KUNDINA

19

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*

19

A tsaye ƙyam na samu Salim, ya harɗe hannuwansa a ƙirji, fuskarsa a ɗaure, kamar ba waccen Salim ɗin da muka zo tare ba..

"Ta ce ka shigo" na faɗa a hankali don ɓoye tashin hankalin da nake ciki...

Bai ce min komai ba, ya bi bayana..

Mun samu Hajiya Babba ta yafa mayafin da daa ɗaurawa tayi, Farida tana zaune a gefenta.. Ganinsu da nutsuwarsu gaba ɗaya yana kan ƙofar shigowa..

Tare da Salim muka yi sallama, na raɓe daga can gefen  na zauna a ƙasa.

 Salim bai zauna a ƙasa ba, a kujerar da na raɓe  ya zauna..

Cikin ladabi ya gaishe da Hajiya Babba..

Da fara'a kamar ba ita ba ta amsa sannan ta ɗora da;

"Ohh ni kuwa kamar na sanka"

Wani irin murɗawa cikina ya yi, na ƙara yin ƙasa da kaina gumi na tsatsafomin ta ko ina..

Salim murmushi ya yi bai ce komai ba..

Da salon dakar ciki Hajiya Babba ta ƙara cewa;

"Kayi min kama da Ɗan gidan Hajiya Salamatu Turai Bamalli, tare mukayi sakandaren kwana da ita, Salim ko?"

Wani irin bugu zuciyata ta dinga yi akai-akai, kamar na miƙe na zura da gudu.

"shinkenan tawa ta ƙare" .

na faɗa a hankali hawaye na gangarowa kuncina...

Salim murmushi ya yi, ya ɗan saki jikinsa kaɗan ya ce;

"Eh ni ne"

Hajiya Babba murmushi tayi farin cikinta ya bayyana ƙaraƙara ta na cewa;

"Oh yaushe rabona da Turai Bamalli, tun kuna ƙanana, Masha Allah kun gado kyanta kam.

 Ban saka ran zamu ƙara haɗuwa da ita ba, sai gashi Allah Ya kawowa ɗiyata ɗanta har gida neman aure, gaskiya naji daɗin wannan lamari, Allah Ya tabbatar da alkhairi..

 Bari na baka wayata ka sakamin lambar wayarta"

Ta ƙarasa faɗa tana lalubo wayarta, ta miƙawa Salim..

Kamar na doke hannun Salim haka naji amma babu dama..

A gayance Salim ya amshi wayar, ciki ƙasa da minti ɗaya ya saka mata lambar ya miƙa mata...

Bai bari ta cigaba da labaranta ba ya miƙe, cikin ladabi ya ce;

"To Hajiya zan wuce Nagode ƙwarai Allah Ya saka da alkhairi"

Ido Hajiya Babba ta zaro ta ce;

"Salim tafiya tun yanzu, baka sha komai ba, don Allah ka tsaya a kawo maka abun jiƙa moƙoshi"

Salim ƙasa ya yi da kansa cikin ladabi ya ce;

"Ahh na gode Hajiya babu komai, In Sha Allah gaba idan nazo zan sha, Na gode Allah Ya ƙara girma"

"Amin Salim, ka gaida gida ka ji, naji daɗi ƙwarai"

Hajiya Babba ta faɗa tana washe baki..

Kuɗi Salim ya zaro masu yawa ya ajjiye a gefen Farida..

Hajiya Babba ta hau zuba godiyar da kana ji kana san bana kuɗin da ya ajjiye a gefen Farida ba ne, na jin daɗin samun lambar ƙawata da ta yi ne..

Kafin Salim ya nufi ƙofa tuni na rigashi..

Ina tafe yana bi na a baya..

Ganin mun nufi Harabar da aka jera kujeru domin hutuwa yasa ya magantu cikin Muryar da ban sanshi da shi ba ya ce;

"Meyasa ba zaki kaini wajen Mama ba, ina nufin mahaifiyar da ta haifeki mu gaisa, ko har yanzu baki yarda da ni a matsayin wanda zaki aura ba"

Ƙarfina ne naji ya ƙare, zuciyata ta karaya gaba ɗaya, bansan san da na durƙushe ƙasa na fashe da kuka ba..

Cikin kukan da yake fitowa tun daga ƙasar zuciyata na ce;

"Mamana ta tafi, ƙaddarar cikin Kundina da ka ƙi bani damar na sanar da kai, shiyasa Baba ya saketa, Yayyena sun mutu, ni kaɗai nake rayuwa a shashenmu, ko na kaika ka gaishe da Sashen?"

Na tambayeshi da wani irin marainiyar murya ina shesheƙa da ke nuna gazawata..

Ban san Salim kuka yake yi ba, sai da naji shirun ya yi yawa, na ɗago shima sai na ganshi a ɗurkushe yana kallona, fitilun da aka ƙawata wajen da su, sun haske kyakkyawar fuskarsa da hawaye ya ɓata...

