SARTSE COMPLETE

10

by @legendspen


    (10)

Dariya suka kece da ita sannan Malaika ta ce. 

“Yarinya ta ji daɗin aure.” 

Ni kuwa na ce. 

“Ba dole ba? Mene wanda nake so mijina ba ya yi min, a zaman nan namu sau uku yana fita dane manyan wajen cin abinci, gaskiyya  duk wacca ta yi dacen miji ta yi riba.” 

Haka muka yi ta shan hirar mu muna dariya, wajen ƙarfe biyar Sardauna ya kirani a waya, a gabansu na ɗauka ya ce dani yana son na yi masa cous-cous da miyar kaza. Ina gama wayar na kallesu sannan na ce. 

“Bara na shiga kicin.” 

“Kaga matar aure.” Suka faɗa suna dariya, suna nan zaune na shiga kicin na fara haɗa masa girki, sai dai sanda na duba friza ɗaukar kaza babu kaza, sai a lokacin na tuna gaba ɗaya na yi amfani da ita, waya na ɗauka na kirashi sai dai bai ɗauka ba. Sai kawai na ɗora cous-cous ɗin. Ina cikin Kicin ɗin Fauziya ta sanar da ni cewar zasu tafi, haka na fito falon mu ka sake taɓa hira kafin su ka tafi, Naira dubu biyar na basu na ce su hau mota, ni kuma na dawo kan girki na.  Ashe Sardauna ya kira ni ban kula ba ina kicin wayar na falo, ganin lokaci zai ƙure sai kawai na ɗora miyar na yi masa ta nama, amadadin kaza tun da duk nama sunansa nama. 

Bandaɗe da gama abincin ba ya shigo, da murna ta kamar ko yaushe na je na tare shi, na yi tsalle na faɗa jikinsa ya rungumoni yana faɗin. 

“Hon yau bana jindaɗi.” 

“Meke damunka?”

Na tambaya ina amsar jakarsa hannunsa, zama ya yi kan kujera tare da miƙamin ƙafarsa na fara cire masa takalmi. 

“Wane mistiyacin yaro ne a family, ya dawo ƙasar shine yake neman yi min rashin kunya.” 

Ya faɗa yana taɓe baki, sai duk na ji ba daɗi.

“Ka yi haƙuri ka ƙyaleshi kawai.” 

“No! Turaki bai isa na ƙyaleshi ba, dole na ɗau mataki zan nuna masa ni ba sa’ansa ba ne.” 

“Kai Sardauna shi Turaki?” 

Tambayar da na fara yi kenan, kallona ya yi sannan ya ce. 

“Granny ce ta sama na sunan dukkanmu, sa’a na ne, kusan lokaci ɗaya aka haife mu da shi, amma na girmeshi. But seriously Nana tun ina ƙarami bana son yaron nan, abokin dabi na ne, komai na yi sai ya ce zaiyi, natsani na ganshi da abuna ma gaba ɗaya.” 

“Ka daina faɗin haka Hon, ba a cewa antsani musulmi, mussaman shi da yake ɗan uwanka.” 

“Ƙyale wannan maganar Hon! Yunwa nake ji.”

Ya faɗa yana tashi zuwa wajen dinning, nima na ta shi na shiga da takalmi da jakarsa ɗaki. 

“Me ya sa ma bazan yi biyyar aure ba, bayan Yaya Rumaisa da kanta ta ce Biyayya na ƙara soyayya kuma gashi ina gani, ni ina mamakin matan da basa yi wa mazajensu biyayya. Me suke nema a duniyar?.” 

Na faɗa bayan na ajiye kayan, sannan na fito falon yana zaune kan kujerar dinning yana jirana. Plate na fara ajiye mai sannan na buɗe cous-cous ɗin na fara zuba mai, sai bayan na gama na buɗe miyar na fara zubawa. 

“What is this?” 

Ya katseni. 

“Abincin.” 

Na faɗa muryata na rawa, leƙa miyar ya yi sannan ya kalleni. 

