KUNDINA

20

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*

*NAFISA ALIYU SASAAL*
        ***

             

                20


BABA; 

bayan ya tabbatar Fatima ta kullo sashen, gefe ya matsa kaɗan, ya saki kuka mara sauti, Allah ne shaida duk cikin ƴaƴansa ya fi sonta da jin tausayinta, amma ya ya zai yi? Dole haka zai yi haƙuri har Allah Ya kawo musu ƙarshen wannan Jarabawar da ya afka musu dukka..

"Allah ka ba ni ikon cinye wannan jarabawar" 

Ya faɗa a hankali yana share hawayensa..

Jiki a mace ya nufi Sashensa..



HAJIYA BABBA;

Su Fatima su na fita ta kama haɓa tana kallon Farida ta ce;

"Lallai wannan sha-sha-sha mara tarbiyyar bata san ɗan gidan da take so ba, Turai Bamallin ce zata yarda ɗanta ya auri yariyar da ta gama zubar da mutuncinta a titi? Abun dariya ma wallahi...

Da alama Turai bata da labarin inda Ɗanta yake zuwa da sunan neman aure, dole na kirata gobe da safe tun da wuri tayiwa tufkar hanci.

Kin ga yaro ya zama ƙaton saurayi kyakkyawa da shi Masha Allah, ai dole na kirata, banda ma ban san inda suka koma yanzu ba, ai da sai dai kawai ta ganni"

Farida ba tace mata kanzil ba,  saboda hassada da kishin da ya turniƙeta, ace wai Fatima da ta aikata abun kunya taƙara samun Mijin aure amma ita ko ohoo, idan tace lamarin nan yayi mata daɗi tayi ƙarya...

Ai gara Hajiya Babba ta gayawa Iyayen Salim gaskiya, wataƙila ma su hana aure su ce ya aureta, amma bazata jure ace wai Fatima ta samu miji tayi aure ta barta ba...

Haka kowannen su ya nufi makwanci da saƙe-saƙe kala-kala a ransu...


FATIMA;

A bakin ƙofa na ɗurkushe, gumi irin raɗaɗin da nake a cikin zuciyata yana tsatsafomin ta ko ina. 

Wani kuka da ya sirka da murmushi ne ya ƙara ƙwacemin na fara magana kamar da mutane a kusa da ni.


"Ina mata ƴan uwana? ina zan ganku na baku labarina. 
Tabbas nasan wasu sun kuskuren da nayi kuma su auri wanda su ka aikata kuskuren tare da shi, to amma irina da suke faɗawa halin ƙaƙanikayi sun fi yawa.. ku daina tura tsaraicinku, karku wulaƙanta surarku mai daraja da ƙima don kawai Namiji ya tsaya ya aureku, wanda yake da niyyar rayuwa aure da ku tsakani da Allah zai tsaye ba tare da wannan ba. Yau ina Sadiq?  ya gudu ya barni ni da Iyayena cikin ƙuncin zuciya.. kuma labarina kuskuren da ya tunzirani na aikata ba zai goge ba, har ajalina"....

Na ƙasara faɗa ina fashewa da kuka jikina yana tsuma...

Da jan jiki na isa bakin kujera, na kwantar da kaina haɗe da rintse idona...

*INA SADIQ YA KE? MAIYASA YA YAUDARI FATIMA? SHIN YA SAMU KWANCIYAR HANKALI A AUREN DA YA YI?*

Tun daga ranar da ya samu Fatima ta fara nuna masa jikinta a video call, zalamammiyar zuciyarsa mara godiya Ubangiji yafara dasa masa zargi da kokwanto kala-kala...

Kenan Fatima zata iya yarda da wani namijin bayan shi? tunda gashi ya yi mata daɗin baki ta yarda shi..