Hannu ya kawo zai kamo nawa, komai ya tuna sai kuma ya fasa ya nuna min kujeru da ke jere, alamar mu ƙarasa mu zauna...

Jiki a mace dukkanmu muka ƙarasa muka zauna, Kujerun mu na fuskantar na juna..

Hasken wajen ya bamu damar ganin fuskokin juna da kyau..

Mun kai tsahon minti biyar a zaune, sai da nutsuwarmu ta fara dawowa jikinmu sannan Salim ya ce;

"Daga bugun ƙofar sashen da muka shiga na ƙarshe, da irin buɗewar da akayi mana, nasan kina cikin matsala Wifey.. zamanki a ƙasa maimakon kujerar da ƴar uwarki take zaune akai da yananin fara'arta Hajiya da maganganunta har da neman lambar wayar Mahaifiyata da tayi ya ƙarasa na ƙara gazgata ki na cikin matsala..

Yau na baki dama Fatima ki bani labarinki, sai dai inaso na fara baki nawa, domin hakan zai baki ƙwarin gwiwar gayamin gaskiyar da bakyaso na ji a wani waje"

Cikin taushi da tarin nadama, Salim ya bani labarin ƙaddarar da ta afka musu shi da Marigayiya Badawiyya..

Salim ya yi gaskiya domin labarinsa ya bani ƙwarin gwiwar ƙin ɓoye masa gaskiyar komai tun daga kan labarin su Marigayiya Aunty Su'ada, har zuwa kan Soyayyarmu da Sadik da abubuwan da suka faru bayan nan..

Hular da yayi ado dashi ya cire ya ajjiye akan gwiwarsa, ya ɗaga kansa yana kallon sama..

Cikin taushin muryar da banyi tsammani ba ya ce;

"Da sani da ban bata lambar Hajiyar mu ba, da na sani dana baki dama kin bani labarinki tun farko da hakan bata faru ba, Mahaifana suna da ƙarfi a kaina Fatima, rayuwar walwalata kaso 90 a cikin ɗari da dukiyarsu nake yi, bazasu shatamin layi na iya tsallakewa ba. Amma nasan Allah baya barci, ya san irin son da nake miki, ba zai bari mu wahala ba.

 Ina so kiji ƙwarin gwiwa Fatima kamar yadda nake ji, na roƙe ki"

Ya ƙarasa faɗa yana dawo da kansa saitin Fuskata da tayi jajir saboda tashin hankali...

Cikin dauriya na ce "In Sha Allah"

Miƙewa ya yi, nima na miƙe muka yi sallama, ya ƙara kwantar min da hankalin In Sha Allahu babu abinda zai faru, idan ya je gida, zai yiwa Iyayensa bayani da kanshi yadda zasu fahimta, kafin wani ya gaya musu...


Kawai da "to" na bi Salim amma matsawar Hajiya Babba zata shiga cikin wannan lamarin to kamar komai ya lalace ne....

Har bakin Mota na rakashi, motarsa tana barin gidanmu na durƙushe a ƙasa na fashe da kuka...

Muryar Baba na jiyo a bayana, cikin rauni ya ce; 

"Fatima, Fatima tashi, ki daina kuka, na kasa barci nace na leƙo ko kin shiga ciki"

Ban yi wata-wata na miƙe na rungumeshi da iya ƙarfina, cikin kukan da ya haɗe da rauni na ce;

"Ashe Baba Mahaifiyarsa ƙawar Hajiya Babba ce, kuma ta ƙarbi lambarta, sannan Salim ya shaidamin iyayensa suna da ƙarfi akansa da bazarsu yake taka rawa, ba zai iya tsallakewa layin da zasu shata mai ba"

Sautin murmushin Baba na ji, a hankali ya zaroni daga jikinsa yana kallona ya ce;

"Ni mahaifine a gareki Fatima, kuma na roƙa miki Allah Ya baki mijin da zai tsaya miki, da zuciyarsa, da ƙwanjinsa da dukiyarsa, nadamarki ya zama abin duba a gareshi ba kuskurenki ba, nasan Allah Ya na jina kuma Ya amsa,In Sha Allahu lokaci zai nuna komai, ki saka a ranki addu'a ta a gareki karɓaɓɓe ne, ki kwantar da hankalinki kinji"

Kai na ɗaga, ina jin ƙwarin gwiwa a duk sassan jikina, tare da tuna gatan da na ce na yiwa kaina, na wata rana Salim zai iya bari na..

Hannuna Baba ya riƙe muka je har Sashena, ba tare da ya ƙara cemin komai ba, har na buɗe na shiga...

Sai da yaga shigata na kulle ƙofa tukunna sannan ya juya...✍🏻