“Bance miki chicken nake so ba, me ya sa naga beef?” 

“Ahm. Daman kazan ne babu, da na duba sai naga saura nama shi ya sa na yi na nama” 

“Me ya sa baki sanar dani ba?” 

“Na kiraka baka ɗauki wayar ba.” 

“Ban kiraki ba bayan nan? Me ya sa baki ɗauka ba, sabida kina can ƙawayenki sun zo ko? Ni ban isa na sa ki abu ba? Ban isa na ce ga abinda nake so ba ni da gidana?” 

Ya yi maganar cike da tsawa kamar zai dake ni. 

“A’a ba haka ba ne, ka yi haƙuri wallai gobe zanyi.” 

“Dalla malama rufemin baki, shashasha marar hankali, abinda zaki fara yi min kenan? To wallahi Nana baki isa ba.” 

Yana gama faɗin haka ya yi fatali da abincin ya yi waje, wani irin zafi na ji ya mamayeni, kamar ba wacca take cikin Ac ba, jikina gaba ɗaya ya fara rawa ba shiri na tsugguna ƙasa na fara raira kuka, sai da na yi kusan minti talatin ina kuka na babu mai rarrashina sannan na tashi daga baya na shiga kwashe kayan, sannan na gyara wajen na koma kan kujera na zauna.

Ba Sardauna ya shigo ba sai wajen ƙarfe tara, kallo ɗaya ya yi min ya ɗauke kai, da sauri na tashi ina faɗin. 

“Dan Allah ka yi haƙuri.” 

Ɗauke kai ya yi ya shige ɗakinsa, ya tura ƙofar ya murɗa mukulli, haka na yi ta faman bugu amma bai buɗe ba, sai wajen ƙarfe 12:30 na je na kwanta ganin Sardauna bazai buɗe ba. 

Wannam shine karo na farko da muka sami saɓani da Sardauna tun zuwana, wannan ta kasance baƙar Rana a wajena domin naga abubuwa kala kala, ko baccin kirki ban iya ba. 

Washe gari da safe tun da na yi sallar asuba ban koma ba, na shiga kicin haɗa masa abincin kari mai kyau da lafiya, sabida ina son na burgesa kuma ya yafe ni. Gurasar da na koya wajen Anty  Adiza na yi masa da miyar farfesun naman rago, na juye a plast na kawo kan dinnig ɗin. Na shirya na dawo falon na zauna jiranshi, bai fito ba sai ƙarfe tara kasancewar yau Asabar ne kuma babu aiki. 

“Ina kwana?” 

Kallona ya yi sannan ya kalli dinning ɗin, ya nufi wajen ba tare da ya ce da ni komai ba. Na bi bayanshi ina kuka ina faɗin. 

“Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi bazan sake ba dan Allah.”

“Uhm.” Ya faɗa yana zama kan kujerar, ya fara zuba abincinsa, in tsaye akansa ina faman zubar hawaye amma ya yi banza dani kamar bai san ina wajen ba, har ya kammala sannan ya kalleni. 

“Ki biyo ni.” 

Ba shiri na bi bayanshi zuwa falo, ya zauna akan kujera ni kuma na zauna a ƙasa, sai da aka kusa minti biyar sannan ya ce. 

“Nana!” 

“Naam.” 

Na amsa masa. “Nana wanene ni a wajenki?” 

“Mijina.” 

Ya kalle ni sannan ya ce. 

“Shine matsayina a wajenki?” 

“Eyh.” 

“Nana” 

Ya sake kiran sunana, na sake amsa masa. 

“Nana,  ina so ki canja min matsayi daga na mijin da kika ba ni. Ina so ki bani matsayin da yafi kowanne matsayi a wajenki, ki bani matsayin Uwa, Uba, dangi, Nana ina so ki ɗauke hankalinki daga komai daga kowa ki mayar dashi kaina, Nana ni kaɗai. Nana irin son da nake yi miki bana so naga kina mu’amala da kowa a duniya, Nana ina jin kishin akan kowa ciki har da ‘yan uwanki, Nana ko da mace naga kina magana ina jin zafi a cikin raina, ina jin duniya ta yi min zafi. Nana zaki iya yi min wata alfarma?” 

