10
*KUNDINA*
*NAFISATUSASAAL*
***
10
Bayan watanni biyu. Babu irin videon jikina da ban turawa Sadik ba, saboda imanin da nayi cewa ba zai barina ba har abada, kamar yanda yake faɗa min kullum...
Abinda ya fara tsoratar da ni a kwanakin da suka biyo baya, shine sauyin Sadik.
Ba ya ba ni lokacinsa kamar da. Idan na yi magana sai ya ce;
"Babyy da ni da lokacina dukka naki ne, kawai aikin da na kusa kammalawa ne yake ci miki lokacina, ko kina so na samu matsala a result ɗina?"
Ya ƙarasa faɗa yana marairaice muryansa kamar kullum.
Sai da na ɗan yi jim, saboda kokwanton da zuciyata ta fara yi akansa na ce;
"A'a, Allah Ya bada sa'a"
"Ameen Baby, dafatan har yanzu kina saka liƙab ɗin da nace, saboda ba na so kowa ya ganemin wannan kyakkyawar fuskar taki"
Wani irin daɗi na ji, mahaukaciyar ƙwaƙwalwata ta hau kan kalamansa daram.
Da sanyi murya daɗin da ya lulluɓe ni na ce;
"Kullum ina sakawa Yaya"
"Yauwa Babyna ni kaɗai, yanzu ki kwanta kin ji, anjima zan kiraki, ina sonki sosai"
Lumshe ido nayi na ce;
"Tohm Yaya, nima ina sonka"
Daga wannan kiran Sadik bai ƙara nemana ba, WhatsApp ɗinshi ma baya hawa, idan na kirashi ma a gurguje zai ɗaga ya ce min;
"Baby wallahi aiki ne ya riƙeni, yanzu ki ba ni minti ɗaya, zan kira ki kinji ina sonki sosai. Bye"
Daga nan ba zai ƙara kirana ba.
Duk yanda na kai ga zama mara wayo akan soyayyar sa, sai da na fahimci waccen Sadik ɗin daban wannan ma daban.
Haka na share sati guda Sadik baya bani lokacinsa, kuma na kasa gayawa kowa.
Idan Mama ta tambayeni, lafiya ta ganni kwana biyu shiru, sai na ce mata babu komai.
A cikin kwanakin da suka biyo baya muka fara exams, yanda aka bani takarda a ɗakin Jarabawa haka nake kofe questions na miƙa bana fahimtar komai.
Ranar da muka yi jarabawar ƙarshe na dawo gida ya gajiye na buɗe wayata.
Kai tsaye WhatsApp na shiga, ban cika duba Status ba, musamman a irin yanayin da na tsinci kaina na rashin samun kulawarka Sadik. Kamar zan sauka sai idona ya faɗa kan Status ɗin ƙanwarsa.
Ɗan dakatawa nayi, saboda ban saba shiga Status ɗin ta ba, amma da nayi tunanin wataƙila zan ga wani abu daya danganci Sadik sai na shiga.
Videon Sadiq ne, yana saukowa daga Mota, ya yi haske ya ƙara kyau, dama can ɗan gayu ne, don da iya saka sutura shine kyau, da sai nace ya fi ko wani Namiji da na sani kyau a rayuwata.
ihun murnar dawowarsa suke yi, daga gefe naji muryar wata da na ke kyautata zaton Yayarsa ce tana cewa;
"Ohhh Sadik angon Fatima, ko dayake naji Mommy tace yanzu Angon Raheela ne"
Na maimaita kallon videon na manna shi a kunne na yafi sau ashirin.
Ni sai naji kamar tana cewa; "angon lahira, ba angon Raheela ba"
Sai tin zuciyata na dafe, kuka mai raɗaɗi da ciwo ya tahomin.
A zuciye na fara neman layin Sadik, sai dai wani ɓangaren na zuciyata ya kwaɓeni, na yi haƙuri, na jira na gani ko zai kirani ya gayamin ya dawo.
A ɗaki na kulle kaina, dama Mama taje unguwa, haka na wuni da waya a hannuna, ko ƙarar saƙo na ji sai na firgita.
A daddafe na yi kwana biyu ban kirashi ba, shima bai kira ni ba, bai turomin da saƙo ba, gaba ɗaya ma baya hawa WhatsApp.
A daren ranar da ya yi kwana biyu da dawowa na yanke shawarar kiransa.
Sai a kira na biyu ya ɗaga muryarsa ƙasa-ƙasa kamar mara lafiya ya ce;
"Baby kin jini kwana biyu shiru ko? Wallahi ba ni da lafiya ne, amma na kusa kammala komai na dawo gida gaba ɗaya"
Wani iri bugu zuciyata tayi, cikin Muryar kukun da ke nuna karayar zuciyata a sarari na ce;
"Tun yaushe kake yi min ƙarya Sadik? Maiyasa zaka yimin haka? Maiyasa zaka yimin ƙaryar rayuwa da ni har abada? me na yi maka ka zaɓi ka rusa zuciyata"
Murya a buɗe Sadik ya ce;
"Sadik? Sadik fa kikace Fatima? Sunana kike kira kai tsaye saboda baki da kunya? Hm a haka zan aureki, wallahi ba zan iya ba, Allah Ya haɗa kowa da rabonsa"
Dariya mai haɗe kuka na saki, duk yana jina bai katse kiran ba.
"Ashe haka rabuwa yake da sauƙi a wajenka, maiyasa zaka yaudareni, ina zaka kai haƙƙina"
Tsaki mai tsaho Sadik yaja cikin raini ya ce;
"Shasha kawai" haɗe da katse kiran.
Ihu na kurma, ina maimaita; "Sadik meyasa zaka yimin haka? bayan ka gama ganin komai na jikina, na shiga uku, ina Mama zata kai dukka kayayyakin da ta siyamin? "
A daidai lokacin Mama ta shigo da sauri, da alama ta gama jin duk abinda nake faɗa.
Mari mai zafin gaske ta zubamin, tasa iya ƙarfinta ta fizge wayan hannuna.
Binciken wayar ta fara, ihun salati tasa, cikin gajen haƙuri, da rashin hangen nesa irin na Mama ta nufi sashen Baba da wayar....