13
13
Da ƙarfin gwiwar da nake ji, na zura kyakkyawar ƙafata da baƙin Takalmi ya haska, ƙaton ɗakin ɗaukar darasi..
Ban damu da idon da kowa ya zubo min ba, na nemi waje na zauna..
Sosai nake fahimtar abinda ake koyamana.
Ƙarfe 9:30 muka fito, ba mu huta ba muka ƙara shiga wani.
Ko da muka fito, ban nemi yin Ƙawance da kowa ba, na nufi inda naga ake zuwa siyan abinci...
Ko da siyo kayana ban yiwa kowa Bismillah ba, kamar dai kurma, haka na zauna na take cikina..
Waje mai kyau na nema na zauna, ina kallon yadda ɗalibai suke zirga-zirga..
Idan na kalli namiji da mace a zaune suna hira, ya ziro kansa saitin Fuskarta ya na zuba mata surutu sai na ji tausayin macen ya kamani... Saboda gani nake yi kowa ma irin Sadiq.
A ranar sai yamma liƙis na iso gida, raina fari fes, ina jin kaina a matsayin mutum mai daraja kamar kowa...
Ban leƙa sashen Hajiya Babba ba sai bayan Magriba.
Ina ƙwanƙwasawa Farida ta ɓude, tana ganin nice ta fara ƙunshe dariya, ba ta yimin magana ba, nima ban yi mata ba, ta bani hanya na wuce..
Hajiya Babba; a hakimce na sameta tana kallo.. kamar kullum da na gaisheta ba yabo ba fallasa ta masa..
Cikin gatse ta ce;
"Ina dai kin ji faɗan da Alhaji ya yi miki? Hmm Fatima kenan aike kamata ya yi ma kawai ki cire rai da lamarin aure wallahi, don ko Namiji ya ganki yana so, yana jin abinda kika aikata zai gudu"
Sak nayi ina kallonta, ni a ganina menene ya kawo irin waɗannan maganganun? Ita kullum bata gajiya ne.
Cikin ƙosawa da lamarinta na ce;
"Hajiya ai nima ban ce ina son aure ba"
Zaro ido tayi kamar na yanki naman jikinta ta ce;
"Na shiga uku, iyye daga fara barinki zuwa makaranta shine har bakinki ya buɗe, ina magana kina magana, matso nan"
Ta ƙarasa faɗa tana yafito ni da hannu..
Ƙasa nayi da kaina ban ƙarasa kusa da ita ba, saboda nasan marina zata yi..
"Au bazaki matso ba?" Ta tambaya tana zaro manyan idanuwanta..
Shiru nayi ban motsa ba, amma jikina tuni ya fara rawa..
"Farida janyomin ita nan"
Da yake Farida tafi ni jiki sosai, tuni ta finciko ni, ta ɗurƙusar da ni a gaban Hajiya Babba..
"Ɗagomin Fuskarta" Hajiya Babba ta faɗa tana gyaran zamanta zuwa dai-dai saitin Fuskata..
Da iya ƙarfinta Farida tasa ta ɗago Fuskata ina fizgewa..
Mari ta so ma zubamin ta ko ina tana cewa;
"Don kinga Alhaji yayimin faɗa a kanki ranan nan, shine yanzu zakiyimin rashin kunya, ni sa'arki ce? Tambayarki nake yi ni sa'arki ce eh? Mara kunyar banza"
Tun ina kuka ƙasa-ƙasa har na fara ihu, hancina ya ɓalle da jini, duk da haka bata ƙyaleni ba...
Tana turani gefe da iya ƙarfinta aka fara dukan ƙofan kamar za'a ɓalla, don ba'a tsaya amfani da Door...
Kafin Hajiya Babba tayi magana, Farida a gigice ta nufi ƙofar ta buɗe..
Baba ne, da Aunty Amarya a bayansa..
Sak ya yi na wasu daƙiƙu shi da Aunty Amarya suna kallon fuskata da irin kukan da nake yi..
Sannan nan da salon danne ɓacin raisa ya ce;
"Saratu lafiya? yanzu masu aikinki suka kirani, wai suna jiyo ihu a sashenki, kuma na ganku ke da Farida lafiya ƙalau, wanene yake ihu?"
Ya yi tambayar kamar bai ganni ba, ya zuba mata ido yana jiran amsar ta..
A ɗan gigice ta kalleni ta ƙara kallonsa taga dai ita yake kallo, cikin kame kame ta ce;
"Fatima ce tayimin rashin kunya, shine na mareta"
"Saboda ke kika haifar min ita?"
Baba ya tambayeta da buɗaɗɗen muryar da amsa parlon..
Tunda Hajiya Babba ta ji ya faɗi haka tasan ta ƙure haƙurinsa..
Tana ƙoƙarin ƙara kare kanta ya ce;
"Tunda baki san lallashi da ƙimarki da nake gani ba, bari na tuna miki abinda kika manta, ban gida Iyalina akan tozarci da son zuciya ba, don haka babu wanda zai shigomin da shi cikin zuri'a, idan kika ƙara maimaitawa zan baki mamaki Saratu.
Hanifah ɗauketa ku tafi, kuma daga yau na haramtawa Fatima zuwa sashen kowa karɓar abinci zata girka nata da kanta a Sashenta"
Cikin borin kunya Hajiya Babba ta fara masifa;
"Ni zaka tozarta akan yarinyar da ta ɓatawa zuri'armu suna, har kake yimin faɗa a gaban yara da bare, koma dai mai zaka yi baka isa ka cireni daga rayuwarka ba Alhaji, domin abinda ya yi ka shi ya yi ni.
Kuma wallahi kar na ƙara ganinta a Sashena tunda bata da kunya, dama da haka uwarsu ta raine su..."
Babu wanda ya tanka mata, har Baba, muka bar Sashen..
Har Sashena Aunty Amarya da Baba suka yimin rakiya.
Aunty Amarya ta taimakamin na wanke fuskata, ta rakani har cikin ɗaki na kwanta.
Ba su wani jima ba, su ka yi min sallama, Aunty Amarya tace zata aiko mai aikinta da abinci.
Ba a ɗauki lokaci ba, mai aikin Aunty Amarya ta kawomin abinci mai kyan gani a ido, daga gani zai daɗi..
Mai aikin Aunty Amarya, bata bar Sashen ba, sai da ta tabbatar na ci, sannan ta kwashe kayan abincin tayi min sallama..
A daddafe nayi sallar Isha'i na kwanta, zuciyata cike fal da tsoron halin Hajiya Babba.
Na rasa me na tare mata...
Allah Ya azurtata da ƴaƴa kuma duk suna raye Ya ɗaukaka mata su, saɓanin Mama da ni kaɗai na rage mata, nima ɗin dana rage abinda na aikata yasa ta rasa aurenta, to me Hajiya Babba take yiwa kishi bayan duk wannan ni'imomin da Ubangiji Ya yi mata?
"Rashin godiyar Allah"
Zuciyata ta bani amsa..
Da wannan tunanin barci mai nauyi ya ɗaukeni✍🏻