SARTSE COMPLETE

09

by @legendspen


    (09)

Da ido kowa yake kallonta, dan babu wanda yasan ma suna saurayin nawa bare familinsa a tsakanin Alhaji da Ra’is da suka san maganar, bare Hajiya da batasan komai a kai ba. 

“Hajja wane yaro kike magana a kai?” 

Alhaji ya tambaya, dan shi tunaninsa ko Isah Nadabo zata ce, shine ta ce Ta ambo, dan dai dukkansu sunsan Familin Ta ambo ba ƙaramin ahali ba ne.

“Ka ce haka mana, wallahi zama da wannan matar ta shafa maka mugun abu, shi ya sa na gwammaci na ƙyale mata kai ka je ka ƙarata daman ba wata tsiyar kake ban ba, to yanzu gashi ɗan gidan arziƙi yana son yarinyar Gawasiya take kowa, mai dai sunan Mutanen can, jiya da daddare yazo gidana ya cika shi da abun arziƙi sannan ya cika mini ƙugu da sulalla. Dan haka abinda nazo na faɗa ma shine, idan kana nan da wannan mummunan ra ayin naka na sai yara sunyi karatun yawudu da nasara ta ka sauke shi akan yarinyar nan, dan na yi mata miji na ce ya tura maka iyayensa ko sati yake so ka fito da kuɗi, kema ki fito da kuɗin shanu, aje a aurar da ita.” 

Ta ƙarashe maganar tana kallon Hajiya, ƙasa Hajiya ta yi da kai ba tare da ta ce ko ƙala ba. 

“Magana nake da kai fa.” 

Cike da ladabi da girmamawa Alhaji ya ce. 

“Hajja bangane kan zancen ba.” 

“Baka gane ba, mene baka gane ba, ke yi masa bayani.” 

Da sauri na kalle ta na ce. 

“Wane bayani kuma?” 

“Yaron da yake son ki.” 

Gaba ɗaya idanuna sun cika da ruwa na rasa me zance. 

“Ko kema bakya son sa? ‘yai mai baƙin hali.”

Gaba ɗaya Hajja ta rikita gidan, kowa ya kasa gane inda ta nufa, kuma taƙi ta yi bayani yadda za’a gane sai faman cewa take. 

“Ni dai na faɗa ma zai tura iyayensa.” 

Da ta gama banbamin ta tafi, Hajiya ta kalleni bayan Alhaji ya fita rakata ta ce. 

“Wane yake zuwa wajenki?” 

Ra’is ya yi saurin cewa. “Akwai saurayinta da yake zuwa wajenta wanda har Alhaji yasan maganar ya ce yana son ganinsa.” 

“To shine ɗan gidan da Hajja take faɗa?” 

Girgiza kai ya yi sannan ya ce. 

“Wannan ne kuma bansaniba.” 

“Dake nake.” 

Hajiya ta faɗa tana kallona, na gyaɗa kai kamar ƙadangariya sannan na ce. 

“Eyh… eyh, a gidan Ta Ambo yake.” 

“Aina ya san Hajja? Har yasan gidanta?” 

“Ya tambayeni yana son ya je ya gaida ‘yan uwanmu ne na ce masa na Hajiya ba anan suke ba, na Alhaji ne anan.” 

“Shi baki faɗa masa halinta ba.” 

“Bansan ma zai gane gidanta ba, kuma na ce mai ma bata son mu.” 

Daidai lokacin Alhaji ya shigo, sai da ya ƙare min kallo sannan ya ce. 

“Yaron da yake zuwa wajenki ɗan gidan Ta 
Ambo ne?” 

“Eyh Alhaji.” 

“Shine kika ce masa ya je ya sami mahaifiyata, ya bata abun duniya?”

Da sauri na girgiza kai sannan na ce. 

“Wallahi A’a.” 

“To Lallai kisa shi yazo.” 

Daga haka ya juya ga fice, ni kuma na yi cikin ɗaki. 

A ranar na sake sanar da Sardauna saƙon Alhaji, cikin wayo da dabara ya dinga tambayata abubuwam da Alhaji yake so akaina, nan na sanar dashi zance karatu, kuma yana son nasami miji mai ilimi da tarbiya. 

