KUNDINA

17

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*
 *SASAAL*

       17


*DAWOWAR LABARI*;

  FATIMA;
★washe gari, tunda nayi sallar Asuba na koma barci, ban tashi ba sai ƙarfe tara da ƴan mintuna..

A gurguje na haɗa sauƙaƙeƙƙen abin kari.. ban zauna na ci ba, sai da nayi wanka na shirya.

Da sauri na kullo sashen, saboda Lecture ƙarfe goma nake da shi.


Sashen Baba na biya don sanar da shi saƙon Salim.

A nutse nayi sallama na shiga.

Ya na zaune kamar kullum, sai da na gaisheshi na ƙara saita nutsuwata sannan na yi masa bayanin na gayawa Salim saƙonsa da abinda Salim ɗin ya ce..

Shiru Baba yayi na sakanni sannan ya ce;

"Ki ce musu su zo jibi ranar Asabar.  Ina kuma so ki kwantar da hankalinki akan duk abinda zai biyo baya, Allah Ya na tare da ke, kuma duk abinda ki ka ga bai zama naki ba, to dama can Allah bai ƙaddara rabonki ba ne.. tashi ki je Allah ya bada sa'a"

"Ameen Baba" na faɗa jikina a sanyaye ina miƙewa..

Har na isa Makaranta ban daina tunanin maganganun Baba....

Ina shiga aji nayi tozali da Salim a gefen Lecturer da muka haɗu da shi a Ofishinsa, ya yi kwalliyarsa cikin ƙananun kayan da suka fidda kyansa..

Murmushi na yi haɗe da yin ƙasa da kaina...

Kamar daga sama naji ya kira sunana. Idona na runtse, kowa na ajin ya zubomin ido..

Ba ni da zaɓi dole haka na ƙarasa kusa da shi..

"Ina kwana na faɗa cikin taushin murya"

Bai amsa ba, sai murmushin da yayi ya karkatar da kansa gefe ɗaya ya na kallona.

Hannayesa ya zuba a ciki aljihun wandonsa ya na cigaba da ƙaremin kallona...

Ya kai minti ɗaya a haka, sannan ya yi murmushin da ya bayyana haƙoransa ya ce;

"Ki kulamin da kanki. Anjima zan sa a kawo miki lunch, ki ci sosai kin ji?"

Kai na ɗaga mai, kunya ya lulluɓeni, kamar mara lafiya haka na juya idon kowa a kaina... 

Muna ɗaukar darasi lokaci zuwa lokaci idona ya haɗuwa dana Salim mu sakarwa juna murmushi...

Kafin mu gama, ya fita... 

Bayan mun gama inda na saba zama na fito na zauna, na cire wayata da silent na kira Mama..

Bugu ɗaya ta ɗaga bayan na gaisheta, cikin kunya nayi mata bayanin Salim da abinda Baba ya ce..

Itama nasiha tayi min da addu'a kamar yadda Baba ya yi min, sannan muka yi sallama...

Ina nan zaune aka kawomin saƙon Salim..

Kunya tasa na ƙasa buɗewa anan na tashi na tafi aji...

Ina shiga aji kafin na buɗe saƙon kiransa ya shigo...

Ina ɗagawa ya ƙyalƙyale da dariya, kunya kamar na nutse, saboda nasan ba zai wuce ya ga sanda na tashi ba..

Sai da ya tsagaita ya ce;

"Haba Mrs Salim daga kawo abinci sai ki tashi, don Allah ki dawo ki zauna, tunda bakya so na ganki zan tafi office na zauna"

Kasa magana nayi saboda kunyar da ta lulluɓe ni.. 

"Fatima are you there" ya tambaya muryarsa a nutse..

Jin nayi shiru ya ce;

"Okay tunda bazaki yi min magana ba, bari na biyoki har inda kike kici abincin akan idona"

Ban san sanda nace; "Innalillahi" ba

Dariya ya kwashe da shi ya na cemin "bye" haɗe da katse kiran..

Wayan na ajjiye a gefena ina murmushin salon barkwancinsa..

Daƙyar na buɗe abincin saboda gani nake yi kamar yana kallona..

Abinci ne mai rai da motsin da ya sani haɗiyar yawu..

Bismillah nayi na fara ci, ina koɗa daɗin abincin a cikin zuciyata...

Bayan na gama ban fita ba, sai da lokacin Sallah ya yi..

Har na dawo gida bamu ƙara haɗuwa da Salim ba...

Ban yi girki ba, sai tea na haɗa na sha bayan nayi sallar Isha..

Ina cikin saka kayan barci kiran Salim ya shigo wayata, ban ɗaga ba, sai da na kammala na kirashi..

Bai ɗaga ba ya katse ya kirani...

Da salon barkwancinsa muka gaisa..

Bai sakomin maganar abincin ɗazun ba, kamar yadda nayi tunani, wata hirar ya sakomin da ban...

Sai da zamuyi sallama na gaya masa abinda Baba ya ce...

Sosai ya nuna farin cikinsa, tare da addu'ar Allah Ya sa mu zamewa juna alkhairi..

Daga haka muka yi sallama, barci mai nauyi ya ɗauke ni.

BABA;
babu wanda ya sanarwa da batun zuwan magabatan Salim, sai amininsa guda ɗaya..

A tsakankanin dare biyun da suka biyo baya kafin zuwan Magabatan Salim, kullum sai Baba ya tashi ya roƙi Allah Ya zaɓawa ƴarsa abinda ya fi alkhairi..

MAMA;
Tun da Fatima ta kirata, akan maganar da Salim, ta gayawa Mahaifiyarta, da yayyenta su tayata da addu'a, idan Salim alkhairi ne, Allah Ya tabbatar Ya kawar da idon maƙiya akansu.. itama duk dare sai ta tashi ta gayawa Allah...

FATIMA;
ranar Juma'a har na je Makaranta na dawo ba mu haɗu da Salim ba, mun dai yi waya...

Haka da dare yayi ya kirani mun jima muna hira, ya gayamin ƙarfe 12 Magabatansa zasu zo, na gayawa Baba..

A daren bayan mun gama waya, na kira Baba na sanar da shi, ya ce babu matsala, Allah Ya kai mu..

A wannan dare ban runtsa ba, kwana nayi ina gayawa Allah idan Salim alkhairi ne, Allah Ya sauƙaƙamin Ya tabbatar da alkhairin dake tsakaninmu...

★washe gari ranar Asabar; da misalin ƙarfe goma abokin Baba, ya zo..

Baba da kanshi ya zo Sashena ya sani na shirya abinci, da abun jiƙa moƙoshi...

Da na gama da kaina na kai, kamar yadda ya buƙata ba tare da sanin kowa ba...

Ina fitowa daga Sashen Baba, mota da nake kyautata zaton na Magabatan Salim ne ya Kunno harabar gidanmu..

Da hanzari na nufi Sashena zuciya tana bugu da sauri- da sauri...

Ko da na shiga na kasa zaune na kasa tsaye, ban san sanda kuka ya tahomin ba, na durƙushe a ƙasa inayi a hankali, zuciyata na hasasomin shikenan na rasa Salim...✍🏻