18
*KUNDINA*
***
18
SASHEN BABA;
Tarba ta mutunci ƙannen mahaifin Salim su biyu, tare da abokin babansa guda ɗaya, suka samu a wajen Baba da abokinsa.
Bayan sun gama gaishe-gaishe, suka ɗan taɓa abincin da aka gabatar musu, sannan suka fara tattauna muhimmin batun da ya tarasu.
Cikin natsuwa da girmamawa, Baba ya nuna cikakkiyar amincewarsa da Salim.
Su ma ba su ɓoye farin cikinsu ba, domin sun nuna gamsuwa da gidan da Salim ya zo neman aure.
Har bakin mota Baba da abokinsa suka yi musu rakiya.
Har suka bar gidan, Baba yana tsaye yana kallonsu. A ransa ji yake yi kamar ba za su ƙara dawowa ba...
Abokinsa ne ya dafa shi, yana jinjina masa kai tare da dafa kafaɗarsa, alamar ƙarfafa gwiwa.
Baba ya lumshe idanuwansa, ƙwallar da ta taru a cikinsu ta sauko ƙasan gashin idonsa.
Cikin rauni ya ce:
"Ina jin tausayi, Fatima Alhaji Ahmed. Har na kan rasa ya ya zan yi da raina. Kawai daurewa nake yi, amma Allah Ya fi ni sonta. Allah Ya bata ikon cinye wannan jarabawar."
Gwauron numfashi Alhaji Ahmed ya sauke, shima jikinsa a sanyaye ya ce:
"Ameen, Ya Allah."
A nan suka yi sallama. Alhaji Ahmed bai koma ciki ba, saboda uzurin da zai gabatar.
Baba, jikinsa a sanyaye, ya wuce sashen Aunty Amarya.
A zaune ya sameta tana kallo.
Aunty Amarya gaba ɗaya hankalinta ta mayar kansa, cikin damuwa ta ce:
"Baba, yara lafiya?"
Kai Baba ya girgiza alamar a’a, sannan ya fara yi mata bayanin halin da yake ciki.
Cikin tausayawa ta ce:
"Kada ka bari Fatima ta ga karayarka a sarari. Ƙwarin gwiwarta zai gushe, ƙarshe ta samu wata matsala. Ni kaina tausayi take bani, amma mu barwa Allah komai."
Sosai Baba ya samu natsuwa, da furucin Aunty Amarya, har barci ya ɗaukeshi a parlonta.
Bai tashi ba, sai da Aunty Amarya ta tashe shi sallar azahar, ya yi alola ya nufi masallaci.
Daga masallaci sashensa ya wuce...
FATIMA;
Na jima a durƙushe ina kukan ƙaddarata. Sai dai tuna cewa kukana ba zai canza komai ba, ya sa na miƙe, na share hawayena ina roƙon Allah a sarari tare da miƙa masa dukkanin lamurana.
Haka na yini cikin zullumi. Baba bai kirani ba, shima Salim bai kira ni ba...
A daddafe na yi sallar Magriba, ko abinci kirki na kasa ci saboda fargaba.
Ina ƙoƙarin cire hijjabina, wayata ta fara ringing.
Tsabar fargabar da na saka wa raina, har tsorata na yi.
Sunan Salim ne ya bayyana a kan screen.
Sai da na daidaita nutsuwata sosai sannan na ɗaga.
Da wata irin taushin murya mai cike da barkwanci ya ce:
"Assalamu alaikum, rabin raina. Irin wannan shareni da kika yi yau haka, anya idan muka yi aure za ki kula da ni kuwa? Ace gaba ɗaya yau kin jini shiru, amma kika kasa kirana. Gaskiya ban ji daɗi ba."
Da rawar murya da ya kusan fallasa halin da nake ciki na ce:
"Ka yi haƙuri, Sir."
"Me na ji kin ce Sweetheart? ‘Sir’ fa na ji kin ce! Shikenan tawa ta ƙare!" ya faɗa yana dariya a ƙasa-ƙasa.
Ni ma murmushi na yi, ban ce komai ba, har sai da ya ƙara cewa:
"Gaskiya ni ba na son wani ‘Sir’ ki canza min suna.