Bayan Magariba Alhaji ya dawo, sabida zuwan Sardauna, wanda bai zo ba sai ƙarfe takwas. A tsakar gida suka zauna mu kuma duka muna cikin ɗakin gaba ɗayanmu, amma hankalina gaba ɗaya yana kan su Sardauna da Alhaji. Yadda Sardauna yake magana da Alhaji cikin ladabi da nuna tsantsar tarbiya ya burge mu duka da muke cikin ɗakin, Hajiya, Ra’is da Ni. 

Yadda yake nunawa Alhaji zallar soyayyarsa ga karatu da burin na zama wani ya haifar da soyayyarsa mai girma a zuciyar Alhaji, haka kuma yadda yake magana da Alhaji kamar yana karɓar Umarni wajen mahaifinsa ya nuna tsantsar tarbiyarsa.  

“Ma sha Allah, ubangiji Allah Ya sanya albarka a taraiyyarku, ya albarkace ku da zuri’a ta gari.” 

Alhaji ya faɗa, daga cikin ɗakin na ji wani daɗi ya ratsani har cikin zuciyata. 

“Ka sanar da magabatan naka, sai su zo Allah Yasanya alheri.” 

Maganar Alhaji ta ƙarshe kenan, bayan Sardauna ya tafi Alhaji ya haɗa mu gaba ɗaya har da Yaya Ridwan. 

“A gaskiyya na yaba da irin nutsuwa da tarbiyar yaron nan da Nana ta kawo, dan haka na bashi damar ya turu magabatan nasa.” 

“Gaskiyya ne Alhaji, ni kaina daga cikin ɗaki na tsinci nitsuwa a cikin muryarsa, Allah Ubangiji yasanya alheri.” 

“Amin Amin.” 

Farin ciki ya cika rayuwata gaba ɗaya, bacci rabi da rabi na yi shi. Gari na wayewa ko takwas ban bari ta cika ba na je gidansu Amina na sanar da ita, ƙawayena sai murna suke. 

Kwana biyu a tsakani ‘yan uwa Sardauna suka zo gidanmu aka tsayar da rana wata uku, lokacin na kammala jarabarwata. 

Lisaafi ya canja, abubuwa sun ɗau harama, ni da ƙawayena babu zama. Kowa ya ganni yasan wanda nake so zan aura, Su Yaya Rumaisa da Yaya Radiya da Ra’is kowa farin ciki yake ta ya ni, idan ka cire Ridwan da na kasa gane kansa, ko sakarwa Sardauna fuska ba ya yi, idan muna tare zai zo ya wuce sau ɗari bai isa ya kalleshi ba, Hajiya ta ce mu dinga taɗi a cikin ɗakinsu amma Yaya Ridwan ya ce ban isa ba, gaba ɗaya gani nake ya tsani Sardauna. 

A cikin wannan lokacin ne auren Isah Nadabo yazo da matarsa Adizatu ‘yar jihar kano, biki ne aka yi shi na alfarma daidai zamani, kuma mun halarci komai na bikin tun daga farko har ƙarshe, kano ne kawai ba mu je ba, Amma Alhaji, Yaya Ridwan, da Ra’is duk sun je. Tun da Sardauna ya ji na ce masa matar Isah Nadabo  ‘yar kano ce Sardauna ya dame ni akan naje ta koyan girkin kano, yadda ake sarrafa fulawa ayi gurasa da su cincin. 

Ni ban fiya shigewa mutane ba, amma akan sardauna sai da na shigewa Anty Aadiza, daman ba ta da wata matsala tana son mu ta ɗauke mu ƙannen miji, ta ɗauki Hajiya Uwar miji, dan ko da aka kawo ta daga kano hannun Hajiya aka miƙa ta. A hankali ta fara koyan sarrafa fulawa mussamman da na faɗa mata wanda zan aura ne ya ce yana so. 

Hajja ba ta cika zuwa gidanmu ba, tun da Sardauna ya kan je ya kai mata kuɗaɗe da kayyaki har gida lokaci zuwa lokaci. Shi ya sa ta ƙyalemu mu ci tsiyarmu. 

