KUNDINA

15

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*
 
*NAFISATU ALIYU SASAAL*

15

"Kinyi shiru Fatima, ko kunyata ki ke ji?"

Salim ya katsemin tunani na..

Murmushin yaƙe nayi, na tattaro jarumtata na ce;

"Ina son mu tattauna muhimmiyar maganar da ta shafi rayuwata, kar sai tafiyarmu tayi nisa ka ji a wani waje, ka ce ban kyauta maka ba"

Fararen idanuwansa ya zaro, ya saki dariyar da yasa zuciyata ta ƙara kamuwa da son sa ya ce;

"Fatima maimaita abinda kikace a ƙarshe, idan na fahimta kin amince da ni kenan, tunda har kike hasashen zamu yi nisan tafiya a soyayyarmu, kai Alhamdulillah, na ji daɗi.. ba daɗin baki zanyi miki ba, amma ina tare dake Fatima, nasan ba zai wuce wani kuskure da kika aikata kike son sanar da ni ba, ni ma ai baki san nawa kuskuren ba.. mu karɓi juna a yanda muke Fatima, lokaci shi zai bayyana komai.  Saka min numberki, kuma ki rufe bakinki"

Ya ƙarasa faɗa yana dariya da kallon yanda na saki baki ina Kallonsa..

Da sauri na adana siraran leɓɓana, kunya ya kamani, nayi ƙasa da kaina ina murmushi..

Wayarsa ya miƙomin yana sakin dariyar nishaɗi..

Kasa karɓa nayi saboda rawar da hannuna yake yi, sai faɗa masa nayi ya saka da kanshi...

Da wani irin salon da ke nuna sanyinsa ya yi min sallama yana murmushi.

Ƙwalla ne ya cikamin ido, na bi bayansa da kallo..

Ban ga laifin zuciyata da tayi saurin aminta da Salim ba, domin cike take da kaɗaici, saboda babu kowa a kusa da ni...

Mama ba kullum muke waya ba, idan ma na kirata hirarmu bata wuce ta minti biyu zuwa uku, haka shima Baba tsakanin shi da ni, nasiha ce ta tambayata yaya karatu..

Ko a WhatsApp ba ni da abokanan hira, ga dai group ɗin dangi da na ƴan makarantar mu duk ina ciki amma ba na iya magana saboda kunyar abinda na aikata..

A yanzu da Salim ya ce yana sona, sai na ji kamar ana yiwa furannin cikin zuciya ban ruwa daga macewar da suka yi..

Alƙawarin da na yiwa kaina akan salim duk da yana da nauyi; shine sanyawa zuciyata wata rana zai bar ni, ban bari kokwanto ya shiga ciki alƙawarin da na yiwa kaina ba, balle na saka rai, zamu dawwama tare.

amma ko ba komai zan samu abokin hira na ɗan wani lokaci...

Ƙwallar da ya silalo ƙasan kuncina na share ina murmushi..

A yinin ranar zuciyata ta samu sarari, amma hakan bai sa na canza daga ɗabi'ata  ƙin kula kowa ba... Haka na wuni a makaranta, har na dawo gida..

MAMA;
Daga ranar da ta bar Fatima shekaru biyu zuwa uku da suka shuɗe, babu wanda ya goyi bayanta akaf danginta, kowa ita yake ɗora laifin..

Mahaifiyarta ce kawai ta sassauta mata ta hanyar yi mata nasihar;

"Yayin da aka saka ranar auren yarinya, muhimmin abinda ya kamata Iyaye su fi mayar da hankali akai shine motsinta, wayar da take yi da wanda zata aura, Chating ɗin da suke yi, idan da hali ma gaba ɗaya ta rage samun lokacinsa domin daga nan hira banza yake shiga tsakani.

Wasu mazan kuma dama irin wannan damar suke jira, su yi amfani da shi su cutar da yarinya. 

Don kuskure Fatima tayi kuskure, amma laifinki yafi yawa Maryam.."

Wannan nasihar shi ya sassauta zuciyar Mama, ta kuma amshi laifinta, amma ta ce ita da wani auren har abada...


HAJIYA BABBA;

Tun ranar da Alhaji ya ja mata kunne akan Fatima take gaba da shi, ƴaƴanta da dangi kuwa babu wanda bata kira ta gayawa Fatima tayi mata rashin kunya ba..

Ko gaishetan da Fatima take zuwa yi daƙyar take danne zuciyarta tana amsa mata amma ba don ranta ya so ba..

Ita kanta bata san me Fatima ta tare mata ba...

FATIMA;

Bayan nayi sallar Magrib na tabbatar Baba ya dawo ya huta, ya tafi sashen don sanar da shi maganar da muka yi da Salim.

Na yi sa'a shi kaɗai na samu..

Bayan na gaisheshi nayi masa bayanin abinda yake tafe da ni..

Shiru ya yi na ɗan lokaci sannan ya numfashi ya ce;

"Fatima idan da alkhairi Allah Ya tabbatar, amma inaso ki kwantar da hankalinki, wallahi na rantse miki Fatima idan Mijin da Ubangiji Ya ƙaddara rayuwarku tare ya bayyana zaki yi mamakin yadda komai zai gudana, domin babu wani suka da zai hana wannan auren kin ji, ki kwantar hankalinki, ki mayar da kai kiyi karatu, ki riƙe Allah wata rana zaki ce ashe Baba faɗamiki..

Idan kunyi waya da Salim ki ce masa ya turo a nema masa izinin zuwa wajenki".....✍🏻

Ku yi afuwa In sha Allah anjima ƙarfe 8 zamu yi page 16, Please kuyi like👍🏻 ko comment idan muna tare..