21
*KUNDINA*
21
Ɗakin da yake jikin wanda ya baro Rahila a ciki ya shiga, hankalinsa a tashe a zaro wayarsa, bai tsaya shiga cikin contact ba, kawai lambobin Mommynsa da ya jima da haddacewa ya daddanna ya kira..
Bugu biyu ta ɗaga, muryarsa a disashe saboda gajiya, ta ce;
"Hello Babana, ka je gida lafiya?"
Kai Sadik ya girgiza kamar tana ganinsa ya ce;
"Mommy ba lafiya ba, yarinyan nan ta yaudare, ta cuce ni, sakinta zanyi ba zan iya zama da ita ba"
"Ka ce me Sadiq? Lafiyarka ƙalau kuwa? Ko kasha wani abun ne?"
"Mommy ban sha komai ba, Rahila ta yaudare ni, na cuci kaina da na rabu da Fatima na aureta, dan Allah kiyi wani abun"
"Menene wani abun da zanyi Sadiq? Da alama ka samu matsala a cikin kanka, ba ka yimin bayanin komai ba, sai sabbatun banza da na wofi kakemin a kunne, ka yi bayani menene ya haɗaka da Matarka"
Cikin nadama da kame-kame ya kwashe komai ya gayamata..
Ɗan jim tayi da alama jikinta ya yi sanyi, sai dai bakin alƙalami ya riga ya bushe.. don haka cikin sanyi murya ta ce;
"Babana haƙuri zakayi, ka ga itama ba haka taso ba, ƙaddara ta ce ta zo a haka, batun sakin a tsakanin ku kuma bai taso ba, mutuncinmu zai zube, maƙiya su yi mana dariya, kaje ku sasanta a tsakaninku kaji, Nima gobe zan shigo, nayi mata nasiha, Allah Ya baku zaman lafiya"
Bata jira cewarsa ba ta datse kiran..
Itama Rahila Sadiq ya na fita ta kira Mahaifiyarta tana kuka, tana bata labarin abinda Suraj ya turowa Sadiq..
Daƙyar Mahaifiyarta ta lallasheta akan zasu nemo Suraj a duk inda yake su ɗauki tsatsauran mataki akan sa.
A wannan darw Sadiq bai nemi Rahila ba, itama bata nemeshi ba, haka suka yi kwanan baƙin ciki.
★washe gari ma, babu wanda ya kula ɗan uwansa, har baƙi suka zazzazo suka tafi..
Sai dare Mommyn Sadiq ta zo gidan.
A Parlo ta haɗasu, cikin lallashi ta fara yiwa Rahila faɗan bata kyauta ba.
Buɗar bakin Rahila sai cewa tayi; ai ba ita kaɗai zata yiwa faɗa ba, har da Sadiq tunda shima yaudararta ya yi..
A zafafe Sadiq ya miƙe, cikin zafin rai ya fara yiwa Rahila faɗan tana yiwa Mahaifiyarsa rashin kunya.. Nan da nan rigima ta kacame a tsakaninsu, yana faɗa Rahila tana faɗa, duk yadda Mommynsa ta so dakatar da su hakan bai samu ba, har da Sadiq ya kai ga furta mata kalmar saki...
A nan Rahila da gigice itama Mommynsa ta gigice..
Bai ƙara ko minti biyar ba ya bar gidan..
Kai tsaye gidansu ya tafi ya ɗauki muhimman takardunsa da passport da ba'a riga a kai gidansa ba ya bar gidan...
Rahila tana kuka Mommyn Sadik tana kuka suka nufo gida tare, suna tambayar Sadik?
kowa ya ce bai ganshi ba.
Anan fa zance ya fara yawo ƙusƙus a tsakanin ƴan uwan da basu tafi ba, aka fara gulmar ga Amaryar nan ta dawo gidan surukai tana kuka, an nemi miji an rasa..
★washe gari dole Mommyn Sadik ta bawa ƴan uwanta labarin duk abinda ya faru, saboda har lokacin babu Sadik babu alamarsa ko sun kira wayarsa basa samu.
