12
SASAAL
12
Ban ƙarayin saurayin da ya yi sati yana zuwa wajena ba, don da zarar sun fara zuwa za'a basu labarin abinda na aikata har da ƙari...
Rayuwar maraicin da ban akwai irinsa ba nayi na tsahon shekaru biyu, cikin ƙasƙanci, don ko Farida ban isa nayiwa kallon da bai yi mata ba, zata fara ƙyalƙyala dariya tana nuna ni...
Gane yawan kuka, da nadama ba zasu yimin amfani ba, yasa na dage da addu'a... Cikin ikon Allah Aunty Amarya da tun farkon lamarin bata ce komai ba, ta kirani har sashen Baba...
Gaskiyar da kowa ya kasa faɗamai ta gayamai cikin taushin lafazi...
"Kuskuren Fatima bai kai ta amshi irin wannan hukuncin ba, banzatar da ita ba zai rage maka abinda kake ji ba, don kuskure tayi kuskure bata kyauta ba, amma kar mu bari zafin abinda ta aikata yasa mu ƙara barinta ta dilmiya, ina roƙawa Fatima afuwarka, don Allah ka yafe mata"
Ta ƙasara faɗa tana yin ƙasa da kanta da alama hawayen tausayina ne ya taho mata...
Shima Baba ƙasa ya yi da kanshi...
Wani irin soyayyar Aunty Amarya ne naji ya shiga cikin zuciyata.
Ta yimin abinda kowa ya kasa yimin.. kuka na fashe da shi, na nufi ƙafafun Baba na kifa kaina ina kuka kamar raina zai fita..
Na jima haka, sannan ya ɗagoni ya rungemin, ina jin saukar hawayensa a bayana..
Cikin taushin da muryarsa tayi ya ce;
"Na yafe miki Fatima, Allah Ya ƙara shiryaminku, Ya jiƙan yayyenki, nayi bincike sosai, basu da alaƙa da abinda Saratu(Hajiya Babba) ta faɗa, Mijinne yake ƙuntata musu a ɓoye, ba su da laifin komai shine mugu, Allah Ya saka musu, Ya bi musu haƙƙinsu"
Ido na lumshe, nauyin zuciyata ya na ragu, a hankali na ce;
"Amin"
Aunty Amarya ita ce tayi sanadiyyar da fara samun kulawar Baba. Jefi-jefi takan yi min kyautar kuɗi da kayan sawa.
Hajiya Babba kuwa tsakanina da ita gori ne da habaici, har su Aunty Ummi ba'a bar su a baya ba, wajen yadamin baƙaƙen maganganun da zasu sosamin zuciya... Ban taɓa tanka musu ba, sai dai na dawo Sashenmu nayi ta kuka..
Ƙauyen mu ma, bana iya zuwa, saboda kallona suke yi, kamar wacce tayi wanka da najasa..
Ban daina tunawa da Sadiq ba, sai dai ina tunashi ne a matsayin darasin da na koya a rayuwata, ba a matsayin masoyi ba, ban goge komai daya danganceshi ba, kuma ban nemeshi, hakan ya na ƙara tabbatarmin da yanzu nasan kaina, na bar baya a matsayin darasi gareni da mata masu irin tunanina..
Duk da Baba ya fara sakarmin fuska na kasa tunkararsa da batun komawata makaranta, sam babu ƙwarin gwiwa a tattare ni..
Sai dai fahimtar tsoro, da tuna baya, da kuma rashin ƙwarin gwiwar da nake ji, ba zasu kaini inda nake so naje ba yasa na tunkari Baba da batun komawata makaranta...
*DAWOWAR LABARI*
Littafin na kifa a saman fuskata, nayi kuka nayi kuka, ƙawayen duk sunyi aure, rayuwar mutanen da na sani, duk ya sauya, sun samu cigaba sama da na baya, zan iya cewa a masu irin shekaruna 25 dana sani da yawansu sun yi aure, wasu sun kammala karatu sun samu aiki, rayuwarsu gwanin sha'awa..
Amma ni makauniyar soyayya ya dawo da nawa rayuwar baya, babu Miji babu karatu....
A nan inda nake a kishingiɗe barci mai nauyi ya ɗaukeni.
Ban farka ba sai cikin dare, nayi sallar Isha'i na jima ina roƙon Allah Ya tsare ni, Ya zama gatana, Ya bani miji nagarin da dubi sauyina ba kuskuren da na yi a baya ba...
Sai can dare sosai na kwanta saboda da safe zamu fita ni da Baba..
★washe gari, bayan nayi sallar Asuba barci ya ƙara ɗauke ni a inda na yi salla, sai wajen ƙarfe bakwai saura na farka...
A gurguje nayi wanka, na shirya cikin atamfa mai kalar ruwan ƙasa a jiki da yawa, na ɗauko hijjabi shima, kalan ruwan ƙasa na saka, na ɗauki Takalmi da jaka baƙaƙe, da Takarduna...
Har zan fita na tuna da Mama, jikina a sanyaye na dawo baya na kirata a waya...
Da sallama ta ɗaga, bayan na amsa na gaisheta muryata tana rawa na ce;
"Na ce Mama zan tafi Makaranta"
Shiru ta ɗan yi, kafin ta fara magana cikin sanyi murya kamar zata yi kuka;
"Na yi miki addu'a Fatima, na yi miki addu'a da iya ƙarfin lafiyar da Ubangiji Ya ba ni, da ƙarfin mulkinSa za kiyi narasa, kuskurenki ba shi yake nufin kin faɗi ba, tunda Allah Ya nufeki kin yi nadama, ki tunkari karatunki da ƙwarin gwiwa, ki riƙe mutunci wata rana zaki yi dariya ko ba na raye"
Ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka, haɗe da katse wayar..
Wayar na kafe da ido hawaye na biyowa kuncina, ban motsa ba har sai da Baba ya Turo Driver Hajiya Babba kira na..
Kalaman Mama sune suka zama tsanin da nake ji na akai, ko da naje yiwa Hajiya Babba sallama, kalaman kushenta sam basu dame ni ba..
Aunty Amarya addu'a tayimin cikin sanyin halinta na halitta..
A gurguje na fito muka wuce Makaranta..
*********
Bayan mun isa Baba bai tafi ba, sai da muka kammala komai, ya bani kuɗin kashewa da na Mota, sannan ya yi min rakiya har inda ake ɗaukar darasi...
Muryasa a tausashe cikin tsananin soyayyar Uba da Ƴa, ya ce;
"Allah Ya baki sa'a Fatima, ki mayar da kai kin ji"
Kai kawai na iya ɗagamai na kasa magana, saboda kukan da ya tahomin..
Shima bai ƙara cewa komai ba ya juya....✍🏻