KUNDINA

14

by @nafisatusasaal01

14

Tunda na kwanta, ban farka ba, sai da alarm ɗin sallar Asuba ya tasheni..

Ban yi mamakin irin barcin da nayi ba, saboda yinin da nayi jiya a makaranta ..

Alola na ɗoro na tayar da Sallah, ban koma barci ba, har gari ya yi haske..

Lecture ƙarfe 9 muke da shi,  don haka ban koma barci ba na shiga wanka..

Ban gama kimtsawa ba, sai wajen ƙarfe 8:05 ina yunƙurin saka hijjabi, naji ana ƙwaƙwasa ƙofa..

Mai aikin Aunty Amarya, da kayan karin kumallo a mazubi masu kyau..

Murmushi nayi na gaisheta, haɗe da karɓar kwandon hannunta na bata hanya.

Cikin girmamawa ta amsa, ta yimin yaya jiki?

Murmushi kawai nayi ban amsa mata ba..

Tana zaune na gama karyawa kamar jiya, sannan ta kwashe kayan abincin tayimin sallama..

A gurguje na fito na nufi sashen Baba..

Tare da Aunty Amarya na same shi, suna hira..

Cikin ladabi na gaishesu.

Su ka amsa suna yimin jajen abinda ya faru..
Ban ce komai ba sai murmushi da nayi ina sunkuyar da kaina..

Kuɗi Baba ya ɗauko ya bani, ya yi min bayanin anjima za'a kawo kayan abinci Sashena, na ajjiye mukullin a wajen Aunty Amarya.. 

Rai na fari fes, na ajjiye ɗan mukullin a gefenta nayi musu sallama..
***********

Ban sha wahalar samun abun hawa ba..

Kamar dai Jiya haka na gudanar da rayuwata a makaranta.

Tsakanina da ƴan ajinmu tambaya ce akan abinda ban sani ba, da zarar sun ba ni amsa zan ja bakina na tsuke...

Ƙarfe 2 da ƴan mintina na dawo gida.

Sashen Aunty Amarya naje ƙarbo mukulli, na samu bata nan, amma ta bawa masu aikinta su ajjiyemin..

Kamar yanda Baba ya faɗa, nauyin kayan abinci da na ciye-ciye  kala-kala na samu jibge a Parlo, ban san sanda na saki dariya ba..

Jakata na jefar gefe, na nufi ɗakin barcina da sauri, KUNDINA na ɗauko na rubuta abinda Hajiya Babba tayimin da kayan abinci da Baba ya siyomin..

Bayan na gama rubutawa, ajjiyar zuciya na sauke, sannan na tashi na mayar da littafin..


Daga wannan rana rayuwata ta sauya, na zama mai cikakkiyar ƴanci, babu ruwana da kowa, daga makaranta sai sashen Baba dana Aunty Amarya.

Mu na waya da Mama jefi-jefi, sashen Hajiya Babba ma, na kan shiga lokaci zuwa lokaci na gaisheta ta amsa a daƙile..

Sababbun ɗabi'una  basu sauya ba, ba na ƙawance da kowa, ko irin hiran nan na cikin makaranta ban yarda na yi da kowa ba..

A daidai wannan gaɓar Salim kyakkyawan Matashi ɗan kimanin shekaru Talatin da ɗoriya ma'aikaci a Makarantarmu ya soma bibiyata..

A ofishin lecturer mu muka haɗu da shi...

A ranar da ya ganni ya bawa wacce muka je tare saƙon ta gabatarshi ta faɗamin ya na so na, shiru na yi na tsahon lokaci, kafin nayi murmushi na ce mata ta gayamasa zanyi shawara...

Bayan kwana biyu ya ƙara turota, amsar farko na ƙara bata..

Bayan wasu kwanakin biyun ya ƙara turota.

Ban bata kalar amsar da na saba bata ba, nace ta gayamasa ya zo da kansa muyi magana...

Ko da na koma gida,  na jima ina tsara irin amsar da zan bashi idan mun haɗu..

★washe gari a gurguje na shirya, saboda lecture ƙarfe 8:30 mu ke da shi... 


 Cikin blue black ɗin Abayar da ya haskani sosai na shirya..

Sai da na je na gaishe da Baba, kamar kullum sannan na tafi.

Ina shiga aji na hango Salim a tsaye tare da lecturer mu..

Fuska nayi kamar bangane shi ba, na shige ciki na nemi waje na zauna, daga can baya.

Muna lecture ina ƙare masa kallo.

Kyakkyawane, kamar dai yadda na ganshi ofishin lecturer mu, mai siffar shiru-shiru.

Daga yanayin kamewarsa zaka  fahimci yasan kanshi..

A take  naji jikina ya yi sanyi, tsoron faɗa masa abinda na ya faru da ni ya ɗarsu a raina.. sai dai bana ganin ƙin faɗa masa a matsayin mafita, gara ya sani kawai ayita ta ƙare...

Bayan lecturer mu ya gama tare suka fita da Salim..

Ina fitowa na nufi wajen da na saba zama, ga mamakina Salim na hango a zaune yana danna waya..

Kamar ance ya ɗago muka haɗa ido. Kyakkyawan murmushi ya sakarmin, yana sosa ƙeyarsa.. ban san sanda nima na saki murmushi ba ina yin ƙasa da kaina..

Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, haka na ƙarasa na raɓa gefensa na zauna ina ƙara yin ƙasa da kaina..

Cikin taushin murya ya ce;

"Tunda kin nuna baki gane ni ba, kuma ba zaki gaishe ni ba, to bari ni na gaisheki, Ina kwana Aunty Fatima"

Ban san sanda na saki ƙaramin dariya ba ina ɓoye Fuskata a cikin tafukan hannayena..

"Ba zaki amsa ba" ya faɗa da dariya..

Cikin tsananin kunya na ce;

"Ka yi haƙuri Sir, Ina kwana, ya ya aiki"

"Alhamdulillah, ya ya karatu, ina fatan kina ganewa"

Ban yi magana ba, sai kai da na ɗaga mai..

"Masha Allah" ya ce yana mirza tafukan hannayensa..

Sai da ya bari na ɗan saki jiki, sannan cikin barkwanci ya ce;

"Gani, ance kin ce na zo da kaina, tunda kin hanani lambar wayarki, faɗamin abinda ki ke son gayamin" 

Kamar ya kwaramin ruwan sanyi haka naji jikina ya yi sanyi ƙalau, zuciyata ta cika da kokwanton na faɗa masa gaskiya tun yanzu, ko kuma na bari tukunna sai mun fahimci juna?....✍🏻