KUNDINA

16

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*
 *SASAAL*
***


    16

Cikin ladabi na amsa mishi da; "tohm"

Murmushi ya yi ya ce;
"Tashi ki je ki huta, Allah Ya yimiki albarka"

"Ameen Baba" na faɗa ina miƙewa..

Ina tafe ina murmushi zancen Baba, "wai sai ya ce, idan lokacin aure na ya yi Mijina har cikin gidanmu zai biyoni, ko ta yaya oho? ni da a dangi kowa  guduna yake yi, balle na ce wani a cikinsu zai ganni ya ce ya na so, to idan ba ɗan danginmu ba wanene zai shigo har cikin gidanmu yace ya na so na? hmm Baba kenan" 

Na faɗa a sarari ina murmushi.

Ina shiga Sashena ko zama ban yi ba, kiran baƙuwar lamba ya shigo wayata..

Ban amsa kiran ba, sai da na nemi waje na nutsu na zauna, saboda ba na raba ɗayan biyu Salim ne..

Da sallama na ɗaga muryata ƙasa-ƙasa..

A jiyar zuciya aka sauke, sannan akayi sallama..

"Ashe dagaske kai ne" baki na ya suɓuta..

Sansanyar dariya nishaɗi Salim ya saki ya ce;

"Allah Ya kamaki, gayamin awanninki nawa kina jiran kirana?"

Kunya ne ya kamani na kasa magana, a ɓangarensa dariya ya ƙara saki cikin zolaya ya ce;

"Anya Fatima ta iya gaisawa kuwa"

Da sauri nace; "Barka da dare Sir, ina wuni"

Dariyar da ban kawo ya iya ba ya saki...

Ya ɗauki sakonni ya na yi, sannan ya tsagaita muka gaisa.. daga nan ya fara jana da hira.

Hirar mu bata yi nisa ba, na sanar da shi saƙon Baba..

Sosai ya nuna jindaɗinsa cikin kamewar da babu rawar kai..

Kafin mu yi sallama ya ce zai yiwa magabantansa magana, idan suka tsayar da rana zai kirani ya faɗa min na gayawa Baba...

Cikin barkwancin da yasa zuciyata ta ƙara nutsuwa da shi mukayi sallama...

Zuciyata sakayau na gabatar da Sallah Isha'i, ban nemi abinci ba, saboda bana jin wunya na kwanta.. raina cike da fargabar abinda zai biyo bayan zuwan Iyayen Salim..

★washe gari ba ni da lecture a gida na wuni, Salim ya kirani wajen sau biyu yana tambayar lafiyata cikin kulawa...

Da dare ya yi ya ƙara kirana mukasha hira, ya ce na sanar da Baba iyayensa suna nan zuwa washe gari...

Ba muyi sallama ba, har sai da barci ya fara ɗaukata...



WAYE SALIM;

Salim Auwal Bammali shine cikakken sunansa,  ƴan asalin Bammali ne dake jihar Jigawa. Aiki ne ya  kawo Iyayen garin Kano, suna zaune a unguwar Hotoro, su uku iyayensu suka haifa daga shi sai ƙanwarsa Mace ɗaya da ɗan autansu Namiji...


Iyayensa masu kuɗi ne, ya yi karatu daga matakin Sakandare har zuwa Masters, inda yake aiki a matsayin HR a jami'ar Bayero, a gefe ɗaya kuma yana haɗawa da kasuwancin amfanin gona...

Menene ɓoyayyen sirrin Salim; 

Salim mutum ne mai sanyi hali, haƙuri da juriya, sai dai a ɓangaren halittarsa na buƙatuwar ɗa Namiji sam bashi da juriya.. gashi iyayensa sun ɗora burin sai yayi ilimi mai zurfi zai yi aure..

Yana cikin wannan tsananin ƴar ƙanwar Mahaifiyarsa Badawiyya ta zo gidansu hutu.. dama kuma an turota ne saboda su samu fahimtar juna a haɗasu aure...

Irin huɗubobin da akayiwa Badawiyya na kyautatawa Salim ne, ya kai shi ga yi mata fyaɗe, saboda yawan zaryarta a ɗakin barcinsa, duk da sunan kai masa abinci..

Ƙaddarar Salim bata tsaya a iya nan ba, sai da Badawiyya ta samu ciki, ruɗanin da Salim ya shiga  tun farkon faruwar lamarin yafi na iyayensa..

Don yana kuka ya ke cewa Iyayensa shi a ɗaura masa aure da ita kar a bari kowa ya sani kunya yake ji..

Cikin da ya bayyana a jikin Badawiyya ne ya tsayar da komai..

Salim shi ya tsayawa Badawiyya gaba ɗaya ta dawo gidansu da zama..

Yadda Salim ya firgice ya lalace ne, yasa kowa ya fahimci ƙaddararsa ce ta zo a haka, bai yi da niyya ba...


Bayan Bdawiyya ta haihu, Allah Ya amshi ranta da abinda ta haifa...

Salim ya yi kuka, har sai da kowa ya dawo koka mai....

Daga lokacin Salim bai ƙara yin budurwa ba, har Allah ya haɗashi da Fatima..

Labarin Salim kenan, sai dai ko Iyayensa zasu amince ya auri Fatima???✍🏻