Ki fito bakin gate, ina jiran ki, kar fa ki tsaya kwalliya ba!"
Ya ƙarasa yana dariya, haɗe da ya katse kiran.
Dariya ne ya kubce min ina kallon wayar.
A ɗan hanzarce na miƙe, kamar ba ni ba ce na yi laushi ɗazun ba.
Ban tsaya shafe-shafe ba. Na zura doguwar rigar atamfa, na yafa mayafi mai dai-dai da kalar kayan. Na zura takalmi, na ɗauki wayata sannan na fice.
Ina tafe ina saƙa-saƙen abin da Salim zai ce dangane da zuwan magabatansa.
Shashen Baba na fara biyawa, na yi kuwa sa'a yana tare da Aunty Amarya da alama ranar girkinta ne..
Cikin kame-kame kunyar da ya lulluɓeni na gaya musu Salim ya ce ya zo yana jirana a waje...
Murmushi dukkansu suka yi, sannan Baba ya ce naje na shigo da shi..
Kaina a ƙasa na fice zuciyata cike fal da saƙe-saƙe...
A cikin mota mai kyan da ban yi tsammani ba, na hango Salim a zaune.
Ya yi ƙasa da gilashin saitin inda yake zaune, idonsa ƙyam a kan ƙofar gidanmu.
Ya na hangoni, ya saki murmushi.
Bai jira na ƙaraso ba, ya buɗe motar ya sauko.
Ya na cewa;
"Oyoyo, wifey!" ya faɗa da ɗan ƙarfi da zan jiyo shi.
Baya na juya masa, na rufe fuskata da tafukan hannayena ina murmushi...
Daƙyar na juyo, na gaishe shi, yana dariya muka nufi motarsa, ya buɗemin wajen mai zaman banza na zauna...
Baba mai gadi bai nemi ba'asi ba, saboda gani na a cikin motar ya buɗewa Salim Gate..
Bayan ya daidaita parking hanani saukowa ya yi, sai da ya sauko da ya buɗe min. Cikin barkwancinsa ya ce:
"Bismillah ranki ya daɗe"
Kunyace ta ƙara lulluɓe, na kasa kallonsa duk da irin kyan da ya yi..
Kafin na ce komai ya ce na kai shi ya gaishe da su Baba..
Ina tafe yana bi na a baya..
A zaune muka samu Baba kamar yadda na baro su, sai dai shi kaɗai ne babu Aunty Amarya...
Da fara'a Baba ya tarbi Salim, bayan sun gaisa, ya yi masa nasiha mai kama da jirwaye cikin hikima, sannan ya ce na kai shi ya gaishe da su Hajiya Babba...
Saboda fargabar abinda zai biyo baya, sashen Aunty Amarya na fara kai shi..
Mun same ta tana yunƙurin kulle ƙofa da alama sashen Baba zata koma...
Fasawa tayi muka shiga suka gaisa, itama tayi masa nasiha.. sannan muka nufi sashen Hajiya Babba zuciyata na tsananta bugu...
Mun jima a tsaye bayan an tambayi waye, na amsa da ni ce, sannan Farida ta buɗe mana ƙofa tana ƙarewa Salim kallo fuskarta a haɗe..
Kallon Salim na yi, da mamaki ƙarara ke bayyana a saman fuskarsa na ce;
" ina zuwa bari na yi maka iso"
Kasa magana ya yi, sai kai da ya jinjinamin...
Hajiya Babba tana zaune, tana shan kayan marmari, bayan na gaisheta ko gefena bata kalla ba tace min;
"Lafiya?"
Muryata na rawa, cikin kame-kame na ce;
"Dama, dama wanda yake so na ne, Baba ya ce na kawoshi ya gaisheki"
Daina shan kayan marmarin tayi ta maido da hankalinta kaina.
Murya ƙasa-ƙasa ta ce;
"Yanzu da baƙo kike Fatima amma kika barshi a waje, maza kice masa ya shigo"
Ban yi tsammanin jin haka daga gare ta ba, don haka na miƙe a hanzarce na nafi ƙofa...✍🏻