Shi kaɗai wasu lokutan ya kan cewa kanshi;

"Gaskiya Fatima ba ta da aji sam, bata san kanta ba ko kaɗan, kenan Namijin da ya fini kyau, ya fini iya kalamai, ya fi ni kuɗi, nan da nan zai gama da zuciyarta, ƙarshe na aureta ta dawo tana cin amanata da wasu Mazan da zarar sun mata daɗin baki, tunda dole idan ta gama karatu zata yi aiki, ko batayi aiki ba, ban isa na hanata hawa social media, gaskiya ba zan iya aurenta ba, amma bari na cigaba da tambayarta ko wata rana zata shatamin layi.."

Babban kuskuren da Fatima tayi; shine ƙara biyewa Sadik da shi har cikin zuciyarsa tasa manufar da ban take..

A hankali rashin kame kanta daga gareshi, yasa ya ji tafara fice  mai daga rai gaba ɗaya, ba ya taɓa cewa eh akan abu mara kyau tace a'a..

Wasu lokutan yana sane yake kafewa akan abinda yasan bashi da kyau, maimakon Fatima ta matsa lamba ta nuna tasan darajarta ta ce bata amince ba, sai ta bishi a yanda yake so..

Sai ya zamana kullum Fatima tana available bata da wani aji balle daraja irinta ƴa mace, bata da lokacin kanta, har gadinsa take yi ya hau online saboda tana tsoron rasashi..

Sadiq bai ƙarajin Fatima ta sire mai ba, sai da ya haɗu da Rahila a Instagram...

Babu irin daɗin bakin da bai yiwa Rahila ba na ta tura masa hoton jikinta, tsahon watansa biyu yana magiya da kalamai masu daɗi iri-iri da tura mata kuɗi masu nauyi, amma Rahila tace sam bata san zancen ba..

A waya ya kira Mahaifiyarsa domin itace ta hannun damansa, kuma mai juya akalar gidansu..


Bai ɓoye mata komai ba, ya kuma shaidamata wallahi ko ya auri Fatima hankalinsa ba zai kwanta ba, yafi son Mace mai ajin da take  fahimtar banbancin yaudara da so..

Sosai Mommynsa tayi na'am da zancen sa, tace ya tambayar mata Rahila adireshin gidansu ..

Ciki da waje sai da Mommyn Sadiq tasa aka bincika mata wacece Rahila, kuma bata samu wani aibu nata ba. Don haka ta sanar da mahaifin Sadik a nemarwa Sadik izini, saboda a san da zamanshi...

Da farko mahaifinsa bai yarda ba, acewarsa Mahaifin Fatima Abokinsa ne, sai dai yanda ta buɗe wuta kamar yadda ta saba na bin Malamai a sirrince, yasa dole Mahaifin Sadiq ya shirya tawagarsa zuwa gidansu Rahila..

Lungu da saƙo a dangi kowa sai da ya ji labarin Sadiq fa ya sauya matar aure daga Fatima zuwa Rahila..

Nacin Fatima yasa Sadik ya yi blocking ɗinta, saboda gaba ɗaya baya jin yana da lokacinta a cikin lokacinsa ko na sakan ɗaya...

Bayan dawowarsa da faɗansa da Fatima, ya ce ya haƙura da kuɗin da ya kai Gidansu, amma Mahaifiyarsa ta nuna sam bata yarda ba, tunda Fatima bata da tarbiyya..

A kan wannan mahaifinsa kafewa ya yi akan ba zai iya zuwa ba, don haka ta nemo waɗanda aka kai kuɗin tare da su, su je su karɓo mata..

Sam ba taji daɗi labarin abinda Baban Fatima ya yi ba, har tayi kurarin banda tana gudun zubewar mutuncin Sadiq da wallahi sai tayi ƙararsu sun dawo da kuɗin..

Sadik bai bar videon Fatima a iya wayarsa ba, da Abokinsa ya yi masa faɗan bai kyautawa Fatima ba, sai ya tura masa Videon..

Dama kuma abokin yana bibiyar Farida taƙi bashi fuska, don haka shima ya tura mata don ya ja hankalinta..

