11
11
A ranar kwananan Hajiya Babba ne, don haka tana sashen Baba, Mama ta shiga da wayar hankalinta a tashe...
Ban san yaya suka yi ba, sai ganinsu nayi dukkansu a kaina..
Dukan da ya fitar da ni hayyacina Baba ya yimin ya na cewa;
"Kin cuceni Fatima, ke a tunanin wulaƙanta kanki ne zai sa Sadik ya so ki, kalar tarbiyyar da na baki kenan?"
Caraf Hajiya Babba ta cafe;
"A'a Alhaji ai wannan kalar tarbiyyar da uwarta ta bata ne, ta yaya kina tare da yarinya, yarinyar ma ƙwalli ɗaya, a sashe ɗaya ace bazaki saka ido akan duk wani motsinta ba, ai daga ranar da akace Namiji ya kawo kuɗin auren yarinya daga ranar zaki ƙara tsantsaini da saka ido akan komai nata, kai hatta wayar da suke yi, sai kin saka ido.
To waya sani ma ko irin abinda su Marigayiya suka aikata kenan da Samarinsu , Mijin yake ta gana musu azaba a ɓoye har suka rasa ransu, ke kam anyi sakarar uwa wallahi, sai aukin tara kayan kitchen da tarkacen banza kika sani, ke ga ki ƴarki ta samu Miji ko?"
Duk da, da salon makirci Hajiya Babba ta saki maganganunta, ba ƙaramin shigar Baba suka yi ba, domin sak ya yi a tsaye yana kallon Mama..
Cikin zafin zuciyar da ba zai rasa nasaba da tuna rasuwar su Aunty Su'ada da ya yi ba, muryarsa na rawar kukan da ya taho mai ya ce;
"Maryam ki je na sakeki saki uku, saboda baki da amfani, gara Fatima ta rayu ita kaɗai, nasan ita kaɗai ce bata da uwar da zata bata tarbiyya, akan dai ta rayu da uwa irinki"
Ina kallon Mama ta share hawayenta, ba tayi ihu ba, ba ta ce komai ba, da alama gigitar da take ciki yafi ƙarfin kwanyarta..
Hannun Hajiya Babba Baba yaja suka bar Mama a tsaye..
Su na fita ta durƙushe ƙasa ta saki kuka, jikinta yana tsuma;
Nima kuka nake yi ina kallonta. Ina ƙoƙarin jan jikina zuwa inda take, naga tayi sauri ta miƙe...
Daga wannan ranar ban ƙara ganin Mama ba, ban san sanda ta tafi ba, bata ɗauki komai nata ba, sai suturar sawa..
A haka nayi rayuwar sati ɗaya, cikin tsananin da ƙunci...
Lungu da saƙo babu inda Hajiya Babba bata bi ta bayar da labarin abinda na aikata ba, kaf dangi babu wanda labari bai je masa ba..
Baba ya daina kulani, Sadiq bai ƙara nemana ba.
Idan na kirashi don na bashi haƙuri ya rufamin asiri ya aure ni, sai ya ƙi ɗauka, ƙarshe ya toshe duk wata hanya da zan iya samunsa..
Itama Mama ta toshe duk wata hanya da zan iya samunta, na yi kuka nayi nadamar da bata da amfani..
Sai a lokacin na fahimci cewa; mace ta siyar mutuncinta ko akasin haka ba shi zai sa Namiji ya aureta ba..
Da birge Namiji zai saka ya auri Mace da Sadiq bai guje ni ba.
Da kuma irin abinda ya saka ni aikata, shine dalilin da yasa ya guje ni, da macen da tayi yawan duniya bayan ta shiryu ba ta auru ba.
Dama can Sadiq ba so na yake yi ba, bashi da niyyar aurena, domin shi masoyi na gaskiya yana tsayawa a kowani irin yanayi zai tsaya...
Ranar da magabatan Sadiq suka zo yiwa Baba bayani, korar kare ya yi musu, har maƙota suka fara shigowa, daƙyar hayaniya ta lafa, ina laɓe a window ina kallon komai...
Nayi kuka, tare da tabbatarwa da kaina na rasa Sadiq har abada, samun Mijin aure kuwa sai dai naga anayi...
Bayan wani lokaci, tunani da ƙuncin rayuwa suka sako ni gaba, ba ni da gatan komai..
Farida tabi ƙawayena na Makaranta duk ta basu labari.. a dai-dai wannan gaɓar na daina fahimtar karatu, dama ko waccen Jarabawar ban yi abun arziƙin ba....
Ban san garin yaya ba, sai gashi videona ya fara yawo a Makaranta...
Ina ji ina gani hukumar Makaranta ta koreni.. komai na rayuwata ta tsaya cak..
A ranar sai da Baba ya ƙara yimin dukan da ya kusa zautar da ni, da jan ƙafa na dawo Sashemu...
Sati biyu bayannan number da ban sani ba, ta turomin video kala-kala na bikin Sadiq ta WhatsApp..
Na jima ina kallon fuskarsa, daɗaɗan kalamansa na yiwa kunnuwana amsa kuwa, yawan bayar da haƙurinsa idan ya yi laifi, faɗin ba zai rayu ba idan babu ni, ashe duk yaudara ne...
Kuka da dariya ne suka tahomin lokaci ɗaya...
Daga wannan ranar littafin da na siya don rubutu kalaman soyayyar Sadiq ya koma littafin da na yiwa take da *KUNDINA*
Daga ranar na fara rubuta labarina, ba kuma zan tsagaita ba har ajalina, ko da ya cika, zan siyo sabo na ɗora...