Kwance tashi ba wuya a wajen Allah, har muka kammala jarabarwamu, inda bayan sati biyu aka ɗaura mana aure da Sardauna, biki ne aka yi shi na garari, masu kuɗine ke hada hada ta ko ina a wajen events ɗin da familin su Sardauna suka shirya. A cikin raina babu abinda nake ƙauna da tsumaye irin a gama wannan kiɗe kiɗen akaini gidan Sarduna, inda zan samu soyayya mai daɗi. 

Daga wajen taron aka wuce da ni gidana na Takur, tun ina cikin mota nake mamakin irin girman gidan, da aka fito da ni kuma sai na fara mamakin irin tsaruwar gidan. 

Haka aka shiga dani cikin gidan, kowanne ɗaki a tsare yake kuma sannan a cike yake da kaya. 

“Allah Sarki Alhaji da Hajiya, Allah Ya ƙara muku arziƙi, lafiya da nisan kwana.” 

Na faɗa a raina lokacin da aka shiga dani ɗakin gadona, nan masu kawo ni suka zauna suna ta faman yi min nasiha, nikam gani nake kawai ƙari suke domin Abinda Alhaji da Hajiya suka faɗa min, bana jin zan sake samun nasihar da ta wuce wannan, haka ma ‘yan uwana. Yaya Ridwan ma ganin dai dagaske za a kaini ɗakin aure ya zo ya same ni da yau da safe, ya yi min nasiha mai ratsa jiki. Akwai kalma da ya faɗan guda ɗaya wacca har yanzu tana nan daram a kunnuwana. 

“Nana ba tsanar saurayinki na yi ba, da ki kaga ina miki haka, Nana ina matuƙar kishin ‘yan uwana mata, bana son naga wani abu zai wahalal da su.” 

Wannan kalmar kishin ta tsaya min sosai a zuciyata, nasa hannu na goge ƙwallar da ta fito daga idona. 

Haka aka tafi aka barni da ƙawayena, suma ba su wani daɗe ba Sardauna da abokansa suka zo suka tafi da su, aka barni daga ni sai Sardauna. 

“Nana!” 

Ya kira sunana a hankali, nima na amsa masa a hankali. 

“A yau sai mu gode Allah da ya cika mana burinmu, ya nuna mana wannan ranar ga ni ga ki a matsayin miji da mata, tabbas ina cikin farin ciki da hakan Nana, ina farin ciki marar misaltuwa.” 

Ya ƙarasa maganar tare da tasowa zuwa inda nake, yasa hannu ya yaye lulluɓin fuskata, ya kalli fuskta da take sheƙi, ya sa hannu ya jawo ni jikinsa. 

“Nana kina jin sauti bugun zuciyata.” 

Na ɗaga kai tare da cewa. 

“Ina ji.” 

“Nana ki saurare abinda zan faɗa daga zuciyata bawai bakina ba, ina matuƙar ƙaunarki Nana, ƙaunar da nima bansan irin ta ba, ina jinki cikin jini da tsokar jikina, ina son ganin walwalrki Nana, ina jin wani irin shauƙi idan na ganni ga ki.”

Kalaman Sardauna suka kashen jiki, suka haifar min da wani irin yanayi mai daɗi, tabbas Nana na yi sa’ar miji, na yi da ce da miji na gari. 

“Nana.” 

Ya faɗa yana matseni a jikinsa. 

“Kina jin yadda nake ji?” 

“Uhm.” 

“Kina jin kamar ki cinye ni, na koma jikinki gaba ɗaya?” 

“Uhm.” 

Haka Sardauna ya yi ta yi min kalamai masu nuna zallar soyayya da shauƙin ƙauna, mun kusa awa ɗaya a wannan yanayin sannan ya ce da ni. 

“Nana ta shi ki yi alwala mu yi sallah, mu miƙa godiyarmu ga Allah.” 

A hankali na tashi daga jikinsa na nufi toilet na ɗaura alwala, bayan na idar na fito shima ya shiga ya ɗaura tashi alwala daga nan ya ja mu mu ka yi sallah, tare da addu’o’i na neman albarkar aure. 

Daga nan muka ci nama da lemo sannan ya kalli ni. 

“Kin gaji ko?” 

“A’a.” 

“Ta shi ki canja kaya ki zo mu kwanta.” 