Ita kuma Farida saboda baƙin kishi ta turawa ƙawarta, ƙawarta ta dinga nunawa mutane video a Makaranta, har zancen videon yaje kunnen hukumar makarantar, kuma ko da aka buƙaci ganin videon babu kunya babu tsoron Allah ƙawar Farida ta nuna musu, wai itama an tura mata ne, don tayi hankali da Fatima tunda suna gaisawa kar ta lalata mata tarbiyya..

A wannan gaɓar Fatima ta rasa karatunta..

Abunka da masu hannu da shuni da kuma sanin manya Sadik bai daɗe da dawowa daga bautar ƙasa ba, ya samu aiki mai tsoka a Abuja, kuma har lokacin bai daina gwada Rahila ba, amma ƙiri-ƙiri ta nuna bata san zancen ba...

Shin dagaske Rahila mutuniyar kirkice kokuwa Sadik take ɓoyewa ainihin wacece ita?

Rahila irin ƙaddarar Fatima ce ta taɓa faɗamata, wannan yasa ta ɗauki darasi mai girma domin ita ba iya video ba ne, har lalata Saurayinta Suraj ya yi da ita, abinda yasa nata bai yi tasiri ba, Iyayen Suraj ba su kai nata kuɗi ba, wannan dalilin yasa Mahaifanta ya kai shi ƙara police station, aka yi masa duka haɗe karɓe wayar gaba ɗaya akayi kwatsa kwatsa da ita, sannan aka yi masa tsakani da ita...


Watan Sadik uku da fara aiki akayi bikinsu shi da Rahila, na gani na faɗa...

Sadik da kanshi yasa aka turawa Fatima videon bikinsa, don ta cire rai da shi..


A daren da aka kai Rahila gidan Sadik na Kano kafin su wuce gidansa na Abuja..

Daga shi har ita basu runtsa ba, waccen videon da aka ƙwace wayar tsohon Saurayinta akai aka fasa, shi aka turowa Sadik ta WhatsApp da voice note ɗin da suka saurara tare, kowannesu na haɗa gumin tashin hankali;

"Ga sakamakon wulaƙanci da Iyayenki suka yi min nan, na turawa mijinki, ki ji irin ƙasƙancin da na ji, lokacin da suka wulaƙantani. Kina tunanin zan ajjiye videonki a iya wayata ne ni kaɗai, bayan kin yaudareni kin rabu da ni? Dama shima mijin da kika aura abinda ya yiwa wata kenan ya gudo wajenki, sai ku taru ku rufawa juna asiri, Mayaudirin Ango da Mayaudariya  Amarya.. Allah Ya ba ku zaman lafiya"

Sanyi jikin Sadik da na Rahila ya yi, kishi na nuƙurƙusar zuƙatan kowannesu...

Cikin fushi Sadiq ya fara sabbatun ta yaudareshi, itama cikin fushi ta fara masifar itama ai yaudararta ya yi..

Buɗar bakin Sadik sai cewa ya yi;

"Amma ai ni ban taɓa lalata ba"

Cikin zaƙalƙalewar da bai san Rahilan da shi ba ta ce;

"Wa ya san iyakacin ƴammatan da ka lalata? mayaudari mai yiwa ƴaƴan mutane wayo ka lalata tarbiyyarsu, wallahi da na san irin halin Suruj ne da kai da ban aureka ba, macuta azzalumai kawai, wato nima da na tura maka jikina haka zaka gudu ka barni ko? Mayaudari kawai"

Tsit Sadik ya yi yana kallonta zuciyar na tafarfarsa, shi babban baƙin cikinsa gujewa auren Fatima da yayi.

 To idan zai zargi Fatima da shi ya koya mata, ina kuma ga Rahila da har lalata ta taɓa yi... Bai san sanda ya fashe da kuka ba haɗe da barin ɗakin...

Muna tare🙌