“Eyh zan iya.” 

“Nana ina so ki cire kowa a rayuwarki, ki cire komai sai ni Nana, ni kaɗai zaki gani, ni ka ɗai zaki ji.” 

“Na yi maka alƙwarin.” 

“Ta shi ki zauna anan.” 

Ya faɗa yana nuna min kusa da shi, na miƙi na zauna ya kama hannuna. 

“Nana ni mijinki ne, mai sonki! Da ya sadaukar da dubban farin ciki dan ya rayu dake, Nana ina son sakayya mai girma dan Allah.” 

Da irin waɗannan kalaman Sardauna, ya dinga dasa zazzafan tausayinsa a zuciyata, har na ji babu wani a rayuwata sai Sardauna. 

Daga nan komai ya dawo daidai tsakanina da  Sardauna, muka ci gaba da rayuwa cikin soyayya da farin ciki. Sardauna yana yawan magana akan ayyukan gida sun yi min yawa, hakan yasa ya kawo ‘yar aiki me ta ya ni aiki, a farko mun fara zama tare da ita tana ta ya ni aiki, amma daga baya na fara fuskantar abubuwa sun fara yi wa Sardauna yawa, mussaman yadda wata rana ya fara magana akan yawan kuɗin wuta da aka kawo masa bill. Hakan ya sa na sallami ‘yar aikin, da ya yi magana na ce masa bana son yana yawan kashe kuɗi, amma bayan kwanaki ya sake dawo da ita na sake sallamarta, a haka ya kawo har guda uku ina sallamarsu, daga baya ya daina kawo wa. 

Haka mu ka ci gaba da rayuwa cikin so da ƙaunar juna, Sardauna yana riritani tamkar ƙwai akan cokali wanda ake tsoron faɗuwarsa. Ina rayuwa ta cikin farin ciki kowa yana ta ya ni murna, na je gida sau biyu sannan na je gidan yayuna sau ɗai ɗai, suma sun zo baki ɗaya har da Ra’is amma banda Yaya Ridwan.  

Ranar wata juma’a bayan ya dawo, yake sanar dani wai ƙarshen wannan satin ranar Lahadi suna da baban family meeting, kuma ana buƙatar kowa yaje har da iyalansa. 

Tun da Sardauna ya faɗan na fara tunani, danni ban taɓa haɗuwa da ‘yan uwansa ba tun lokacin biki, sai dai ‘yan gidansu da ya kaini sau ɗaya. Hajiyarsa mutuniyar arziƙi da ƙannensa duk ba su da matsala, amma fa wannan ya ce wai babban famili meeting, duka ‘yan uwansa zasu je. 

Washe gari na kira Yaya Rumaisa a waya na faɗa mata bayan ya fita, nan ta bani shawarar irin yadda zan shirya, yadda zan kama kaina a cikinsu, da sauran abubuwa.

Ranar Sunday tun safe, na fara shirina amma ina yin komai cikin nutsuwa sabida kar ya ga rawar kaima, kamar yadda Yaya Rumaisa ta faɗa. Bayan munyi breakfast ya ce dani. 

“Ki shirya muje da wuri, zan ajiye ki sai na fita zuwa 12:00 ake farawa, zan dawo kafin lokacin.” 

Tashi na yi na shiga ɗaki, na ƙarasa shirina daga nan na dawo falo lokacin shima ya gama shiryawa. 


FADA AREA
09:30am. 

Babban gidane na gaske da ya ji kayan more rayuwa, mutane ne tsilli tsilli cikin gidan sabida basu gama hallara ba, yana gaba ina binsa a baya ya yiwa wayanda ya ga dama magana, ya yi banza da wayanda ya ga dama, har ya kaini inda Hajiyarsu take tare da ‘yan uwansu. Dukkansu na gaishesu kamar yadda na ga ya yi, suna ta samin albarka kowacce fuskarta washe da fara’a. 