Daga nan ya tashi ya fice, nima na tashi na sauya kaya zuwa na barci, bayan na sauya na zauna ina jiranshi. ‘Yan mintina kaɗan shima ya shigo cikin shirinsa na bacci. 

“Wai baki kwanta ba? Sannu Nana.” 

Ya faɗa yana hawa kan gadon. 

“Matso kusa.” 

Ya faɗa tare da jawo ni, ya rugume ni jikinsa a hankali bacci mai daɗi ya ɗauke mu. A raina ina faɗin haka ake aure? Haka rayuwar take da daɗi? 

Kiran sallar asuba ne ya tashe ni na buɗe idona, idan da sabo na saba dan dama shine daidai lokacin tashinmu. Ina matsawa daga jikinsa ya buɗe ido.

“Come on Nana.” 

Ya faɗa cikin magagin bacci. 

“Kiran sallah ake.” 

Na faɗa a hankali. 

“I know, matso!” 

Ya faɗa yana kamo ni, ba shiri na koma na kwanta ya sake rungume ni bacci ya sake ɗibansa, ni kam idona biyu ina ta faman saƙe saƙe. Ba shi ya farka ba sai 6:30. 

“Honey! Baki san irin gajiyar dake jikina ba.” 

Ya faɗa yana kamo hannuna, na yi murmushi sannan na ce. 

“Ina kwana.” 

“Mu fara sallah mana.” 

Toilet na shiga, sai kawai na ga shima ya biyo ni. 

“Mu fara yin wanka, sai mu yi sallah.” 

Abu kamar wasa  Sardauna ya ce tare zamuyi wanka, haka kuwa akayin, daga nan mu ka yi alwala mu ka gabatar da sallah. 

Bayan mun gaisa ne ya ce. 

“Ya kwanan sabon gida?” 

Na yi murmushi sannan na ce.

“Da godiya.” 

“Nana i really love you, i love you smile please keep it.” 

Muna zaune muna hira ya hanani tashi naga shiga kicin,  sai da aka yi masa waya sannan ya tashi, can ya shigo yana cewa.

“Je ki haɗa mana breakfast.” 

Na tashi na fita, wani babban kwando nagani ya ajiye akan centre table na ɗauka na kai kan dinning sannam na shiga kicin. Ba ƙaramin mamakin irin girman kicin ɗin na yi ba, dan zai iya fin girman wani ɗakin a gidanmu, amma duk da haka an zuba kaya masu yawa a ciki. 

Da kansa ya zagaya dani ko ina na gidan, ya nuna ko ina har da ɗayan part ɗin, da kuma ɗakinsa na nan. 

Sai can yamma sannan ‘yan uwana suka yi min zuwan nan da suke yi, da daddare ma cikin irin yanayin jiya muka sake kwana da Sardauna. 

Har tsawon kwana goma da aurenmu muna zaman jin daɗi da soyayya da Sardauna ina samun soyayya da kulawa a wajen Sardauna, yana riritani kamar jaririya, ko ƙwai da ake tsoron fashewarsa. 

Ranar juma’a su Malaika, Amina da Fauziyya suka shirya zuwa, tun safe nake rawar jiki da zuwansu, na faɗawa Sardauna ya kai sau goma, tun yana kulani har yafara min banza, haka har ya tafi ofis, girki wajen kala uku na yi musu sabida murnar zuwansu. 

Wajen ƙarfe ɗaya suka zo, har wani tsalle na yi da na gansu, suma cike da farin ciki suka tarbeni suna murnar ganina cikin farin ciki, bayan sun zauna na shiga yi musu safarar abun sha, lemo kala kala na gora da na kwalli, sannan kuma wa’yanda na yi da kaina. 

“Oh my, Nana kinga yanda kike glowing.”

Malaika ta faɗa tana kashen ido. 

“Nana duk waɗannan abun shan namu ne mu kaɗai, duniya sabuwa.” 

Amina aminu ta faɗa, na yi dariya sannan na ce. 

“Ku yara ashe haka aure yake da daɗi? Haka ake rayuwar auren, ai wallahi aure yafi komai daɗi idan kuka sami irin mijina. A shawarce karku ce zaku zauna, wallahi kuna komawa gida ku ce sai anyi muku aure.” 

Legendspen
***