yi kyau sosae, daga gani cikin jin dadi take
"Maryam, na ji labarin daukakar ki a matsayin Pilot, a bakin mamma kuma naji dadin ganinki matsayin amaryar Farooq Na yi kewarku sosae," Nusaiba ta fada tana kuka.ki yafe mana nusaiba dan Allah kawayen suka fada suna rungume juna
An dauki hotuna na musamman (pics sau 4) don tuna wannan ranar. Wannan taron ya sanya Farhana jin cewa duk wani abu da ta rasa a baya, Allah ya mayar mata da shi cikin girmamawa.
Lokacin liki ya yi, filin taron ya sake kaurewa da sauti. Hamma Fahad da Hamma Sajid suka fara fitowa fage, fuskokinsu cike da alfahari. Suka fara zubar da sabbin 'yan dubu-dubu a kan kanwar tasu, suna nuna wa duniya cewa yau farin cikinsu ya cika.
A ransu, dukkan su ji suke yi wannan auren ya fi na AK farin ciki da albarka. Farooq ya zo musu a matsayin dan uwa, ba wai kawai suruki ba.
Zayd: Balaraben Arewa
Kowa a wajen taron ya zuba ido yana kallon Zayd. Zayd ya fito sanye da danyar shadda da babban riga, kansa sanye da hula irin ta manyan mutanen Arewa. Duk da cewa babban rigar tana ta faman bashi wuya (struggling) saboda bai saba da ita ba, hakan bai hana shi fitowa fili ya rinka likawa Farhana kudi ba.
"Look at Zayd! He looks like a real Sultan," Isabella ta fada tana dariya yayin da take daukar sa bidiyo.
Matan Kaduna kuwa sai faman rada suke yi:
"Wannan baturen ko Balaraben ne? Kalli yadda babban rigar ta zauna masa!"
"Wannan bikin Captain Maryam daban yake, har da larabawa da turawa
A can gefe guda, Abdulkadir (AK) yana zaune a cikin duhun dakin sa, hasken wayarsa ne kawai yake haska fuskarsa dake nuna tsantsar bacin rai Yana ta faman scrolling a Instagram inda hotunan bikin Farhana suka karade ko'ina.
Ganin hoton Farhana sanye da mayafi, tana murmushi kusa da Farooq, ya sanya AK jin wani abu ya shake shi a wuya. Ya ga bidiyon su Zayd da Hamma Fahad suna liki, ya ga kwarjinin da Farhana take da shi wanda bai taba gani ba sanda take gidan sa.
"Ya Allah!" AK ya fada yana watsar da wayar gefe, numfashinsa yana neman daukewa. "Ashe da gaske ne? Maryam ta zama matar wani? Maryam din da na saka , yau ita ce sarauniyar zuciyar Farooq?"
Wani irin daci ya ratsa shi Ya san ya rasa ta, kuma wannan karon babu sauran "Zan yi tunani." Mutuwa ne kawai bai yi ba ranar ashe haka farooq yaji a wancen lokacin
An kammala shagali lafiya, inda aka tsara cewa sati mai zuwa su Isabella, Hailey, da Kevin zasu koma Amurka tare da su Farhana. A halin yanzu, Farhana zata zauna a bangaren Mamma a cikin katafaren gidan ta na alfarma dake Kaduna.
Hamma Fahad da Hamma Sajid sun dauki baki zuwa Abuja, inda suka yi alkawarin nuna musu wuraren tarihi irin su Zuma Rock da sauran kyawawan wurare kafin ranar tafiya ta yi
sunyi sallama cikin begen juna
Sai dai kuma, akwai wata matsala: Lamido.
Yaron ya kankame Farhana, yana ta faman kuka. "Ni nan zan kwana! Ni da Ammi na zamu zauna!"
Farhana ta rinka lallashinsa amma ya ki sakewa. Mamma ta shigo dakin tana murmushi, ta kalli Lamido dake faman kuka.
"Barshi kawai Maryam," Mamma ta fada tana daukar yaron. "Sultana dama tuni ta riga ta shiga mota da uncles dinta, shi kuma wannan tunda ya nace zai zauna da Ammin sa, mu kyale shi ya dan huta
Farhana ta yi murmushin kunya, tana kallon danta.