Bayan mun gaisa ne na koma gefe na zauna a babban falon inda naga Lubna ƙanwarsa ta zauna, shi kuma ya tashi ya fice. Kowa sabgar gabansa yake masu danna waya na dannawa masu hira na taɓawa cikin harshen turanci, ba ruwan kowa da ni, hakan ya sa nima na ja waya ta na fara dannawa, nan ga message ɗin Amina Aminu cewar an fara cire WAEC, sun cire tasu a cafe kuma sun sami 8 credit, sannan an fara registration ɗin Jamb. Na yi mata reply da cewar Okay idan ya shigo zan faɗa masa sai ya ciro min. 

“Salamu alaikum.”

Da sauri na ɗaga kai sabida yadda na ji muryar kamar ta Sardauna sai da ba shi ba ne, wannan wani matashin ne daban shima ɗan gayu amma Sardauna yafi shi kyau nesa ba kusa ba. 

“Uncle Turaki Welcome.” 

Na ji muryar wata yarinya ta faɗa tana nufo sa. 

“Dotti, how are you.” 

Ya faɗa cikin wani irim ƙwarewar turanci, kamar ma bai iya hausa ba, a raina na ce. 

“Wannan shine TURAKIN? Duk rashin girman SARDAUNA da nake gani, sai naga wannan yafi ƙanƙantar jiki.” 

Na faɗa a cikin raina, ƙarasowa ya yi inda iyayensu suke ya fara gaishesu cike da girmamawa, ya ɗan fi Sardauna sakin fuska amma Sardauna yafi shi komai na duniya, haka kawai sai na ji bai yi min ba sabida yadda suke da mijina. Daga nan ya juyo inda sauran yayunsu suke suka ya fara gaishesu, yadda yake ɗan wasa da su Sardauna duk ba ya haka, dan ko da yazo daga Ina wuninku, Ya iyalai shikenan ya tashi ya fice. Amma shi gashinan sai hira suke har da wasa da yaransu, suma sai jan shi suke da hira mafi akasarin hiran na su ma cikin harshen turanci suke. 

A raina na ce. “Su waɗannan sun maida turanci yaren uwarsu da ubansu, ba ga yaran ba ga iyayensu ba.” Daga nan kuma ya juyo inda muke nan kowa ya fara gaisheshi, nima na gaisheshi ya amsa ba tare da ya kula da ni baƙuwa ba ce a cikinsu. Wata da na ji suna cewa Sister Seemah ta ce. “Blood meet your Amarya.” Ta faɗ tana nuno ni, gaba na ne na ji yana faɗawa sabida irin kallo daya ke min, sai da ya kalleni tas sannam ya dawo inda nake. 

“Daga ina?” 

Ya tambayeta, Sister Seemah ce ta matso sannan ta ce. 

“Sardauna’s Wife.” 

Kallona ya sake yi tare da jijjiga kai, sannan ya ce. 

“Matar ƙanina kenan? Me sunanta?” 

“Nana.” Lubna ta faɗa. 

“Sannu Amaryarmu, sunana Turaki yayan mijinki Sardauna, kuma babban abokinsa.” 

Na yi murmushi sannan na sake cewa. 

“Ina kwana?” 

“Lafiya ƙalau, ina ɗan uwan nawa?” 

“Yanzu ya fita zai dawo.”

Na faɗa a raina na fara mamakin me ya sa to basa mutunci da Sardauna, amma shi ga shi anan yana sakar min fuska har da cewa matar ƙaninsa. 

“Okay zan jirashi a main falo, ya gidan?” 

“Lafiya lau.” 

“To Allah Ya sanya alheri, Allah Ya bada zaman lafiya.” 

Na buɗe baki da niyar cewa Amin, muryar Sardauna ta cika ɗakin. 

“Malam matsa daga kusa da matata.” 

Legendspen
***.