Da yawan ƴan uwan Sadik, sun mara masa baya, acewarsu Rahila bata kyauta ba, tunda har aka zo yi musu sasanci har gida, sai ta haƙura har komai ya dawo daidai..
Rahila kasa kiran gida tayi tun a ranar, washe gari kuwa dole dangin Sadik suka tusata a gaba har gida..
A gaban danginta da basu gama tafiya ba, dangin Sadik suka yiwa Iyayen Rahila bayanin abinda tayi da hukuncin da Sadik ya yanke...
Mahaifiyar Rahila bata ƙarasa jin bayanin dangin Sadik ba, ta tashi ta rufeta da duka ta ko ina...
Babu wanda ya bata haƙuri, sai da Rahila ta daku tukunna, sannan aka fara ƙoƙarin janyenta wasu suna ce wa;
"Ke ma ai ba a haka ake yi ba, Mahaifiyar mijinki ai mahaifiyarki ce"
Ita dai Rahila sakin da Sadik ya yi mata ya fi dukan da tasha a hannun mahaifiyarta ƙona mata rai...
Haƙuri dangin Sadik suka ƙara bawa Mahaifiyar Rahila da Danginta suka baro gidan..
A kwanakin da suka biyo baya, babu wanda bai yi nacin kiran layukan Sadik ba, amma ba'a samunshi.
Ƙarshe haka Rahila da Iyayenta suka haƙura aka kwaso kayan jeranta na gidan Sadik, bayan alwashi iri-iri da suka ɗauka akan Suraj da suka kasa samun inda yake..
Har tsahon watanni biyar babu wanda ya ƙara ganin Sadik, ya dai kira gida sau biyu, shima ma kuma babu kalan nacin da ba'ayi ba, ya faɗi ƙasar da yake ya ƙi...
DAWOWAR LABARI;
FATIMA; na jima a zaune jingine da kujera, kafin na miƙe jikina babu ƙarfi.
A daddafe nayi sallar Isha. Kamar na kira Mama, sai kuma na fasa kar na ɗaga mata hankali..
Wanka na shiga na ƙara yi, na saka kayan barci.
Zugum nayi a zaune, bayana jingine da gado, ina jiran kiran Salim..
Amma har na fara gyangyaɗi Salim bai kirani ba..
Tunawa nayi ai kamata ya yi na kirashi naji yaje gida lafiya..
Don haka na lalubo wayata..
Zuciyata tana bugawa na danna mai kira ina rintse idona saboda fargaba..
Bai ɗaga ba, ya katse, sai gashi ya kirani, muryasa a sanyaye fiye da yanda na sani ya ce;
"Wifey ba ki yi barci ba"
Kalmar ƙarshe na; "ba ki yi barci ba" ba ƙaramin sosamin rai ya yi ba kenan ba shi da niyyar kirana? Na tambayani kaina a cikin zuciyata..
A zahiri kuma murmushi na yi nace;
"Dama na kira ne naji ka je gida lafiya"
Murmushi ya yi mai sauti, muryarsa da wani irin sanyi fiye da na daa ya ce;
"Lafiya ƙalau na dawo, sai dai jikina ya mutu Fatima, ina so kiyimin alƙawari ɗaya kin ji"
Zuciyata kamar zata faso ƙirjina ta fito, na ce: "Tohm"
Sai da ya sauke numfashi sannan ƙasa-ƙasa ya ce;
"Kiyimin alƙawarin kome zai je ya dawo zaki jure, ki rayu da ni"
Duk da ban san me yake nufi da duk abinda zai je ya dawo ba, amma kalamansa sun yi min daɗi, kuma sun ƙaramin ƙarfi gwiwa, don haka na ce;
"In sha Allah"
"Yauwa Wifey, yanzu ki kwantar da hankalinki ki kwanta ki yi barci kinji, ki tasheni da Asuba"
"In Sha Allah" na ƙara cewa muka yi musayan kalaman soyayya sannan muka yi sallama...
Afuwa Mutane na😂🙌